Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   14 / 66

39K to 42K   out of 196.2K words

da ta gama had'iye na bakinta tace "kai ma dai kamar wani baka san ba ta son hanta ba?" Shiru yayi ya zuba mata ido,ya d'aga girorinsa yace "Ohh! Na manta" ta ci gaba da cin abunta,sanda suka cinye ta d'auki fura ta kora,tana gamawa tayi hamdala tace "Allah maka albarka.. Yanzu da irin haka ne tsakaninmu har wani ma ya ji kanmu da kai?" Yayi murmushi ya koma kan kujera yace "saura labari na" tayi dariya tace "yanzu kuwa za ka ji su sai ka ce ya isa.." Labarin zamansu a Saudiyya ta fara masa tave "ai na fad'a maka zama Saudiyya ba dai dad'i ba.." Ya gyad'a kai yace "haba?" Tace "da gaske ma kuwa.. Komai baja-baja kake samunsa,shi yasa idan muka je harami babu abunda muke sai ibadah. Wata rana kawai muna cikin tafiya ba sai ga askar ba" yace "askar?" Tace "ehh! Kan kace me mutane sun fara gudu,radadada kowa sai gudu,ni dai ban san ya akayi ba kawai sai gani na nayi a gida ina mayar da numfashi,nake fad'a maka ban sani ba ma ko suma nayi a lokacin,ko wani ya kawo ni,na kalli Hjy Tasallah nace "wa ya kawo ni gida?" Y'ar kan uban yarinyar nan tana kallo na kawai sai ta kwashe da dariya,Hjy Tasallah tace "wa kuwa zai kawo ki idan ba k'afafun ki ba" na kalleta nace "aradun Allah bani iya dawowa gida da kaina" tace "to ai shi kenan tunda kinyi min musu" nake fad'a maka yarinyar nan ta zauna ta dunga min dariya,sai daga baya take fad'a min wai "Dadda kinyi rabin gudun ki a duniya" na tambayeta "wane gudu kuma Allah na tuba zan iya yi ni?" Tace "wallahi yau dai kinyi" nace "ni d'in?" Tace "ehh! Kinyi rabin gudunki dai" ni dai kamar zanyi kuka dan haushi nace "wai wane irin gudu ne nayi?" Kawai ta sake fashewa da dariya tace "rabin gudun famfalak'i mana" wai ashe da ina gudun ceton raina ne hijabina ya cika da iska.." Dariyar Amaar da Ameerah yasa Dadda juyawa ta kalli gurin da suke,ta gansu zaune kan kujera bata san yaushe suka shigo ba Ameerah har da kwanciya,Waleed kam tab'e baki yayi yace "kuma yanzun wannan labarin yayi miki kama da wanda nake so?" Ta kalleshi da sauri tace "yo kai dai ba labari kace na maka ba" yace " ba irin wannan nake so ba" tace "Iiiiiihhh! Wane iri kai d'in kake so?" Yace "mai dad'i dai haka" kallonsa ta dunga yi can ta tab'e baki tace "kai ni rabu da ni bacci nake ji,ku dai da ba'a raba ku da surutu sai kuje kuyi ta yi" wani murmushi yayi yace "ai biyana za kiyi" ta kalleshi tace "me na ci maka da zan biyaka?" Ya d'aga mata gira yace "nufinki nama da furan da na kawo miki a banza kika ci?" Tace "Iiiiiihhh! Daman biyanka kake nufin zanyi?" Yace "Uhn! Ke nufinki da bati kika ci?" Kamar za tayi kuka ta kalli Amaar tace "yanzu fisabilillahi d'an fodiyo dan wani cikinku ya siya min abu na ci sai kuma ace na biya? Dukiyarku ba ni da hak'k'i a cikinsa?" Amaar dai dariya kawai yake yi ya girgiza kai yace "a'a Hjy ta,ya ma za'ayi ace ki biya ko duka dukiyar kika cinye ai kin ci bulus" ta gyad'a kai tace "Uhn! Ka ji batu Malam" Waleed ya d'aure fuska yace "da gaske fa nake yi sai kin biya ni" ta kalleshi da sauri tace "to ba sai ka k'wata ba" yace "haka muka yi da ke?" Dadda ta hak'ik'ance tace "yo ko bamu yi ba da yanzu dai kam munyi,naci dubu sai ceto" murmushi yayi ya mik'e yace "za ki biya ni ne wani lokacin yanzu dai na yafe miki" tace "yo ko baka yafe ba ma yaya za kayi da ni?" Hanyar kitchen ya nufa ta bisa da kallo har ya tura k'ofar bata daina masa mita ba,Amaar ya kalleta yana sakin murmushi yace "a'a fa Hjy dan dai kawai ya ce ya yafe ne" ta juyo a fusace tana maka masa harara tace "yo ko bai yafe bama ai dole ya yafe,tunda dai ba zai yanki namana a matsayin kud'insa ba ko?" Hannunsa ya wanke ya fito da ruwa a hannunsa na roba,sanda ya koma ya zauna yana bud'e ruwan yace "kyaleta dan ta samu na ce na yafe mata ne,sai ma nace na fasa sai kin biya ni" mik'ewa tayi da sauri ta kama waistband tace "yo Allah na tuba sai dai mu dambatu mai k'arfi ya k'wata" yayi murmushin da ya bayyana hak'oransa yace "yanzu ko cewa aka yi ni dake muyi dambe,ai kya gudu kice a'a" tace "Iiiiiihhh! Saboda me?" Yace "haba Hjy ki kalle ni fa,ko wani namijin zai ji tsoron mu had'a jiki bare ke" harararsa tayi tace "ehh! Namijin ma sai dai idan sauna ne zai k'i" dariya sosai Amaar ya dunga Ameerah tana tayasa,Dadda ta wuce kitchen tana mita,Waleed yayi murmushi ya kalli Ameerah yana d'aure fuska yace "ke je ki d'auke wancan kayan" da sauri ta shiga taitayinta ta tashi ta d'auke plate d'in,ta kai hannu za ta d'auki robar ice creams d'in yace "banda wannan" ta wuce kitchen ta kai,da ta dawo ta wuce hanyar d'aki because ta san zama kusa da shi baka isa kayi kwakwkwaran motsi ba yanzun nan sai rai yazo yana b'aci,har ta kai kusa da k'ofa yace "su wannan d'in kina jira sai na ce ki d'auke?" Ta dawo da sauri ta d'auka a hankali gabanta yana fad'uwa tsabar tsoronsa tace "Yaya ina zan kai maka?" Wani kallo ya maka mata yace "kin tab'a ganin ina shan ice cream?" Ta girgiza kai da sauri yace "kin b'ace min daga gani ko sai na zane ki?" Da sauri ta wuce za ta sa a fridge ya mata tsawa yace "idan kika bari na ganshi da safe jikinki sai ya fada miki" cak ta tsaya idanunta suna kawo ruwan hawaye ta juya tana kallonsa tace "Yaya to ni ban san na waye ba" ya maka mata harara yace "ki jira na fad'a miki" daga haka ya d'auke kai ya ci gaba da kallon sport da ake haskawa,tsaiwa tayi a gurin ta kasa tafiya sai da ya d'ago ya kalleta ta shige d'aki da sauri,ta tarar da Manar a kwance ta k'arasa tana sauke ajiyar zuciya tace "shi wallahi Yayan nan ya cika takura" Manar tayi dariya tace "ki fad'a ya ji" a tsorace ta zaro idanu tace "Tabbb' so kike ya karairaya ni?" Tace "ashe kina tsoron yaji?" Zama Ameerah tayi kusa da ita tace "ga shi" Manar tayi saurin kallonta tace "mene ne?" Ameerah tace "ice cream" saurin tashi tayi ta zauna,ta d'auki d'aya ta bud'e Ameerah ma ta d'auki d'ayan suka fara sha suna hira. Ranar monday 7am ya shigo part d'in cikin k'ananun k'aya da suka amshesa yayi sallama,a zaune yaga Dadda kan darduma tana gyangyad'i bai yi magana ba ya kalleta ya wuce hanyar bedroom,ya tura k'ofar ya shiga,ya hangota kwance a saman gado tana bacci ya k'arasa ya kai hannunsa ya yaye duvet d'in da ta rufa,tayi juyi ta kai hannunta tana laluben bargon,ya tsaya ya zuba mata ido sanda taji ta kasa kamo bargon ta bud'e idanunta a hankali,a kansa idanunta suka sauka tayi sauri ta tashi ta zauna tana murza idanunta,ya maka mata mugun kallo yace "get up Malama ki shirya kada ki b'atan lokaci" ta dunga kallonsa kafin ta daure tace "ina za mu Yaya?" Yace "ban sani ba" ya juya zai fita,har ya kai bakin k'ofa yace "mintuna goma ki shirya ki fito ina jiranki a parlor" ta zumb'uro masa baki tana k'unk'uni,ya juya yace "me kika ce?" Da sauri ta sauka daga gadon ta wuce bathroom tace "nifa ban ce komai ba" ya gyad'a kai ya koma parlor ya zauna,kusan mintinsa biyar a gurin yana danna wayarsa yaga Dadda ba ta da niyyar kwanciya,yayi murmushi ya tashi ya matsa kusa da ita,shoulders d'inta ya kama zai kwantar da ita ta bud'e idanu a firgice suka had'a ido dashi tace "A'uzhubillahi minashshaid'anir rajiim" wani kallo ya mata ya saketa ya koma inda ya taso,ta gyara zamanta tana hamma,ya tab'e baki yace "ki kwanta mana" da sauri tace "na kwanta a wannan lokacin?" Yace "mene ne idan kin kwanta yanzun?" Ta girgiza kai ta d'auki carbinta tana ja,tace "banji shigowarka ba yaushe ka shigo?" Bai kalleta ba yace "kina gyangyad'i ya za'ayi kisan na shigo dama" suna zaunen Manar ta fito sanye da dogon wando da t-shirt kanta babu hula sai kamshi take bakin nan bad'au da chapstick,tun kafin ta k'arasa turaren da ta sa ya sanar masa,ya d'aga kansa ya kalleta ya girgiza kai cike da takaici ya mik'e tsaye yace "d'auko hijab muje" kallon Dadda ta tsaya tana yi tana jira taji ko za tayi magana taga bata ko kallesu ba,shi kam tuni har ya nufi k'ofar fita ta juya ta d'auko ta kalli Dadda ranta a b'ace tace "mun tafi" Dadda ta d'auke kai tace "Allah tsare hanya" daga haka ta mik'e ta fara karkad'e kura,tana fita ta hangoshi a parking space ta k'arasa a hankali,ya bud'e front seat ya shiga ba tare da ya ce mata komai ba,ganin ta tsaya ya lek'o fuskarsa a d'aure yace "za ki shigo mu tafi ko tsaiwar za ki ci gaba da yi?" Ta tab'e baki ta bud'e ta shiga ta rufe,ya kalleta kafin ya fara warming motar then yayi zooming off suka bar gidan,suna isa makarantar yayi parking a inda aka tanada,science academy ne mai kyau da yake had'e boys and girls,yayi parking ya fita yayi gaba,ita kam tana ciki sai zare ido take sai da ya juya yaga bata fito ba ya mata tsawa yace "get down Malama" ganin yanayin fuskarsa yasa ta bud'e ta sakko ya wuce forefront ta dunga binsa a baya har suka k'arasa office d'in principal,cike da girmamawa matar tayi welcoming d'insu dan tsaf ta shaida Waleed ta nuna musu guri suka zauna,after sun gaisa da Waleed Manar ta gaisheta,matar ta kalleshi tace "Mr Maji dad'i! Meke tafe da ku?" Waleed ya gyara zama yana kallon Manar ya mata bayanin abunda ya kawo su,ta gyad'a kai ta kalli Manar tace "ya sunanki y'an mata?" Manar dake b'ata rai tace "Manar Muh'd Maji dad'i" cikin barkwanci matar tace "wow! Triple M ko?" A hankali Manar ta d'aga kai ta kalleshi,yadda taga ya had'e rai ta sunkyar da kanta tana wasa da fimgers d'inta,Waleed da ya zuba mata ido ya juya ya kalli matar yace "Zainab Muh'd Maji dad'i shi ne sunanta" principal ta gyad'a kai tace "wane class ta gama can makarantar da ta baro?" Wani murmushi Waleed yayi ya kalli Manar cike da takaici yace "madam a tunaninki wane class ne ya dace da kamarta?" Principal tayi murmushi tace "think s.s one ko j.s.s three?" Waleed ya sake yin murmushi yace "ku kaita j.s.s one.." Matar ta kalleshi cikin mamaki tace "j.s.s one?" Waleed ya gyad'a kai,principal tace "amma ba ka ganin shekarunta da girman jikinta ya wuce na y'an j.s.s one?" yace "wane aji kike ganin ya dace da ita idan ba can ba?" Principal tace "j.s.s one duk k'ananun yara ne babu sa'anninta a can,ina laifin ma a kaita ko j.s.s 3 d'in" waleed yace "Ko kin san iya karta primary daga nan bata ci gaba ba?" Matar tace "wannan ai ba wani abun damuwa bane" yayi wani murmushi mai had'e da k'wafa yace "please madam ku kaita j.s.s one" sheshshek'ar kuka Manar ta fara,ya waigo da sauri ya kalleta,babu shiri ta rufe baki,ya sauke numfashi ya mayar da hankalinsa kan principal yace "madam she deserved nowhere than j.s one" principal tace "why not baza'a a had'a ta da y'an uwanta ba,idan yaso sai ku nema mata lesson teacher da zai na guiding dinta a gida.."



#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2021.





*♡MANAR¸.•💥*





*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA


_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._




13.


#Problematic..


Shiru Waleed yayi yana tunanin maganar principal d'in kafin ya gyad'a kai yace "alright!" Manar dake gefe taji ya ce haka,though bata gane me yake nufi ba tayi ajiyar zuciya,duk abunda ake buk'ata shi ya biya,principal ta basu uniform da kayan karatunta,suka yima juna godiya,ta rakosu har premises d'in makarantar then suka yi sallama suka tafi,a hanya motar tayi shiru babu mai magana da d'an uwansa,ya kalleta yaga ta juya tana kallon hanya fuskarta a had'e,ya tab'e baki ya d'auke kansa,kamar wanda aka yiwa dole sai ya mata magana yace "me yake damunki?" Bata juyo ba tace "babu komai" idanunsa akan hanya yace "babu komai kike b'ata rai?" Ta masa shiru ta k'i magana,ya gyad'a kai yace "kin san ba na son iskancin nan ko?" Da sauri ta waiga tana kallonsa kamar za tayi kuka tace "ni to me nayi maka?" A fusace yace "ni zan miki magana kimin shiru bayan na san kina ji na?" Rau² idanunta suka yi ta zumb'uro masa baki tace "ni fa yunwa nake ji,ka dena min magana" burki yayi saurin takawa Manar da babu belt a jikinta kad'an kanta bai daki glass d'in motar na gaba ba yayi saurin fizgota,a tsorace ta fasa k'ara ta k'ank'ameshi,yayi tsaki ya turata ta zauna,yana mata wani kallo yace "ni za ki rainawa hankali kice min kina jin yunwa?" Kuka ne ya kufce mata ta kifa kanta tsakanin thighs d'inta a hankali ta fara sheshshek'ar kuka muryarta tana rabewa tace "to ai dai ka san ban ci komai ba muka fito" ya zuba mata idanunsa a hankali ya kai hannu ya d'agota ta fizge da k'arfi za ta koma ya mata tsawa "keep ur mouth shut kafin na mareki" d'agowa tayi tana kallonsa sai kuma ta koma can jikin k'ofar ta kece da wani kukan mai shiga rai,ya zuba mata idanunsa yana kallon shagwab'arta,sanda ya tabbatar baza ta daina ba ya tada motarsa ya bar gurin,taji sai tafiya suke ita dai bata d'ago ba bare taga ina yake shirin kaisu sanda suka shiga hospital da yake aiki yayi parking ya bud'e ya fita bai saurareta ba yace "idan kin gama kukan kya fito" yayi gaba abunsa,d'ago kanta tayi ta harareshi har ya yi nisa ta goge hawayenta ta bud'e motar ta fita,taga ba gida ya mayar da ita ba da sassarfa ta bi bayansa tana kwala masa k'ira "Yaya!" Yana jinta bai tsaya ba ya ci gaba da tafiyarsa,da muryar kuka tace "Yaya ka tsaya ni na gaji" murmushi yayi yace "kiyi sauri" tace "Allah ni dai na gaji kuma kak'i tsayawa sai sauri kake" yana shiga ward d'in da office d'insa yake ya bud'e ya shiga yana lumshe idanunsa,ta turo k'ofar da k'arfi tana shiga ta zube a k'asa ta saki sabon kuka,saurin juyawa yayi ya mata tsawa,cikin kuka tace "to ni me na maka da za kana azabtar da ni?" Ya bud'e idanunsa sosai yana kallonta ta ci gaba da kukanta,bai sake mata magana ba ya k'arasa ya d'auki lab coat d'insa yasa,ya wuceta zai fita ta mik'e da sauri a tsorace tace "Yaya ina za kaje ka barni ni kad'ai?" Yace "ban sani ba" da sauri ta biyo shi ya juya ya mata wani kallo yace "ina za ki bini?" A shagwab'e tace "to ni kad'ai za ka barni kuma?" Yace "wani abu ne zai cinye ki idan kin zauna?" Tace "to ai tsoro nake ji" ya juya zai fita yace "idan kika biyo ni jikinki zai gaya miki" ta zumb'uro masa baki hawaye sun cika mata ido tace "ni dai ka mayar dani gida yunwa nake ji" yayi gaba abunsa yace "kafin na dawo na tarar kin mutu k'arewan yunwa.." Yana gama fad'a ya fice ya rufe ta a ciki,k'wafa tayi ta koma ta zauna ranta a b'ace,almost one hour sannan ya dawo ya tarar da ita a kwance kan kujera tayi kuka har ta gaji baccin wahala ya d'auketa sai ajiyar zuciya take saukewa,ya kalleta ya k'arasa wajen table d'insa ya fara zare lab coat d'in kafin ya zauna kan kujeran,ledar dake ajiye kan table d'in mai d'auke da tambarin Galaxy friends and delivery yasa shi d'agowa da sauri ya kalleta kafin ya zaro pack d'in ya duba,yaga ko tab'awa bata yi ba,ya kalleta da tunanin tun lokacin da aka kawo take bacci ko kuma fushi tayi tak'i ci,ya ajiye ya tashi ya isa gurin da take a hankali ya tsuguna kusa da fuskarta in a way style ya kai hannunsa fuskarta yana shafa side d'in fuskarta,sake gyara kwanciyarta tayi tana sauke numfashi,ya d'anyi tapping fuskarta a hankali ya kirata "Manar!" Kamar ta jisa tayi masa murmushi tace "shhhiii!" Ya zuba mata idanunsa cike da mamaki ya sake kiranta,hannunta ta kai ta rik'osa gaba d'ayansa da muryar bacci tace "nifa ba na son komai,bazan ci ba.." Ta b'ata rai a shagwabe ta zumb'uro masa baki tace "fushi ma nake yi da kai ai,kayi tafiyarka ka barni,bayan na ce ma yunwa nake ji" ta fara sheshshek'ar kuka duk a cikin baccin tace "kuma sai na fad'awa Abba nace har gurin aikinku ka tafi da ni kayi ta min fad'a kana min tsawa.." Wani murmushi yayi da ya fahimci bata san me take ba,ya zareta da kyar daga jikinsa ya tashi ya koma kan kujeransa ya fara duba files da suke gurin,bai fi mintuna goma ba da barin kusa da ita ta farka da kuka,ya kafeta da idanunsa yana d'aure fuska yace "meye matsalarki?" Tace "Yaya yunwa fa nake ji ka mayar da ni gida" harara ya aika mata yace "ki cire tunanin zan mayar da ke gida yanzu.. Oyah! Tashi kije ki wanke baki kizo kici abinci acici" zumb'uro masa baki tayi tace "bazan ci ba" ya d'aga shoulders yace "cikin ki ba nawa ba" harararsa ta dunga

14 / 66