Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   36 / 66

105K to 108K   out of 196.2K words

akanki ne naga kin mallakesa ke kad'ai,zuwan da muka yi ma saboda muna son ki kiras ne ki lallab'asa ya dawo,ba yanda banyi da shi ba ya k'i" wani murmushi Afiyah tayi tace "ai kuwa idan haka ne ya zama dole na kirasa na lallab'asa har ya dawo" Mama cikin zumud'i tace "yawwa yar gari, idan ya tambayeki kice masa kin koma gidan tuni saboda gudun b'acin ransa" Afiyah ta gyad'a kai tace "yeah! That's why nake k'ara sonki my in-law" Mama tayi wani murmushi tace "to ya za'ayi,ai dole ya zame min na soki Afiyah saboda ke yar Sahibata ce" Afiyah tayi dariya tace "let me call him muji ya ake ciki" Mama tace "maza yi hanzari ki kirasa" sai da Afiyah ta yima Waleed kusan kira biyar bai d'auka ba har ta ji haushi za ta ajiye ta fasa dai ta k'ara kiransa,Waleed da duk kiran da ake masa yana kallo ganin daman d'auka ne baiba,sanda ya gaji da ganin kira daga number da bai san na waye ba ya d'auka cikin hasala yace "who's this fool da yake kira,ba ku san kuyi hak'uri ba idan kun kira sau d'aya ba'a d'auka ba?" Afiyah da taji wani b'acin rai kan maganar da Waleed ya fad'a ta daure tace "it's me Afiyah" saurin daga wayar yayi yana kallon number kafin ya mayar da ita kunnensa yace "ohh! How are u and what's up kike kira na by this time around?" D'an shiru tayi tana had'iye b'acin ranta tace "dama na kira ka ne tunda kai baka kira ba since ka tafi" ya tab'e baki yace "okay thanks zan kashe ina wani uzuri yanzun" Afiyah tace "alright but ai ya kamata ka saurareni da uzurin da yasa na kiraka ko?" Waleed cikin hasala yace "don't tell me that rubbish.. think munyi magana dake kika rantse sai kin rafi gidan ku?" Afiyah cikin kwantar da murya tace "but after then ai na koma gidanka ko?" Waleed yace "kada kimin k'arya" Afiyah tace "da gaske nake maka fa na koma,ka tambayi mahaifiyarka kaji" yayi wani murmushi yace "okay let me call u" bai jira cewarta ba yana sakin wani murmushi ya katse ya kirata video dan ya tabbar da gaske tana gidan nasa ko a'a,sanda Afiyah taga kiransa wani zaro idanu tayi tana nunawa Mama call d'in tace "me zan ce masa yanzu idan ya ganni a nan?" Mama tayi shiru tana tunani har sai da kiran ya katse,Hjy Izzatu tace "think he calls don ya tabbatar da maganarki na cewa kina gidansa,and if muna son ya yarda yabi all maganar mu ya zama dole mu koma gidan yanzun" Afiyah tace "but i think.." Da sauri Hjy Izzatu tace "don't say anything! Kawai ku tashi mu tafi aiwatar da abunda zai fiye mana,idan mun gama sai mu dawo" here suka yi shirin tafiya,sanda suka isa gidan get keeper ya bud'e musu yana masu barka da zuwa,suka shige compound d'in babu wanda ta damu ta amsa masa gaisuwarsa,Afiyah tayi parking suka fito suka wuce cikin gidan da sauri,mugun k'ura suka tarar gidan ya yi,Mama da Hjy Izzatu suka shiga suka d'auko tsintsiya suka fara karkad'e chairs,sanda suka share parlon tsaf suka goge,suka haura sama shima suka gyara,d'akin Afiyah kam sanda suka bud'e kallon² Mama suka yi ganin yanda Afiyah ta cika gadonta da kaya duk kuma sun yi k'ura,but haka suka shiga suka gyarasa suka kwashe kayan suka wanke suka shaya mata,kafin suka koma k'asan suka tarar da Afiyah zaune tana danne² a wayarta,dai² lokacin Mama tace "ki k'ara kiransa muji" Afiyah ta gyad'a kai tace "okay!" Then ta kira Waleed,kamar ba zai d'auka ba da farkon ya daure dai ya yi answering call d'in,Afiyah cike da kissa tace "D ka kira ni ina bathroom" Waleed yace "okay! We will talk later" ya katse wayar ba don ya yarda da abunda tace ba. Almost two days ranar da za'a fara biki ya shirya dawowa without ya sanarma kowa yana tafe,ko da yama driver waya yaje ya d'aukosa sai da ya masa warning kada ya sanarma kowa yana hanya,daga airport kai tsaye yace ma driver ya wuce da shi gidansa idan ya huta zai je su gaisa,driver yana saukesa gidan bayan sun gaisa da get keeper ya wuce ciki,gently yake tafiya yana k'arema ko ina kallo,sanda ya tsaya balcony ya danna bell,shiru d'in da yaji yasa shi cire keys d'insa ya bud'e,tun daga saka k'afarsa cikin parlon ya fahimci Afiyah ba ta nan kamar yadda ta sha masa k'aryan tana nan,ya gyad'a kai ya k'arasa shiga a nutse ya haura sama ya shigar da trolley d'insa bedroom then ya zaro wayarsa ya kirata,tana d'auka yace "where have u been?" Tace "ina gida fa" yace "wane gidan?" Tace "gidan mu mana" d'an shiru yayi then yace "gidan ku kika tafi?" Da sauri tace "a'a ina fa gidan mu ni da kai" wani gyad'a kai yayi yace "but i didn't see u.. Kin shiga wani guri kin b'oye kanki ne?" Afiyah ta zabura ta mik'e zaune tace "ban gane ba? Ina zanje ni kuma?" Kai tsaye yace "okay! Fito ga ni cikin gidan ina jiranki" wani zaro idanu tayi kafin tace k'ala ya katse wayarsa ya juya ya fita daga d'akin...




#Aasiif habibtiies wallah da kyar nayi typing d'in nan,i don't really know what happened to me duka haka nan dai nake jina tun da muka gama bikin nan,kuyi hak'uri da yanda kuka ga posting d'in yau i know it's short but ku min uzuri ba na jin dadin jikina duka.. Thanks for ur prayers,mun gama biki har an kai amarya..




#Asli Smasher.
[2/16, 8:31 PM] My number 1: 34...





*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*


*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*





Mummunan tashin hankali Afiyah ta shiga ta dunga kallon wayar hannunta,kafin ta daure ta kirasa back,yana gani ya share ta ya k'i d'auka,get ya fita ya samu get keeper d'in gidan nasa ya masa sallama yana kallonsa yace "ina matar gidan fa?" Get keeper yace "ai yallab'ai tun tafiyarka ba ta k'ara zama nan ba,sai sau d'aya da suka zo tare da Hajiyarka" Waleed ya dunga kallonsa yana maimaita hajiyarsa,get keeper ya tabbatar masa haka ne,Waleed ya gyad'a kai ya masa godiya then ya juya ya koma ciki,lokacin Afiyah sai k'ara kiransa take ya k'i d'auka,k'arshe da ta damesa yasa wayar flight mode. Afiyah taga bazai d'auka ba here tayi deciding kiran Mama ta sanar mata halin da ake ciki,Mama ta kitsa mata ta kira Dadda taji ko gaske ne ya dawo,dan ita bata ji a jikinta da gaske yake ba,Afiyah tace "toh.. Amma kin san ba ni da number ta" Mama tace "I'll send it to u" tana katse kiran ta tura mata number,sanda Afiyah ta gani ta kira Dadda,Dadda na d'agawa ta kwad'a sallama saboda hayaniyar da take ciki,Afiyah ta amsa tace "ina wuni Hjy?" Dadda tace "lafiya lau,waye don Allah,ni dai aiki nake ta yi ina hidimar bikin jikata,a bari idan na natsu bayan biki a sake kira na" Afiyah tace "Afiyah ce Hjy" Dadda tace "waye haka kuma?" Afiyah ta tab'e baki tace "matar Waleed" zaro ido Dadda tayi tace "iiiihhh! Dama Safiyah ce,ince an kai maki goron bikin kema?" Afiyah tace "a'a Hjy babu wanda ya gayyace ni" Dadda tace "tabb' d'i aiki ga mai k'areka,yanzu kina surukuwar gidan nan amma a rasa mai kai maki goron gayya,ai shi kenan ni dai kiyi hak'uri dama ba laifina bane,duk Asama'u ta k'i maida hankali ta shiga ayi hidimar biki da ita,da yanzu kema kin zo gidan ai" Afiyah tace "haka ne Hjy,but zan samu na shigo maki Allah sanya alkhairi,tunda an mance da ni ba'a gayyace ni ba" da sauri Dadda tace "a'a wallahi ko kusa ko alama,ni dai na gayyace ki yanzu,maza ki samu ki b'illo bikin ayi da ke kema" Afiyah tayi murmushi tace "toh Hjy ai kuwa zan zo" Dadda tace "toh na gode ni dai zan ci gaba da aiki" da sauri Afiyah tace "arhm! Hjy wai kuwa kuna waya da Waleed?" Dadda ta kame baki tace "ni jikar mutum hud'u,haihuwar mutum biyu.. Ina na isa mutumin ya kira ni,sai dai idan ni ina son masa magana nasa Manar ta kira min shi,kinji yadda muke yi da shi" Afiyah ta gyad'a kai tace "toh ai ni ya kirani yanzu yace min ya dawo k'asar" Dadda ta zaro idanu tace "a'a toh wallahi ni dai ban sani ba kin ganni dai sai hidima ake yi gidan,duk yawan jama'a ai bazai sa na mancesa ba,ni dai ban gansa ba" Afiyah tayi ajiyar zuciya tace "toh ina jin ko tsokanata yayi ya d'auka ba na gidan" Dadda tace "iiiihhh! Ina kika je idan baki gidan kuma?" Afiyah tace "a'a tunaninsa ko na tafi gidan mu ne" Dadda tace "ikon Allah to ke kuwa mai zai kaiki gidanku tunda sun aurar dake?" Afiyah ta yatsina fuska tace "ohon masa dai shi haka yake da zargin bala'i" Dadda tace "iiiihhh to ba dole yayi ba,ai haka uwarsa ma take kiji in fad'a maki,ni dai bari inje mutane na can suna ta jira na" Afiyah tace "toh Hjy sai na shigo" Dadda tace "toh ki fa samu ki shigo d'in" Afiyah tace "toh Hjy" suka yi sallama,suna ajiye wayar ta sake kiran Mama ta sanar mata yadda suka yi da Dadda,Mama tace "wallahi ina bak'in ciki da auren da yarinyar za tayi,ba don haka ba ai nima sai inda k'arfina ya k'are wajen ganin auren nan ya fasu,toh shi malamin dake mana taimako akai ya ce sai anyi babu fashi" Afiyah ta tab'e baki tace "ai shi isa yarinyar ma take ganin kowa a banza,ita a dole zata auri yaron nan,za ta shiga gidan sarauta to taga samu ta ga rashi kuwa tunda har ta tab'o ni" Mama tace "wallahi da za kiyi haka zan fi kowa farin ciki dan kin gama min komai a duniya idan har muka had'a k'arfi da k'arfe muka tarwatsa lamarin nan,wallahi da tsakaninki da Waleed sai dai mutuwa ya rabaku" nan Mama taita d'ora Afiyah hanya mara kyau,har sai da taga Afiyar ta amince za suyi yak'in tare,Afiyah ta gyad'a kai tace "ki kwantar da hankalin ki Mama,ai tunda na shiga maganar an gama komai,dama tun ranan da na fara ganinta na tsani yarinyar,ki manta da duk shirin da kike,yanzun za mu shirya mata gadar zaren da tana takawa zai dulmiye da ita" Mama tace "ai babu matsala.. Amma dai bazan fasa shirin da nake ba,burina kullum na kunyatar da yarinyar da uwarta,ke har tsohuwar nan ma dake nuna fifiko tsakanin yaranmu,yanzu dai ki shirya tunda ta gayyatoki ki shigo sai mu san abun yi kan lamarin" Afiyah tace "ni fa da banyi niyyar zuwa ba,na dai amsa mata kawai" Mama tace "ki dai shigo d'in akwai inda nake tunanin za muje dama" suka yi sallama akan sai ta zo d'in. Tun da ya fito gidan ya yiwa driver waya ya dawo ya d'aukosa ransa a mugun b'ace suka nufo family house d'in nasu,driver yayi parking cikin compound d'in ya fito,gently yake tafiya ya nufi b'angaren Dadda,ganinsa kawai tayi ya shigo da sallama a ciki,ta d'aga kai ta bisa da kallo can dai ta kasa hak'uri tace "waye wannan kuma?" Wani kallo ya mata bai tankata ba ya gaida tsofaffin dake parlon then ita da har lokacin bata bar kallonsa ba,Dadda ta kame baki tace "yanzu kuwa muka gama waya da matarka wallahi,ta kira ta gaishe ni,take ce min ka kirata ka ce ka dawo,ni dai nace ban ganka ba,ashe kana hanya kuma" shi dai bai ce mata komai ba ya mik'e ya nufi hanyar fita,Dadda ta tab'e baki tace "toh ai shi kenan tunda dai ka dawo d'in,sannu Allah huta gajiya" tuni ya fice ya barta sai suturu take,yana tafiya compound zai je apartment d'insu ya d'an kalli gidan su Manar,haka nan yaji rashin dacewar ya wuce,ya k'arasa balcony yayi knocking kafin ya tura k'ofar ya shiga da sallama,ya samu b'angaren da sauk'in mutane,mother ce sai wasu k'awayensu tun na skul sai Mommella da tazo k'asar suna hira,Mommella na ganin shigowarsa da fara'a a fuskarta tace "son saukar yaushe?" Yayi murmushi yana shafa sumar kansa yace "yanzu na shigo Mommella,kun zo lafiya?" Tace "lafiya lau alhamdulillah,ai tuni nake ta tambayarka akace min ba ka k'asar,thought ma baza mu had'u ba har mu koma" yayi murmushi yace "ina wuni?" Tace "lafiya lau,ya aiki?" Yace "alhamdulillah! Ya taro?" Tace "taro an gode Allah" ya gyad'a kansa yace "maa sha Allah² sanya alkhairi" tace "ameen" ya gaida mother da sauran matan da suke parlon ya mata Allah sanya alkhairi,after then ya mik'e ya fita. Bangarensu ya wuce nan ya samu babu mutane,ya wuce sama kai tsaye zuwa d'akin mahaifiyarsa,yayi knocking kofar daga ciki Mama da Hjy Izzatu da suke k'ulle² Mama tace "waye ne?" Waleed bai yi magana ba ya tura k'ofar da sallama,a tare suka kalli gurin Mama ta zaro idanu tana kallonsa tace "saukar yaushe?" Fuskarsa a d'aure yace "yanzu.. Ina wuni?" Tace "lafiya lau,ya hanya?" Yace "alhamdulillah!" Ya gaida Hjy Izzatu dake kallonsa,daga haka ya tashi zai fita,har ya je bakin k'ofa,Hjy Izzatu ta tab'o Mama ta mata alamar ta tambayesa,da sauri Mama tace "umm! Waleed nace ka je can gidan naka ne?" Yace "ehh! Daga can nake" wani fad'uwa gabanta yayi but da yake y'ar duniya ce ta wayance tace "aihoo! Ai kuwa Afiyar ma tana gidansu ta d'an yi rashin lafiya kwana biyu nace taje gida ta huta" Waleed dake tsaye door way ya waigo ya kalli mahaifiyar tasa calmly yace "but ya akayi bata sanar min ba,tace min tana gidan naje ban sameta ba?" Mama ta gwalo ido tana lallon Hjy Izzatu tace "kiji dai wani shirme a gurin Afiyah kuma,banda abunta meye na yiwa miji k'arya kuma?" Shi dai kallonsu kawai yayi ya juya ya fita bai sake cewa komai ba,ya k'arasa bedroom d'insa zai shiga Manar ta hauro saman tana ganinsa ta zaro idanu da gudu ta kwaso ta fad'a jikinsa,fuskarta d'auke da wani expression tace "Yaya! Yaushe ka dawo?" Yayi mata murmushi sai kallonta yake ganin yanda ta k'ara kyau tana wani glittering yace "yanzu" ta gyad'a kai tana masa murmushi tace "sannu da dawowa,ya hanya?" Yace "alhamdulillah" cikin zumud'i tace "bari na d'auko abu d'akin Aunty na dawo" yace "alright! But ki d'an samo min abinci please" ta amsa ta sakesa ta wuce d'akin Aunty,ya bita da wani kallo har ta shige then ya bud'e d'akin ya shiga,dai² lokacin Afiyah ta kirasa,kamar ba zai d'auka ba dai yayi answering,Afiyah cikin wani murya tace "kayi hak'uri D" fuskarsa d'aure yace "for what?" Tace "na rashin sanar maka da banyi ba" yace "me fa?" Tace "na je gidan mu ba ni da lafiya,and mahaifiyarka tasa na tafi" wani tsawa ya mata ransa a b'ace yace "wait please.. Kada ki raina min hankali,kina nufin tun da na tafi kike rashin lafiyar?" Tace "a'a amma.." A tsawace yace "but what?" Tace "bai fi sati biyu ba na bar gidan fa" ya gyad'a kai yace "okay! Me yake damunki?" Tace "ciwon mara mana,ka tafi ka barni cikin mugun yanayi.." Tab'e baki yayi tunawa da kafin yayi tafiyar yanda take zuba masa raki tun a first round trip bata iya jurewa,ragwancin bala'i ne da ita,k'arshenma ya zama idan yana son wani abu sai dai ya biyata in ba haka ba ko mutuwa zaiyi babu ruwanta sai ya dire mata cash d'in data yanka masa,k'arshen da abun ya ishesa ya koma yin azuminsa saboda rage ma kansa sha'awa,yayi wani murmushi yace "yanzun kin samu sauk'i ne ko da saura?" Tace "alhamdulillah! Na samu sauk'i" ya gyad'a kai yace "alright! Let me freshen up" tace "okay a fito lafiya" ya fara katse wayar ya cillar,a ransa yana mamakin halin mahaifiyarsa,tsaf ya gama fahimtar k'arya suka shirya masa but ya k'udurce a ransa duk zai bisu a hankali har ya hargitsa musu lissafi ta yanda basu yi tunani ba. Sanda ya shiga wanka ya fito Manar ta shigo hannunta d'auke da tray,ya bita da kallo har ta k'arasa shigowa ta ajiye,tace "Yaya ga abincin" ya gyad'a mata kai yace "thank u" ta fita tace "Yaya sai mun dawo" bai ce mata komai ba ya bita da kallo zuciyarsa a cunkushe,ko minti goma ba'ayi da fitar Manar ba Afiyah ta shigo gidan,ta mata kallon banza itama ta mata,ta wuce ciki ta samu Mama da Hjy Izzatu can k'arshen d'aki suna k'us²,suka gaisa Mama tace "to kin kirasa ne?" Afiyah ta gyad'a mata kai tace "ehh! Ya ce min zai yi wanka" Mama tace "alright! Let me call him muji yana ina yanzu" ta d'auki wayarta ta fara kiran line Waleed,Waleed dake tsaye gaban mirror ya kalli wayar ya sauke numfashi ya d'auke kai,sanda aka sake kira ya kai hannunsa yayi answering yasa wayar a handsfree,Mama ta fara cewa "Waleed kana ina?" Yace "ina bedroom" tace "ka tafi gida ne?" Yace "a'a ina nan" tace "alright!" Ta katse wayarta da sauri tana kallon Afiyah tace "maza tashi kije yana d'akinsa ki samesa daga nan ki sanar masa za muje unguwa" Afiyah ta amsa ta tashi ta fita,bedroom d'insa ta bud'e ta shiga,ya waigo da sauri jin an bud'e k'ofar idanunsa suka sauka kan Afiyah dake shigowa,ta k'arasa kusa da shi tana kallonsa tace "sannu da dawowa D" bai tanka ta ba ya wuce ya ajiye towel d'in hannunsa,Afiyah ta k'arasa a hankali ta zauna bakin gadon tana sake kallonsa,ya gama duk abunda zaiyi ya zauna yana cin abincin da Manar ta kawo masa,seeing that bai da niyyar mata magana tace "D za mu d'an fita da Mama" bai d'ago ba yace "baza kije ba" ta masa wani kallo tace "kamar ya bazan je ba?" D'ago idanunsa yayi yana kallonta yace "kamar dai yadda kika ji na fad'a" a tsiwace tace "wallahi baka isa ba Waleed,tun yaushe ka hanani fita,kai kayi tafiyarka ni ka hanani,akan me za ka

36 / 66