abu kuma sai muce a barshi?" Yace "idan baza kuce ba sai aka ce ana cewa ga shi ku karb'a? Jira kuke a baku kenan?" Tayi shiru,ya mata tsawa yace "ba dake nake ba?" Ta zumb'uro baki tak'i cewa komai,yayi k'wafa yace "gobe zabga wanda za ku sake bi" tace "kai za mu bi" da sauri ya taka brake ya kalleta a hasale yace "ni kika ce?" Ta girgiza masa kai da sauri tace "nifa bance komai ba" yayi k'wafa yaci gaba da driven,har suka je gida bai sake mata magana ba,yana yin parking ya bud'e ya fito musu da kayan yace "maza ku d'auka ku b'ace min d'aga gani" kafin ma ya k'arasa ta fizgi carton d'in malt d'in ta yi gaba,ya bita da kallo bai ce mata komai ba,Ameerah ta fito ta d'auki na ruwan da ledar da aka basu tabi bayan Manar,sai da yaga shigarsu gidan ya juya ya shiga na su gidan,a bedroom ya tarar da Mama yayi sallama,ta d'ago tana masa murmushi tace "Waleed! Har ka dawo?" Yace "ehh! Ta ce a gaishe ki" tace "muna amsawa,oa same su lafiya?" Yace "lafiya lao" shiru ya d'anyi then ya tashi yace "sai an jima" sanda yaje bakin k'ofa ta kirasa,ya tsaya a gurin ya waiga,tace "kun had'u da Afiyah?" Shi dai so yake kawai ya bar d'akin yace "ehh mun had'u" tayi wani murmushi tace "good.. Ya ka ganta,i mean ta yi maka matsayin matar aure?" Wani zaro ido yayi yace "zabiya ce fa" tace "zabiya ba mutum bace?" Ya girgiza kai yace "no! I just mean ni gaskiya ba irinta nake son.." Bai karsa ba tace "ni kuma itace tayi min,and ita na zab'ar maka matsayin matar aure.."
#Share pls.
#Asli Smasher.
[1/21, 6:54 PM] My number 1: 17...
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*
Jikinsa har tsuma yake wajen tambayarta "Mama ita wannan d'in?" Tace "yes! Itafa!" Yace "Mama please.. Dan Allah ki bari na nemi type d'in da za tayi dai² da ni,wallahi Mama ni dai yarinyar nan sam bata min ba" wani kallo ta dunga binsa da shi,a wani iri tace "na barka ka nemi type d'in da za tai maka?" Yayi shiru bai yi magana ba,cikin hasala tace "Waleed! Wai ni sa'ar wasanka ce?" Yayi k'asa da kansa yace "i'm sorry Mama" taci gaba da fad'a "idan ba kana son mayar da ni sakarai ba,ni zan nema maka mata kace min bata maka ba? Yarinya y'ar gidan mutunci" ya d'ago a hankali ya d'an marairaice fuskarsa yace "i'm so sorry Mama,ni ina da dalilin da yasa nace miki haka" a fusace tace "dalilinka na banza da wofi? Wallahi Waleed ka mayar da hankalinka jikinka,kafin na sab'ar maka,ka san Allah da gaske idan ka turje zan gwada maka k'arfin ikona,anything can happen at anytime wallahi" numfashi ya sauke a hankali yace "Mama kina ganin yin haka shi ne dai²? Nifa na fad'a miki ina da personal problem da zaisa nak'i amincewa" Mama dai sai kallonsa take ranta a b'ace tace "Waleed ni kake fad'ima haka?" Ya girgiza mata kai yace "no! Mama ya kamata ki fahimce ni,idan kika ce sai na aureta zai iya kasancewa na cutar da ita,u know already i've my own problem,she's not my type and she can't take me at all.. Idan kun takura aka yi auren a haka za mu cutar da juna ne kawai.." Gaba d'aya idanun Mama suka rufe gani take kamar raina mata hankali yake son yi ta k'ara fututtuke fuska tace "na rantse da ubangijin sammai da k'assai bakwai idan ka ga an fasa abun nan sai dai in yarinyar ce tace ba ta so,amma dan kai baka isa bad'a min k'asa a idanu ba,wallahi baka isa ka kunyatar da ni a gurin aminiyata ba" shiru yayi kawai ya rasa abun da zai sake fad'a mata ta gane me yake nufi,though ya fad'a a yanayin da dole ma sai ta gane d'in,yadda ta rufe ido tana masa fad'a nan da nan yaji ransa ya b'aci a fusace ya juya ya bar mata gurin,tana masa magana ma ko saurarenta bai tsaya yi ba ya fice,gidan Dadda ya wuce sai huci yake kamar kububuwa ya shiga babu ko sallama,Dadda da su Manar sun baje suna kwasar garar arziki,sunyi dumu² da paper chicken da suka zo da shi,Manar ta d'aga kai tace "Hjy kuma fa har kud'in ma ita ta bamu" Dadda tace "dubu goma fa" Manar tace "ehh ai dan baki ga gidan ba,da ba za kiyi mamaki ba ma,ko Meerah?" Ameerah ta gyad'a kai dai² lokacin Waleed ya kwanta kan kujera ya dafe kansa da yake jin ya fara sara masa,Dadda ta d'auki wani k'aton tsoka ta kai baki tace "Iiiiiihhh kuma shi mutumin fa me yace?" Manar ta d'ago ta saci kallonsa,shigowarsa yasa ta fasa fad'awa Dadda abunda tayi niyya,da sauri ta d'auki nasa kason da Dadda ta ware masa ta matsa kusa da shi tace "Yaya" bai iya d'agowa ba yace "leave me alone please.. I'm not in the mode" sororo ta tsaya kansa tana kallonsa ta sake cewa "Yaya!" A fusace ya d'ago kamar zai bugeta yace "I said leave me alone" wani kuka ne ya kwace mata tsabar firgitar da yasa tayi ta juya da sauri za ta wuce d'aki ya rik'o hannunta,cikin kuka tace "ni ka kyale ni" ya furzar da wani zazzafan numfashi yace "zo ki zauna muyi magana" ta girgiza masa kai tace "ni bazan zauna ba" ya mata wani kallo yace "sit please" sai da ta kalleshi kafin ta zauna,ya kalli Dadda da ta kafesa da idanu hannunta rik'e da namanta kamar wadda akayi pausing ko irin a shirin film d'innan,shi kansa da baya cikin yanayi mai dad'i sai da tasa ya murmusa ya juya ya kalli Manar a hankali ya rad'a mata "ko dai muje backyard muyi hira?" Da sauri ta kalleshi ya d'aga mata girorinsa,tace "toh" ta tashi shima ya mik'e,Dadda da ta bisu da kallo baki sake tace "ikon Allah.. Ni dai ban gane wannan k'us² da kuke yi ba,ko kuma dai wani sabon gulma da kinibibi ne hakan?" Waleed da ya kai k'ofa ya waiga yace "sai dai ki biyo mu kiji" ta saki baki har ya fita bata kuma cewa komai ba,sai kwafar da tayi tace "y'an banten uba,da ni kuke zance har gadon barci na za ku same ni" shi dai tuni suka yi gaba suka barta tana mita,a bayan ya ganta ta zauna kan wani dakali ya k'arasa yana kallonta ya zauna kusa da ita,gaba d'aya suka yi shiru ita tana kallon shuke² da bishiyun da suke kad'awa suna k'ara wadata gurin da yalwatacciyar iska,tayi ajiyar zuciya a hankali tace "Yaya na fara jin bacci" ya kalleta da kyau yace "really?" Ta waigo ta kalleshi,yayi murmushi yace "mu bar maganar ba yanzu ba?" Tace "a'a ka fad'a kawai" sai da ya ja fasali kafin yace mata "Mama ta nema min matar aure" zabura tayi bata san daga ina ba taji maganarsa ya sa ta k'warewa,da sauri ya matsa ya rik'eta sosai a jikinsa yana shafa bayanta,sai da ta koma normal ya janye hannunsa yayi shiru yana tunani damuwa k'arara a fuskarsa,wani dariya Manar tayi cikin murna tace "Yaya yaushe ne auren?" Ya zuba mata idanunsa yana kallon yadda take murna yace "kina farin ciki da auren?" Tace "sosai ma ni fa Yaya ban tab'a ganin anyi biki ba a gidan nan" ya maka mata harara yace "wai ke baki ji komai ba ma?" Tace "me zan ji?" Haushi ne yasa shi cewa "ban sani ba" tayi dariya tace "Yaya Allah ni dai murna nake yi za kayi aure,ka ga zan samu gidan da zan dunga zuwa ina yin hutu ko?" Kallonta ya dunga yi da mamaki ita matsalarta kenan,yace "wait.. Kin san wacce zan aura ma?" Ta girgiza masa kai,yace "wannan yarinyar" squeezing fuskarta tayi tace "wacce?" Yace "ta gidan da muka kaje.." Idanunta ta zaro tace "Yaya wannan zabiyar?" Ya gyad'a mata kai ransa yana kuma b'aci,wani dariya ta fashe da shi cike da wauta tace "shi kenan Yaya sai kuyi ta haifar k'warori" ya d'aure fuskarsa yace "waye ya fad'a miki haka?" Tana dariya tace "to ba ita zabiya bace" yace "dan tana zabiya ni kuma fa?" Kallonsa ta tsaya yi,ya d'aga mata gira ganinin kallon da take masa yace "what?" Tace "Yaya kuma kana sonta?" Gab'a d'aya ya d'auke wuta ya rasa wane irin amsa zai ba-ta,ta kai hannu ta tab'asa tace "Yaya!" Ya d'an dawo nutsuwarsa fuskarsa tana bayyanar da damuwa yace "ba na jin sonta at all" k'uri ta masa da ido tace "to Yaya itafa tana sonka?" Ya tab'e baki yace "ban sani ba" shiru tayi tana kallonsa fuskarta babu isashshen walwala tace "to Yaya kai me yasa ba ka sonta?" Ya d'aga kansa looking to the sky kamar yana counting stars a hankali yace "there's some special,wanda aka halicceta daga jikina,aka halicceni da komai nawa saboda ita,ita kad'ai nake muradin aure,itace kadai zuciyata ta aminta da ita,nake kuma fatan mu rayu k'ark'ashin roof d'aya" dariyar da ta kyalkyale da shi ne yasa shi kallonta yace "me ya baki dariya?" Ta tsagaita tace "kai ne mana Yaya na ji sai magana kake kamar malamin soyayya" ya lumshe idanunsa kad'an yace "baza ki gane irin son da nake mata ba" gyara zamanta tayi tana kallonsa tace "Yaya to kai me yasa baka fad'a mata kana sonta ba?" Yace "there's someone da yayi intervening tsakanina da ita,and abunda yasa ban fada mata,but i just don't know ko itama tana sona kamar haka? Ko kuma dai ni kad'ai nake haukan sonta" Manar tace "kaiiii! Yaya son maso wani fa kenan kake yi" yayi murmushi mai ciwo yak'i cewa komai,ganin yayi shiru ta d'ora hannunta kan kafad'arsa tace "Yaya me yasa to baza ka fad'awa Mama kana da wacce kake so ba ta kyaleka?" Ya girgiza mata kai cike da jimantawa kansa yace "ta ruga da ta yanke hukunci tun farko" wani zaro ido ta sake yi jin ya ambaci sunan Mama a karo na biyu ta san ma ba abun arziki zai biyo baya ba tace "to Yaya auren dole Mama za ta maka ne?" Ya gyad'a kansa yace "kusan haka ne" wani tausayinsa taji da taga fuskarsa ta sauya,ta kwantar da kanta jikin kafad'arsa,a hankali tace "ni dai Yaya idan ba ka son auren ka fad'awa Abba to ko Dadda mana,su ai Mama za taji maganar su" ya girgiza mata kai yana jin wani tuk'uk'in bak'in cikin da ya tokare masa wuya yace "no way Baby,dole ne nayi hak'uri na karb'i auren" tace "saboda me?" Ji yayi idanunsa sun cika da kwalla ya daure yace "she said idan ban amince ba za ta tsine min" wani irin tausayi taji ya ba ta tayi shiru ta d'auke wuta,gaba d'aya ta shiga damuwa,almost 2 hours suna zaune babu wanda ya sake magana sai tunanin da zuciyoyinsu suke,ganin dare ya fara yi sosai ya sauke numfashi yace "ta shi muje na raka ki gida" ta d'ago kanta daga jikinsa jikinta duk a mace ta mik'e a hankali,ya tashi shima suka jera babu mai iya cewa komai suka zagaya,sai da yaga shigarta kafin ya lumshe idanunsa a hankali ya bud'e yana shak'ar numfashi then ya juya ya fara tafiya cikin nutsuwa. A yadda Waleed ya wuce ya barta tsaye a gurin ganin tana masa magana bai kula ba,hakan yasa ta sake shak'a,it was there ta yanke shawaran kiran Hjy Sahiba a waya,bayan sun gaisa Hjy Sahiba tace "na ga aikenki,but Waleed ya ce za kiyi min bayani ko?" Mama ta sauke wani numfashi tace "yeah! Later my friend,yanzun dai akwai maganar da na kira muyi" Hjy Sahiba tasa serious tace "wane magana ne?" Mama tace "a zahirin gaskiya yau na turo Waleed gidan ki ne for nothing other than suga juna da Afiyah,idan zai yuwu mu had'a su aure.." Hjy Sahiba ta gyad'a kai tace "wow that's very good.. Amma gaskita aminiya kinyi tunani mai kyau" Hjy Asama'u tace "fatan dai baku mata miji ba" da sauri Hjy Sahiba tace "ko anyi mata ma ai sai mu fasa tunda ga na gida yana nema,wanda zai rik'e mana ita da mutunci fiye da na waje,dama ai a rashin wanda ka sani za ka bawa bare yarka" Mama ta ji dad'i sosai tace "na gode sosai aminiya,but ki fara tuntub'ar Afiyah kiji idan babu matsala,nan dai ta b'angaren mu babu ko wane irin matsala gaskiya" Hjy Sahiba tace "alright! Zan tambayeta naji zuwa gobe duk abunda ake ciki i'll let u know" suka yi sallama. Almost 3 days da yin maganar Mama ta samu tabbaci kan Afiyah ba ta da ko tsayayyen saurayi,and tun ranar da su Waleed suka je gidan ma take damun Mummy'nta da zancensa,here ta mayar da hankali wajen tursasa Waleed ya tsayar mata magana d'aya because tana son tunkarar Abba da zancen,amma sai hanya² yake mata,ba ya son ko had'uwa ma suyi da ita bare dogon magana ya had'a su,idan ya zama lallai sai sun had'u kuwa gaisuwa ne shima yana tafiya yake gaisar da ita ba ya bari magana yayi tsayi tsakaninsu,yau kam da suka yi magana da Hjy Sahiba har ta tura mata digit d'in Waleed da Afiyah ta dameta ta nema mata,Mama ta tura sai dariya take yi tace "Sahibatiiy anya Afiyah bata zurma da yawa ba?" Hjy Sahiba sai dariya take itama cikin jin dad'i tace "wallahi fa kema kya fad'a,nima nan tsiyar da nake mata kenan kullum ba ta da magana sai na Waleed" Mama cikin jin dad'i tace "banda abun Afiyah idan ta yi hak'uri kwana nawa ne maye ya yi amarya ya lashe? Kin san dai baza mu saka tsababan kwanaki ba,so nake ayi abun nan a wuce gurin.." Hjy Sahiba tace "gaskiya kam,gara ayi a wuce gurin,tunda suka fara nuna rawar k'afa kada suyi abun kunya a gaban idanunmu wata rana.." Hiran da suka dunga yi kenan kafin suka yi sallama suka ajiye wayar. Washe gari Waleed ya fito zai tafi office,duka kwanakin ba ya cikin walwala sosai duk a kan maganar auren da Mama take damunsa da shi danma yana dojewa bani cika tsayawa suyi dogon magana ba,har ya nufi stairs zai sauka ya hango parlon babu kowa,ganin haka ya san akwai dalilin da yasa bata fito ba,here ya koma da baya duk da yadda gabansa yake fad'uwa ya daure ya lek'a bedroom d'inta,a tsaitsaye yana rik'e da k'afarta ya gaisheta yace "Mama na fita office" har ya juya zai rufe mata k'ofar ta kira sunansa,ya waiga ya tsaya rik'e da handle d'in,tace "magana nake son muyi,za ka iya shigowa ciki?" Yace "Mama ina sauri ne an kira ni a hospital" tace "kenan ban isa nayi magana da kai a lokacin da nake so ba?" Yace "not at all" ta daure fuskarta race "to ya ya ake ciki? Za ka shigo ne ko kuwa tafiyar za kayi sai ka ba ni lokacin ganinka?" Komawa yayi cikin kad'an ya cusa hannunsa d'aya cikin aljihunsa yana jira yaji me za tace,tace "maganar yarinyar nan da mukayi 3 days back nake son mu k'are ta yau" da sauri ya d'aga kansa ya kalleta yace "amma Mama think an bar maganar tun ranar fa?" Fuskarta babu alamun wasa tace "ba'a barshi ba" yayi still yana kallonta,tsabar mamakinta yasa shi cewa "to Mama ni yanzu me kike son nace?" Tace "maganar kud'in lefe zan maka dama da kake gudun mu had'u,zan ta jiranka ne kana min hanya²? Na gaji na sanar da Abban ku,yanzu mu suke jira dan tuni sun tsayar da ranar auren one month" kallonta ya dunga yi ya kasa magana,tace "sai ka tura min kud'in through account za mu shiga kasuwa da Hjy Izzatu mu had'a kayan tunda kai ba ka da lokaci" yace "amma Mama na fad'a miki matsalata fa!" Tace "ni yanzu ba maganar matsalarka nake ba,abunda nace maka ka tura min kud'in kaya,ban nemi muyi dogon magana da kai ba" ya gyad'a kai yace "alright! Mama kin fi amincewa ayi auren a haka?" Tace "sure!" Yace "kuma kina sane da matsalar da nake fad'a miki?" A fusace tace "wannan wane irin zancen banza ne kake min shi Waleed? Kullum kaita fad'in matsala²,wane irin matsala kake tare da shi ne kam da ni ban san shi ba?" Wani murmushi yayi mai ciwo yace "Mama wallahi kika bari aka yi auren nan a haka,wata rana sai yarinyar nan ta gudu da k'afarta!" Ta d'aga kai tana kallonsa tace "za ka koreta ne hala?" Ya girgiza kansa had'e da d'aga hannayensa alamun surrender yace "not at all Mama!" Tace "to idan ba haka za kayi ba,me kake nufi?" Numfashi ya sauke ya tafa hannuwansa yace "yeah! Yanzun kika yi magana Mama" ta dunga binsa da kallo tana jira taji me zai ce,yace "Mama kinsan Allah yarinyar nan baza ta iya jurewa zama da ni ba" da sauri Mama tace "za ka dunga yankan naman jikinta ne?" Yace "um'um! I just meant she can't take me" wani kallo ta maka masa tace "goyaka za tana yi ne da kake fad'an haka?" Wani dariya yayi yace "Mama kin fa san maganar da nake,kuma kina sane da cewar na mata yawa" kallonsa ta dunga yi tace "wane iskanci ne haka kake fad'a min Waleed?" Yace "daga ganinta Mama baza ta yi lafiya ba,so ni kuma kinga lafiyayye ne,kayan aikina lafiyar su lou,shi ne kawai bayanin da nake miki" yana fad'ar maganar tamkar ya fusatota ta bud'e masa wuta tana fad'a,ganin haka ya girgiza kansa cike da takaici,ya san baza ta tab'a hak'uri ta bar maganar ba,ko me zai ce mata kuwa,kawai sai ya juya yace "shi kenan Mama zan tura miki idan na je office.. Allah sa hakan shi ne mafi alkhairi." Yana fad'an haka ya fice yana jin ransa duk a jagule,yana k'arasawa office ya mata