Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   4 / 66

9K to 12K   out of 196.2K words

taron dangi ba ehee,itama tana da wanda za su shigar mata" wani kallo Diyanah ta watsa mata tace "matsa kafin na bigeki" Ameerah ta fashe da dariya tace "wa za ki bige? Ai sai dai mu buge juna" Diyanah tace "dallah malama matsa!" Da karfi ta tura Ameerah saura k'iris ta fad'i tayi sauri ta rik'e pillar,ranta a mugun b'ace tana d'agowa ta fizgo Diyanah,a fusace Diyanah ta kaiwa ameerah mari tayi sauri ta goce bata sameta ba,kafin ta sauke hannunta k'asa Ameerah ta kai mata nata marin ji kake tass,gaba d'aya suka tsaya kamar wad'anda aka dannama pause har su Manar da suke kokawa,a fusace Diyanah ta k'unduma zagi "kan uba! Ni kika mara?" Ameerah tace "an mareki d'in ko an fad'a miki tsoronki ake ji?" Gadan² Diyanah tayi kanta za ta cakumota,Deejah ma ta yo kanta ita mai y'ar uwa za su mata taron dangi,Manar ta fizgota tana haki tace "ina za ki ai bamu gama ba" tana fad'a tana kai mata duka,nan kokawa ya kacame tsakaninsu,Deejah da Diyanah sai zage² suke su kuma su Manar sai jibgarsu suke suna haki. Cikin shirin tafiya masjeed Waleed ya bud'e k'ofar zai fito,kokawan da yaga suna yi yasa shi tsayawa ya zuba musu ido yak'i cewa komai,babu wanda ta kula da tsaiwarsa sai nishi suke suna dukan juna,can da yaga abun nasu ba mai k'arewa bane ya musu tsawa,gaba d'aya suka saki juna kowacce ta koma gefe suna mayar da numfashi,ya dunga binsu da mugun kallo kafin yace "ku mahaukatan ina ne daga dawowarku za ku fara ma mutane dambe a gida? Filin wrestling kuka samu?" Kawunansu Deejah a k'asa suka fara bashi hak'uri,wani tsawa ya watsa musu yace "be quite! Did i insist anyone to talk?" Manar ta tab'e baki ta d'auke kai,Waleed dake kallonsu fuskarsa babu wadataccen fara'a yace "i just gave u an hour kuje duk abunda za kuyi ku gama before,idan na dawo ban tarar da ku a nan ba jikinku duk sai ya gaya muku.." Yana fad'a ya wuce zai bar gurin,da sauri Manar ta juya za ta taci itama,Ameerah tayi saurin rik'o hannunta tace "don't go Sis! Allah Yaya zai miki babu dad'i" fizge hnnunta tayi tace "ku dai da kuke jin tsoro sai ku tsaya" wani juyowa yayi ya kalleta ba tare da ya ce mata k'ala ba ya gyad'a kai ya wuce parking space,Ameerah ta sake rik'ota tace "kinga kallon da ya mana ko? Let's go" Deejah da ba da ita Ameerah take ba a fusace tace "ke ma ki rabu da ita taje mana idan tana ganin zai kyaleta" wani kallo Manar ta mata tace "hala dukan da na miki bai isheki ba?" A tsiwace Deejah tace "to ko za ki k'ara dukana ne?" Manar tace "kiyi min abunda zan dakeki kiga idan ban fasa miki jiki ba" matsowa gaban Manar ta fara tana rik'e waistband d'inta,a tsiwace tace "ga ni ai ki dake ni kiga idan zan kyaleki" da sauri Diyanah ta rik'o hannunta k'asa² tace "muje Yaya yana kallonki" saurin waigawa tayi ta hangosa zaune cikin mota ya zubo musu idanunsa,da sauri ta juya tayi k'wafa k'asa² tace "next time,we'll meet!" Suka shige ciki da sauri,tab'e baki Ameerah tayi ta juyo ta kalli Manar tace "let's go sis! Ai ko yanzu jikinsu ya fad'a musu" wani murmushi Manar tayi suka shiga gidan tare. After an sakko masjeed motar Waleed ya shigo gidan,tun daga nesa ya hangosu a gurin su uku suna kneel down ya gyad'a kai ya samu guri yayi parking ya fito ya rufe motar,yana k'arasowa gurin ya kalli Ameerah yace "where's *MANAR?"* In'ina ta fara tana son kare Manar,da sauri Deejah tayi zaraf tace "Yaya! Bata zo ba mu kad'ai muke yi tun d'azun" wani kallo ya aika mata yace "who asked u?" Sauke kanta k'asa tayi tace "i'm sorry" ya aika mata wani kallo yace "idan na sake magana ba dake nake ba kika sa min baki saina fasa miki jiki.. Stupid girl" ya juya yana k'ok'arin barin gurin yace "je ki kiramin ita" Ameerah ta tashi da kyar k'afafunta duk sunyi tsami ta nufi hanyar part d'in Dadda,a parlor ta tarar da Dadda zaune ta zubawa TV idanu ba ta ko gane me ake cewa,ta shiga tana tambayarta Manar,Dadda ta juyo ta kalleta ta d'auke kai tace "tana mad'bak!" Da sauri Ameerah ta nufi hanyar kitchen d'in,a door way ta tsaya tana kallonta tace "Sis ki zo inji Yaya" juyowa Manar tayi saurin yi ta kalleta,tana squeezing fuskarta tace "me zan masa kuma?" Ameerah tace "ya dawo bai ganki ba a gurin shi ne yace na kira ki" rau² idanunta suka yi,da muryar kuka tace "kiyi tafiyarki dama ni kada ki tsaya jira na" Ameerah ta bud'a idanu tace "Yaya ne fa yake kiranki" Manar tace "ni dai bazan je ba,dama kice baki ganni ba" Ameerah tace "kizo muje kada ki k'arawa kanki laifi please" a fusace Manar ta juyo hawaye kwance cikin idanunta tace "na ce miki ki tafi ko?" Dadda ta jiyo su tace "me yake faruwa?" Manar ta lek'o daga kitchen tana share hawaye tace "wai Yaya ne yace ta kira ni" Dadda tace "akan wane dalilin zaisa a kira ki?" Ameerah tace "d'azu ne ya ganmu muna kokawa da su Deejah shi ne yace muyi kneel down kafin ya dawo daga masjeed" tab'e baki Dadda tayi tace "meye kuma nil doo?" Ameerah ta fashe da dariya tace "kneel down fa aka ce" Dadda tayi mitsi² da ido tana kallonta tace "ohoo! Muku ku kuka san shi,ni da ban yi boko ba,ai ba rubutawa aka yi dole sai na fad'a dai² ba" Ameerah ta dunga dariya,Dadda ta d'auke kai ta ci gaba da kallonta,sanda tayi mai isarta tana kallon Manar dake b'are garlic za tasa a farfesun da ta d'ora tace "ni dai Allah da za ki ji ki zo muje kawai" tsuke fuska Dadda tayi a fusace ta juyo tace "kije kice masa na hanata zuwa" Ameerah ta gwalo ido tace "Dadda ki bari mu tafi,Allah idan ya kamata ko?" A fusace Dadda tace "idan ya kamata ya zare mata rai,kije ki ce masa ni na hanata zuwa,na ce baza ta zo ba d'in" jikin Ameerah a sanyaye ta juya ta fita daga part d'in,a hanya suka had'u da Waleed,tun daga nesa ta hango irin kallon da yake mata,tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa bakinta har b'ari yake tana fad'a masa sak'on Dadda,k'ala bai ce mata ba ya wuce ta,yana shiga yaga Dadda ita kad'ai ya had'e rai yace "ina wannan yarinyar take?" Dadda tayi kamar bata jisa ba ta kafe TV da ido,gyad'a kai yayi har ya juya zai fita ya jiyo motsi a kitchen,fasawa yayi ya nufi hanyar da yake jin motsinta,cikin d'aga murya Dadda tace "me za kaje yi nan kuma?" Bai tankata ba ya shige,Manar dake tsaye wajen sink tana wanke naman da za ta d'ora a wuta ta juyo da sauri jin k'amshin scent's d'insa yana kusantota,ido biyu suka yi da shi yana shigowa,ya mayar da k'ofar ga rufe saboda Dadda da ta biyosa fuskarsa a d'aure yana aika mata wani kallo yace "har ni zan aiko kiranki kik'i zuwa? Ke har kin isa? Nawa kike?" Baya tayi da sauri ta jingina da cabinet idanunta sunyi rau² tace "Yaya ni fa ban ce mata bazan zo ba" wani tsawa ya mata,Dadda dake waje ta fara buga k'ofar tana kiransa "Mamman! Yalla iftahal baab" banza da ita yayi kamar bai san me take cewa ba,ya zuba idanunsa da suka yi jaa akan Manar dake zumb'uro baki yace "idan baki ce baza ki ba,ai kina da wanda za ta hana ki zuwa right?" Shiru tayi bata ce komai ba,Dadda sai buga k'ofa take tana kiransa ya k'i bud'ewa,cikin jin haushi tace "idan baka bud'e ba billahillaziiy zan kira ubanka na sanar masa,ni ban san wane irin jaraba ne yake damunka ba da ranar Allah ka shige ka kulle k'ofa me za ka yiwa y'ar mutane? Ni dai gaskiya ka fito kafin na tara maka jama'ah,tun wuri ka bud'e min k'ofar nan na shigo kada ka cuceni ina tsaye sake da baki a nan" wani b'acin rai Waleed ya dunga jin kalaman Dadda suna saukar masa,a mugun fusace ya dunga kallon Manar bai iya ce mata komai ba ya bud'e k'ofar da sauri Dadda ta fad'o kitchen d'in kamar an cillota,k'arasawa inda Manar take tayi da sauri ta rik'o hannunta tana dudduba jikinta tana tambayarta "babu dai abunda ya miki ko?" Manar ta d'ago ta kalleshi bata ce komai ba,Dadda ta ci gaba da duba jikinta tana sake tambayarta "ince dai bai miki komai ba da ya rufe k'ofar ko?" Nan ma shiru tayi babu amsa,jan hannunta Dadda tayi za su fita,Waleed yayi saurin fizgo Manar a tsorace ta fasa k'ara,Dadda ta juyo a fusace tana fad'in "ni dai yau na shiga uku da wannan mutumi,kai wai dan Allah ba ka da aikin yi sai na zuwa ka sani magana ne?" Idanunsa sun k'ank'ance yana mata wani kallo cike da b'acin rai yace "me kike nufi? Me maganganunki suke nufin zanyi mata?" Mitsi² tayi da idanu tace "kaga Mamman ka fita idona na rufe,zan maka wulak'anci a gidan nan" gyad'a kai yayi yace "tambayar ki nake me kike nufi da maganganun da kika fad'a?" A fusace tace "ban sani ba ubana,sai ka matse baki na sai na fad'a maka" wani yawun b'acin rai ya dunga had'iyewa ya kalleta ya kalli Manar ya kasa sake cewa komai da sauri ya juya zai fita,Dadda cikin d'aga murya tace "kuma dama zan sanar da uban naka abunda ya faru,idan ma baza su d'auki mataki ba ni zan d'auka.. Ni tun kana tsummanka na san ba k'aramin jarababbe za'ayi ba,yadda kake rik'e jelarka kana soshe²,banda kukan tsiya da kake damun mutane da shi,ai ko yanzun ma Allah ne ya rufa mana asiri na shiga na fita sai da na samo maka maganin k'aik'ayin nan sannan muka huta da masifar kukanka,yanzun ka zama mutum shi ne za ka saka min da rashin kunya da d'iban albarka.." Yana jinta bai tsaya mata magana ba ya fice daga part d'in gaba d'aya,zuciyarsa banda tafasa babu abunda take,ko ganin inda yake sa k'afarsa baya yi,daf zai shiga part d'in suka bangaji juna da Amaar,ya wuce bai ce masa k'ala ba,Amaar ya bisa da kallo har ya shige mamakin abunda yake faruwa da Waleed yasa kai tsaye daga nan bai zarce ko ina ba sai part d'in Dadda,a yadda yaga fuskarsa ya san b'acin ransa bazai rasa nasaba da can ba,tun daga bakin k'ofar shiga part d'in ya fara jiyo fad'anta cikin hayaniya,ya k'arasa da sallama still bata fasa masifa ba a hakan kuma ta amsa sallamar ta ci gaba da fad'anta,Manar dake kitchen har sannan ta fito tana b'ata rai tace "dan Allah mu dai kin ishemu haka nan,sai mita kike tayi bayan shi ya ma tafi" kallonta Amaar yayi saurin yi yace "me yake faruwa?" Kai tayi saurin girgiza masa alamun bata sani ba za ta juya,yace "k'arya kike" ta zumb'uro masa baki da sauri ta shige kitchen d'in,wucewa yayi zai bita kitchen d'in cikin sauri Dadda ta katse mitar da take tace "ina za ka kai kuma?" Amaar ya tsaya yana kallonta yace "dalilin fad'an ki nake son sani,and na ga Waleed yanzu a hanya ransa kamar a b'ace" kyab'e baki tayi tace "ai bama kamar,ni ce nan na b'ato masa rai" Amaar ya bud'a idanu yace "akan me? Wani abu yayi miki?" Tsaf ta kwashe komai ta sanar masa,shi kansa kallonta kawai ya dunga yi cike da takaici ya kasa cewa komai,kalmomin da ta sanar masa ta fad'awa Waleed babu wanda ya dace ace ita ta fad'a,idan akwai mutum d'aya da zai fara fad'an halayen Waleed tabbas zai kasance ita ce,saboda ta fi kowa sanin wane ne Waleed a duka gidan kasancewarsa rainonta,shi kansa da ba shi ta fad'awa maganar ba,abun ya mugun tab'asa bare Waleed,da ya sansa da bak'ar zuciya,abu kad'an yake fusatasa,ba wai dan Waleed yana stepbrother d'insa ba but kyawawan halayensa kad'ai sun wuce a jefesa da irin maganar,ba tare da ya iya ce mata komai ba ya juya ya fita daga part d'in dan bai ga amfanin zamansa ba ko sake yin magana da grandma d'in nasu..

#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2020.


                    *♡MANAR¸.•💥*
               

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA  

_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._


                                04.


#Holding his hand..

       
        Da dare lokacin Manar tana parlor tare da Ameerah suna kallo Amaar ya shigo fuskarsa babu fara'a,a tare suka masa sannu da zuwa,bai kallesu ba ya amsa ya ciro wayarsa ya fara making call,wayar yana shiga aka katse aka kirasa video call,d'auka yayi saurin yi yayi sallama,muryar mace ce ta amsa shi,da sauri Manar ta kalli direction d'insa,idanunsa akanta shima yana kallonta har suka gama gaisawa,tana jin sanda matar tace "kana tare da su ne yanzun?" Ya gyad'a kai yace "sure!" Tace "where's my kid? Ba ni ita!" Kallon Manar yayi kafin yace "she's right here tana jinki ma" Da hannu ya yiwa Manar alama tazo,ta taso da sauri ta k'araso inda yake,ya mik'a mata wayar yace "Ga Mommella za kuyi magana" murmushi tayi cikin zumud'i ta karb'i wayar ta tashi daga kusa da shi,hak'oranta a waje tsabar murna tayi sallama,kyakykyawar matar da ta bayyana screen d'in wayar k'irar Apple (IPhone 11 Pro) sai murmushi take yi ta amsa sallamar da tayi mata,bayan sun gaisa cikin tsananin farin ciki tana kallon Manar tace "Baby! Haka kika zama? Me kike ci? Me Hjy take ba-ki kika yi girma haka sosai?" Dariya tayi cike da jin kunya ta b'oye fuskarta tace "Mommella! Yaushe za kuzo?" Wani murmushi Mommella tayi tace "muna nan a hanya in sha Allah" ta gyad'a kai tace "Allah kawo ku lafiya.." Mommella dai sai kallonta take yi cike da mamakin girman da ta k'ara yi cikin y'an shekarun da basa k'asar tace "baki tambayi bhai d'inki ba?" Murmushi tayi tak'i cewa komai,Mommella ta zaro idanu tace "Ohh! Baki damu da tambayarsa ba ko? Shi kenan zan fad'a masa nace ko tambayarsa baki yi ba" saurin girgiza kai tayi tana dariya tace "a'a Mommella!" Mommella tace "haka ne mana" girgiza kai ta sake yi za tayi magana ta jiyo wani sanyayyan murya yana fad'in "nima na yi fushi.. Mommella ki fad'a mata ko na je Nigeria ba zan kulata ba!" Dariya ta fara tace "a'a kayi hak'uri!" Tana jiyosa yace "na k'i wayon" dariya ta dunga yi,yace "u see dariya ma kike yi? Kinga baki damu ba kenan ko?" Tana dariya tace "a'a na damu mana!" Yace "baki damu ba baby.." tace "da gaske na damu" yace "ban yarda ba,da kin damu da tuni kin kira kiji lafiya na ko ki tambayi Mommella ina nake" wani irin b'ata rai tayi kamar za ta fashe da kuka a shagwab'e tace "ai to ba ni da waya ni" yace "u most be jocking.. Kamar ki ace ba-ki da waya?" Tace "da gaske fa nake yi,ka tambayi Mommella ma kaji" saurin bayyana kansa yayi a fuskar wayar,kyakykyawan matashi ajin farko,fuskarsa tana bayyanar da wani sihirtaccen murmushi yana kallonta yace "ya akayi babu phone a hannunki?" Tana tab'e baki  tace "nima ban sani ba" shiru ya d'an yi kamar yana tunani then yace "any ways.. Amma dai kin ganki fa kin zama k'atuwa,yanzu ai ke za kina goyani ki ramamin goya kin da nayi sanda muke 9ja ko?" Wani kunya taji da sauri ta b'oye fuskarta ta kyalkyale da dariya tace "ai ka fini girma,ni bazan iya goya ka ba" murmushi yayi yace "raguwa kawai,ni zan goyaki idan na zo" gwalo idanu tayi tace "ina da nauyi fa" yace "duk nauyin ki zan goya ki,kin manta lokacin da muke nan?" Rufe fuskarta ta sake yi tana dariya tace "kai dai Yaa *AZAAN* ba ka mantuwa" yace "ya za'ayi na manta? Bayan ba wasu shekaru ne da yawa ba" sun jima suna hira kafin suka yi sallama,za ta katse kiran Azaan yace "but ban tambayeki ba?" Tace "me za ka tambaya?" Yace "phone d'in waye wannan?" Tayi squeezing fuskarta tace "a ina?" Yace "i mean wanda yake hannunki" d'an murmushi tayi tace "na Yaa Amaar ne" murmushi yayi shima yace "yana ina?" D'agowa tayi ta kallesa kafin tace "gashi a zaune" da sauri Azaan yace "ba-ni shi muyi magana" gyad'a kai tayi ta tashi ta kaiwa Amaar wayar,yana karb'a ya mik'e ya nufi hanyar fita. Almost one week da zuwansu tun ranar da suka yi fad'a da su Deejah Manar bata sake sa Waleed a idanunta ba,ko apartment d'insu taje ba ta ganinsa,Dadda kanta tun ranar bata kuma ganin ya shigo mata ba,da farko ta yi tunanin ko ba ya nan ma,sanda ta tambayi Amaar ko Waleed ya yi tafiya ne bai mata sallama ba? Ya kalleta yace "yana nan babu inda yaje" mamaki yasa Dadda tace "yana gari amma ba ya zuwa gaishe ni?" Amaar yace "a'a! Kefa kika koresa kika ce ya daina zuwa" gwalo idanu tayi tace "ni azumi? Kada ka min sharri da raina,ta ina zance ya daina zuwa bayan duk cikin jikokinta na fi sonsa" wani kallo Amaar ya mata yace "to ni dai ya fad'a min ke kika ce ya daina zuwa.." Rau² tayi kamar za tayi kuka tace "Wane irin laifi na masa ni kuwa da zamu kwana gida d'aya mu tashi bai zai zo ya gaishe ni ba,sai kace muna gab da juna?" Amaar ya dunga kallonta kamar zai yi dariya,ya mik'e da sauri yace "a'a nima dai ban sani ba,sai dai kije kiyi bikonsa kyaji daga bakinsa" yana fad'a ya kama hanyar fita zai bar apartment d'in,Dadda tayi shiru ta kasa masa magana har ya fita,har dare maganar bai bar damunta ba,lokacin Manar ta shigo daga apartment d'in mother ta d'ago ta bita da kallo har ta zauna kan kujera,kamar ance ta kalli Dadda taga ta yi fuskar kuka,dariya ta fara yi k'asa²,Dadda ta kasa daurewa ta mik'e da sauri Manar

4 / 66