"zanje na karya a gida sai mu tafi" da sauri Dadda ta tashi ta d'auki mayafinta ta yafa tace "iiiihhhh! Kuma zama kike so nayi jiranki? Gaskiya ba na iyawa muje can kya ci ai gidan Yayanki ne,matar tasa ba sai ta dafa maki duk abunda kika ce kina so ba" Manar ta kalleta d sauri tace "a can kuma zan ci?" tace "iiiihhhh! Gidan Mamman d'in ba'a cin abinci ne? Muje kin ji kada rana ya k'ara yi,gara muje yanzu ba muje musu da wannan ranar fatsar² ba" ta wuce gaba tana mita Manar ta bita a baya tana b'ata rai. Sanda suka sauka mota a bakin get driver ya tsaya Dadda ta fita tana kallon gidan,ta kalli Manar tana washe baki tace "nan shi ne gidan Mamman din?" Manar dake jin haushi tace "ni to ya za'ayi na sani" Dadda ta kalleta,ganin yadda fuskarta yake d'aure tace "to ko dai haushi na kike ji na hana ki tsaiwa kici abinci?" Manar tace "a'a" Dadda tace "iiiihhh! Me aka maki to?" Tace "babu komai" Dadda tace "babu komai kike b'ata rai?" Ta mata shiru bata amsa ba ta wuce gaban get d'in tayi knocking,get keeper ya bud'e yana kallonta yace "wa kike nema?" Ta d'aure fuska tace "gurin me gidan muka zo" a masife Dadda data tsaya baya ta lek'o tana kallonsa tace "Kai d'an nan gurin jika na muka zo,maza ka bud'e mana mu shiga" get keeper sai kallon Dadda yake ya k'i bud'e musu,Dadda dake jiran yace su shiga taga ba shi da niyyar bud'e musu,rai b'ace tace ma Manar "ke ina salularki?" Manar tace "na barta a gida" Dadda ta saki baki tana kallonta kamar za tayi kuka tace "yanzu fisabilillahi idan ba dama kin so a walak'anta mu ba,yaushe za ki bar wayar a gida?" Manar dai ta k'i kulata,cikin sanyin jiki da ba murya Dadda ta kalli mai gadin tace "yanzu kai d'an nan da gaske baza ka bud'e mana mu shiga ba?" Yace "baba ba nan gidan bane kuje gaba" Dadda ta bud'e baki tana kallonsa,cike da jin haushinsa tace "kai allan musuru ne da ka san ba nan muka zo ba?" Yace "ba shi bane,amma bazan bari ku shiga ba" Dadda ta ji haushi sosai tace "kada Allah yasa ka bari mu shiga d'in,idan ka barmu mun taka ciki ba ka k'aunar Allah da manzonsa" yace "sai dai ki fad'i koma mene,amma bazan bud'e muku ba" k'wafa tayi mai ciwo ta koma gefe tana mita,Manar dake kallonta ta ciro wayarta daga jaka ta fara kiran Waleed,bugu d'aya ya d'auka yace "what?" Ranta a bace tace "ga mu bakin get ka fito" yace "baza ku shigo ba?" Tace "to ba get keeper d'in ya hana mu ba" da sauri Waleed ya sauka d'aga kujeran da ya kwanta tun asuba da ya dawo daga masjeed yace "alright! I'm coming" ya katse kiran,a nutse yake tafiya ya bud'e get ya fito,Dadda sai mita take ma Manar tana fad'in "amma wallahi sai Allah ya saka min tsaiwan da kika ja min a rana,haka kawai dan k'aryan bala'i kice kin bar salular a gida.." Tana ganin Waleed ya fito ta nufesa kamar za tayi kuka tace "gaskiya Mamman ka yiwa Manar nasiha,wannan dai ba halin kwarai bane ta daddage tayi k'arya alhalin ta san ba haka bane.." Waleed dake kallon Manar tun fitowarsa yace "ku zo muje" suka bisa,Dadda ta waiga ta galla ma get keeper kallo tace "d'an bak'in ciki sai dai ya mutu,ko yanzu ma za ka hana mu shigar ne?" Murmushi yayi bai ce komai ba ya koma kan bench ya zauna,Dadda suka shiga gidan tana ma Waleed mitar "gaskiya Mamman wannan mutumi baida kirki ko d'is.." Waleed dake gaba yace "me ya maki?" Tace "shi haka ake yi sai yace mutane baza su shiga gidan ba.. To ko dai baka fad'a masa muna zuwa ba?" Yace "nace masa me?" Tace "kai kuwa ai da sai ka ce masa kakarka da k'anwarka suna zuwa ya bud'e musu k'ofa" yayi murmushi suna zuwa balcony Dadda har lokacin tana masa mita,ya bud'e musu k'ofar suka shiga parlon,Dadda ta washe baki tana kallon lafiyayyun leather chairs d'in parlon,Manar tana biye da ita,da k'arfi bayan ta gama shiga tace "salamu alaikum" da taji shiru ta sake maimaitawa,wani kallo Manar tayi mata cikin jin haushi tace "kai Hjy kiyi a hankali mana.." Matsawa Dadda tayi ta bud'e baki tana kallonta,Manar ta turo baki ta d'auke kanta tace "kawai sai kiyi ta maimaitawa da k'arfi kamar ba safiya ba kuma ce miki aka yi ba'a ji ba?" Dadda za ta yi magana Waleed dake bayansu ya yima Manar wani kallo yace "kyaleta Hjy kada ki kulata" Dadda ta washe baki tana kallonsa tace "ai dama ko baka fad'a ba bazan kulata ba,yo ce mata aka yi nima irinta ce?" Kallonsu kawai Manar tayi fuskarta a d'aure,can ta juya a hankali,kallonta taga Waleed yana yi,ta sunkuyar da kai tace "ina kwana Yaya?" Kafin ya amsa suka ji muryar Dadda tace "ina amaryar taka kuma Mamman?" Waleed ya juya ya kalleta yace "tana sama" zaunawa suka yi Waleed yana kallon Dadda yace "ina kwana?" Ta washe baki tace "Lafiya lao Mamman tun asuba da na tashi nayi wanka wallahi,banda su da suka b'ata min lokaci da tun gari bai gama wayewa ba za ku ganmu" shafa beard d'insa yayi yana sakin lallausan murmushinsa,Dadda tana kallon pillow da aka ajiye kan lallausan sabon rug d'in parlon tace "wai ita amaryar taka baza ta sakko ba ne kuma Mamman?" Waleed yace "tana sama fa think bata tashi ba.." Yana fad'in haka ya tashi ya wuce sama,Dadda ta k'ara kallon pillow dake parlon murya can k'asa tace "Manar waye kuma ya kwana a parlor?" Manar tayi murmushi tace "kai Hjy me ya ruwan ki kuma?" Dadda ta tab'e baki tace "iiiihhh! Ba ruwana kuwa" ta rik'e bakinta tana sake k'arema parlon kallo,can ta cire mayafinta ta nad'e tana kallon ko ina tana murmushi tace "sabon gida ba dai kyau ba" ta mik'e ta nufi wani k'ofa ta bud'e tana lek'a ciki ta k'arasa shiga sai kalle² take yi kafin ta fito ta rufe tace "to shi kuma Mamman duk shi ya zuba lafiyayyun kayan nan ko iyayen zabiyar ne suka mata?" Ta tab'e baki ta tafi ta bud'e kofar kitchen tana lek'en ciki ta zaro ido tace "Waiii.. Ai kitchen d'in ma ba masaka tsinke,shak'e yake shima da kaya,ashe dai ba gwalagwalan k'arya aka dunga fantamawa da shi ranan bikin ba" Manar dai ta had'e rai sai kallonta take ta k'i ce mata komai,Waleed yana haurawa sama ya bud'e d'akin Afiyah,bacci ya sameta tana yi ta you d'ai² a gadon,ya shiga ya kulle k'ofar ya k'arasa kan gadon ya d'an bugi pillow d'in yana kallonta,sai da ya sake bugawa da k'arfi for the second time sannan ta bud'e ido,tana ganinsa tayi sauri ta mik'e zaune tana kallonsa da wani expression,yace "kin ma yi sallah kuwa?" D'auke kai tayi tace "haba don Allah sai ka wani buga min pillow kamar za ka tada k'ato? Kai baza ka iya min a hankali har na tashi ba?" From head har toes d'inta ya dunga kallonta,ta tab'e baki ta kalli agogo,cike da tsiwa tace "sallah kuma tunda na san wajibi ne a kaina ai dai dole nayi ko k'arfe nawa ne" da mamaki yake kallonta yace "a gidan ku kina kaiwa har k'arfe goma baki yi sallah ba?" A fusace tace "toh gajiyan daka tara min fa zai barni na iya tashi yin sallah da wuri aka ce maka? Please Waleed ba fa haka ake treating new bride ba,u are not romantic at all wallahi,haba don Allah sai kace ba namiji ba kai" wani kallo kawai yake mata fuskarsa a d'aure yana kad'a mata index finger yace "look Afiyah i won't tolerate this,a gidana kina min wannan iskancin bazan d'auka ba idan kin saba haka a gidanku ni daka ki zanyi kin sani.. Tun asuba na shigo na tashe ki kiyi sallah shi ne har yanzu baki yi ba,is this ur home training?" Wani kallo ta dunga masa daga sama har k'asa tace "kai don Allah baka ji kunya ba?" Ta yatsine fuska tana kallonsa tace "wani wai tun asuba ka shigo ka tashe ni,ain't u ashamed of ur self please?" Tsaki tayi ta sauka daga gadon da y'ar figigiyar rigar baccinta za ta nufi bathroom,ya fizgota da k'arfi ta dawo yana kallonta ransa a b'ace ya cillata gadon,ya fara k'ok'arin cire jallabiyar jikinsa,ta matsa k'arshen gadon da sauri cike da tsoro tace "me za ka min?" Ya mata wani kallo bai ce komai ba ya bita saman gadon,tsoro fal idanunta tace "Waleed stop" yace "ni sa'anki ne?" Da sauri ta girgiza masa kai,yayi k'wafa ya sauka sanda ya juya zai fita yace "ki same ni downstairs yanzu idan kin gama" daga haka ya fice ya bar mata d'akin yana gyara rigarsa,yana sakkowa Dadda ta mik'e tana kallonsa tace "wai ka ji daga nace amaryar baza ta fito gaisheni ba har yanzu,shi ne wannan mata take min fad'a kamar ta haife ni,ni dai gaskiya Mamman idan baza mu zauna lafiya da ita ba sai ince mata ta tafi na sameta a gida,don da kyar ma idan ba kwana zan yi a nan ba gaskiya,tunda dai ga d'akuna nan birjik a gidan" Waleed ya k'arasa ya kunna TV yace "za ta sakko yanzu ta gaishe ki" Dadda ta koma kan kujera ta zauna ta tsuke fuska tana kallon TV,zaunawa Waleed yayi kan kujera yana kallon Manar ta gefen ido,ta b'ata rai sai turo baki take,wani murmushi yayi jin footsteps a stairs ya juya,Afiyah ce take sakkowa sanye da riga da wani crazy jean damamme,tana ganinsu tayi still a gurin,Dadda tayi mitsi² da ido tana kallonta da kyau itama,Afiyah ta d'auke kai ta k'arasa sakkowa ta shigo cikin parlon,Waleed ya kalleta yace "meet my grandma and my lil sis Manar.." Dadda ta washe baki tace "sannu Amarya! An tashi lafiya?" D'auke kai Afiyah tayi ta tab'e baki murya can k'asan throat tace "ina kwana?" Dadda tace "lafiya lao,sai dai ko sunan ki ban sani ba har yau" a hankali tace "Afeeyah" Dadda tace "To Safiyah Mamman dai ga shi nan kin tsinci dami a akala,ni nayi wahala da shi tun yana lab'ub'unsa,wahalar da nayi da shi kuwa wallahi sai dai Allah ya ban ladan,amma banda nak'udarsa Babu abunda Asama'u tayi masa kiji in fad'a miki" d'aure fuska Waleed yayi yana kallonta,Afiyah tayi sauri ta mik'e za ta wuce sama tace "sai an jima Hjy ina aiki a sama" kallon Waleed Dadda tayi,ya kalli Afiyah fuskarsa a murtuke yace "mind u,aikin da kike ya fi su muhimmanci ne?" Dadda ta gyad'a kai tace "aatooo! Gara dai ka tambayeta muji idan aikin ya fi mu daraja da k'ima" Afiyah ta d'an tab'e baki tace "this is not my business.. Zan je nayi abunda ke gabana.." Da sauri Dadda tace "ba zancen kije kiyi abunda ke gaban ki ba y'ar nan,kinga yanzu dai ko karyawa ba mu yi ba muka fito gidan,Manar ma da kyar na tado ta muka taho,ko d'an baccin safen nan da ake yi ban bari ta yisa ba.." Manar na kallon Dadda tace "ni kin ji na ce maki ina jin yunwa ne,ko wani ya fad'a miki ban ci abinci ba?" Wani matsiyacin kallo Afiyah ta jefa mata ta kalli Dadda bluntly tace "eyyyahhh! Ai kam sai dai kuyi hak'uri dan ba komai a gidan yanzu haka" wani kallo Waleed ya dunga mata trying hard to control his temper,Dadda ta bud'e baki tana kallonsa tace "toh me kuka ci a gidan ku?" Afiyah dai tuni tayi wucewarta sama bata ma tsaya sauraren Dadda ba saboda kallon da taga Waleed yana mata,tana wuce ya mik'e da sauri ya bi bayanta,yana shiga d'akin ya kulle k'ofar yana nunata da yatsa cikin tsawa yace "let me give u this warning Afiyah,if u don't want to show the other side of me u've got to respect my family,albarkacinsu ya sa zan kyaleki yanzu,but na rantse da Allah zan yi taking action d'in da zai mugun ba ki mamaki idan baki maida hankalin ki jikinki ba,breakfast kuma nace ki je ki had'a masu yanzun nan kafin na chanja shawara.." Ya k'are maganar a fusace yana kallonta,gaba d'aya ta gama tsorata sai kallonsa take tana komawa baya,lokaci d'aya hawaye suka kawo idanunta ta fashe da kuka mai cin rai,ya d'auke kansa da sauri zuciyarsa tana bugawa,right from time a rayuwarsa ya tsani ganin hawayen mace,ya sassauta muryarsa a hankali yace "u know babu yanda za'ayi y'an uwanki su zo nayi musu gaisuwar wulak'ancin da kika ma grandma dit'a right?" Ta d'aure fuskarta tace "amma kana ganin wannan yarinyar fa ko gaisheni bata yi ba" shiru yayi da farkon sai kuma yace "mind u ba sunanta kenan ba" tace "wace ce d'in ka ita?" Ya kalleta da kyau yace "she is my cousin sis" wani kallo ta dunga masa,ya gyad'a mata kai,ta tab'e baki kad'an bata ce komai ba ta juya,yace "ki fito ki had'a musu breakfast" daga haka ya juya zai fita,ta waiga ta bisa da kallo,Allah ya sani so ba na wasa ba take masa,tun ganin farko da ta masa a gidansu taji idan ba shi kamar baza ta iya rayuwa ba,dan haka take jin za ta iya yin komai a kansa. Waleed yana dawowa parlon ya tadda Manar ita kad'ai tana kallo,tun da ta kallesa sau d'aya ta d'auke kanta,ya k'arasa kusa da ita yace "me yasa baki gaida Afiyah ba?" Ta turo baki ta k'i cewa komai,da k'arfi ya daki kujeran da take zaune yana kallonta da kyau yace "look! Duk sanda kika zo gidan nan dolene ki gaidata because she is my wife.. Kin ji abinda nace?" Ta had'e rai bata yarda sun had'a ido ba tace "why will i greet her? Beside ko kallona fa bata yi ba,shisa nima nak'i gaisheta tunda ba wajenta muka zo ba.." Kallonta kawai yake ganin yanda take masa magana cike da tsiwa,ya d'auke kai yana sakin murmushi,zai yi magana ya ji motsi a kitchen ya kalli gurin kafin ya mik'e da sauri ya nufi gurin,seeing Dadda alone tana magana,ya tsaya a door way yana kallonta yana sakin murmushi,tana k'ok'arin kunna gas take cewa "idan ba jaraba irin na Mamman ba da safen ma bazai iya hak'uri ba,shi ne ya kama ya bi figaggiyar zabiyar matarsa d'aki bayan tare suka kwana daren jiya k'wak'ume da juna,yana ji fa nace masa ban karya ba ga yarinya na taho da ita itama bata karya ba,dama da ya ta yarda ta biyoni ma muka zo fisabilillhi.."
#Share pls.
#Asli Smasher.
[2/2, 5:58 PM] My number 1: 25...
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*
Dariya sosai ta basa,tana ganinsa tayi shiru tace "a'a har ka fito Mamman?" Bai amsa ba yace "me za ki yi ne Hjy?" Dadda tace "iiiihhh! Yo bazan tashi na nemawa cikina abunda zan ci ba tunda na kwaso yunwar cikina,ga Manar ma bata karya ba na hana ta zama,da kyar ma fa ta yarda ta biyo ni... Abu dai da raina da lafiya ta,tunda ita wancan matar dake sama uwa tsuntsuwa baza ta kula mu ba,ni ba sai nayi mana ba ai dai babu wanda zai hana ni ko yace don me ko?" Murmushi yayi yana shafa beard d'insa yace "kiyi hak'uri yanzu za ta zo ta had'a maku" da sauri Dadda ta ajiye match d'in tana kallonsa tace "amma anya ka ce mata nice na haifi ubanka kuwa?" Yayi murmushi yace "a'a sai dai yanzu ki fad'a mata tunda kin zo" ya juya ya fita yana murmusawa. Afiya ta sakko parlor ta dunga yiwa Manar wani kallo mai cike da tsana tana tafiya,suna had'a ido Manar tayi tsaki ta d'auke kai,tsayawa Afiyah tayi tana kallonta zuciyarta kamar zai fito waje tace "u had better respect ur self idan ba haka ba wallahi gidana kika zo jikinki ne zai mugun yi miki tsami.. Banza k'aramar y'ar iska" kallonta Manar tayi da sauri tace "gidan ki ko gidan Yayana? Gidan ku na can kin baro sa malama don haka baki isa ki min warning a gidan Yaya ba.." Da sauri Waleed ya k'araso wajen jin muryar Manar,ya tsaya kallonsu da mamaki kafin yace "Lafiya? Me ya faru?" Manar tace "wai ce min take in shiga hankalina nan gidanta ne,kuma fa ba abunda na mata daga sakkowarta ta fara min fad'a tana min warning" baki sake Dadda data fito take kallonsu tace "iiiihhh! Ki shiga hankalinki kuma? Anya Safiyah kin san wace ce ita kuwa? To bari kiji wallahi wannan da kike gani ta fiye ma Mamman kowa a duniyar nan,kaji min zabiyar matar nan dai,ita da gidan Yayanta kice ta shiga hankalinta saboda baki da ta ido? To wallahi akan Manar sai nasa Mamman ya kora ki gidanku yanzun nan,gwara ma ki zageni da ki tab'a min Manar,duk da dai zagin nawa ma kinyi kawai dai ni me hak'uri ce na ja bakina nayi shiru ban tanka maki ba,kaji min shafaffiyar mata dai za ta saka ma jikata ido bayan gidan d'an uwanta tazo" mik'ewa Manar tayi kamar za ta yi kuka ta nufi k'ofa tace "ni dai sai kin taho Hjy,dama sai da nace bazan zo ba tun farko.." Dadda ta saki wani salati tana kallon Waleed da yayi still bai ce komai ba tace "yau ake yinta.. To wai dama Mamman baka zaunar da matarka ka sanar mata matsayin mu bane?" Shi dai bai ce komai ba yabi bayan Manar da sauri seeing that har ta fice parlon,yana fita yaga ta nufi gate ya bita ya rik'ota da sauri yace "ina za ki?" Kamar za ta yi kuka tace "ni dai gida zan tafi me zan zauna yi bayan kana gani matarka ta gama zagina" kallon eyeballs d'inta ya dunga