Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   11 / 66

30K to 33K   out of 196.2K words

a b'ace sai masifa take tana fad'in "kinga ba na son shashanci idan baza ki zo ba ki fad'a min" bai ji me aka ce a d'ayan b'angaren ba yaji ta yi k'wafa tace "shi kenan ke kika sani idan baki zo ba,kanki za ki yiwa ba ni ba" k'it ta kashe wayar ta ajiye sai huci take,Abba ya k'arasa inda take a hankali ya dafa shoulder ta d'aya yace "lfy? Ko akwai wani matsala ne?" Asama'u da bata ji shigowarsa ba sai maganarsa ta tsinta tayi saurin waigowa ta kalleshi,fuska babu wadataccen fara'a tana sauke ajiyar zuciya tace "wallahi ni da wannan sakarar ce Rabi" a hankali Abba ya zauna gefenta yana rungume da Waleed a jikinsa yace "Uhn! Me yake faruwa?" Kawar da kai tayi tace "it's a secret" ya kalleta da kyau yace "really?" Ta gyad'a masa kai,jinjina kai yayi bai sake mata magana ba ya ajiye Waleed ya tashi,ta kalli yaron ta tab'e baki tace "sun yarda sun ba ka shi ka dawo min?" Saurin kallonta Abba ya juya yayi yace "ban gane me kike fad'a ba" tace "wasu yara k'awayen Hafsah masu iyayin bala'i da suka zo,akan su nake magana" dariya ta bawa Abba yadda yaga tana magana,yace "Ohhhoooo! Ko su ne naga Waleed a gurinsu?" Da sauri Asama'u ta kallesa tace "Waleed d'ina?" Yace "sure!" Tayi murmushi tace "Waleed d'in da ba da kowa yake yarda ba shi ne suka d'auka?" Abba yace "kina mamaki ne?" Tace "ai dole nayi,Yaron da muma bai bari ba wani lokacin k'uiya yake mana idan za mu d'aukesa shi ne yau ya yarda da bak'i?" Shi dai Abba ganin ta mayar da maganar abun reputation kamar tana son k'aryatasa kawai sai ya fara cire kayansa ba tare da ya sake ce mata komai ba ya wuce toilet. Washe gari gaba d'aya su Hafsah basu zauna a gidan ba sun tafi gyaran jiki,tun safen Asama'u take kiran Rabi amma ta k'i zuwa sai yamma,kusan a tare suka shigo da su Hafsah,suka gaisa da ita cikin sakin fuska,suna shigowa compound Hafsah ta hango fitowar Prince Mahmoud Maqbool daga b'angarensu ta yi still tana mamakin yaushe yazo,mutumin da babu jimawa ya mata waya shi ne bai sanar mata yana hanya ba,yadda ta tsaya tana kallonsa fuskarta cike da mamaki yasa Maryam ta rik'ota tace "what happened sister?" Hafsah tayi ajiyar zuciya tace "kun ga mutumin nan d'azu fa muka yi waya shi ne bai ce min yau zai zo ba" dariya suka yi Fatima tace "banda abunki surprise yake son baki,and da alamun kin karb'a" dariya itama tayi musu suka k'arasa sai kallonta yake yana sakin murmushi,Fatima tace "amma fa sister kinyi sa'a wallahi mijin kin nan he's more than handsome,banyi tunanin haka zan gansa ba" Maryam tace "nima dai banyi tunani ba,but duk da haka our princess ta fisa had'uwa" suka yi dariya duka,suna cikin gaisawa tana gabatar masa da k'awayenta,Muh'd ya fito daga apartment d'in yana dariyar Mama azumi,tsayawa yayi cak idanunsa akan Maryam dake magana da Mahmoud tana sakin murmushi,lokaci d'aya yaji kamar an kwad'a masa guduma a kai,ya dunga jin wani irin sensational feeling yana taso masa,Hafsah da taga fitowarsa tace "Yaya tare kuke ne?" Murmushin k'arfin hali yayi mata yace "no! Nima ban san da zuwansa ba ganinsa kawai nayi,tunda ya zama d'an gari,ya daina nemana sai dai na gansa kawai" ta gyad'a kai tana sakin murmushi sai dai bata sake cewa komai ba,su Maryam suka gaishe shi then suka wuce suka bar Hafsah gurin masoyinta,Mahmoud yayi saurin matsowa kusa da ita da turanci yace "me kuke cewa ke da yayanki? Kin san ba gane yarenkun nan nake ba" tayi dariya tace "nima ai ba jin naka yaren nake ba" murmushi yayi mata yace "after munyi aure zan koya miki" tace "sure?" Ya gyad'a mata kai yace "nima ai za ki koya min naku ko?" Tace "idan kana so me zai hana" yayi murmushi yace "yana bani sha'awa sosai and ina so na iyasa" tace "babu matsala nima idan ka koya min naka sai na koya maka namu" da murnansa yace "really?" Ta gyad'a masa kai tace "absolutely sure" basu wani jima suna hiran ba sosai yace ta shiga gida ta huta anjima zai dawo,suka yi sallama ya wuce part d'in Muh'd itama ta shiga gidan. Rabi ce tayi sallama part d'in yayarta,Asama'u tana jinta ta fara k'unduma mata ashar,ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba,fad'a kamar za ta aro baki,Rabi ta tsaya kallonta da mamaki tace "wai duk akan me kike wannan kumfar bakin?" Asama'u tace "ban sani ba,banza mara hankali,tun wancan satin nake kiranki kizo Muh'd ya zo,amma yarinyar nan saboda kin mayar da ni sha³ kin d'auke ni y'ar iska kika k'i zuwa sai yau,ai ki ma tattara kayanki ki koma zuwanki yanzu baida wani amfani" zaunawa tayi tana sauke ajiyar zuciya tace "kema dai da tun farkon kin fad'a min haka ai da tun a ranar na taho" harararta Asama'u tayi ta d'auke kai,Rabi tace "to yanzun ya ake ciki?" Ajiyar zuciya Asama'u tayi tace "ki tashi kije ki gaida Hjy yanzu ki dawo kin san ta gurinta za mu fara kamun k'afa" Rabi tayi dariya ta mik'e tace "bari to naje na dawo" ta fita da sauri tayi b'angaren Mama azumi,sanda ta shiga ta tarar da su Maryam suna hira da Mama ta zauna bayan sun gaisa suka d'an tab'a hira da su Maryam then ta fita,tana komawa ta sanar ma Asama'u,here ta d'an mata lecture akan yadda za ta shigewa Muh'd har shi da kansa ya fito yace yana sonta,bata zo da niyyar kwana ba amma Asama'u sai da ta san yadda tayi ta rinjayi ra'ayinta tace "ba dai kayan sawa kike tunani ba?" Tace "ehh! Wallahi kinga ban taho da komai ba" Asama'u tace "kada ki damu zanje gidan gobe gurin Hjy sai na taho miki da su.." Tun daga ranar Rabi ta fara baza komarta sai dai ta kasa kama kifin,gaba d'aya ma tunda tazo ko hanya basu had'o da Muh'd ba,sai ranar dinner auren hafsah shima ba ita da shi ba,can a gurin dinner ta hangosa kusa da abokinsa gefensa Maryam suna d'an magana da ita k'asa² suna dariya,d'ayan side d'in kuma Fatima,har aka tashi gurin dinner bata samu damar ganinsa a keb'ance ba,suna komawa gida take fad'awa Asama'u tace "wai dama haka Muh'd ya sake zama handsome?" Asama'u ta maka mata harara tace "ban sani ba,da da nake kiranki kina min iskanci,yanzun ai idanunki sun gane miki" Rabi tace "gaskiya idan na samu guy d'in nan na yi sa'a" Asama'u ta karb'e zancen da fad'in "idan kika tsaya kallon ruwa kuma kwad'o zai iya yi miki k'afa ba" Rabi tace "wane irin kwad'o ne wannan? Ai wallahi duk abunda zai shiga tsakanina da shi zan iya kawar da shi daga duniyar" wani dariya Asama'u tayi tace "anzo gurin!" A nan ta fara kyankyasa mata batun su Maryam da yanda za tayi har dai ta janyo ra'ayinsa kanta.. Alhamdulillah an gama biki lafiya amarya ta tare a katafaren gidanta da Raj Maqbool yasa aka gina musu cikin wata guda saboda makarantarta za su fara zama a nan idan sunyi hutu kuma su wuce India har zuwa lokacin da za ta kammala karatunta,bayan y'an rakiyar amarya sun tafi gida ya rage amarya da k'awayenta su Fatima,suka yi mata sallama za su koma gida sai washe gari su tafi gidajensu,Hafsah tana kuka suma suna yi ga shi sun rungume juna da kyar Muh'd ya rik'o hannun Maryam yayi waje da ita,ya sata motarsa ya shiga ya fara bata baki yana cewa "ai ba shi kenan kun rabu ba,za kuzo ku ganta itama za taje inda kuke,mene abun kuka kuma?" Sanda ya samu tayi shiru ya wuce da su gida shi ya rakasu har b'angaren Mama azumi,washe gari ko da za su tafi bayan sun yi sallama da Mama ta had'a su da kayan gara da abun arziki tayi musu addu'ar suma Allah kawo musu mazajen suma,suka fita suna k'walla saboda cikin y'an kwanaki suka yi saboda kowa na gidan banda Asama'u,bayan fitarsu Muh'd ya fara kaisu gidan Hafsah a can suka wuni daga can ya mayar da su gidajensu bayan ya musu siyayyar arziki da yake Maryam da Fatima unguwarsu d'aya line su ne dai ba d'aya ba,da zai tafi ya karb'i digit d'in Maryam suka yi sallama. Tun daga ranar yake kiranta suke gaisawa a haka mutunci ya shiga tsakaninsu,a hankali² alak'arsun ya fara rikid'ewa ya koma wata irin shak'uwa mai k'arfin gaske,haka kawai idan yana gari ma sai yace zai zo su gaisa,a zuwan da yake gurinta ya cusa mata ra'ayinsa,ba tare da jinkiri ba lokacin da yake sanar masa yana sobta itama ta karb'a,ko da ya kaiwa Mama azumi maganar ya samu matar aure tace "a ina take?" Kai tsaye ya sanar mata k'awar Hafsah ce k'anwarsu,Mama ta yi farin ciki sosai tayi addu'ar fatan alkhairi tace za ta fad'awa Malam,ko da Malam ya dawo ta sanar masa ya kira Ibrahim ya fad'a masa maganar,Abba yana sosa backhead yace "Baba nima ai fad'a muku ne banyi ba ya riga ni,amma nima ina da burin k'ara aure,harka na samu mata" Mama tace "da wuri haka Yaro?" Malam dai yace "maa sha Allah,a ina ita kuma take?" Yayi k'asa da kansa yace "ai itama k'awar Hafsah ce" Mama tace "ko dai Fatima kake nufi?" Cikin jin kunya yace "Ehh! Itace" Mama tace "ikon Allah! Ashe ni duk surukaina ne suka zo min har gida ban sani ba,ai kam na yi farin ciki wallahi,idan wannan abu ya tabbata Hafsah ita za ta fi kowa murna yayyenta sun aure k'awayenta.."



#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2021.





*♡MANAR¸.•💥*





*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA


_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._




10.


#Her tears..


Washe gari Malam Usman ya samu Alh Na Abba da maganar saboda yanzun amincin da ke tsakaninsu ya wuce na tsakanin yaron shago da uban gida,Malam Usman a yanzun yaransa sun kafa masa kasuwancinsa zaman kansa yake yi a kasuwar da yaransa shima da suke ci a k'ark'ashinsa,a ranar suka tsayar da ranar da za suje nemawa yaran aure,sun fi son ayi komai lokaci d'aya a gama,sanda Asama'u ta samu labarin Abba zai k'ara aure ta tada haukan ba'a isa a mata kishiya ba,har b'angaren Mama azumi taje ta mata tijara tana cewa ai duk itace tsohuwar najadun da ta k'ulla makircin za'a mata kishiya,shima kuma Muh'd itace tayi sila yak'i auren k'anwarta saboda bak'in cikin su zo su huta,k'arshen dai akan maganar Abba ya dank'ara mata saki d'aya yace taje gida duk sanda tayi hankali ya dawo da ita shima kuma saboda darajan Waleed dake tsakaninsu ne ba zai iya wulak'anta ta ba,wannan abu ya yima Asama'u zafi sosai,sanda Malam ya dawo ya samu labarin abunda ya faru yaje har gida ya dawo da ita saboda darajan marik'inta Alh Na Abba,ya yiwa Abba fad'a sosai,sai wani abu kuma tunda Asama'u ta dawo gaba d'aya ta fita sha'anin Mama azumi,even gaisuwa ya daina had'a su,haushin kowa take ji a gidan,amaren da aka kawo kam suna zaune lafiya ko tsakaninsu da Mama azumi kullum girmamawa ne da kyautatawa,Waleed yana da Shekaru biyu a duniya Fatima ta haifi d'anta namiji Abba yasa masa Usman aka mayar masa sunan Malam aka masa alkunya da Amaar,a hankali rayuwa ya dunga tafiya,while a gefen Hafsah da Maryam babu wanda ta yi ko da b'atan wata har Fatima ta yaye Amaar ta sake samun wani cikin,a lokacin itama Asama'u tana d'auke da juna biyu suka haifi yaransu mata Fatima da Waleed yake kira Aunty ta haifi y'arta Maryam,ita kuma Mama (Asama'u) ta haifi Aisha,tun daga nan haihuwar nasu sai ya zama kamar gasa,suka koma haihuwa lokaci d'aya,the next haihuwa shima suka sake haifar mata,Aunty ta haifi Fatima (Batool) sai dai bata yi nisan rai ba,Mama kuma ta haifi Khadijah (Deejah),har a lokacin bangaren su Hafsah da Maryam shiru dai babu wani bayani,it was there Asama'u ta fara zuga Mama azumi ta k'ark'ashin k'asa kan me yasa baza ta sa Muh'd ya k'ara aure ba ko Maryam d'in ce juya baza ta haihu ba,yanayin zuga abunda za'a fad'a yau daban na gobe ma haka,tun Mama Azumi bata gamsu ba har dai ta fara yiwa Muh'd maganar k'arin auren,shi kam da yake lokacin ba samun zama yake ba rayuwarsa kusan tana lagos sai ya shafe watanni baya gari ko da Mama azumi ta zo masa da maganar yace "shi gaskiya bai da burin cika gidansa da mata,d'ayan ma ta ishe shi,maganar haihuwa kuma na Allah ne,idan ita ance mata juya daga aurensu,k'anwarsa Hafsah me za'a kirata,ita da ta riga su auren?" Mama azumi tayi shiru tana tunani,daga bayan dai da ya fahimtar da ita tace "ai shi kenan,dama shi zai zauna da su tunda baya ra'ayi shi kenan" still Asama'u bata hak'ura ba ta dunga mata famfo a sonta sai lallai Mama tasa baki a had'a Muh'd da k'anwarta Rabi,Mama ta bad'e ido da toka tace "ita fa a kyaleta tunda yace baya ra'ayi,a rabu mata da d'a bata son sabgar takura kai" Asama'u bata ji dad'i ba ta dai had'iye b'acin ranta gudun kada ta janyo abunda Abba zai sake sakinta,taje ta zayyanawa mahaifiyarsu komai,Hjy Ladi tace "su kyalesu da ita suke zancen.." Sanda ta fara shige² itace gurin wannan Boka yau,gobe tana gurin wancan,but duk inda taje sai ace mata babu nasara,Muh'd ya cika taurin kai a tsaye yake zai yi wahala duk abunda za suyi yayi tasiri akansa,haka ko itama Mama azumi da suke tunanin za suyi nasara idan sun had'a da ita,abu dai duk yak'i dad'i k'arshe sai b'arnar kud'in su da suka dunga yi. Bayan lokaci Mama sun yaye su Deejah,suka sake samun ciki a lokacin ne Allah ya k'addara faruwar abunda ya hukunta,kaf gidan babu wanda ya san Maryam na da shigar ciki,hatta ita kanta sai da ciki ya fito b'aro² sannan Mama azumi ta kula,here ta fara murna tana ratatun cewa "Dama ta san lokacin samun k'aruwarsu daga b'angaren Maryam ne bai ba,yanzun ga shi Allah ya kawo lokacin" ta dunga nan² da ita,a cikin shekarar ne kuma Allah ya karb'i rayuwar Malam Usman da maimartaba sarki Maqbool surukin Hafsah,a zuwan da su Hafsah suka yi India rasuwar surukinta though dama suna zuwa tun ma kafin lokacin,bayan an share makoki aka fara shirye²n sabon nad'i aka d'ora Yayan Mahmoud Jarood Ibn Maqbool matsayinsa na babban d'a ga sarki Maqbool,a lokacin sarki Jarood yaronsa d'aya Muh'd Azaan,tun a wancan lokacin da su Hafsah suke zuwa k'asar Allah ya had'a jininta da Azaan,lokacin ko da suka je rasuwar Raj Maqbool da za su dawo Nigeria haka nan Azaan ya mak'ale mata yace shi sai ya bita,a lokacin shekarunsa duka 15 ne,babu irin lallashin da ba'a masa ba ya dage lallai sai ya bisu,Raj Jarood yace a had'a masa kayansa su tafi tunda yana so,haka kuwa akayi tahowar su Nigeria babu jimawa Mama,Aunty Bebie da Aunty Mammy suka haife yaransu duka mata,ita Mama aka sa mata Halimatus'sadiya (Diyanah),while su kuma yaran wajen su Aunty duka aka sa musu (ZAINAB) sunan Mama azumi,Zainab d'in wajen Aunty Bebie ana kiranta (Ameerah),ita kuma ta wajen Aunty Mammy tun da aka haifeta Azaan yake ce mata (MANAR) shi kenan sunan ya bita,sai ba'a sake mata alkunya ba,tun daga haihuwar Manar tsanar da Mama take ma Maryam ya shafi y'arta,ko sanda suke yara suna koyan tafiya idan ta shiga gidan sai dai a kawowa Mother ita tana kuka,bata tab'a d'aga kai ta ce komai ba sai dai ta d'auki y'arta ta lallasheta,sanda al'amari ya fara tsanani Mama azumi ta gaji da halin mother ta d'auke Manar,rainonta da komai na ta ya koma gurinta sai idan ta yi kuka tasa a kira mother,akan idanunta za ta shayar da ita ta ajiye mata ita ta k'ara gaba,ta hana kowa d'aukanta ya shiga da ita gidan Abba sai dai a d'auko mata Ameerah a kawota b'angarenta suyi wasan a can,yayin da a gefen Mama kuma daga kan Diyanah sai haihuwa ya tsayawa mata,da yake tun haihuwar Deejah dama ita bata cika lafiya ba,sanda suka tasa tsakaninta da Diyanah idan ba wanda ya sansu ba sai yayi zaton y'an biyu ne,Aunty da Mother suka koma haihuwa kusan tare,bayan Manar mother ta haifi Mu'awiyah,Mahmoud,Ibrahim khaleel,sai auta Hafsat wanda take shayarwa,ita kuma Aunty ta haifi Aliyu (Asad) da Mus'ab,daga nan itama haihuwa ya tsaya mata. Dalilin rashin jituwan Azaan da Waleed kuwa tun lokacin yarinta ya samo asali,a lokacin haihuwar Manar,sanda su Hafsah suka dawo Nigeria tare da Azaan wanda Raj Jarood ya musu kyautansa,ko da mother ta haifi Manar gaba d'aya sai Azaan ya dawo gurin mother kullum yana lik'e da ita da Manar yana mata wasa,sanda hutunsu ya kusa k'arewa,Hafsah suka shirya mayar da shi still ya dage shi dai sai a barshi gurin mother da baby,Mahmoud yayi waya da yayansa ya sanar masa halin da ake ciki,Raj Jarood Ibn Maqbool yace su kyalesa kawai a gurinsu shima bai basu shi dan su dawo da shi ba tunda Allah bai ba su haihuwa ba and matarsa a lokacin kuma tana d'auke da juna biyu yace ya basu shi duniya da lahira,to kuma a dai² lokacin ne matarsa Rani Naheed itama ta sake haihuwar y'a mace *RANIA* tun da Azaan yaji labarin mahaifinsa ya barshi ya zauna a Nigeria yake murna,Muh'd mahaifin Manar ya nema masa makarantar su Waleed,da yake shekarunsa d'aya da Waleed aka kaishi class d'insu,yayin da a b'angaren Waleed haka nan tun zuwan Azaan gidan yaji bai masa ba ba ya kuma k'aunar ganinsa kusa da Manar ko kad'an,a haka dai suke rayuwa Azaan ya fi shak'uwa da Amaar duk da ya girme masa da 2yrs amma idan ka ga yadda suke da Amaar sai kayi tsammanin

11 / 66