me.." Ta turo baki a shagwab'e tace "ba guduwa ma kayi ba ka barni ina kuka" ya lumshe idanuwansa a hankali yace "i want u so bad.. But idan na tsaya zan iya yin abunda ba d'ai² ba" tace "nima haka" zaro k'ananun idanunsa yayi yana sauke ajiyar zuciya,lokacin duka ya manta da wani maganar aurenta da Azaan enjoying lokacinsa da ita kad'ai yake suna musayar dirty talk,sai da jirgi zai tashi ya mata sallama yace "I'll call u idan mun sauka.. Ki kularmin da kanki" ta gyad'a kai a sanyaye tace "toh! Yaya Allah sauke ku lafiya" yace "ameen.. Thank u" suka ajiye wayar tare tana blushing,shi kansa murmushi yake fitarwa ya lumshe idanunsa,a hankali jirgi ya tashi da shi yana tuna yanda suka rabu. Ita kam a nan sanda ta ajiye wayar bayan ta shiga bathroom wanka tayi tayi sallar asr then ta koma kan gado ta kwanta kamar wata marainiya tayi shiru,a haka bacci ya d'auketa cike da mafarkin abunda ya wanzu tsakaninsu,ba ita ta farka ba sai maghreb ana ta kiraye²n sallah,ta tashi ta duba time then ta wuce ta d'auro alwala ta fito ta tada sallah,after then ta fita jikinta duk yayi sanyi ta wuce part d'insu a can tayi dinner ta shige bedroom d'inta ta kwanta lamo,sanda jirginsu Waleed ya sauka k'asa mai tsarki ko da ya samu kansa a masaukin da yama kansa bai ko tsaya hutawa ba ya fara kiran Manar,lokacin har ta gaji da jiran kiransa,tana kwance shiru ita kad'ai a d'akinta ta ji k'aran wayarta,da sauri ta sauka ta d'auka ta kai wayar kunnenta tace "hello! Yaya" Yayi ajiyar zuciya ya zauna gefen bed yace "na'am my lilac" tace "ka sauka lafiya?" Yace "alhamdulillah! Sai missing d'inki da nake" wani murmushi tayi cike da tsokana tace "ko dai na zo?" Yace "da za ki zo zan fi kowa farin ciki" tayi dariya tace "ai we are far for each other" yace "kina dariya saboda ba na kusa ko?" Tace "ehh" hira sosai suka yi suna dariya kafin suka yi sallama yace zai d'an kwanta,suna ajiye wayar tayi wani ajiyar zuciya ta lumshe idanunta tana jin yanda iska ke ratsa every vein,b'argo da jininta da kewarsa,ranar da kyar ta samu bacci ya d'auketa,duk lokacin da wani abu ya faru tsakaninta da shi haka take kwana juyi ba ta iya cikakken bacci,duk sanda ta faka kuma sai ta tab'a jikinta,wanka kuwa ba'a magana ma saboda yanda take wetting kanta da tunaninsa. A haka kwanaki suka yi ta juyawa zuwa sati,daga sati zuwa wata,tafiyar Waleed ma an samu kusan two months,su Manar tuni har sun fara exam d'insu na SSCE,da yake lokacin ana cikin watan Ramadhan,sosai ake kwad'a rana mai d'an karen zafi,mafi yawan lokaci a mugun wahale suke dawowa gida,duk ranar da suke da paper kuwa da kyar suke tsinana wani abun,yayin da har lokacin babu labarin Waleed bare asa ran zai dawo,sanda Mama ta masa waya take tambayarsa yaushe zai dawo cewa yayi ba yanzu ba,babu yanda bata yi da shi ba amma fir ya nuna shi fa bai jin zai dawo ma sai an gama azumi kaf,dole ta hak'ura ta kyalesa,ranar ana sallah saura kwana uku aka kawo lefen Manar,fad'an irin kayan da aka zuba mata kamar b'ata baki ne,tunda Mama ta samu labarin shigowar y'an kawo lefe though maza suka kawo ta kasa zaune waje d'aya ta dunga safa da marwa daga d'aki zuwa parlor,haka ko su Deejah ma taita sawa su gano mata idan yan kawo kayan sun tafi,can dai ta gaji ta kira Hjy Izatu duk ta sanar mata abunda ake ciki,Hjy Izzatu tace "toh meye abun d'aga hankali kuma Allah na tuba,ke da aka gama baki tabbataci akan yarinyar nan sai ta yi auren nan babu fashi,kin san fa abune da ba zai tab'a yiwuwa ace an fasa ba,to meye abun damuwa kamar baki yarda da bawan Allan nan ba.. Tunda yace ki jira ayi auren akwai yanda zai yi ya raba,ki bari dai har yayi abunda zai iya muga,idan babu nasara ne sai mu nemi wani ko kuwa?" Hankalin Mama a tashe tace "na sani Hjy ba wai ban yarda bane,ni kawai burina bai wuce naga yarinyar da uwarta sun ji kunya ba,kuma dai kin san yanda muka yi da Waleed akan yarinyar ko ba haka ba? Ga shi ma ya yi tafiyarsa ya zauna wata k'asa duk akan maganar auren yarinyar ya gujewa zama a nan,ni dai idan da taimakon da za'ayi ina son ayi ya dawo ayi bikin a kan idanunsa dan ya tabbatar bazai samu yarinyar ba.. Banda ma abu ai wallahi ko shi yaron dake nemantan ban so aka ce lallai saii ya aureta ba,so nayi ace lalata ta yayi ko wani jigataccen almajiri ya fito zai aure shegiyar yarinyar.." Dariya Hjy Izzatu ta fara tace "kai k'awata ba ki da dama wallahi" Mama dai ta yi kicin²,Hjy Izzatu tace "babu damuwa za mu san yanda muka yi da Waleed ya dawo" Mama tace "yawwa dan Allah ayi duk yadda za'ayi asa shi ya dawo gida" Hjy Izzatu tace "an gama fa kada kiji komai,kamar ya dawo ma an gama" lokacin suna cikin maganar kamar ance ta d'aga kanta taga Azaan da Amaar suna shigowa,yanayin kallon da suke mata yasa ta sha jinin jikinta da sauri ta yiwa Hjy Izzatu sallama ta katse wayar,fuskarta a d'aure tana aika musu mugun kallo,su dai suka wuce sama babu wanda yace mata k'ala,jin an sake bud'e k'ofa da sauri ta d'aga kai she thought su Deejah da ta aika su mata investigation ne,Aunty ta shigo da farin ciki sosai tace "Hjy an kawo kayan Manar,kaya na gani a fad'a wallahi son kowa k'in wanda bai samu ba,akwatuna sha biyu..." Mama ta d'auke kai tana tab'e baki da kyar ta iya cewa "toh Allah dai yasa ba yaudara bane,wannan kayan kamar za'a siyar da yarinya.." Juyawa Aunty tayi ta nufi sama tana cewa "ai da yake itama iyayenta ba fatararru bane,in dai arziki ne gadonsa tayi,dan an kawo mata kaya irin wannan ba komai bane da arzikinta ta zo" tai wucewarta sama ta bar Mama da sakakken baki,y'an kawo kaya suna barin gidan aka kwashi kayan aka kai part d'in Dadda,Dadda ta saki baki tana kallon maids da suke shigo da kayan tace "wannan kuma fa daga ina? Meye wannan d'in a ciki?" Ruqayya na murmushi tace "kayan takwararki ne" Dadda ta mik'e da sauri tace "wa ya kawo?" Ruqayya tace "iyayen wanda ke sonta ne suka kawo,Alh yace a shigo da su nan" Dadda ta saki wani kabbara sai kuma ta fara gud'a tana rawa,can dai ta dakata tace "yaushe suka zo?" Ruqayya tace "basu jima da tafiya ba" zaunawa Dadda tayi ta fashe da kuka tace "Allah sarki takwarata,shi kenan haka za ta tafi ta barni ni ni kad'ai raina.." Shigowar su Dadday tare da Abba yasa tayi shiru tana share hawayen idonta,suka zauna suna gaisheta,ta amsa cikin rawar murya tace "kuma har lokacin aurar da Manar d'in ya yi ne?" Daddy dai bai bata amsa ba sai kallonta yake,Abba ne ya mata bayanin komai da lokacin da aka tsayar sallah da sati biyu,Dadda ta sake rangad'a gud'a tace "Alhamdulillah! Takwarata ta yi goshi,Allah na gode maka,Allah ka ara min rai da lafiyar ganin y'ay'anta,na rainesu kamar yadda na raineta in sa masu albarka" sai kuma ta fashe da kuka,Ameerah da ta shigo ganin kayan tana ganin Dadda na kuka ta fashe ba dariya,su Daddy dai suna gama magana suka fita,Dadda ta kalli Ameerah tace "maza janyo su mu gani y'ar nan" suka dunga d'aga kayan suna kallo...
#Ku k'ara hak'uri muna cikin hidimar biki ne,Saturday and Sunday ba lallai nayi online ba..
#Asli Smasher.
[2/15, 10:01 PM] My number 1: 33...
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*
Suna shiga bedroom Azaan ya waigo yana aikama Amaar wani kallo cike da tuhuma,Amaar ya d'auke kansa yayi kamar bai ga abunda Azaan yake ba,Azaan yace "har yanzun kana da abun fad'a?" Amaar yayi saurin kallonsa yana squeezing fuskarsa yace "think i didn't get it right" Azaan ya sauke numfashi idanunsa akan Amaar yace "baka gane ba?" Amaar yace "yeah! Me kake son cewa ne?" Azaan yace "kana nufin baka ji maganar da step Mom d'inku take yi ba?" Amaar ya tab'e baki yace "ba wannan ne lokaci na farko da naji irin maganar nan a bakinta ba" Azaan ya d'an zaro idanunsa yace "ohhh! Ka san maganar kenan ni ne ka rainawa hankali?" Amaar ya girgiza masa kai yace "nope!" Azaan yace "uhn! What's up?" Amaar yayi d'an tsaki cike da takaici yace "forget the matter please.. Think bai kamata mu b'ata ma kanmu lokaci akan maganar ba" Azaan yace "ko saboda me za'a barshi?" Amaar yace "because ba shi da wani value" girgiza kai Azaan yayi yace "i want to know me ka sani akan case d'in nan" da sauri Amaar yace "please brother" Azaan yace "baza ka fad'amin ba?" Amaar yace "wai mesa kake son tada ma kanka hankali ne akan maganar?" Azaan yace "just wanted to know,idan baza ka fad'a ba kuma fine" Amaar zai yi wani maganar Azaan yace "please idan baza ka fad'a min abunda nake so ba,just keep quiet.." Kallon Azaan Amaar ya dunga yi da mamaki,he just wish zai iya keeping secret d'in da Aunty tace yayi but yanda Azaan ya damesa da maganar at last dole ya hak'ura yayi exploding masa gaskiyar abunda ya sani,Azaan ya dunga kallonsa and he couldn't take off his eyes on him,can ya ja numshi ya sauke a hankali yace "but me yasa shi Waleed yayi keeping maganar tunda he loves Manar?" Amaar yace "don't u understand maganar Mom d'insa?" Azaan yace "na ji.." Amaar yace "ka san Waleed yana da mugun zurfin ciki,ba komai ne da ya shafesa yake bari a sani ba.. So maybe yayi keeping maganar ne all because of abunda ita Mama take fad'a" Azaan ya dunga gyad'a kai ba tare da ya sake cewa komai ba suka yima juna shiru kowa da tunanin da yake damun ransa. Da dare after isha'a Dadda na zaune tana lazimi Amaar ya shigo parlon yana kallon Dadda dake laziminta yace "ina wuni" ta masa gyaran murya sanda ta kai k'arshe tana washe masa baki tace "lafiya lau d'an fodiyo,hala kaima kaji batun kawo kayan ne ka taho gani? Ai wallahi kai dai baka ga kaya ba kamar za'a bud'e kanti wallahi,takwarata ta yi goshi.." Za ta sauke masa yace "Hjy ai bama sai kin bud'e ba,ni da ba sanin yanda ake yi nayi ba,ki barshi kawai Allah sanya alkhairi ya ba su zaman lafiya" tace "Ameen dai d'an nan dama ganin kaya kam sai mata" shi dai bai ce mata komai ba ya juya zai fita yace "sai da safe" tace "toh! Allah maka albarka,ya kaimu lokacin da zamga na ka auren.." Murmushi yayi ya fita,Dadda ta ci gaba da laziminta. Washe gari da safe wajen k'arfe goma Manar ta shigo b'angaren ta tarar da Dadda suna d'aga kayan da aminiyarta Tasallah,tana ganinsu ta juya za ta koma,Dadda ta kwalo mata kira,ta juya tana kallonta daga bakin k'ofar,Dadda tace "to kuma ki shigo mana kiranki fa nake dan walak'anci kika tsaya nan kina kallona" Manar ta k'arasa fuskarta a d'aure tace "ga ni" sabon wayarta da Amaar ya siya mata k'iran Tecno mai keypads ta mik'a mata tace "maza ki lalubo min zaran da zai had'a ni magana da Mamman" Manar ta kalleta da sauri tace "Yaya?" Dadda ta mata wani kallo tace "to da idan ba shi ba wa nake nufi kuma?" Manar ta shiga contact ta lalubo number sa ta kira mata shi,sai da kiran ya katse kafin Waleed ya kirata,da sauri ta karb'e wayar ta kai kunne without ta yi answering ta fara magana,Manar ta bita da kallo,jin bai yi magana ba Dadda ta d'ago wayar dake ring har lokacin ta kalli Manar tace "to kuma ya haka na ji shiru bai ce komai ba sai kafirin kid'an dake tashi?" Manar tace "to ai baki answering call d'inba kike magana" da sauri Dadda ta mik'a mata wayar tace "to d'an sake lalubo min shi muji" Manar tace "ki danna wajen koren alamar mana" da k'arfi Dadda ta daddage ta danna kamar za ta b'urma button d'in,then ta kai wayar kunnenta,kafin Waleed yayi magana Dadda ta fara cewa "to wai ni kuwa sai yaushe za ka dawo k'asar ne Mamman? Haka kawai ka tafi wata k'asa ka share gindi ka zauna,kai ko kad'an baka ji kewar gida ya dameka ba?" Waleed dake sauraronta yayi Murmushi yace "to ki bari dai har ki had'iye yawu mana,kina ta magana ba coma bare fullstop,sai magana kike kamar an bud'e lalataccen radio" fuska d'aure Dadda tace "ehh lallai Mamman ni kake fad'awa haka? To ka gayama ubanka Yaro ko Asama'u" dariya yayi yace "ba dai haushi kika ji ba ko?" A fusace tace "sai dai kaje ka tambayo uwarka d'an nema" ya d'aure fuskarsa yace "kinga ni idan ba ki da abun fad'a zan kashe wayana,haka kawai kin kira mutum kuma kina masa fad'a,zan tafi masjeed idan kin tuna abunda za ki fad'a later sai ki kira ni" da sauri tace "umm! Dama lefen k'anwarka fa aka kawo nace bari na sanar maka" wani fad'uwa gabansa ya dunga yi yace "lefe?" Ya maimaita,Dadda tace "ehh wallahi kai dai baka ga kayan da suka kawo ba,kamar za'a bud'e kanti,yo abunka da gidan manya,ka san fa gidan sarauta za taje" a fusace yace "don't tell me that.." Da sauri Dadda ta zaro ido tace "inji dai ba zagina kayi ba da wannan kafirin yaren naku da kuka aro gurin yahudu da nasara?" Waleed ya sauke numfashi yana matse forehead d'insa da veins d'in gurin suke harbawa da k'arfi ya d'an girgiza kansa a hankali yace "not at all.." Mitsi² Dadda tayi da ido tace "wallahi to ba da ni kake ba da Yaro kake.." Yadda tayi magana makes Waleed fashewa da wani dariyar da bai shirya ba,yace "to wai ke wa yace maki zaginki nayi ma? Da kike sako Abbana a ciki?" Dadda tace "ohoon maka dai ni ba dani kake ba wallahi kaji in fad'a maka" babu shiri Waleed yace "bari naje masjeed na dawo zan kira ki" tace "to ai shi kenan.." Har za ta katse kiran sai kuma tace "to dama k'asar da kaje d'in suna sallah ne?" Waleed yace "a'a sai kin zo kya koya musu yadda ake yi" yana fad'a ya katse wayar yana dariyar halin grandma d'insu,sanda yaje masjeed ya dawo tuni ya manta da batunta ya shiga wani uzurin,wasa² har ana saura kwanaki uku bikin bai yiwa kowa waya ba kuma ba shi da niyyar dawowa gida,at that same day da dare suna waya da Manar dake d'aki a kwance tace "Yaya sai yaushe za ka dawo?" Yace "babu rana" ta zaro idanunta tace "Kai Yaya yanzu kana nufin baza kai attending event d'in biki na ba?" Waleed da yaji kamar she pours him boiled water ya runtse idanunsa yayi shiru,Manar taji bai ce komai ba ta kirasa a hankali "Yaya!" Still ya kasa amsawa,ta sake kiransa cike da damuwa tace "Yaya what happened?" K'in cewa komai yayi k'arshe kawai ya katse wayar yana sauke numfashi da kyar²,Manar tana jin ya yi cutting kiran ta fara kiransa cike da damuwa,but ya k'i d'auka babu shiri ta tura masa text tace "Yaya! Wai me yake faruwa? Ka san dai hankalina bazai kwanta ba idan ba sanin abunda yake faruwa nayi ba" cike da k'arfin hali Waleed ya bi content d'in lokaci d'aya ya kirata vedio,da sauri tayi picking tana kallonsa a kwance saman lafiyayyen gadon hotel d'in da yake tace "Yaya!" Ya runtse idanunsa yana calming kansa a hankali,Manar ta sake kiransa da muryar kuka tace "tell me please me yake damunka?" Lokaci d'aya ya bud'e idanunsa da suka juye yana kallonta yace "kece" ta zaro idanunta dake cike taf da hawaye tace "ni me nayi maka kuma?" Yace "me yasa kike son tada min hankali ne?" Tace "Yaya me nayi?" Yace "kina min maganar aurenki da wani,do u know how much ur words hurts me?" Ta girgiza masa kai hawaye suna saukowa fuskarta cikin raunin murya tace "I'm very sorry Yaya,ban san ba ka son maganar ba da ban fad'a ba" ya lumshe idanunsa a hankali yace "okay" daga haka hiran na su ya canja. Mama zaune tare da Hjy Izzatu a parlon gidansu Afiyah suna gaisawa da Afiyar da tun bayan barin Waleed k'asar itama ta tattara ta tafi gidansu a cewarta baza ta zauna masa gadin gida ba,su Maman nema suke gaida ta tana amsa musu a wani iri,can dai tana yatsina fuskarta tace "a kawo maku abinci?" Mama tayi murmushi tace "um'um wallahi alhamdullillah! Ai daga gida muke,takanas nace bari dai muzo muganki,sannan mu yi wata magana da ke mai muhimmanci" Afiyah na kallonta tace "okay ina jinki Hjy" Mama ta d'an yi shiru sai kuma tace "hope dai komai lafiya?" Afiyah ta tab'e baki tace "lafiya lao fa though d'anki ya ajiye ni tunda ya tafi ko waya bai min,tunda ya kira nace masa na tafi gidanmu duk sanda ya dawo na koma yake jin haushi na" Mama tace "kayyah! Me isa kika sanar masa ke kuwa?" Afiyah tace "how on earth zan zauna gidansa ina masa gadi? Abunda aka aureni yi masa kenan?" Mama ta girgiza kai tace "ai da baki sanar masa ba,saboda duk shirin da muke yi yanzun na ya dawo ne,ya shaida auren yarinyar can,yanzu kinga kin rusa mana wani plan d'in because duk sanda ya kira ina sanar masa kina gidan tare da su Deejah" Afiyah tana mata wani kallo tace "k'arya kika shirya masa kenan?" Mama da bata ji komai a maganar da Afiyar ta fad'a ba tace "to dama shi wannan mutumin ai sai da k'aryan,wallahi duk fad'i tashin da nake