"yeah! I knew shi kike so,but what about me? Ba kya so na baza ki iya aure na ba?" Rau² idanunta suka yi,muryarta yana cracking tace "kai fa Yaya na ne" yace "shi Yaya ba'a aurensa?" Ta gyad'a masa kai da sauri tace "ehh" murmushin takaici yayi yace "alright! Je ki gida za mu k'arasa maganar a waya" tace "toh" ta fita motar ta rufe masa,yana kallonta jikinsa a mugun sanyaye yace "bye" ta d'aga masa hannu ta wuce part d'in Dadda,yana tsaye sai da yaga shigarta gidan then ya juya kan motarsa ya bar gidan. Sanda ta shiga gidan da Dadda ta fara had'uwa tsaye a parlor,tayi sallama za ta wuce Dadda ta bita da ido tace "ina kuma kika tsaya ina ta tsumanki?" Tace "Yaya ne ya tsayar da ni" Dadda tayi mitsi² da ido tana kallonta tace "ince dai bai maki komai ba?" Manar ta kalleta tace "kamar ya?" Dadda tace "ina nufin bai matseki irin na d'azu a gidansa ba?" Wani kallo ta mata ta wuce d'aki k'asa² tace "me yasa baki tsaya kin gani ba za kina tambayata" tayi shigewarta tana turo baki,kayanta ta fara ragewa ta d'aura towel ta shiga wanka,tun tana ciki take jin ring d'in wayarta,sanda ta gama ta fito ta d'auki wayar tana dubawa,taga mafi yawan kiran ma Waleed ne sai na Azaan,tayi murmushi kafin ta fara kiran Waleed,yana ganin call d'inta ya katse ya kirata video dan gaba d'aya kalamanta sun sanyayar masa da jiki,kiran yana connecting yayi ajiyar zuciya a hankali yana kallonta yace "thought kiran nawa ma baza'a k'ara d'auka ba" tace "why not?" Yace "na sani tunda ance ba'a so na hakan yasa an yanke hukuncin dai na min magana" murmushi tayi kawai bata amsa ba,yana kallonta yace "wanka kika yi ne?" Ta kalli jikinta a hankali ta gyad'a masa kai tace "ehh" yace "okay! Bari na kyaleki ki shirya ko?" A hankali tace "toh" yana mata wani kallo yace "za ki min flash idan kin gama?" Tace "ehh" yace "okay! Thanks" suna ajiye wayar kiran Azaan yana sake shigowa,ta d'auka da sauri tace "Yaya!" Yace "My Guddi! How are u?" Tayi ajiyar zuciya tace "i'm fine,u?" Yace "alhamdulillah! But not feeling good" a rikice tace "Yaya me yake damunka?" A hankali yace "kece kike damuna" tace "ni kuma?" Yace "sure" kamar za tayi kuka tace "ni to me nayi maka?" Yace "kin hana zuciyana nutsuwa" wani ajiyar zuciya tayi tace "thought ma wani abun za kace na yi maka" yace "shi wannan ba wani abu bane?" Tace "ehh" yace "really?" Tace "yeah" yace "ke dai kika d'auka haka" tace "ai kowa ma haka zai d'auka" wani murmushi yayi yace "okay! Let's back to serious" tace "uhn" yace "Mujse shaadi karoge? (Will u marry me?)" Da wani irin zumud'i tace "yes³" yayi murmushi yace "really?" Tace "absolutely sure" yace "thank u Guddi,saboda amsan da kika ba ni yanzun nan har na ji ina son zuwa Nigeria na ganki" tace "nima haka" yace "okay! Ki kwanta kiyi bacci,da safe za muyi waya" tace "toh" yace "goodnight love" tace "goodnight.." Tun suna waya kiran Waleed yake shigowa,tana k'ok'arin ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa ta d'auka kafin ma tayi magana yace "thank u!" Fad'uwa gabanta yayi tace "me nayi Yaya?" A fusace yace "meye ne ma baki yi ba,saboda kin raina ni ni zan dunga kiraki k'i d'aukan wayana,ko da yake kina waya da wanda kike so ya za'ayi ki saurare ni" yadda yake mata magana cikin fad'a nan da nan hawaye suka kawo idonta,bai saurareta ba yace "shi kenan kiyi yadda kike so zan kyaleki.. Dama na takura maki ko?" Ta girgirza masa kai kamar tana gabansa,kafin tayi magana yace "thank u.. Goodnight" tana shirin yi masa magana k'it ya katse wayarsa,tun daga ranar ko a mafarki bai k'ara kiranta ba,idan ya shigo gidan ma ba ya yarda ta gansa,duk hanyar da yasan zai had'asu duka ya toshe su,ko gaishe da Dadda idan zai zo sai ya daidaici lokacin da ba ta nan zai shigo,kafin ta dawo ya fice abunsa,tun abun bai damunta har dai ta fara shiga damuwa,idan ta kirasa a waya ba ta samunsa yanzun,ko chat ma bata ganinsa,haka nan idan ta tura masa sak'o zai nuna mata ya tafi amma ba ta gane ya gani ko bai gani ba. Shi kam a nasa b'angaren yana sane yayi mata hakan,dan ya gwadata yaga da gasken ba ta sonsa ko kuwa dai fad'a masa hakan kawai take yi,duk hanyar da yasan zai had'a su gaba d'aya ya rufeta,ba iya chat da ya danna mata block ba,hatta contact d'inta ya sa number ta blacklist,shisa ko ta kirasa ba ta samu,text ne kad'ai idan ta masa via inbox ko tayi mailing nasa yana ganin wannan but ba ya tsayawa ba ta amsa,ana cikin hakan tafiya ya taso masa zuwa India zai je wani course,ranar da zai tafi ya zo gidan suka yi sallama da mutanen gidan a lokacin suna skul,ya gama abunda zai yi Amaar ya kaisu airport shi da Afiyah,though bai yi niyyar zuwa ko ina da ita ba,Mama ta takura masa lallai sai ya tafi da ita tunda ba kwana kusa zai dawo ba,haka nan babu yadda zai yi ya shirya musu tafiya tare,daga bayan ne Manar ta samu labarin ba ya nan,tayi kuka sosai lokacin ta shiga damuwa dan har wani k'aramar jinya tayi,bayan nan kuma ta share komai ta ci gaba da harkokin gabanta,shi kam Waleed sanda suka sauka India a New Delhi suka ya da zango,da suka yi waya da Mommella yake sanar mata suna k'asar ta so sun sauka gurinta so sai akayi rashin sa'a kuma tsakaninsu akwai d'an nisa,hakan yasa dole suka nemi matsuguni nan tunda ita tana yankin vishakpatnam ne,but lokaci² yana Yana zuwa ya kai mata ziyara. Some years later aka fara shirye²n saukan su Manar had'e da graduations d'insu,during this period soyayya mai zafi suke yi da Azaan amma ta waya,gaba d'aya yanzun ba sosai yake zuwa ba,dan kusan tun bayan tafiyar Waleed bai fi sau biyu yazo ba,ta rasa me yasa sai dai suyi chat ko waya ma yanzun sai su d'auki tsayin lokaci basu ji muryar juna ba,while a gefe d'aya kullum zancensa shi dai ji yake kamar ya jawo kwanakin da suka yi saura,though bai fi 3 month ya rage su fara exam d'in waec ba,idan sako zai bayar a kawo mata kuwa dama ta hannun Amaar yake zuwa gareta,ranan wata Sunday ya kama saura sati biyu saukarsu,ranan kuma ya kama 2 and ½ years da tafiyar Waleed India wanda ake saka ran dawowarsa cikin satin,around 4pm suka sauka Nigeria,Amaar kad'ai ya sanar ma yace kada ya fad'awa kowa suna hanya,Amaar ya tura driver yaje d'auko su a airport ya masa gargad'in kada ya fad'awa kowa,ba tare da ya fad'a ba ya d'auki mota ya nufi airport,sanda motar su ya shigo gidan,uban sun lace ne jikin Afiyah sai mayafi da ta sak'ale a wuya hannunta rik'e da handbag sai takalmi mai tsini da ta sa,ta yi kyau har ta gaji,sai k'amshi take bazawa Kamar dai ba itace idan kaje d'akinta za ka gansa kaca² ba,fuskar nan nata ya sha make-up har ba a cewa komai,motar yana yin parking Waleed dake sanye da 3 piece men's suit kalar green mai duhu ya fito,part d'insu ya nufa direct tana biye da shi a baya,su a shiga da ihu Deejah da Diyanah suka tare su,suka yi welcoming d'inta da fara'a ta amsa masu da siririyar muryarta tana murmushi,Ameerah dake shigowa lokacin ta gaishesu ta tafi sama ta kira Aunty,Aunty na sakkowa tace "a'a su Aunty amarya ne a k'asar namu,sannu da zuwa" Afiyah ta kalleta tace "yauwa.." Aunty ta zauna tace "fatan kun dawo lafiya? " Afiyah tace "lafiya lau,ya gida?" Aunty tace "Alhamdulillah,ya hanya?" Afiyah tace "lafiya lau" Aunty tace "maa sha Allah.." Waleed dai sai kallon Afiyah yake jin bata gaisheta ba,bai ce komai ba ya kalli Aunty yace "Abba fa?" Aunty tace "tun safe ya fita" ya mik'e yace "okay! Bari mu gaida Hjy" Aunty tace "toh sai kun dawo" yace "Daddy fa ya dawo?" Aunty tace "a'a bai dawo ba" k'ofa ya nufa Afiyah ta mik'e ta bi bayansa,Aunty ta bi ta da kallo har suka fita,ta girgirza kai ta mik'e ta tafi ta ci gaba da abunda take,suna fita Waleed ya kalleta fuskarsa a d'aure yace "abunda kika yi kin kyauta kenan? She's my Mom too amma ki kasa gaishe ta?" Tsayawa tayi tana kallonsa with suspicion tace "me nayi kuma?" Yace "did u greet her?" A fusace tace "kai komai mutum yayi sai ka yi k'orafi,ba sai kayi correcting d'ina ba cikin lalama,gaba sai na gyara,amma ka fara min fad'a daga zuwanmu" juyawa kawai yayi ba tare da ya ce mata komai ba ya ci gaba da tafiya ta bisa a baya tana tab'e baki,part d'in su Manar taga zai shiga ta masa wani kallo ta tsaya tace "nan ne part d'in Hjyr?" Ya juya ya mata wani kallo yace "part d'in uncle d'ina" bai jira cewarta ba ya shiga parlon da sallama,d'an tsaki tayi kafin ta shiga,Mother tana zaune a parlon tana ganinsu tayi musu sannu da zuwa da fara'arta,Waleed ya zauna ya gaisheta ta amsa tace "sannun ku da zuwa" Afiyah dai kallo d'aya tayi ma Mother ta wani d'aure fuska tana kallon TV,Mother ma tun da ta kalleta sau d'aya taga ba ta da niyyar gaisheta bata sake kallonta ba,ta tafi kitchen tana cewa "bari in kawo muku ruwa" wani kallo Waleed ya dunga yima Afiyah da ta bud'e jaka ta d'auko phone tana operating,murya can k'asa yace "did u greet her?" Tayi masa banza tana danne²nta,Mother ta fito ta ajiye musu ruwa da drink saman couch dake kusa da shi,yana k'irk'iran murmushi yace "Mother daga gida fa muke" ta zauna saman kujeran da ta tashi before then tace "drink d'in kawai?" Ta d'auki bottle d'aya ta bud'e ta tsiyaya masa cikin cup,ya d'auka ya sha yace "Daddy yana Lagos ne?" Mother tace "a'a yana Abuja yanzun" yace "alright! Za mu je gaida Hjy" tace "toh sai kun fito,na gode k'warai" mik'ewa yayi ya nufi k'ofa Afiyah tabi bayansa,mother ta bi ta da kallo,sai da suka fita balcony ya juya yana kallonta kafin yayi magana,ta wucesa da sauri tana d'aure fuska,ya gyad'a kansa ya nufi hanyar part d'in Dadda,Dadda tana share parlonta taji footsteps ta d'aga kai tana kallonsa tace "waye wannan kuma?" Bai tanka ta ba ya cire takalminsa ya shiga parlon,Afiyah tana k'irk'irar murmushi tace "sannu da aiki Hjy,shara kike yi ne?" Dadda tace "wallahi fa wannan yaran suka shigo min suka b'ata,suka fice suka barni kuma" Afiyah tayi murmushi tace "kawo na taya ki" Dadda tace "a'a bar shi kiyi wucewar ki ciki,daga zuwa kuma sai ki hau shara?" Afiyah tace "don Allah ki kawo na k'arasa miki" mik'a mata tsintsiyar Dadda tayi ta karb'i jakar hannunta da mayafi tace "ai kuwa na gode,dama dan dai wancan matar tana kwance d'aki ne na san da tuni ta sharesa tsaf,to tun jiya take fad'amin ba ta jin dad'i,ashe kuwa da gaske take na d'auka ma wasa take min sai d'azun kawai ciwon ya kwantar da ita,dad'in ta ma na san abunda ke damunta,shi sa ban wani tada hankalina ba,Allah dai ya yaye mata wannan bala'a'en ciwon mara,abu dai yak'i ci yak'i cinyewa shekara da shekaru sai fama take.." Kallonta Waleed ya dunga yi kafin ya kalli k'ofar d'akin da yake tsammanin tana ciki ba tare da ya ce komai ba,Afiyah ta gama share parlon ta kwashe dattin da parker ta mik'e tana murmushi tana kallon Dadda tace "ina zan zubar da sharan?" Dadda tace "kina fita akwai kwandon shara yana nan za ki gansa daga gefe" Afiyah tana fita daga parlon Waleed ya kalli Dadda yace "me ya sameta?" Dadda dake k'ok'arin zaunawa tace "wai Manar?" Yace "ehhh" tace "to hailarta ne dai ina jin zai zo,idan ba haka ba dama me zaisa ta ciwo ita kuwa,ai lafiyayya Maryam ta haifeta dama,d'azu ta gama sharb'an kukanta a nan,babu inda bata zagaya ba a gidan nan,to nace ta tafi gidansu ko uwarta za ta kaita kyamis ta k'i ya zanyi da ita?" Mik'ewa yayi da sauri,Dadda tace "ka rufa min asiri kar kaje ka tasheta na samu ta yi bacci da kyar,d'azu wannan d'an albarkan dake neman aurenta ya aiko d'an fodiyo da wani likita ya dubata ya taho da magunguna da allurai.." Tsayawa Waleed yayi yana kallonta,Afiyah ta shigo parlon ta zauna k'asan rug tace "ina wuni Hjy?" Dadda tana murmushi tace "lafiya lau 'yar nan,ya hanya kuma? Kin dai yi kyau wallahi,zama wancan k'asa na su Hafsatu ya karb'eku,ince dai ko har kin samo mana tsaraban ciki a can ba'ayi zuwan banza ba?" Sunkuyar da kai Afiyah tayi tana ta k'irk'irar murmushin k'arfin hali kirjinta sai dukan you take yi,Waleed zai shiga d'akin da Manar take Dadda tayi saurin kallonsa tace "yau na bonu ni jikar laraba,ai fa Allah kuma ya dawo da kai,yanzu zan shiga uku da yawan sa ni magana.. Waleed na ce kar kaje ka tasheta,wallahi alluran da aka mata yasa ta samu bacci,ya zan yi da raina idan ka tasheta yanzu fisabilillahi?" Bai tsaya saurarenta ba ya shiga d'akin,Afiyah ta kalli Dadda da sauri tace "waye ba lafiya?" Dadda tace "wallahi Manar ce,kamar bazata yi rai ba d'azu,na ce kar yaje ya tasheta amma ya k'i saurarata,jibi dai duk ya rikice daga zancen Manar babu lafiya.." Mik'ewa Afiyah tayi da sauri tace "Ya salaam.. Bari naje na dubata" daga haka tabi bayansa zuwa cikin d'akin,sanda ya shiga tsayawa kawai yayi akan Manar dake bacci yana kallonta,yanda ta k'ara girma jikinta ko ina was full da kayan alatu har wani special ajiyar zuciya yake saukewa yana k'are mata kallo,bacci take sosai kamar babu abunda yake damunta,ta yi wani fresh ga kyaun da ta k'ara da d'an k'ibar da tayi kad'an,ya zauna gefenta a kan gadon idanunsa akanta,then ya kai hannunsa forehead d'inta yana kallon fuskarta,ta bud'e idonta a hankali ta sauke su kansa,lokaci d'aya gabanta yayi mugun fad'uwa ta dunga kallonsa tana ganin kamar cikin nightmares da ya saba mata gizo ne,zai yi magana Afiyah ta shigo d'akin kamar an cillota,ganinsa kusa da Manar ta rik'e kugu tana kallonsu,Manar tana ganinta ta zaro ido it was there ta tabbatar ba mafarkin da ta saba yi bane,Waleed ya yi mamakin ganin Afiyah ta biyosa but bai nuna mata komai ba ya d'auke kansa daga kallonta,Manar tayi sauri ta mik'e zaune ta d'aure fuskarta tana tab'a mararta da taji ya d'aure,Waleed yana kallonta murya can k'asa yace "wane maganin kika sha?" Medications d'in da Amaar ya shigo mata da su bayan Dr ya dubata ya tafi ta nuna masa,ya d'auko ledan ya ciro drugs d'in yana kallonta yace "waye ya kawo miki?" Shiru tayi ta k'i cewa komai,ya had'e rai yace "i'm asking u" ta turo baki ta koma ta kwanta,Afiyah dai sai kallonsu take rik'e da kugu,Dadda ma ta biyo bayansu har d'akin tana kallon Afiyah tace "Safiyah kike ko?" Afiyah tayi murmushi tace "a'a Afiyah ne Hjy" Dadda ta kyab'e baki tace "to koma dai wa kike,ke kuwa idan kin dubata ai sai ki d'an koma daga parlor ki jira su gama,ko kuma kije gurin Asama'u ya sameki a can" Afiyah dai bata ce komai ba sai murmushin yak'en da take yi tana sunkuyar da kai,kamar an tambayeta Dadda tace "ai babu wani abu dake jikin Manar wanda Mamman bai sani ba in fad'a maki,yanda kika san y'ar uwarta mace haka ta d'aukesa tun tana mitsitsiyarta,ko ina ne taji ciwo kwailayewa take ta nuna masa ba ta jin kunyarsa ko d'is.." Juyawa Afiyah tayi saurin yi ta nufi k'ofa ta fice saboda wani bak'in cikin da maganar Dadda ya saukar mata,Dadda ta bi bayanta tana waigen Manar tace "sannu Manar.. Tunda Allah ya sa ga Mamman nan ya zo sai ki zage ki nuna masa inda ke maki ciwon,karki b'oye ki sanar masa kinji ya duba ki tsaf.. Nan da anjima sai kiga kinyi ras kamar baki tab'a ciwon ba,kinga dai yanzu ba gidan yake ba,kada sai ya tafi ciwon ya dawo maki mu rasa yanda za muyi kuma" d'an murmushi Waleed yayi har Dadda ta fita,can ya d'aure fuskarsa yana kallon Manar yace "kiran saurayin naki kika yi kika ce masa baki da lafiya ko me?" Kamar za ta yi kuka tace "nifa ban kirasa ba Yaya" fuskarsa a d'aure yace "toh wa ya kirasa?" A hankali tace "kira na yayi a waya bai sameni ba shi ne ya kira Ameerah" yana mata wani kallo yace "k'arya kike idan baki ce ta kirasa ta fad'a masa ba za ta kirasa?" Kamar za tayi kuka tace "nifa Yaya ba ni da lafiya lokacin ban san me tace ba" ya k'ara had'e rai yace "shine sai tace masa kina period ko?" Zaro ido tayi tace "Yaya ni fa ban ce ta fad'a ba Hjy ce ta fad'a masa nima kuma sai da naji kunya da tace haka" tana magana tana turo baki,yace "wa yayi miki alluran kuma?" Tayi shiru ta k'i cewa komai,ya mata tsawa yace "answer me now" turo baki tayi tace "Dr da suka zo tare da Yaa Amaar ne yayi min" kallon ta ya dunga yi yana jin zuciyarsa tana masa zafi,a hankali ta d'ago tana kallonsa,ganin yanda ya d'aure fuska ba shiri ta sake shiga nutsuwarta,strictly yace "shi k'aton kika bud'e ma jikinki ya miki allura yana kallon ki?" Dariya maganarsa ya ba ta sai dai babu halin yi,tana komawa baya a hankali tace "nifa ban bud'e masa ba a haka nace yayi min akan skirt d'ina,kuma bari ma kagani har jini ya b'atan pant" tana fad'in haka ta janye skirt d'in jikinta a hankali tana nuna masa saman buttocks d'inta,a hankali ya sauke idonsa yana kallon fresh skin d'in bayanta,lokaci d'aya yaji ransa yayi wani mugun b'aci zuciyarsa tana tafarfasa,tayi murmushi ta rufe gurin tace "ka gani ko?" Fuskarsa a tamke yace "when za ku fara exams?" Ta bud'a manyan idanunta tace "remain 3 months fa" yace "good ana gama saukan ku dama kice za kije gidana kiyi