yi,ganin bai ce komai ba ta kwace hannunta,ya kalli gate lokaci d'aya ya jawota ya had'ata da jikinsa murya can k'asa yace "toh kiyi hak'uri mu koma dama ai ba gurinta kika zo ba ko?" Ta turo baki ta k'i cewa komai,yayi murmushi yace "baza ki hak'ura ba?" B'ata fuska tayi tace "zagina fa tayi kana ji" ya zaro sexy idanunsa still smiling ya ja hancinta yace "banda sharri fa ni ban ji sanda ta zage ki ba" kwace kanta tayi za ta wuce ya sake rik'ota yace "na fa ce kiyi hak'uri ko?" Ta kallesa fuskarta a d'aure kamar za tayi kuka tace "toh baka gaya mata ni wace ce bane?" Dariya sosai tasa yayi seeing that she looks like Dadda da tana magana,ya rik'o hannunta biyu yace "haba na gaya mata mana,but kiyi hak'uri zan sake gaya mata yanzu,mu koma ciki sai ki had'a maku breakfast d'in da kanki mu rabu da ita ko?" Ta turo baki bata ce komai ba,yana mata murmushi yace "idan mun koma kice ma Hjy kin hak'ura don ta daina mitar nan kin ji?" A hankali tace "toh" Yana kallonta har sanan yace "let's go" daga haka suka koma parlon yana rik'e da hannunta,Dadda kad'ai suka tarar a parlon tana kallon stairs tana cewa "banda Allah ya yi ni d'in mai hak'uri ce ma d'azu fa haka kika fito kika gaida ni a tsaye k'ik'am,yo ko uwarki kya yima haka,kuma dan na yi maki shiru bance komai ba,sannan na maki magana bamu karya ba tsabar k'aryar bala'i kince babu komai a gidan,su wancan kaya na cikin d'akin ajiya da firinji kuma fa? Ke kuma irin zaman da za mu yi dake kenan tun ba'a je ko ina ba?" Waleed da ya shigo ya k'arasa kusa da Dadda yace "haba Hjy kiyi hak'uri mana,Manar d'in ma fa ta hak'ura kike mita kuma" da sauri Dadda ta kalli Manar tace "wai haka?" Manar ta gyad'a mata kai a hankali,Dadda ta wani washe baki tace "alhamdulillahi.. Toh ai sai ka ce mata ta sakko ta had'a mana abun karin kumallo ko? Gaskiya dai Mamman baka yi dacen mata ba,tun ba aje ko ina ba ta fara nuna hali,ko da yake ai dama Asama'u ta nemo maka auren dole sai dai muyi ta hak'uri kuma,idan Allah ya yi mai zama tare da mu ce to,idan kuma tafiya za tayi ni sai na nemo maka wacce za kuyi dai² da kaina.." Kallon Manar Waleed yayi ya mata alamar ta tafi kitchen d'in,ta b'ata rai ta rungume hannuwanta a k'irji tace "kuma ni kad'ai zanje?" Dadda ta kalleta da sauri tace "ina za kije ke kad'ai?" Da sauri Waleed ya nufeta yace "mu je tare to" bata masa musu ba ta nufi kitchen d'in ya bi bayanta,tana shiga ta k'arasa gurin gas da Dadda ta bari a kunne ta d'ora musu Lipton,ya mik'a mata kayan k'amshi tasa,ya juya ya d'ebo potatoes ya zube ya d'au wuk'a zai fere da sauri Manar ta karb'a tace "Yaya kawo nayi kada ka yanke" ya mik'a mata yace "okay! But be careful with the knife" bata ce masa komai ba ta fara fere dankalin,ya tsaya jikin kitchen island yana kallonta,duk wanda ta gama ferewa sai ta sa a ruwan da ya kawo mata cikin bowl,shi dai kallonta kawai yake har ta gama,ta kalleshi tace "ai dai wannan ya ishemu ni da Hjy ko?" Ya zaro ido yace "ni kuma fa?" Ta kallesa da sauri tace "za kaci ne?" Ya gyad'a mata kai,ta tab'e baki tace "to ai dai zai ishemu har kai" ta zuba mai cikin fry pan ta d'auki albasa tana yankawa tana masa surutu,lokaci d'aya ta saki wani k'ara ta jefar da wuk'ar kafin Waleed ya mata magana jini har ya fara fitowa,ya rik'eta da sauri yace "Ya salaam.. Garin ya ya Kika yanke?" Wajen sink ya matsa da ita ya kunna tap ya tsaya bayanta yana wanke mata hannun yana kallon cut d'in da ba wani babba ba,a hankali yace "sorry lil sis" yana gama wanke mata ya juyo da ita,yaga hawaye a idonta,tuni ya rud'e yana tambayarta "yana miki zafi ne?" Jikinsa ta fad'a ta fashe da kuka tana yarfe hannun,a hankali ya d'ago kanta ya kai fingers d'insa ya share mata hawayen yace "sorry" ta wani shagwab'e masa tace "sai dai kayi frying d'in kai kuma ni bazan yi ba" murmushi yayi ya ci gaba da goge mata hawayen a hankali yace "na ji zauna to ki jira na gama" ya d'agata ya d'ora saman kitchen island,ya juya ya kallo man da yayi zafi yace "toh ya za'ayi yanzu?" Wani dariya ta fashe da shi tace "baka sani ba Yaya?" Ya bud'a hannu alamar bai sani ba,ta kallesa tana masa murmushi tace "ka wanke dankalin ya tsane tukun" ya juya da sauri yayi yadda tace,ya sake kallonta yace "sai me?" Dariya ta dunga yi kafin ta gwada masa yadda zaiyi,yana kallonta fuskarsa a d'aure yace "kema fa ba girkin kiki iya ba amma kike min dariya" tayi murmushi tace "kaji Yaya wanda kake sawa nayi maka fa?" Ya tab'e baki yace "ci kawai nake amma ba wani dad'i" zaro idanu tayi tace "haka ma za kace?" Da sauri yace "nope! Ba haka nake son cewa ba,sub'utar baki nayi" ta gyad'a kai tace "gobe ma ai rana ce" yayi dariya daga haka ya koma gurin fry pan d'in albasan har ya yi ja,ya kwashe ya zuba dankali ciki,tana zaune tana kallonsa idan yayi ba dai² ba tace ba haka ba,a haka har ya gama ya juya zai ajiye bowl d'in a sink,ta kallesa tace "saura eggs to" ya zaro ido yace "idan ya k'one fa?" Tayi dariya tace "i'll help bazai k'one ba" yayi murmushi a hankali yace "okay" ya d'ebo eggs cikin few minutes yayi chopping onion ya soya musu,duk tana zaune tana kallonsa tana masa dariya,yana gamawa ya juyo yana mata murmushi yace "yeah! I can cook now ba tare da an koya min ba" dariya ta dunga yi tace "kai Yaya it's just potatoes fa and egg kad'ai kayi kake wani zuzutawa" ya cire apron d'in data d'aura masa ya k'arasa inda take ya jingina kusa da ita a hankali yace "I'm happy! U teach me how to cook something" ita dai bata ce komai ba sai dariyar da take masa,a hankali ya sauke numfashi yana shak'ar k'amshinta mai dad'i,jikinsa a mugun mace saboda closeness da suka samu yaji ya fara saukar masa kasala da sauri ya d'an yi taking steps d'insa backward yace "sakko ki je parlor zan kawo breakfast d'in yanzu" ta gyad'a masa kai tace "sauke ni to" yana sauketa k'asa ta nufi k'ofa ya bita da kallo har ta fita,ya dauk'i flask d'in ruwan zafin ya d'aukar musu cups da spoon ya fita parlon,ya ganta ita kad'ai ya kalleta yace "Hjy fa?" Tace "tana salatudh-dhuha" yayi murmushi yana kallo agogo ganin 11am ya ajiye flask d'in hannunsa,then ya koma ya d'auko plate d'in dankalin ya ajiye,ya d'aga kansa ya kalli stairs kafin ya tashi ya nufi sama Manar ta bisa da kallo ta tab'e baki ta d'auke kai,Afiyah tana d'akinta tana waya da Mummy'nta ta sanar mata duk abunda ya faru tun zuwan su Dadda gidan,ran Hjy Sahiba a b'ace tace "dama na san wata rana sai anyi haka,banda kin dage tun farkon sai shi Allah na tuba me za kiyi da irin Hjy Asama'u,ni da ita fa kar ta san kar ne,ke kuma kika ce atafau sai shi kin samu miji,but don't worry wannan ai mai sauk'i ne,ni na san ta yadda zan b'illowa al'amarin,ki kwantar da hankalinki sai kace ba ni na haife ki ba,yadda nake zaune gidan ubanki hankali kwance ba damuwar kowa haka ke ma za ki zauna gidan nan,idan kinga kin fito sai dai gawarki wallahi" Afiyah tayi wani murmushin jin dad'i tace "that's how my Mummy is.. Allah k'ara maki lafiya" Hjy Sahiba tace "ko shi Waleed d'in yazo maki da zancensu kada ki nuna masa komai,ki sharesa kawai har ita yarinyar da ta so take miki rashin kunyar,tunda kin san ta hanyar da aka bi aka yi auren,ki nutsu ki bari har ya gama zuwa hannunki sai ki horasa yadda ya dace.. kinji ko" Afiyah ta gyad'a kai tace "to Mummy" Hjy Sahiba tace "ki kwantar da hankalinki kinji,babu mai saka miki ciwon kai a gidan aurenki,nan gaba zuwa gidanma duk sai yafi k'arfin danginsa in dai ina numfashi cikin duniyar.. Maganar kayan da nace zan bayar a kawo maki suna hanya.." Ji tayi ana tab'a k'ofa da sauri ta d'aga kai ta kalli gurin tace "Mummy za muyi waya anjima" bata jira cewar Mummy'n tata ba ta katse wayar,ta kwanta da sauri ta juya baya,Waleed ya shigo ya zauna gefen gadon yace "tashi ki zauna magana nazo muyi dake" ganin ta k'i tashi ya gyad'a kai yace "ko da baza kice komai ba i know kina jina,so u have to keep this in ur mind,u don't need to worry about what happened between ke da Hjy,that's how my grandma is,idan aka mata abu babu ruwanta da ko kai waye har su Abba bata bari ba sai dai idan basu yi abunda za tayi magana ba,Manar kuma she have no problem apart kawai ba ku fahimci juna bane,but she's very nice and sweet to stay with,ko a gida Hjy ba ta son a tab'a ta,ba ni ba ko waye ma,ranan za'aga other side of her because takwararta ce,besides kuma just few hours za su yi su tafi.." Ita dai bata kulasa ba,ya gaji da sauraren tayi magana ya tashi yace "idan kin gama fushin ki sakko downstairs muyi breakfast" wani juyowa tayi da sauri ta kallesa a fusace tace "bazan ci ba" ya d'age shoulder yace "okay" bai sake bin takanta ba ya juya ya koma downstairs,tun daga nesa yake kallon Manar da ta wani had'e rai har ya shigo parlon yace "baza ki sakko ki had'a shayin ba?" Kamar jira take yayi magana ta zumb'uro baki tace "ni na k'oshi" yayi shiru yana kallonta,can ya k'arasa kusa da ita yace "me yasa baza ki ci ba?" K'in cewa komai tayi,yayi murmushi ya zauna kusa da ita,ta d'auke kanta za ta mik'e ya rik'ota,ta fara k'ok'arin k'wacewa tana cewa "nifa na ce maka ba zan ci ba.." Muryar Dadda suka jiyo tana sakin salati tace "meye haka Kuma nake gani ni jikar laraba?" Saurin sakar mata hannu Waleed yayi,da sauri Dadda ta zauna kan kujera tana kallonsa tace "Anya lafiyarka lao kuwa Mamman kake matse y'ar mutane haka?" Ta gefen ido ya kalleta,Dadda ta juya ta kalli Manar tace "me kika masa?" Fuskarta a d'aure tace "Hjy nifa ba abunda na masa,kawai cewa nayi na k'oshi shi ne wai dole sai na ci" Dadda ta bud'e ido tace "iiiihhh! Kamar ya kin k'oshi kuma haka babu dad'in ji,uban me kika ci?" Ta kalli Waleed da ya musu banza tace "ko ta ci kafin na fito?" Ya tab'e baki yace "a'a" Dadda tace "to kuma shi ne dan munafurci za tace ta k'oshi,bata fa karya ba muka fito.. To ai shi kenan,ni dai rabu da ita ka had'a min shayin" murmushi yayi ya gama had'a ma Dadda shayi ya ajiye a gabanta ya d'auki plate d'in dankalin ya ajiye mata ta zauna k'asa tace "kai dai Allah sa ka gama da duniya lafiya,Allah kuma ya maka albarka ya baka masu maka kaima" yayi murmushi yana satar kallon Manar data d'auke kai tak'i kulasu yace "ameen Hjy" tare suka yi breakfast da Dadda kafin ya tashi ya wuce sama,Manar sai kallonsa take tana ganin ya mik'e ya nufi sama ta d'auke plate d'in da sauri ta gudu kitchen,Dadda ta d'aga kai tana kallonta tace "kuga munafuka da kika ce ba kya ci kuma" bata kulata ba ita dai ta shige ta tsaya jikin kitchen island sai da ta cinye kafin ta dawo parlon ta tattare sauran plate da cups d'in ta kai kitchen ta had'a duk abunda suka b'ata ta wanke,ta mayar da komai gurinsa ta goge kitchen d'in har wall then ta fito,ganin Dadda ba ta nan ta share parlon ta gyarasa shima ta goge ta kunna turare,kafin kace me k'amshi ya cika parlon,Dadda dai tun da cikinta ya d'auka ta shige wani d'aki ta kwanta sai bacci kamar tana gida. Wajen 12 Waleed ya sakko parlon cikin k'ananun kaya da suka mugun karb'arsa,ya dunga kallon Manar dake danna wayarta,yana tsaye kusa da ita yace "Hjy fa?" Ba tare da ta kallesa ba tace "think bacci take" ya gyad'a kai bai ce komai ba ya zauna gefenta,jin footsteps a stairs suka juya tare suka kalli Afiyah dake sakkowa kamar tana tausayin k'asa,fuskarta babu walwala har ta k'arasa sakkowa,tunda suka had'a ido da Manar sau d'aya ta d'aure fuska,itama Afiyah haka tayi tana jin wani tsanar Manar dake taso mata ta wuce su ta shiga kitchen tana sak'e². Da kallo suka bita dukansu,Manar ta tab'e baki ta d'auke kai,Waleed ya kalleta a hankali yace "kun rage wani abu ne?" Ta kallesa tana d'aure fuskarta tace "a'a" yayi shiru yana tunani kafin ya mik'e yabi bayanta,Manar ta bisa da kallo tana murmushin mugunta,yana zuwa ya ganta tsaye ta gama dubawa bata ga abunda suka dafa ba ko kayan da suka b'ata ma bata gani ba,tayi shiru tana tunanin ya za tayi dan wani muguwar yunwa ke cinta,shisa ta sakko babu shiri,yanzun kuma da kunya ta tambayesa breakfast tunda ya mata magana ita tace baza ta ci ba,ya shiga yana kallonta yace "za ki yi girkin ne?" Da sauri ta kallesa tace "wane girki?" Yace "i mean lunch" wani kallo ta dunga masa kafin tace "me zai hana kace ta maku" ya kalleta yace "me yasa ke baza kiyi ba?" Strictly tace "ka ga Waleed ban iya ba,and ko a gidanmu ba ni ke yi ba,maids suke mana komai.. Sannan gaskiya bazai yiwu yarinyar nan tana zuwa min gida ba,daga yau ka fad'a mata kada ta k'ara tako min cikin gida,i'm sorry to say but i dislike ur sis,na tsaneta wallahi with all my heart" kallonta Waleed ya dunga yi da wani expression,fuska a d'aure yace "u are looking into my face and telling me u hate my blood? Meye matsalarki da ita? Let me tell u this ba ki isa ki hana 'yan uwana zuwa gida na ba tunda ba gidan ki bane.. And duk ma yadda za kiyi kiyi ki girka musu lunch" a mugun fusace tace "It's better kai da ka damu suci ka tsaya ka girka musu ko kasa blood d'in taka ta girka,amma wallahi ni bazan yi ba dan banma tab'a yi ba" tana kai wa nan ta fice d'aga kitchen d'in a fusace ta koma sama,Waleed dake tsaye gurin da ta barsa ya fesar da wani hucin iska trying hard to control his temper ya gyad'a kai yace "i've got to screwup that soon" daga haka ya fice daga kitchen d'in,yana fita ya kalli Manar dake zaune har sannan idanunta a kan TV ya koma ya zauna kusa da ita yana calming kansa,sanda ya dai² ta nutsuwarsa yayi lowering voice d'insa a hankali yace "za ki mana lunch?" Ta girgirza masa kai tace "sai dai kayi kai" yana kallon eyeballs d'inta yace "will u teach me?" Ta gyad'a masa kai,yayi mata murmushi yace "okay! Sai anjima sai muje ko?" Ta gyad'a masa kai,ranar a gidan suka wuni sai after maghreb ya d'aukesu ya mayar da su gida,Dadda dai har suka zo gida bata bar mitar matarsa ta yi musu wulak'anci ba,yana ta ba ta hak'uri,yana yin parking ta fice daga motar da sauri fuska d'aure tana ci gaba da mitar ta..
#Asli Smasher.
[2/4, 5:28 PM] My number 1: 26...
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*
Kwantar da kansa yayi jikin kujeran yana kallon Manar,a hankali yace "yaushe za kizo hutun?" Ta kallesa da sauri tace "waye zaizo hutu?" Yace "ke mana ko kin fasa?" Da sauri ta gyad'a masa kai tace "tabb' d'i yauma kana ganin yanda na wuni bare naje hutu gidanka?" Yace "idan kinje sai ki dunga rakani office" murmushi tayi tace "ni dai a'a ba sai na je ba" yace "why?" Tace "Yaya kana kallo fa matar ka ba ta so na" yace "kema ai kin fad'a min bakya sonta" ta d'aure fuskarta tace "to dama why would i love her? Baka ga irin kallon da take min bama" ya dunga kallonta yana sakin murmushi a hankali yace "so yanzun kin fasa zuwa kenan?" Ta gyad'a masa kai tace "yeah! Idan ka zo gida ai za ka ganni" yace "to girki fa waye zaina min?" Kallon idonsa tayi yanda yayi kamar wani maraya tace "ga matarka nan" yace "bata iya ba wai" dariya ta dunga masa tace "sai ka d'auko muku maids suna yi" ya girgirza kansa yace "ba na son abincin maids" tace "to sai na wa kake so?" Wani kallo yake mata k'asa² a hankali yace "na ki nake so" tayi murmushi tace "to ai idan ka zo zan dunga yi maka" ya lumshe idanunsa a hankali yace "nope! Sai dai ki dawo gida na kina yi min" tace "tabb' ni dai ba zan je ba,ni fa daga yau bazan k'ara zuwa ba ma" kallonta ya dunga yi a hankali yace "saboda me?" Tace "matar ka" tana fad'an haka ta bud'e motar za ta fita yace "wait.." ta juya tana kallonsa tace "what?" Ya sauke wani ajiyar zuciya a hankali yace "I love u" dariya tayi sosai tace "love u too Yayana" murmushin jin dad'i yayi yace "really?" Ta gyad'a masa kai,yana kallon eyeballs d'inta yace "will u marry me?" Zaro ido tayi tace "Yaya.." ya rik'o hannunta da sauri yace "shhhiii.. Tell me please za ki iya aure na?" Girgirza masa kai tayi alamun a'a,yace "why not?" Tace "kai ai Yaya na ne,besides kuma ni Yaya Azaan nake so.." Bai bari ta kai k'arshe ba yace