Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   55 / 66

162K to 165K   out of 196.2K words

ne akayi ma,da na san da wannan maganar ai wallahi yau da saina maidawa Hjy Asama'u martani.. Har mu za ta kalla ta fad'ama wannan maganar? Uban meye bamu sani ba kan irin abun kunyar da k'anwarta da uwarta suka yi,a hakan kuma aka so lik'ama d'an uwana Allah ya tsaresa" Dadda dai zaro idanu tayi tana kallon Ameerah nan take ta kece da sabon kuka tace "amma dai wannan y'a kin cuce ni da baki sanar min ba tun farko,ai da ban b'ata hawayena ba a banza.. Amma ko yanzu lokaci bai k'ure ba,wallahi saina maidawa Asama'u martani.." Ta juya da sauri ta fita,kamar za ta fad'i ta nufi b'angaren su Aunty. Tana shiga ta fara kwaloma Mama kira, tun daga downstairsMama dai kuka kawai take ta saka Diyanah a gaba da jaririn,gaba d'aya ma ta kasa kallonta,Dadda ta b'anko k'ofar d'akin ta shiga,tana nuna Mama da hannu tace "amma ke dai wannan² mata sai Allah ya mana sakayya tsakanina dake" Aunty da ta biyo bayan Dadda ta fara ba ta hak'uri,Dadda tace "anya Fatima kin san irin sharrin da matar nan tayi min kuwa? Ashe k'aryar da ta zauna tana gindayawa da munafurci kenan a bayan idanuwana tana cewa na d'auki Manar na kaita karuwanci!" "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Was the first word da yazo bakin Aunty ta dunga kallon Dadda,trying hard not to believe,Aunty tace "a ina kika ji wannan maganar Hjy?" Dadda tace "wallahi³ kinji dai na maki rantsuwa ta fad'i maganar nan,idan k'arya nake mata kuma ga ta nan ki tambayeta" Aunty ta dunga girgiza kai tace "amma kuma Hjy sai yau maganar zai taso?" Dadda tana yiwa Aunty wani kallo ta hak'ik'ance tace "iiiihhh! Tou yauma d'in ba kamawa yayi ba aka tadosa dan mayar da martani" Aunty tayi shiru bata k'ara magana ba,Dadda ta juya ta fara mita,tace "alhamdulillahi! Ni dai na San kou yanzu na godema Allah da yasa Manar Bata d'auko min abun kunya ba har na aurar da ita" Mama ta sunkuyar da kai k'asa kunya kamar zaisa ta nutse a gurin,Dadda ta gama zazzaga fad'anta ta tafi. Sanda su Abba suka shigo gidan tare da Daddy da yamma suka zauna downstairs,Daddy yasa a kira masa Diyanah,ta fito sanye da babban hijab,idanuwanta sunyi ja tsabar kukan da tayi,ta zauna k'asa kanta a k'asa tana share hawaye,Daddy ya kalleta da kyau yace "Halima!" Jikinta har tsuma yake tsabar firgicin kiran da ya mata,here ta fashe da sabon kuka,Daddy yace "ba kuka na kiraki ki mana ba,kin gane kou?" Ta gyad'a kai,Daddy yace "waye ya maki ciki?" Ta dunga girgiza kai tana rufe bakinta,Abba dai baice komai ba kallonta kawai yake tsabar shork d'in da yake ciki,Daddy yace "baza ki fad'a ba?" Ta girgiza kai,yace "uhn! Kou kina so a barki haka har duniya ta san abunda ya faru da ke?" Nan ma ta girgiza kai,yace "uhn! Maza ki sanar min waye shi? Dan waye kuma?" Tana kuka tace "Uncle d'an gidan Alh Idris Baffanyo ne" Daddy yace "wane Baffanyon?" Tace "former minister of finance" Daddy ya dunga gyad'a kai yace "kin tabbatar maganar da kika fad'a haka yake?" Tace "ehh Uncle" yace "alright! Je ki kawo min Babyn" tace "tou" ta tashi jikinta a mugun sanyaye ta haura upstairs,sanda ta d'aukon Babyn dake bacci ta kawowa Daddy,ya karb'esa yace "Brother muje" a tsorace Diyanah ta dunga kallon Daddy hawaye suna saukowa fuskarta,sai dai ta kasa magana har suka fita daga gidan,a waje suna fita suka had'u da Waleed da tun bayan da ya san maganar,sanda ya tafi massalaci bai k'ara dawowa gidan ba sai lokacin,Daddy yace "son ka biyo mu za muje unguwa yanzun" ya amsa yana kallon jaririn dake hannun Daddy an nad'esa cikin towel na jarirai,suka shiga mota Waleed ke driven,Daddy yace "gidan Baffanyo za ka kaimu" yayi saurin kallon Daddy ta mirror yace "Uncle wane Baffanyon?" Daddy yace "wanda dai ka sani" Waleed dai sai mamaki yake a haka ya kaisu gidan dake cikin GRA,yayi parking bakin get,suka fito daga mota su uku,Daddy akan gaba sai Abba da gaba d'aya ya koma dumb,suka tsaya dai² get Daddy ya kalli mai gadin gidan dake zaune kan bench da radio d'insa yana saurare,suka masa sallama ya amsa,Daddy yace "gurin mai gidan muka zo.. Allah sa yana nan" get keeper da yaga ba k'ananun mutane bane yace "yana nan Alh,bari a muku sallama da shi" ya tashi da sauri ya shiga ciki,not too long ya fito yace "yace a shigar da ku ciki" Daddy yace "madalla" suka bisa a baya zuwa ciki,babban gida ne na gaske,fad'an tsaruwarsa da irin uban kud'in da aka narka wajen ginasa ma b'ata baki ne,suka wuce har parlon da aka musu iso suka zauna,mai gadi ya fita ya sanar da uban gidansa an shigo da su,Alh Baffanyo ya fito cikin shigar alfarma,sanda ya shiga parlon yana kallon su Daddy ya saki fuska yana fad'in "General of the army a gidana,ko dai mafarki nake?" Daddy dai bai nuna masa komai ba har suka gaisa,Alh Baffanyo sai kallon hannun Daddy yake yace "ina fatan dai lafiya?" Daddy yace "ita ta kawo mu gareka" Alh Baffanyo yace "uhn! Ina saurarenka" Daddy ya mik'a masa jariri without ya masa bayani,Alh Baffanyo yace "ban fahimceka ba Alh Muh'd,jaririn waye wannan?" Daddy yayi wani murmushi yace "idan ka karb'esa za ka gane ko d'an waye" Alh Baffanyo sai kallon Daddy yake sanda ya karb'i yaron a tsorace ya zuba masa ido yana kallonsa,jikinsa har wani b'ari yake yace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Daddy ya kalli Abba da Waleed yace "ku tashi muje,Alh Allah ya raya,mu za mu koma,dama abunda ya kawo mu kenan" da sauri Alh Baffanyo yace "dan Allah General ku tsaya mu sasanta kafin maganar ya zagaye gari a san halin da muke ciki.. Ina ga wannan ba abune da za mu tsaya jan zance akansa ba,kamata yayi ace mu rufawa juna asiri da yaranmu" wani girgiza kai Daddy yayi yace "wane irin sasanci kake buk'ata muyi?" Alh Baffanyo yace "dan Allah kuyi hak'uri na san abunda aka muku ba'a kyauta ba,amma dan girman Allah ku saurare ni kuji hukuncin da zan yanke" Komawa Daddy yayi ya zauna yana kallon Alh Baffanyo yace "me kake so ayi?" Alh Baffanyo yace "idan har za ku amince,me zai hana muyi gaggawar had'a iyayen yaran aure a b'oye,ka ga mun rufawa kanmu da yaranmu asiri ko ba haka ba?" Daddy ya gyad'a kai yace "yanzu kazo da magana,amma bari na fad'a maka ka ga yanzu about 6pm,nima zan zartar da nawa hukuncin,nan da maghreb nake lokacin auren kada ya wuce nan" Alh Baffanyo yace "in sha Allah yanda kace haka za ayi,nima ba na so ya wuce haka" Daddy ya gyad'a kai ya mik'e tsaye yace ma su Abba "brother mu tafi" suka tashi suka ma Alh Baffanyo sallama,sai godiya yake musu suka karb'i yaron suka tafi,har bakin get ya musu rakiya gurin mota sanda yaga tafiyarsu kafin ya koma ciki hankalinsa a tashe. Sanda su Daddy suka koma gida babu wanda suka ma bayani,har after maghreb,sai da suka tabbatar an d'aura auren kafin suka shigo gidan,kai tsaye suka wuce b'angaren Dadda..


#Dan Allah duk wanda ya karanta posting d'ina na yau ina rok'onsa yasa mahaifina cikin addu'arsa,yau yake cika shekaru 3,fatan Allah ya gafartama iyayenmu ya musu rahama,mu kuma idan tamu ta zo Allah sa mu cika da imani.. 👏🏻



#Asli Smasher.
53...





*WATTPAD:REAL-SMASHER.*


*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*


*_Allahumma ballighna ramadhana bil iimaan.._*🤲

_Thank u habibties for the prayers.. Shukhraan'kthiir ilaikum._



A nan suka samu Dadda,Mommella,Mother da Aunty suna maida zancen haihuwar,Mommella cikin jimami tace "ni dai na rasa gane yanda akayi wannan al'amarin ya faru,ace kaf gidan nan babu wanda yayi noticing faruwar haka sai yanzu?" Aunty ta had'iye wani yawu fuskarta cike da damuwa tace "ki bari sister,ni kaina al'amrin nan ya mugun d'aure min kai,amma wallahi ban san komai ba akai,tunda yarinyar nan idan nace miki na fi 4 month ban sa ta a idanuna ba kada ki musa,sam ta daina fitowa cikin mutane,ko abinci sai dai a ajiye mata bakin kofar d'akinta idan ta ji yunwa ta fito ta d'auka,jiya da dare kawai sai ciwo Deejah ta zo take sanar min,kafin kice me sai kukan yaro ni dai naji,tsabar mamaki har yanzun na kasa yarda da abunda ya faru.." Shigowar su Daddy dai² lokacin yasa su yin shiru suka amsa sallamar da suka yi,suka zauna bayan sun gaisa da Dadda da su Mommella,Daddy yasa Aunty ta je ta zo da Diyanah da sauran yaran,su Manar dama su suna cikin gidan,Dadda taje k'ofar bedroom d'insu na part d'inta tayi knocking tace "tou kuzo ko ubanku Muhammadu yana kiranku.. Ai tunda aka janyo mana bala'i kuma kun shiga cikin fad'ansa,duk da dai na san ku baza ku aikata haka ba" Manar ta kalli k'ofar daga cikin d'akin tace "ga mu nan fitowa" suka taso su uku ita da Ameerah da Rania suna sanye da manyan hijabs suka fito,a k'asa suka zauna suka gaida iyayen nasu maza,hankalin Manar kaf yana kan Waleed da ya lumshe idanuwa,Abba dai ya kasa magana gaba d'aya ya koma wani dumb,ko magana akayi sai dai ya biku da idanu,su Amaar ma suka shigo tare da Azaan,suka zauna kusa da Waleed da ya zama wani very quiet,sanda Aunty suka shigo tare da su Diyanah, Deejah ta samu guri kusa da su Manar ta zauna,Diyanah dai ta rakub'e gefe tana sharar kwalla,Daddy yayi gyaran murya yayi sallama,suka amsa masa,bayan nan yana kallon occupants d'in parlon yace "dalilin da yasa muka buk'aci ganinku,ba wani abu bane sai domin mu shaida muku,yanzun haka daga masjeed muke,an riga an d'aura auren Halima da yaron wajen Alh Idris Baffanyo,saboda rufuwar asirinmu duka,Alh Baffanyo ya buk'aci ayi d'aurin auren cikin sirri,tou kuma muma sai muka ga dacewar hakan tunda har ya zo da sulhu,ba sai mun tsaya ana jan maganar ba" here yayi musu bayanin duk yanda suka yi da Alh Baffanyo sanda suka je masa da maganar jaririn,Dadda su Mommella duka dai sai gyad'a kai suke cike da gamsuwa,sanda Daddy yayi shiru yace "Allah sa hakan shi ne mafi alkhairi garesu" duka occupants d'in parlon suka amsa da ameen,ya d'an gyara zama ya fito da sadakinta ya mik'awa Dadda yace "ga sadakinta nan da iyayen yaron suka bayar" ya ajiye bundle 5 na 1k a gabanta,bud'a ido Dadda tayi kamar wanda ke jin tsoro tana kallon kud'in tace "iiiihhh! Yo ni ka turo min kud'in kuma? Ba kune iyayenta ba? Fisabilillahi ni me zanyi da dukiyarta da ka bani? Da dai na takwarata ne sai in amshe in sai mata kadara,amma wannan bazan karb'a ba maza mik'a mata abunta Allah sanya albarka.. A toh! Maganar gaskiya fa kenan.." Gyad'a kai Daddy yayi ya mayar da kallonsa kan su Aunty a hankali yace "kafin suyi maganar lokacin d'aukan amarya,tunda ku ne iyayenta sai ku fara shirye²,duk abunda ake buk'ata kuma sai a sanar min" tun bai k'arasa ba Abba ya d'ago yana jifansa da wani kallo,kafin ya girgiza kansa ya kalli direction d'in da Diyanah take cikin kausasa murya yace "ka kirasu yanzu suzo su tafi da ita,babu amfanin da zamanta zai min a gida" Daddy zai yi magana Abba ya d'aga masa hannu cikin fad'an da basu tab'a gani ba yace "wallahil aziim baza ta k'ara min ko da cikakken awa guda a gina ba,idan kuma ka zab'i ta zauna ni zan bar gidan yanzu" baki sake Dadda take kallon Abba jin abunda yace,da sauri tace "iiiihhh! Me yayi zafi haka kuma Yaro? Ai ba sai ka rantse ba,ko ni nan ma ban yarda ta k'ara zama mana a gida ba,tunda an d'aura auren yazo su tafi haka,Allah ba mu alkhairi,mu kuma Allah saka mana da alkhairi" Daddy dai kallon Yayan nasa ya dunga yi ya kasa magana,ganin irin kallon da Daddy yake masa,nan take Abba ya fusata ya mik'e tsaye yace "Allah bamu alkhairi" da sauri Dadda ma ta mik'e tace "a'a Yaro ai ba na bari ka tafi kai kad'ai ba,yo na san inda za kaje idan ka tafi? Tsayani ka ji,duk inda za kaje mu tafi tare.. Yo zan barka ne haka kai kad'ai,wani abu ya sameka ina nan sake da baki in shiga uku" da sauri Aunty da mother suka bisu ganin har sun fita suna basu hak'uri,Dadda ta fashe da wani kuka mai cin rai tace "Allah ma ya sani kaf zuri'ata da ta ubansu babu wanda ya tab'a d'auko abun kunya sai yarinyar,saboda haka idan baza ta tafi ba mu sai mu bar maku gidan kawai" Mother ta sauke numfashi tace "kiyi hak'uri Hjy bari nayi magana da Daddy ya kira gidan mazan.. Ai duk ba'a kai nan ba" Dadda ta tsaya tana share kwalla bata dai ce komai ba,dai² nan Manar ta k'araso tana kallon Dadda tace "Hjy ba'a haka fa,kina ganin Abba zai ji dad'i ne da kika goyi bayan Diyanah ta bar gidan nan? Ko me ya faru ai itama jininki ce,hannunka ba ya rub'ewa ka yanke ka jefar" da sauri Dadda tace "ke y'ar nan wallahi sai dai in bai dameka da warin bala'i ba,amma tuni za ka gutsire d'an banza ka cillar" Manar ta dunga kallonta tace "tou ai shi kena.. Daddy yace na fad'a muku ya kira Alh Baffanyo suna hanyar zuwa yanzu" take Dadda ta washe baki tace "tou² yanzu aka yi magana mai ma'ana,Allah kawo su lafiya,bari naje na sanar ma Yaro ya kwantar da hankalinsa ba sai munje ko ina ba" Aunty dai da Mother kallon juna kawai suka yi,sanda Dadda ta nufi part d'in Abba,then suka koma part d'inta. Sanda su Alh Baffanyo suka k'araso da driver d'insa,har cikin gidan Daddy yasa aka shigo da su b'angaren Dadda saboda Alh Baffanyo ya sanar ma Daddy yana son zuwa ya bawa mutanen gidan hak'urin abunda yaronsa yayi,after an gaisa da shi ya nemi afuwa gurin Dadda da su Aunty kafin Daddy ya musu rakiya har bakin mota,Diyanah kam tare da Aunty suka wuce gurin Abba,tana kuka take neman afuwa,Abba dai ko kallon inda take baiba,Aunty ta zauna kusa da Abba,cikin tausasa murya tace "dan Allah Abbansu kayi hak'uri ka yafe mata,k'addara ne kuma babu yanda za'ayi,dole sai haka ya faru.." Da sauri Abba ya d'aga mata hannu,ya kalli Diyanah da rinannun idanuwansa yace "Allah tsare.." Daga haka bai k'ara cewa komai ba ya mik'e ya wuce sama,kuka sosai Diyanah ta fashe da shi tana durk'ushe gurin ta kasa tashi,sai da Aunty tazo ta kamota ta mik'ar da ita tsaye suka fito,suka k'arasa gurin mota ta shigar da ita back seat ta rufe mata k'ofar tana mata addu'ar Allah tsare tare da fad'a mata sai sun zo ganin gidan da take,ta gyad'a kai tana share hawaye,driver yaja suka bar gidan. A balcony lokacin da Waleed ya fito daga b'angaren Dadda suka had'u da Manar da ta fito b'angarensu,tun daga nesa take masa kallon tuhuma,sanda suka zo kusa da juna taga zai wuceta babu ko magana,da sauri ta kamo hannunsa ta rik'e,idanunta suna tara hawaye ta dunga kallonsa a sanyaye tace "Master! Lafiya kuwa?" 'Dan lumshe idanuwansa yayi yana sauke numfashi ya kasa mata magana,tayi saurin matsowa gabansa ta rungumesa sosai tana kallon fuskarsa da yayi pale kaman wanda ya shekara yana ciwo tana masa wani kallon k'urilla tace "mmm! Anya ma yau ka ci abinci kuwa?" Tayi maganar tana shafa cikinsa dake nan flat,sake lumshe idanuwansa yayi yana tunanin maganar da ta fad'a,da sauri ta kai hannunta fuskarsa ta d'anyi tapping cheeks d'insa tana kallonsa da idanunta da suke shirin fara zubar da kwalla tace "tell me please when last rabonka da abinci?" Girgiza mata kai kawai yayi ya fara k'ok'arin raba jikinsu,da sauri ta k'ara kwak'umesa tana goga jikinta a nasa,ta marairaice tace "ai to baka fad'a min ba kuma?" Kamar zai fashe mata da kuka,dan yau duka ba ya ma son ayi masa magana ya d'an langab'ar da kansa da wani sanyayyan voice yace "ban ci ba tun safe" zaro idanuwa tayi da d'an k'arfi tace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Hawaye suna sauka fuskarta take kallonsa tace "mesa za ka min haka Master? Ka zauna da yunwa idan ni nayi kuma kace za ka b'ata ranka?" Kulle idanuwansa yayi da k'arfi a hankali kamar ba ya son fad'a taji yace "na yi losing appetite,bazan iya ci ba,sam ma ba na jin sha'awar cin komai" cike da tausayinsa ta kai hannunta ta share fuskarta ta zuba masa idanuwanta tana kwantar da kanta saman k'irjinsa tace "idan na kawo maka za kaci ai ko?" Kai ya girgiza mata alamun a'a,ta narke fuskarta kamar za tayi kuka tace "za kaci mana,ai to da kaina ma zan baka" d'an zuba mata idanuwansa yayi da suke a birkice ba tare da ya ce komai ba,ta rik'esa da sauri tace "muje to yanzu sai na kawo maka ko?" Ba tare da ya ce mata komai ba ya fara binta ganin ta rik'e masa hannu alamun su tafin,sanda suka isa part d'insu ta tsayar da shi tace "ka jirani bari na fito" shi dai kamar rak'umi da akala haka ya tsaya a gurin har ta shiga b'angaren nasu,ta wuce kitchen ta had'o masa lafiyayyen sinasir da miyan egusi da yaji nama ta had'o masa da banana and coconut milkshake da yayi mugun sanyi cikin wani midi basket,tana fitowa ta gansa tsaye ya jingina da pillar a balcony d'in sun,ta k'arasa gurinsa da sauri ta rik'o hannunsa tace "let's go Master" binta yayi suka wuce part d'insu,basu tarar da kowa ba da suka shiga suka wuce sama,asalin bedroom d'insa suka shiga tare,Manar tayi sallama k'asa²,suka k'arasa ta fara sakinsa ta wuce ta ajiye basket d'in hannunta,da kallo ya bita sanda ta wuce ta barshi tsaye kafin ya sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya then ya wuce bathroom,k'aran rufe k'ofa yasa

55 / 66