in the paid group.*
Since that day da ta koma gidan kullum idan ya fita,ba ya iya wuni a office ba tare da ya dawo ba,and a rana idan zaiyi zuwa goma kafin ya koma sai ya san yanda ya ribaceta,within short period of time da dawowarta sun manta da kowa da komai,gida ma rabonta da zuwa tun da suka dawo ga shi ana maganar 3 month,idan kaga Manar a lokacin zato za kayi ba ita bace,saboda yanda ta k'ara kyau skin d'inta ya yi wani mugun fresh,ass d'inta kuwa yanda suka k'ara zama wide za ka rantse ta yi haihuwa uku ko sama da haka,kullum tana gida tare da shi,idan ba ya nan ma suna mak'ale a waya,family house kuwa ko sau d'aya bata tab'a masa zancen suje ba ganin yanda ta dad'e a can kafin su dawo,ranan wani Friday da yamma guraren 6pm ya dawo daga aiki ya sameta a parlor a kwance sai juye² take a kan rug,ya k'arasa yana kallonta murmushi kwance a fuskarsa,he just thought ko wasa take masa da farkon,ya kalleta ko bra babu a jikinta yayi d'an murmushin jin dad'i yayi sallama,da kyar ta iya amsawa bata d'ago ba har sannan tace "sannu da zuwa" still yayi yana kallonta,because ya saba yana shigowa zaiji ta d'ane jikinsa tana dariya,idan ta fara kissing d'insa kuwa idan ba shi ya tsayar da itaba sai ya kaisu ga bawa gado hakkinsa,ya kalleta da kyau yana tsugunawa kusa da ita in a way style yace "heyy! Lilac" tace "Mmm" yace "are u okay?" Girgiza masa kai tayi,ya tallafo kanta yana kallonta yace "what wrong? Mmmm?" Tana yatsina fuska tace "i don't know what to say.. Kawai ba na jin dad'i,ina jin kamar ba ni da lafiya,or rashin lafiya na son kamani" yace "since when?" Tace "bayan tafiyarka" d'an jimm yayi yana k'ara tsaneta da idanunsa yace "will u help and explain ina kike jin ciwo?" Da kyar ta bud'a idanunta tana kallonsa sai kuma tayi saurin kullewa tana girgiza masa kai tace "i'm feeling dizzy,a haka ma jiri nake gani,komai juyawa yake yi" ya d'an bud'a idanu yana kallonta yace "sorry!" Zaki iya tashi ko na d'aukeki?" A hankali tace "bazan iya ba fa" yace "okay! Sannu" yayi maganar yana shafa kanta,can yayi d'an murmushi yace "bari na kaiki bedroom,maybe idan kin huta zuwa anjima ki dawo normal" tace "Allah yasa" yace "ameen" ya d'auketa ya nufi sama da ita yana mata sannu,sanda ya kwantar da ita saman bed,ya zauna gefenta yana shafa kanta,a haka wani irin wahalallen bacci ya d'auketa,can guraren maghreb a time d'in ana kiran sallah ya zo da niyyar tashinta yaji jikinta da zafi sosai,hankalinsa a d'an tashe ya kirata,a hankali ta d'an bud'a idanuwanta lokacin sunyi wani iri alamun da gaske rashin lafiya ke damunta,yace "sannu!" D'an lumshe masa idanuwa tayi,yace "tashi muje nasa miki ruwa a jikinki ur temperature is getting high.." Girgiza masa kai tayi,yace "what?" Yana kallonta sosai,ta bud'e baki za ta masa magana taji bakinta ya cika da yawu,da sauri ta fara k'ok'arin sauka,yace "ina za kije?" Bathroom ta nuna masa da sauri ta shige sanda ta zubar ta wanke bakinta then ta d'aura alwala ta juyo za ta fito ta gansa tsaye a door way yana kallonta,ta taho a hankali idanuwanta har lumshewa suke yi,sanda tazo wucesa jiri ya fara k'ok'arin kayar da ita,da sauri ya rik'ota ta fad'a jikinsa,yana kallonta da kyau yace "har yanzu jirin kike gani?" Kasa amsa masa tayi kawai ta fashe da kuka,ya d'aukota ya dawo da ita kan gado ya ajiyeta ya matsa gaban press ya d'auko mata hijab ya shimfid'a mata pray mat then ya d'auketa ya ajiyeta kai yace "yi sallah bari nayi wanka nazo muje hospital" da kai ta amsa masa,ya goge mata hawaye yace "stop shading those tears,u will be fine okay?" Then ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka a gaggauce ya fito ya tarar da ita tana sallah a zaune,wani tausayinta ya dunga ji,ya wuce ya d'auko jallabiyya milk color da skinny jeans sai sleeveless ya shirya ya feshe jikinsa da turarukansa masu dad'i,ya shimfid'a wani pray mat d'in ya kabbarta sallah,sanda ya idar ya juya ya ganta a kwance idanuwanta a lumshe,ya matsa kusa da ita ya kai hannunsa goshinta ya tab'a,a hankali ta bud'a idanuwanta ya dunga kallonta da kyau,can yace "open ur mouth please ki fito min da harshenki" kallonsa ta tsaya yi sai da ya sake maimaita mata then tayi abunda yace ya kai hannunsa ya d'an bud'a idanuwanta,then ya d'agota da kyau ya rik'o hannunta yana duba nails d'inta,d'an gyad'a kai yayi yana sakin murmushi yace "za ki iya daurewa muje hospital?" A hankali ta gyad'a masa kai hawaye cike a idonta,yace "sannu!" Ta sake gyad'a masa kai,ya mik'e ya d'auki car key d'insa then ya dawo ya dauketa ya fita,sanda suka fito daga gidan get keeper yana musu addu'ar Allah ya tsare,Waleed ya amsa ya d'auki hanyar hospital d'insu,tun suna hanya ya yiwa Dr Mahfouz waya,sanda ya d'auka yace "Dr ba dai har ka fita ba?" Waleed yace "yeah! Na je gida na tarar madam babu lafiya,so kana hospital ne na kawota ka k'ara dubata,i'm suspecting something,but ina son kamin confirming ne" Dr Mahfouz yayi murmushi yace "okay! No problem ina office sai kun shigo" suka ajiye wayar ya juya yana kallon Manar da lokaci d'aya ta zama wata quite ya mata sannu,ita dai sai kallon hanya take tana jin zuciyarta tana tashi,har dai suka shiga hospital ya fito ya sake d'aukarta suka k'arasa office d'in Dr Mahfouz,yayi knocking door d'in,daga ciki Dr Mahfouz yace "yes come in" Waleed ya tura k'ofar yayi sallama,Dr Mahfouz yace "ohh! Thought wani ne ba kaiba,kai da za ka shigo ka tsaya knocked?" Waleed yayi d'an murmushi yace "noo! Thought kana wani aikin shisa bamu fara shigowa ba" Dr Mahfouz yace "bismillah!" Ya nuna musu gurin zama,yana kallon Manar yace "Madam barka dai ya gida?" Da kyar ta iya amsawa,then suka gaisa da shi,yace "meke faruwa ne Dr?" Waleed yace "so kake na k'ara maimaitawa kenan bayan na fad'a maka kafin muzo?" Dr Mahfouz yayi murmushi yace "yeah! Ina so ka maimaita min naji,so sai musan me ya kamata muyu" Waleed yayi murmushi yace "i just suspect ta samu shigar ciki ne,so ina son kamin confirming if it's true" Dr Mahfouz yayi dariya yace "tsakani da Allah kai yanzu d'an wannan aikin shi ne ya kawoku?" Waleed yace "yeah! Idan ni nayi ba lallai na gamsu lokaci d'aya ba" Dr Mahfouz yayi dariya yace "alright! bari na kira sister Amina ta d'auki jininta" Waleed yace "alright!" Dr Mahfouz ya mata sannu ya fita,not too long suka shigo da wata nurse kyakykyawa,tana ganin Waleed tayi d'an murmushi tace "Dr ina wuni?" Ya amsa idanunsa akan Manar,Dr Mahfouz yace "ki d'auki jininta da sauri ki kai lab,ina son result d'in yanzu" ta amsa tana kallon Manar tace "sannu Madam" Manar dai babu baki,sanda ya rik'eta kafin ta bari aka ja jininta,duk ta k'ank'amesa ta cusa fuskarta a jikinsa wai ba ta son ganin jininta da aka d'iba,Dr Mahfouz dai sai dariya yake musu ganin dramansu,Nurse d'in da ta d'auki jinin sai dariya take yi itama tace "haba sister kada ki bada mu a gabansu,kina gani har sun fara mana dariya" Manar ta d'ago kanta fuskarta duk gumi kamar wanda aka sha kokawa da ita tace "idan na bada ku wata rana zan karb'o ku" Waleed ya dunga kallonta jin bakinta cakwai har ta iya bada amsa,yace "oooohhh! Ashe dai bakinki bai mutu ba har yanzu" wani kallo tayi masa tace "tou kai ya ka gani da?" Ya gyad'a kai yace "yanzu fa sai da na d'aukeki tafiya kasa yi kike" tace "tou ai dai ba da baki ake tafiya ba,kafafuna sunyi min nauyi ne da kaina" ya gyad'a kai yace "okay! Idan za mu tafi ai kya tafi da kanki kuma" wani marairaice fuska tayi tace "kai Yaya yanzu sai ka barni na tafi da kaina? Idan na fad'i kuma fa?" Yace "ke kika sani kuma" basu wani jima sosai suna jira ba Nurse d'in ta kawowa Dr Mahfouz result,Dr Mahfouz ya karb'a yayi mata godiya,ta fita tana yiwa su Manar sallama suka amsa,tana fita Dr Mahfouz ya warware takardan yana duba content dake zane,wani murmushi yayi ya mik'awa Waleed paper yace "congratulations Dr" Waleed yayi wani kyakykyawan murmushi yace "thanks friend" ya karb'i result d'in yana dubawa,tun bai gama karantawa ba ya gano tana d'auke da ciki na 8 weeks,yayi wani k'ayataccen murmushi yana kallonta da wani yanayin farin ciki mara misali yace "alhamdulillahillaziiy bii ni'imatihi tatimmussalihaat" ya rik'o hannunta da kyau yace "u are once again pregnant.." Bud'a idanuwanta tayi tana kallonsa sai kuma murmushi ya sub'uce mata mai tafe da hawaye,za ta fara masa kuka ya d'agota yace "this is not the time for cry.. Godiya za muyiwa Allah ya mayar mana abunda muka rasa a baya" ta dunga gyad'a masa kai hawaye suna sauka cheeks d'inta,Dr Mahfouz dai sai kallonsu yake ba k'aramin burgesa suke ba,suka tashi tafiya Waleed sai godiya yake masa ya rakosu har bakin mota yana tsokanarsu kafin suka masa sallama suka wuce,a hanya suna tafiya yana kallonta cike da so da nuna kulawa yace "what do u want to eat? Ko ba kya jin sha'awar komai?" Tayi shiru kamar tana tunani,can ta hango apples a jere gurin masu siyarwa anyi packaging d'insu a wani kamar kwando k'arami,ta dunga kallon apples d'in,yanda taji ranta ya biya har ji take idan bata ci ba za'a iya samun matsala da sauri tace "zanci apples" ya kalleta yana sakin murmushi yace "apples ma ba apple ba?" Ta gyad'a masa kai tace "please ka karb'o min ni dai" yace "an gama madam" yayi parking gefen hanya ya fita yaje gurin masu siyarwan ya siya mata kusan package 3 suka saka masa a leda,ya karb'a bayan ya biya kud'in ya k'arasa mota ya bud'e yana kallonta ya mik'a mata ledar itama har saurin kawo hannu take ta karb'a,ta bud'e ta d'auko biyu ta d'auki bottle water dake kusa da ita ta sauke glass ta wanke,yana kallonta ta fara ci ko kallonsa bata kuma yi ba sai da ta kusa cinye d'aya ta juya ta kallesa taga ita yake kallo,tayi masa murmushi tace "na san maka ne za ka ci?" D'an murmushi yayi yace "idan kin bani ba" da sauri ta d'auki d'ayan ta mik'a masa tace "ungo kaci tou" girgiza mata kai yayi yana kallon na hannunta yace "na hannunki nake so" ta kallesa ta kalli gutsiren apple d'in hannunta tace "tou ai na cinye wannan" yace "a haka nace sonsa idan baza a bani ba kuma shi kenan na hak'ura" tayi murmushi tace "zan ba ka ai" yace "ba ni tou" mik'a masa sauran tayi tana kallonsa yasa bakinsa ya gutsira dai² inda tasa bakinta then ya mayar mata abunta yace "na gode" tayi dariya tace "tou ka cinya mana ai na bar maka" yace "noo! Karb'i abunki na gode" ta amsa ta ci gaba da cin abunta,shi kuma ya tada mota suka ci gaba da tafiya,a hanya ya kalleta yace "it's better muje gida mu gaida su,kusan 3 month bamu lek'a ba" tace "ai kaine baka ce muje ba,kuma da ba haka kake yi ba" yayi murmushi yace "ya ya nake yi da?" Tace "kullum fa sai ka je,yanzu kuwa ko maganar ma ni bana jin kana yi" yace "da d'inma akwai abunda yake kaini,yanzu kuma abun yana tare da ni shisa ba na zuwa" ta kalleshi tace "mene ne abun?" Yace "baki sani ba?" Tace "ehh!" Ya gyad'a mata kai yace "lallai! Sai dai ki biyani idan kina son ji" tace "tou ni me zan ba ka?" Yace "ke kike da abun bayarwa kuwa" ta dunda kallonsa sai kuma tayi dariya tace "ni dai ka fad'a min tou" yace "da saboda ke nake zuwa yanzu kuma tunda ina tare da ke shisa ba na jin son zuwa" wani k'ayataccen murmushi tayi tace "Mmm! Dama ba gurin Hjy Siyama kake zuwa ba?" Ya girgiza mata kai yace "kawai dai ina shiga mu gaisa amma ni ba gurinta nake zuwa ba" suna hiran ya tsaya wani eatry yace "ina zuwa Madam" tace "uhn!" Ya bud'e motar ya fita,ya d'an jima kafin ya dawo da leda a hannunsa ta kalleshi tace "me ka siyo?" Yace "ba naki bane Hjy" tana jin ya ce haka ta b'ata rai tace "tou nima ai bance nawa bane" ta murgud'a masa baki,d'an murmushi yayi ya tada motar suka bar gurin,har suka k'arasa gidan ko ya yi mata magana ba ta kulasa,yayi murmushi yace "za kiyi bayani idan na kamaki" ta d'auke kai,yana yin parking ta bud'e motar ta fita,bata tsayasa ba ta wuce b'angaren Dadda,a baya ya biyota da ledan a hannunsa,tana jin footsteps d'insa tak'i tsayawa,ta bud'e k'ofar apartment d'in tayi sallama,Dadda na zaune kan dadduma tana lazimi ta juya tace "eheemm!" Manar ta shiga ta zauna kan kujera ta cire hijab d'in jikinta,Waleed ya shigo yana kallon Manar da tayi kicin² ya zauna kusa da ita yace "wai fad'a muka yi kike fushi?" Tace "ohhoo! Nima ban sani ba" yace "tou kiyi hak'uri kina son gani na nuna miki?" Tace "ba na so" fuskarta a d'aure,yayi k'asa da muryarsa yace "please mana" k'in kulasa tayi ya juya ya kalli Dadda,ita kam lazuminta take bata kullesu ba,a hankali yace "i wish we were at home,so i could do some terrible things to u" kallonsa ta dunga yi ta kasa d'auke idanuwanta akansa,ya k'ara k'asa da kansa yana shinshinota yace "if u don’t stop looking at me like that,we’re going to to have to go somewhere private" saurin d'auke kai tayi tana kallon Dadda ta zumb'uro baki tace "tou wai baza ki gama lazumin ba sai mun tafi?" Dadda ta sake cewa "eheemm!" Manar ta kalleta kawai ta mik'e ta d'auki hijab d'inta tace "sai an jima" tayi hanyar fita,Dadda na mata alamar ta tsaya tak'i tayi ficewarta,Waleed yayi murmushi yace "bari muje za mu dawo" ta gyad'a masa kai,yabi Manar da sauri yana fita ya ganta har taje balcony d'insu ya biyota,da sallama ta shiga parlon mother na zaune tana waya da Daddy ta amsa musu,suka k'arasa parlon Manar ta matsa jikinta ta zauna tana murmushi,Waleed ya zauna wani kujeran daban,har mother ta gama waya da fara'arta tace "kune da wannan lokacin?" Waleed yace "ehh! Mother,ina wuni?" Ta amsa sai kallonsu take yanda suka kara k'iba gwanin sha'awa,hakan ya tabbatar mata hankalinsu a kwance yake,Manar ta gaisheta ta amsa tana kallon yanda ta zama kamar wanda aka hurawa iska,sun d'an jima a part d'in suna hira a nan suka yi sallar ishaa sukayi dinner kafin suka mata sallama suka fita,suka shiga gidansu after sun gaisa da Aunty da Abba,Deejah ta sauko har k'asan suka gaisa ya tambayeta Diyanah tace tana bacci,yace tun yanzu? Tayi murmushi bata ce komai ba,suka fita suka je b'angaren Dadda,sun jima sosai suna hira a can,tace da tuni gobe za tazo gidan nasu tana ta cewa za a kaita ma ta dubasu Abba ya hanata yace yaushe ma duka suka bar gidan,sai kuma ga su ma sun zo,Waleed yayi murmushi tabbas badan Abba da ya hanata ba da ta je musu,sai guraren 10pm suka mata sallama suka fito,suna tafiya a hanya motar ya yi shiru Manar ta d'an zuba masa idanuwanta,yana driving yace "wannan kallon fa?" Tace "i want to talk to u" yace "uhn! Ya akayi?" Tace "maganar yana da muhimmanci mu bari muje gida" yace "alright.." Sanda suka k'arasa gida yayi horn get keeper ya bud'e masa yana musu barka da dawowa,ya shiga yana amsa masa ya masa sai da safe,yayi parking k'asan tent ya fito ya bud'e mata ta fito,ya d'auko mata ledan apples d'inta suka wuce ciki,bayan sun yi wanka sun fito ta fara masa maganar yace ta bari ba yanzu ba ta huta,duk yanda taso ta masa maganar k'in bata chance yayi,sanda suka zo kwanciya,dukansu sunyi shiru suna kallon juna tace "Yaya!" Yace "uhn!" Tace "maganar d'azu" yana jin ta ce haka yace "wai wannan wane magana ne kika damu da shi haka?" Tace "ni dai ka bari na fad'a maka ka ji?" Ba don ya so ba yace "uhn! What's it?" Shiru tayi tana tunanin yanda za ta bijiro masa da maganar,ya d'ago kansa ya kalleta yace "kin fasa fad'a ne?" Tace "a'a" yace "uhn! What happened?" Tace "Mmm! Dama maganar Mama ne nake son maka" kallonta ya dunga yi da idanuwansa yana squeezing fuskarsa yace "wace Mama?" Tace "Mama dai" ya tab'e baki yana b'ata rai yace "kinga ni ban san me kike cewa ba ki barmu muyi bacci" tace "amma Yaya.." Yace "shhhiii!" Ya d'ora hannunsa akan lips d'inta da wani murya yace "just keep quiet.. Kiyi bacci maza" ya tokare hannunsa d'aya ya tallafe gefen fuskarsa da shi,yana kallonta ya kai d'ayan hannunsa yana shafa kanta zuwa fuskarta,kamar za tayi kuka tace "Yaya na san ka gane abunda nake nufi fa" yace "uhn! Cewa nayi ki min shiru kiyi bacci" hawaye suka fara kawowa idanuwanta tace "me yasa ba ka son maganar?" Yace "please kimin shiru haka" still bata gaji ba tace "ka fad'a min mesa ba ka son na maka maganar,can't u think ita ta haifeka? Ko me tayi bai kamata ka mata haka ba,bai kamata kak'i zuwa ka dubata ba,me yasa za kayi haka Yaya?" Kallonta ya dunga yi ya kasa mata magana,tace "please ba dan ni ba kaje ka dubata,about 5 month fa ake magana amma ko waya baka mata,why?³" Ta k'arasa da wani murya mai cike da rauni,k'wafa yayi kawai ya juya ya sauka daga gadon ya nufi k'ofa,ta tashi ta zauna ta fashe da wani kuka tace "yanzu ko ni nayi wani laifin za ka iya juya min baya kenan?" Cak ya tsaya a gurin idanunwansa a kulle yana ta calming kansa..
#Asli Smasher.
50...
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account