nemi kulleni ni ba matar limami ba" bud'a idanuwa Waleed yayi yana kallonta yace "really?" Ta gyad'a masa kai tace "tabbas" ya gyad'a kai yace "okay! U can go,but let me tell u this,billah idan kika sake k'afarki ya taka wani waje without na amince daga can inda kika je ki wuce gidanku and don't even think zan biyo ki.." Saurin kallonsa tayi tace "me kake nufi?" A fusace yace "abunda duk kwakwalwarki ya fahimtar dake" Afiyah ta mik'e tsaye cike da tsageranci tace "wallahi baka isa ka hanani zuwa inda nake so ba" ya gyad'a kai fuskarsa a d'aure yace "okay! Let's see.. Tsakanin ni ko ke muga wanda ya isa" da sauri ta fice a fusace ta nufi d'akin Mama kamar za ta tashi,ta tura k'ofar da k'arfi ta tsaya door way sai huci take,a tare Hjy Izzatu da Mama suka kalleta suna had'a baki suka ce "lafiya?" Afiya ta fashe da wani kuka kamar dama jira take wani ya tanka mata tace "ki kirasa ki masa magana don idan har ban fita ba yau shirin da muke yi ne zai ruguje" Mama ta zaro idanu tace "wani abu yace?" Afiyah ta sanar mata yadda suka yi da shi,cikin b'acin rai Mama ta gyad'a kai tace "kyaleni da shi kawai,na san yanda zan masa,dan na ga take²nsa halinsa na da yake k'ok'arin dawowa da shi" daga haka ta tashi ta fita d'akin,Afiya tana ta zaune har bayan minti talatin ganin Mama bata dawo ba har sannan ta mik'e ta bi bayanta,ta samesu Mama sai balbalin fad'a take masa,Afiyah na shigowa ya d'ago fuskarsa d'aure zai yi magana Mama ta hanasa,dole yayi shiru har dai ta gama ta fita,ya dunga mata wani kallo yace "kina tunanin fad'an da kika sa mahaifiyata tayi min zai sa na barki ki fita?" Ta nufesa tace "wai me ke damun ka ne Waleed,ni dai na san lafiyar ka k'alau ka tafi.." Ko kallonta bai yi ba ya tattara kan phones d'insa zai fita,da sauri ta fad'a jikinsa ta baya tana shafa chest d'insa cike da shagwab'a tace "ni dai wallahi ka gaya min meye laifina,kawai daga zuwanka ka fara min hayaniya" bata jira cewarsa ba ta juyo da shi ta rungumesa gam tana k'ara shige masa,lokaci d'aya tayi turning him on. Sanda yayi mata laga² ya huce haushinsa a kanta,ya sauka gadon ya wuce bathroom ya tsarkake kansa,ya fito ya sameta tana waya tana jin motsinsa tace "I'm coming fa yanzun bari nayi wanka na zo" tayi saurin ajiye wayar ta wuce bathroom,yana kwance idanunsa a rufe ta fito ta gama shiryawa,ta k'arasa kusa da shi ta zauna gefensa tana tab'asa a hankali tace "Dear zanje Mama suna jirana za mu wuce" calmly ba tare da ya bud'e idanunsa ba yace "i said u are going no where ko?" Ta zaro ido tana kallonsa da mamaki don duk tunaninta ya hak'ura,ta d'an marairaice tace "haba dear,ba fa dad'ewa za.." Da sauri ya katse ta ya mik'e zaune fuska a d'aure yace "i'm telling u this wallahi idan kika fita gidan nan yau za kiga the other side of me" yana fad'in haka ya mik'e ya fice,ta bisa da kallo zuciyarta sai tafarfasa take,can ta mik'e ta fice daga d'akin ranta a mugun b'ace taje ta sanar da Mama tace "ya fa k'i bari na biku Hjy,taurin kan Waleed da kafewan da yake kan abu wallahi ni dai tsoro yake bani" da mamaki Mama tace "ya k'i bari ki kifita kuma?" Afiyah tace "ehh" Mama ta gyad'a kai tace "yana ina?" Afiyah tace "ya fita fa" Mama ta gyad'a kai ta fara kiransa a waya,cikin takaici ta sauke wayar tana kallonsu tace "toh ai wayar tasa a kashe yake" Afiyah tace "yanzu ya za muyi to?" Mama tace "ina ga mu bari anjima idan an fara tafiya gurin bikin sai mu fita" Afiyah ta tab'e baki bata ce komai ba..
#Asli Smasher.
[2/17, 10:01 PM] My number 1: 35...
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*
Har ya fita da niyyar barin gidan because bai jin zai iya zama ransa yana b'aci,ko me ya tuna kuma ya dawo,da sassarfa ya haura saman ya nufi d'akin Mama ya kai hannu zai knocking k'ofar,ya jiyo maganar da suke tattaunawa kan fitar da suka shirya,ransa ba k'aramin b'aci yayi ba instead of ya shiga kamar yadda yayi niyya kawai sai ya juya ya fita. After maghreb lokacin motoci suka fara tafiya gurin dinner,Waleed dake zaune cikin line a motarsa yana jiran ganin fitowar su Mama,ya yi shiru yana tunanin wane irin unguwa ne wannan za suje,can yana ta sak'e² yaga motar Afiyah ta fito daga gidan,ya bi motar da kallo har ta kusa fita line kafin ya juya kan motarsa yayi following na su,sun yi tafiya mai nisan gaske sai da suka kusa fita daga Kano kafin suka tsaya bakin wani jeji,Waleed da ya kashe fitilun motarsa yayi parking can nesa da su yana hango sanda suka fito suka rufe motar after sun kunna fitulun wayoyinsu suka fara haska hanya,Afiyah a forefront sai Mama da Hjy Izzatu suna binta a baya,Waleed ya zuba musu idanuwansa yana tunanin me za su shiga yi cikin surk'uk'in jejin da ko shi namiji akace ya shiga zai ji shakku bare su mata,bai gama tsinkewa da lamarinsu ba sai da ya fito ya bi bayansu yaga sai tafiya suke suna k'ara nausawa cikin jejin,sunyi tafiya sosai kafin suka tsaya gaban wani k'aton dutse,yana tsaye cikin duhuwa yaga suna haurawa saman dutsen,sanda ya daina ganinsu kafin ya juya ya fita daga jejin zuciyarsa cike da rud'ani da tarin tambayoyi,ya koma motarsa ya zauna yayi shiru yana jira yaga fitowarsu. Mama da Hjy Izzatu sai Afiyah zaune gaban wani bukka babu kowa sai su kad'ai,kamar daga sama mutumin ya bayyana gabansu,Mama da Hjy Izzatu suka rik'e juna cikin mahaukacin tsoro but da suka ga Afiyah ta dake suma dole suka ari jarumta,zuciyoyinsu suna dokawa bila adadin,Mama cikin rawar jiki za ta fara masa bayanin abunda ke tafe da su Afiyah ta kalleta tace "kiyi shiru ba sai kin wahalar da kanki ba ya san komai" Mama ta kalleta ba don ta yarda ba tace "ya za'ayi ya sani bayan bamu fad'a masa ba?" Afiyah tayi wani murmushi tace "ni nake fad'a miki fa,let's see ke dai za kiyi mamaki" Mama dai duk a tsorace take da lamarin tana jira taji daga bokan nasu,cikin wani kakkaurar murya mai cike da rashin dad'in sauraro ya fara rattabo musu bayanan kaf abunda ke tafe da su,da irin fad'i tashin da suka yi a baya,guraren da suka je neman taimako kaf sai da ya zayyane musu,Mama ta kalli Hjy Izzatu,itama ta kalli Mama cike da tsoro,boka ya bushe da dariya da muryarsa mara dad'in ji yace "yanzu me kuke so ayi muku?" Mama tace "auren ne kawai muke so a fasa idan zai yiwu,sannan ita yarinyar.." Kafin ta k'arasa ya dakatar da ita,Mama sai raba idanu take zuciyarta tana bugawa cike da tsoron kada dai shima yace auren bazai fasu ba,tana cikin tunanin ya miko mata wani k'aho yace "ki tattara buk'atunki kaf ki fad'esu cikin wannan k'ahon za'a biya miki su.. Tun da kika zo nan kin zo intaha,idan kinga buk'atunki basu biya ba,sai dai idan ke kika so.." Jikin Mama har b'ari yake tace "ai ba ma zan so ba" cikin azama ta karb'i k'aho ta kai bakinta,duk mugun nufinta da k'udurinta towards Manar da Mother sanda ta fad'e su kaf,kafin ta mik'a ma bokan,ya karb'a ya gama surutan da zai yi,su dai babu wanda ta san me yake cewa dan wani irin yare yake irin na arnan da suke zama saman dutse,after then yace za su iya tafiya,aikinsu su zuba idanu kawai zuwa nan da kwanaki biyu za suga abunda zai faru,za su masa godiya Afiyah ta kwab'e su suka tashi bayan sun ajiye masa kud'ad'e masu nauyi suka sakko daga dutsen,suna tafiya suna k'ara tattauna matsalar dake gabansu,daga nan direct sanda suka shigo cikin gari wajen dinner suka wuce lokacin har an kusa tashi,suka shiga suka zauna suna kallon mother da Manar dake cikin shigar alfarma,purple d'in lace ne jikinta da ya amsa sunansa,head da komai dake jikinta purple ne ta yi kyau ba kad'an ba,su dai tun zamansu gurin dariya kawai suke saboda sun fi kowa sanin sharrin da suka k'ullo,har sanda aka tashi gurin suka nufi gida suna k'ara tattaunawa. A kusa da motar Waleed dake nan a parking space motarsu ta tsaya,Afiyah ta fito cikin motar tana sakin murmushin kissa ta nufesa, Waleed da bai jima da shigowa gidan ba ya d'auke kansa kamar bai gansu ba zai wuce,da d'an gudunta ta bisa a baya tana kwalo masa kira "D" ya waigo a d'an dake ya kalleta yace "daga ina kike?" Tayi murmushi tace "gurin dinner muka je fa" ya gyad'a kai yace "k'arfe nawa kuka je?" Tace "emmhh! Think wuraren 9pm" yana kallonta da kyau yace "tun yaushe kuma kuka fita daga gidan?" Yadda yake mata magana fuskarsa babu alamun dariya,sai da taji gabanta ya yi mugun fad'uwa da tambayar da ya mata,ta daure though bakinta yana sark'ewa tace "bamu fita da wuri ba ai" wani kallo ya dunga mata cike da tuhuma,sanda ya gama k'are mata kallo yace "really?" Ta gyad'a masa kai a sanyaye,gyad'a kai shima yayi yace "kun fita wuraren 7pm,ina kuka je?" Tayi tsilli² da idanuwa tana in'ina,ya mata tsawa yace "speak well ki bar min in'ina" ta marairaice tace "believe me D" ya d'aure fuskarsa yace "didn't i tell u kada ki fita?" Tace "but munje bikin k'anwarkace fa" yace "okay! Yanzun kuma sai ki juya ki koma gidanku" ta dunga kallonsa tace "D.." A tsawace yace "don't call me,cewa nayi ki wuce ki tafi gidan ku" hankalinta ba k'aramin tashi yayi ba,ta marairaice za ta fara masa magiya ya k'ara mata wani tsawan da sai da tayi baya,she thought ma duka zai kai mata,yana zaro mata idanuwansa yace "i said ki wuce ki bar gidan nan,kada ki bari nayi loosing mind, because zan iya yanke wrong decision akanki.. Maza b'ace min daga gani.." Ya k'are maganar yana nuna mata hanyar get,kuka ta fashe masa da shi tana k'ok'arin rik'esa,ransa a mugun b'ace ya cire hannunsa ya wanka mata marin da sai da taga gilmawar taurarin azaba,a tsawace yace "get lost.." A b'angaren Mother kuwa haka nan tun yammacin ranan take jin gabanta yana fad'uwa,al'amarin bai k'ara tsananta ba sai da suna wajen dinner bikin,sanda kanta yayi mugun sarawa,ta dafe da sauri tana ambato sunayen Allah,Aunty da Mommella da suke tare a table d'aya suka kalleta,Mommella tace "sister ya dai?" Mother ta d'ago idanuwanta da suka fara juyewa saboda sarawan da kanta yayi tace "wallahi i don't really know me yake faruwa da ni,tun d'azun nake ji gabana yana fad'uwa,yanzun haka kuma kaina nake ji yana min ciwo" Aunty ta girgiza kai tace "sannu dear,but ko dai za mu wuce gida?" Mother ta girgiza kai tace "noo! Ina ga ba sai anyi haka ba,minti nawa ya rage a tashi duka" ba do sun so ba suka hak'ura har dai aka tashi,lokacin suna tafiya tayi shiru idanuwanta a rufe,bayan sun dawo gida lokacin tayi musu sallama ta wuce apartment d'inta,tana shiga taga Manar kwance kan kujera head d'inta da komai zube a k'asa tana rik'e da kanta,har mother ta k'arasa shigowa bata sani ba sai da tayi mata magana tace "daughter! What wrong with u?" Manar ta d'ago da kyar ta kalli mother tace "kaina ke ciwo,and tun d'azu a gurin dinner gabana yake fad'uwa" mother ta dunga kallonta cike da tausayi tace "eyyah! Sannu.. Tashi maza kije ki cire kayan,kiyi wanka sai kiyi alwala kiyi nafila ki kwanta?" Ta gyad'a kai a hankali ta tashi jiri ya fara d'aukanta,da sauri ta dafa kujera za ta zauna Mother tace "lafiya?" Ta kulle idanunta a hankali hawaye suna gangarowa fuskarta tace "jiri nake gani mother" mother tace "sannu toh.. ko na taimaka miki?" Ta girgiza mata kai a sanyaye tana share hawaye tace "a'a zan iya" daga haka ta wuce tana tafiya slowly,mother ta bita da kallo cike da tausayi. Tana zaune d'akinta bayan ta fito wanka sun gama waya da Azaan kenan ta shimfid'a pray mat,tayi sallah raka'a biyu ta d'au Qur'an d'inta ta bud'e za ta fara karantawa,aka bud'e k'ofar d'akin mother ta shigo jikinta a mugun sanyaye,ta d'aga kai tana kallonta,mother ta zauna gefenta tace "kinyi sallar ne?" tace "ehh na yi,zan yi karatu ne ma" mother ta gyad'a kai tace "but kin ci abinci kuwa?" Tayi shiru ta kasa amsawa,mother tace "tunda kika yi shiru baki ci ba kenan ko?" Ta gyad'a mata kai a sanyaye hawaye suka kawowa idanunta,Mother ta tashi za ta fita,har ta kai k'ofa ta waigo tace "kina ji na Manar?" Manar dake kallon mahaifiyarta tace "ehh mother ina ji" Mother tace "zan kawo maki abinci yanzu,ki daure ko kad'an kici,zaman da kika yi da yunwa shi yasa kike jin jiri,and ki dage da addu'ah sosai kuma a ko da yaushe,na san kina tashi da daddare kiyi sallah,so no need na zo tashinki tunda already kina yi,amma ki k'ara dagewa kinji? Babu wanda yake samun abunda yake so cikin sauk'i.." 'Dan murmushin jin dad'i tayi tace "in sha Allah zan yi yanda kika ce Mother" mother tace "Good!" Daga haka ta fita d'akin,Manar ta fara rera k'ira'anta cikin cool voice d'inta,ba'a jima sosai da fitar mother ba ta kawo mata abinci ta ajiye mata then ta mata sallama ta fita. Bayan ta gama karatun ta ci abinci ta fito b'angaren dan yadda take jin baza ta iya kwana ita kad'ai ba,a hanya tana tafiya b'angaren Dadda suka had'u da Waleed,ta zaro idanu tana kallonsa tace "Yaya baka tafi ba?" Ya sauke numfashi a sanyaye yana mata wani kallo yace "yeah! Nan zan kwana" tayi d'an dariya tace "alright! Sai da safe" har ta juya za ta tafi ya rik'o hannunta ya juyo da ita,ta d'ago idanunta da sauri tana kallonsa suka had'a ido,ya jinginar da ita jikin bango ya d'ago kanta yana kallon k'wayar idonta,kallonsa itama ta dunga yi,muryarsa a sanyaye ya kira sunanta "Manar!" Da sauri ta kallesa jin yanda ya kirata,yace "da gaske aure za kiyi?" Kasa amsa masa tayi,ya d'an kalleta kad'an jin bata ce komai ba,ya k'ara kiran sunanta,kamar za tayi kuka tace "ehhh!" Bai iya cewa komai ba sai kallonta yake,jin shirun ya yi yawa ta d'aga kai ta kallesa suka sake had'a ido,ta wara masa manyan idanunta tace "Yaya ba ka da lafiya ne?" Yace "me kika ga?" Cike da damuwa tace "u look pale,what's wrong with u?" Kamar bazai fad'a mata ba sai kuma dai a hankali yace "surely akwai abubuwan da suke shirin faruwa that will cause me alot of harms,and that will be the end of my happiness.." Wani mugun damuwa taji ya saukar mata,hankalinta a tashe tace "what's that Yaya? Tell me please" yayi shiru ya kasa cewa komai,da sauri ta rik'o hannunsa idanuwanta cike taf da hawaye tace "Yaya don Allah ka gaya min mene ne ka ji" kasa cewa komai yayi ya runtse idanuwansa da sauri yana jin bugun zuciyarsa da ya canja,Manar na ganin haka ta fad'a jikinsa ta fashe da kuka mai tab'a zuciya,ya kasa cewa komai though har zuciyarsa yake jin kukanta ya dai kasa cewa tayi shiru,sanda tayi mai isarta ta d'ago ta kallesa tace "Yaya ka gaya min please" murmushin k'arfin hali yayi mata,ya jinginar da kansa a bango yana kallonta ta gefen ido,tace "ina ji,tell me what's it?" Jawota yayi jikinsa murya can k'asa yace "forget about it" tace "me yasa?" Yace "it's too late" kallonsa ta dunga yi kamar za ta fashe da sabon kuka tace "kamar ya it's too late? Ka san baza ka fad'a ba kasa ni tsaiwa?" Da wani murya yace "i'm so sorry.. But.." Kafin yayi wani maganar cikin jin haushi ta juya za ta bar gurin,yayi sauri ya rik'ota ya dawo da ita..
#Manage please..
#Asli Smasher.
[2/20, 8:41 PM] My number 1: 36...
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*
Ya marairaice yace "i said i'm so sorry.." Fuskarta a d'aure tak'i kallonsa tace "sai dai idan za ka gayamin shi ne zan hak'ura.." Ya lumshe idanunsa ya bud'e,a hankali yake sauke ajiyar zuciya saboda k'amshinta daya cikasa,shi kansa ya san ba k'aramin dauriya yayi ya iya tsayawa kusa da ita ba tare da ya mata komai ba,da wani murya mai cike da rauni yace "yanzu dai aure za kiyi ki tafi ki bar ni koh?" Tayi dariya tace "toh kai ma ba ka yi auren ka tafi ka bar ni ba?" Wani kallo ya dunga mata kafin yace "sai kuma aka ce miki ina son matar?" Dariya ta sake tayi sosai kafin tace "but ko ba ka sonta ai u are enjoying ur marriage,tunda kuna tare har yau baka saketa ba,wa ya san ma me kuke yi da ita.." Kallonta ya dunga yi ko k'iftawa babu,cikin sanyin murya yace "how did u know i'm enjoying my marriage?" Ta d'aure fuskarta kamar za tayi kuka tace "bayan na gani.." Da sauri yace "kika ga me?" K'in yarda ta kallesa tayi tace "meye ma ban gani ba" da sauri ya juyata ya had'ata da bango,ya tsaya gabanta sosai har suna jin numfashin juna muryarsa a raunane yana girgiza mata kansa yace "noo! Lilac i'm only trying my best na sauke hak'k'inta dake kaina,bayan wannan Allah ma shaida ne ba wani amfanin da auren yake min,ba sonta nake ba kin sani,kawai dai Mama ta takura sai da na aureta" a hankali ta d'ago idanunta tana kallonsa sympathetically tace "to me