ta kike ji?" Kautar da kai tayi tak'i cewa komai,yayi murmushi yace "naga dai babu wani kunya tsakaninmu ko akwai?" Da sauri ta gyad'a masa kai,ya kai hannu ya juyo da fuskarta yana kallonta yace "tell me please me kike jin kunyan?" Saurin fad'awa jikinsa tayi ta b'oye kanta a k'irjinsa,yayi dariya yace "tell me yanzun na cire na baki shi" gwalo idanuwa tayi tace "me za ka ban?" Yace "abunda kike jin kunyan mana" dariya ta fara tace "ni wallahi ba na so" yace "kina so mana,fad'a min naji me kike jin kunya?" Saurin kulle idanuwa tayi tace "ni dai Allah ka bari ba na so" yace "ni kuma inaso,dan haka kima fad'a kafin na miki abunda za ki shekara kina jin kunya" wani zaro idanu tayi tace "me za kayi?" Yace "ina ruwanki?" Da sauri tana turo mai baki tace "nifa kunyarka nake ji ba wani abu ba" dariya yayi yace "ban yarda ba,kuma na san ma abunda kike jin kunyan" da sauri ta d'ago tana kallonsa tace "what?" Belt ya fara kwancewa yana kallonta yace "let me show u" tana ganin ya kwance belt d'in zai sauke trouser k'asa ta kwalla k'ara da gudu ta shige jikinsa ta k'ank'amesa tana fad'in "please ka bari ba na so" rungumeta yayi ya dunga mata dariya,sanda yayi mai isarsa ya d'ago kanta yace "ki bari na nuna miki please" da sauri ta girgiza kanta tace "ni wallahi ba na son gani" wani dariya ya dunga yi yace "it's not a big deal kawai kalla za kiyi ku gaisa,i knew it's a new thing for u but ki daure ki d'an kalleta kad'an" girgiza masa kai ta k'ara yi yace "c'mon it's ur new toy fa za kiyi wasa da shi ne" k'ara girgiza masa kai tayi jikinta was vibrate,yayi murmushi yace "okay! Cika ni tou mu tafi" da kyar ta sakesa tayi baya tana turo mai baki,yayi murmushi sanda ya d'auki numfashinta ya rik'ota,da k'arfi ta fasa masa ihu,ya tuntsure da dariya ya rungumeta yace "matsoraciya kawai.. Muje kada mu b'ata lokaci" saurin wucewa gaba tayi ya bita a baya suka sakko sai kalle² take kamar tana neman abu,hannunta ya rik'o yace "me kike nema?" Ta girgiza masa kai tace "nothing" suka fito ya kulle gidan. Gaban wani had'ad'd'en saloon ya tsaya kafin ya fita ya rakata,sanda ta shiga yana kallonta ya mata murmushi ya mata blowing kiss,tayi dariya ta zauna kan chair da matar take nuna mata,ya koma mota ya zauna sanda ya d'an lumshe idanunsa kafin ya bud'e ya turama Azaan sak'o "kai malam ku muke jira fa,idan kuka b'atan lokaci zan wuce na mayar da ita gida in yaso ka yiwa Hjy Siyama bayani" yana tura masa yayi dariya yana shafa kansa then ya tura masa location d'in da suke,not too long motar Azaan ya tsaya gurin ya sauke glass yana kallon motar Waleed,Waleed ya sauke glass yana kallonsa yana masa murmushi,Azaan ya hararesa yace "ai wallahi za ka san ni kama haka.. Tsaf zan rama abunda kayi min" Waleed sai dariya yake masa ya k'i cewa komai,Azaan ya d'age glasses d'in yana kallon Ameerah dake gefensa a hankali ya d'an karkato da kansa yana kallonta,ganin ta k'i d'ago kai ta kalleshi ya kai hannu ya juyo da fuskarta,still k'in yarda tayi su had'a ido but fuskarta a sake tana masa murmushi,yayi murmushi da wani cool voice kamar ba Azaan ba yace "look into my eyes please" k'in yarda ta kallesa tayi yayi murmushi a hankali ya d'ora lips d'insa kan nata idanunsa suna kallonta yana tsotsa a hankali,Waleed yaga basu da niyyar fitowa ya kira Azaan,da sauri Azaan ya d'auka har lokacin bai saki bakin Ameerah ba,Waleed yace "kai malam kada ka zama cinye du mana,ka saki yarinya taje a mata abunda za'a mata suzo mu tafi" d'an lumshe ido Azaan yayi kafin ya saketa yace "kai kuma d'an sa ido meya ruwanka tunda ka hanamu gurin da zamu huta a gidanka?" Waleed yayi dariya yace "haba so kake na zama babban banza,da na maka k'ok'ari ma na fito maka da ita ban maka ba kenan?" Azaan ya tab'e baki yace "ba wani sosai ba" k'wafa Waleed yayi yace "good.. Ka ga kace gobe ma idan na tashi fitowa ba sai na kiraka ba" daga haka ya katse wayarsa,Azaan ya kalli Ameerah yace "let's go" ya bud'e motar ya fita sai fama yake da jallabiyya kamar wanda ke shirin karb'an shaidan zama limami,Waleed yana cikin motarsa sai dariya yakema Azaan ganin yanda yake wani rawar jiki,yace "tukuna ma guy" yayi wani murmushi ya lumshe ido yana shafa k'irjinsa. Kuka sosai Mama da Afiyah suke yi a gaban bokan Mama fad'i take "yanzu babu wani hanyan da za'a iya bi kuma? Wallahi ba zan iya juran ganinsu tare da yaro na ba,dan Allah kayi wani abu ka rabasu wallahi ba na son ta auran min d'a" boka dai yayi iya yinsa ya d'ago yace "babu wani sauran hanyan da ya rage.." Mama ta d'ora hannu aka tana kuka wiwi tana kiran mutuwa,ni dai na kalleta nace "kuji matar dake gurb'ataccen hanya ita ke kiran mutuwa,to wai idan ma mutuwar ya zo mata,taje lahira a me za ta tashi ne?" Afiyah kam ma gaba d'aya ta kasa magana kukan ma ya k'i zuwa ajiyar zuciya kawai take iya saukewa da k'arfi,boka yace "sai dai kuma idan za ku yi k'ok'arin raba su ta hanyar kissar ku na mata,da zaran kun had'a su fad'a,za mu muku taimakon da zai raba su har abada" a wani irin guje suna had'a baki suka ce "za muyi in dai komai zai dawo mana kaman da" boka ya gyad'a kai yace "ku bani nan da sati biyu kafin ku dawo na kammala duk abunda zanyi" har rige² suke wajen yi masa godiya,kafin suka taho suna tafiya cikin dajin suna k'us² d'in yanda za su gillama Manar da Waleed tuggun da zaisa suyi fad'a kaca². Har ciki Azaan ya raka Ameerah,Manar tana hangosa ta mirror ta kulle idanunta dan wani kunyarsa take ji yanzun data rasa na mene ne,ta k'asan lashes d'inta take satan kallonsu tana b'oye dariyan da take,yama matar bayanin yanda yake so ama Ameerah ponytail style,ya juya zai fita gurin Waleed Manar ta bud'a idanu tana kallon Ameerah tana mata dariya,Ameerah ta gilla mata harara tace "muguwa" dariya Manar ta kyalkyale da shi,Azaan ya juyo yaga Manar tana dariya,kunnenta ya rik'e da kyau tayi y'ar k'ara tace "auch! Yaya it really hurts" ya dungure mata kai yace "za mu had'u dake ne" ya fita da sauri ya barsu,motar Waleed ya bud'e ya shiga yana kallonsa yace "ka kyauta" Waleed ya d'auke kai yana sakin murmushi yana shafa kwantaccen gashin k'irjinsa yana wani lumshe idanu,Azaan ya zaro idanu yace "hey Mr Man" Waleed ya d'an kallesa yana d'aga masa eyebrows yace "what?" Azaan yace "ya dai? Ko baka gama bane har yanzu?" Dariya Waleed yayi yace "baza ka gane ba Bhidu" Azaan ya fara dariya yace "noo! Yanzu kam zan gane,tell me what's going on?" Kallonsa Waleed yayi yace "ka bari dai ba yanzu ba" gyad'a kai Azaan yayi yace "alright.." Sanda aka gama musu gyaran kai kada kuso ganin drama tsakanin Waleed da Azaan,Waleed yana cewa shi zai biya,Azaan yana cewa shima shi zai biya ai both Ameerah da Manar k'annensa ne,Waleed yace "wallahi baka isa ba,akan me za ka biyama matana kudin gyaran kai?" Azaan yana masa dariya yace "mene to dan na biya?" Waleed ya girgiza masa kai yace "it's my duty.. So karb'i kud'inka if not kuma yanzun nasa a mayar mata da kanta yanda yake" matar da ta musu saloon dai ta tsaya kallon ikon Allah tana ta dariya,k'arshe da kyar suka hak'ura kowa ya biya nasa,then suka fito suka kama hanyar gida,ko a mota Waleed suna tafiya suna hira ne,Manar ta zame hijab d'in kanta tace "Yaya ka ga" ta nuna masa fishtail braids da aka mata,d'an kalla yayi yana sakin mata lallausan murmushi yace "awwwn! Ya yi kyau" ya kai hannu yana tab'awa,bige masa hannu tayi tana turo baki tace "to sai ka lalata min kuma?" Yace "ba sai mu koma a sake wani ba?" Harararsa tayi tace "tabbb' da zafi fa suke jan gashin kuma" ya kalleta yace "really?" Ta gyad'a masa kai kamar za tayi kuka,gyad'a kai yayi yace "ohh! Tunda suna yi maki da zafi baza mu sake zuwa ba" ta d'an yi dariya tace "da wasa fa nake yi,da tana tab'a min kai har bacci na fara" yayi murmushi lokacin suka tsaya 2 houses away,motar Azaan ya k'araso gurin yayi parking,a hankali ya kai hannu ya d'an d'aga hijab d'in Ameerah yana kallon style d'in da yasa aka mata,yayi murmushi a hankali ya zame hijab d'in duka ya saita camera ya musu selfie,shooter sound d'in yasa ta d'ago idanunta da suke nan kamar an watsa su cikin ruwa tana kallonsa za tayi magana ya sake d'aukansu,yanda suka yi kyau a pic d'in yasa shi kissing wayan yana sakin mata lallausan murmushinsa,Waleed kam yana can yana latse y'ar mutane a mota,sanda ya gama luguiguita ta ya saketa yama Azaan horn,bud'e motar Azaan yayi ya fito ya bud'ewa Ameerah ta fito Manar tana kallonsa sai dariya take tuntsirawa,sanda ya rakota ya bud'e mata back seat ta shiga ya d'an kashe mata ido da alamar sai sun yi waya,ta d'an gyad'a masa kai a hankali tana satar kallon Waleed,Waleed ya sauke glass yace ma Azaan "malam kana fa zak'ewa da yawa" harararsa Azaan yayi ya juya ya shige motarsa,Waleed ya fara yin gaba yana kallon mirror yaga Ameerah duk ta wani sunne kai,ya d'an tab'e baki yace "munafuka.. Dubi yanda tayi kamar ta Allah" Ameerah ji tayi kamar motar ya bud'e ta nutse dan kunya,dai² get Waleed yayi horn,get keeper ya bud'e masa ya shige,yana yin parking Ameerah tayi saurin ficewa daga motar,lokacin Azaan ya shigo yayi parking,saurin wucewa Ameerah tayi bata ma jira wani ya gansu ba ta wuce b'angaren Dadda,Azaan ya fito ya kulle motar sai wani murmushi yake saki ya nufi cikin gidansu Waleed,da kyar Waleed ya saki Manar tana fitowa daga motar ta kwasa a guje tayi b'angaren Dadda tana shiga d'akinsu ta fad'a kan gado tana maida numfashi,Ameerah dake cire kaya za taje wanka ta tsaya kanta tana kallon yanda take maida numfashi a hankali ta bugi cinyarta,Manar ta bud'a idanu tana kallon Ameerah tace "meye?" Zaunawa Ameerah tayi kusa da ita tace "ke wai kin san me Yaa Azaan yamin kuwa?" Manar ta fara dariya ta tashi za ta fita,Ameerah tace "wallahi duk Yaya ne ya janyo min ni ko hannuna namiji bai tab'a tab'awa ba,amma yau har k'irji na sai da ya mammatse wallahi baki ji yanda suje min zafi ba duk sun yi ja wajen kan" dariya Manar ta dunga tuntsirawa sanda taje k'ofa ta waigo tace "na ki kad'an ne ni meye Yaya bai min ba? Wallahi ko shi Yaa Azaan d'in da ya samu dama ina jin zaiyi abunda yafi haka" Ameerah ta tashi tayi hanyar bathroom tace "ni dai Allah bazan k'ara binku ba,duk inda zaku ku tafi ku kad'ai" wani kallo Manar ta mata tace "munafuka wallahi kema kinji dad'i ni za ki rainama hankali" daga haka ta fice ta bar Ameerah tana dariya dan gaskiya ta san gaskiya Manar ta fad'a,ko yanzu ya kirata za ta iya binsa ya k'ara mammatseta. Kusan a tare suka shiga gidan Amaar dake sakkowa zai fita saboda ya gaji da zaman shi kad'ai su kuma dama ba wai suna fita yawo ba ne tun asali ya ci karo da su suna shigowa Azaan a gaba sai Waleed da kusan button hud'u na rigansa suke bud'e yana tafe yana shafa k'irjinsa yana sakin wani wicked smile,Amaar ya kallesu da kyau ya d'auke kai sanda Azaan yace ma Waleed "brother i'm coming let me took my bath please" Waleed ya gyad'a kai yace "alright" ya kwanta kan kujera har lokacin bai daina shafa k'irjinsa ba,Amaar dai ya kasa hak'uri yana kallon Azaan dake k'ok'arin wucewa sama yace "hey! Wai ina kuka je ne?" Azaan ya saki wani murmushi yace "ina ruwanka?" Da sauri yayi sama,zaunawa yayi kusa da Waleed dake lumshe idanu yace "brother ina kuka je ne?" 'Dago kai Waleed yayi ya kalleshi bai san sanda bakinsa ya kub'uce yace "kayi aure kawai malam ka daina tambayana inda naje" ya k'ara lumshe idanu,wani kallo Amaar ya dunga masa yace "ohh! Ni kuka mayar d'an iska kenan? Yayi muku kyau" daga haka ya mik'e ya fita. Afujajan Mama suka shigo gidan after sallar maghreb lokacin su Waleed suna parlor sai hira suke suna ma juna tsiya shi da Azaan,Amaar dai ya saka su gaba sai kallonsu yake ya buga tagumi da hannuwa biyu yana tausayin kansa shi da ko budurwa bai tab'a yi ba,har Mama ta shigo ta wuce stairs bata kula da su ba sai da suka yi ihu suna dariyan abunda Waleed ya fad'a na taliyar murji,ta waigo da sauri tana ganinsa ta furta "Waleed!" Da wani murya,Waleed da yaji maganarta ya d'ago ya kalleta,karon farko ya kalleta yaji gabansa yayi mugun fad'uwa saboda yanda yaga Mama ta rame ta yi duhu,da sauri ya tashi yana mata wani kallo yace "Mama! Kin yi rashin lafiya ne?" Kuka ne ya kufce mata,hankalin Waleed a d'an tashe ya rik'o hannunta ya jata suka nufi sama yana cewa su Azaan yana zuwa,sanda suka shiga bedroom d'inta ya zaunar da ita bakin gado ya rik'o hannunta yana kallonta yace "Mama tell me what's going wrong? Me ya same ki? Meye matsalar?" Cikin kuka Mama tace "Waleed ina ka shiga? Ka daina zuwa ka ganni? Ko a waya ka daina kirana bare kaji lafiya na? Laifin me nayi maka Waleed?" Wani ajiyar zuciya yayi yace "please Mama kiyi shiru" d'an sassauta kukan tayi tana kallonsa,ya kai hannu ya share mata hawaye,a hankali ya zauna sosai a gabanta yayi flexing legs d'insa,fuskarsa da d'an damuwa yace "Mama me yake faruwa?" Ajiyar zuciya tayi tana kallonsa sosai tace "Waleed" yace "na'am Mama" tayi shiru tana kallonsa da tunanin me za tace,can dai ta daure ganin ita yake kallo tace "ina son tambayarka wani abu ne,ban sani ba ko za ka iya min" yace "ki tambayi ko mene ne Mama if ina da iko da shi zan miki" a hankali tace "za ka iya min duk abunda nace ina so?" Ya gyad'a mata kai yace "ki fad'a kawai" kai tsaye tace "so nake ka saki yarinyar nan" wani zabura yayi ya mik'e tsaye yana kallonta Dldan ya gane wanda take nufi,Mama na ganin haka ta sake fashewa da kuka tace "dama na san baza ka tab'a iya min abunda nake so ba,shi kenan kaje tunda wasu sun fini" Waleed dake tsaye yana mata wani kallo yace "amma Mama" cikin kuka tace "dalla rufe min baki,munafuki ai na san dama baza ka tab'a iya goyon baya na ba,bakinku d'aya da ubanka" d'an numfashi ya fesar idanunsa har sun fara canjawa ya taking steps a hankali ya sake zama gabanta,da wani sanyayyan murya yace "Mama yanzun idan kin sa na saketa me kike so na fad'a ma Abba?" Ta kalleshi tayi shiru kamar tana tunani,ya kamo hannunta ya rik'e a hankali yace "Mama kinga lokacin da kika sa na auri Afiyah kinfi kowa sanin she's not my choice,and Manar kuma zab'in Abba ce,though na tab'a fad'a miki ina sonta ke kika hana na aureta,but yanzun ba ni da ikon sakinta,idan kin sa ni dole na saketa me kike so na fad'awa Abba?" Kallonsa ta dunga yi kafin ta sauke numfashi tace "shi kenan idan har baza ka iya sakinta ba,lallai in so ka dawo da Afiyah d'akinta" kallonta ya dunga yi ya kasa magana can dai ya daure yace "shikenan Mama zan dawo da ita in sha Allah" tana jin ya amsa tayi murmushi tana shafa kansa,shi dai duk bai so tace ya dawo da Afiyah ba dan a niyyarsa tunda ta kwashi k'afarta ta bar gidan bazai tab'a cewa ta dawo ba,because ya gaya mata dama ji ne bata yi ba,Mama sai murna take saboda k'udurinsu zai cika idan har Afiyah ta dawo gidan Waleed,gaba d'aya daren ta hanasa fita suna tare a d'akinta sai wani nan² take da shi kamar ta damu da shi,sai da dare yayi sosai yace zaije ya kwanta bacci yake ji,kafin ta kyalesa ya mata sallama ya fita. Washe gari around 8am jirginsu ya tashi zuwa India,duka gidan aka watse sai Mama kad'ai da y'ay'anta masu mugun hali,tunda suka taso su Waleed suke tsokanar Amaar,shi dai bai ce musu komai ba suka yi suka gama,sanda jirginsu ya sauka India manyan motoci suka tarar da za su d'aukesu zuwa yankin Vishakpatnam,kuzo kuga idon Dadda a India,sanda suka isa ana musu barka da zuwa,Dadda ba Indianci sai raba ido take ba ta jin yaren,gara Waleed da Amaar ma sai Manar da yake itama tayi zaman gidan Mommella a nan ta iya wasu abubuwan,Raj Jarood bn Maqbool da matarsa Rani Naheed sai *RANIA* k'anwar Azaan da aka haifa kusan tare da su Manar sun fito compound d'in gidan tarban bak'insu lokacin da motocinsu Dadda suka fara parking suka fito cikin mutunci aka dunga musu barka da zuwa kafin suka d'unguma gaba d'aya suka shiga cikin gidan sarautar,hadimai suka dunga shigowa da kayansu zuwa masauki,sanda aka zauna cikin makeken parlon aka fara gaisawa da harshen nasara,Mahmoud mijin Mommella shi ya gabatar da kowa ga Raj Jarood kafin suka d'unguma aka fara lunch a makeken table d'in da kaf sai da ya d'auke su duk yawansu,bayan an gama ciye² aka fara hira ana labarai,Dadda da rigima tace sai tayi magana ga ta muguwar comedian in ta fad'i abu dole sai Azaan yama iyayensa translation,suna ta dariya saboda su basu tab'a ganin Dadda ba,Ameerah anzo gidan surukai sai wani sunk'e kai take,Manar ta zungurota tace "dallah mene haka kuma?" Ameerah tace "ke kunya nake ji" Manar ta fara dariya,tana d'agowa suka had'a ido da Waleed ya lumshe mata idanuwa ya mata blowing kiss,murmushi tayi ta d'an kautar da kanta,Rania k'anwar Azaan ta tab'a Manar tace "kuzo muje d'aki na" suna tashi za su bar wajen