Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   39 / 66

114K to 117K   out of 196.2K words

ba,Mama ta k'arasa gaban Abba cikin kid'imewa bakinta yana rawa haka ma ko ina na jikinta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.. La'ilaha illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz'zalumiiyn,dan girman Allah Alh ka min banyani yanda zan gane,wallahi ban fahimce ka ba,ban gane ba sam kwakwalwata ta dod'e ba na iya fahimtar maganarka,wane Waleed d'in kama aure? 'Da na kake nufi? Wanda na haifa da cikina? Ko kuma wani mai irin sunan ka samu? Kayi min bayani don girman Allah Alhaji" Mommella dai da duka sauran occupants d'in parlon da kallo suka binta ganin yanda take hauka tuburan sun kasa d'auke idanunsu daga kanta,Mommellah dai ta yi tagumi sai kallon Dadda data tsume fuska ta k'i cewa komai take,Manar kam sai lokacin ta gama fahimtar abunda Abba ya fad'a few seconds ago,tun bayan maganarsa komai ya tsaya mata,ta daina fahimtar abunda ake fad'a,da kyar ta gano me yake faruwa da ita bayan ta gama tattara maganganun Mama,can ta juya a hankali ta kalli inda Waleed yake zaune,ganin ya rufe fuskarsa da palms d'insa ba ka iya gane wane irin yanayi ne akan fuskarsa ta sake duk'ar da kanta,ko da Abba ya tambayeta tana son Waleed k'asa magana tayi,Mama ta durkushe kan knees d'inta ta fashe da kuka,gaba d'aya ta birkice bata ma san inda take ba,Aunty dai sai murrmushi take cikin farin ciki tace "lallai alk'awarin Allah tabbatacce ne.." A hankali Waleed ya zame hannunsa daga fuskarsa da ya rufe yana kallon Mama da idanuwansa da babu komai cikinsu face zallar farin ciki,Abba ya waiga yana kallonsa yace "kana son Manar?" Sai da ya d'an kalli gefen Mama kafin ya gyad'a kansa a hankali,lokaci d'aya kuma ya mik'e ya fice daga parlon without ya bari Mama ta ga fitarsa,tafiya yake yana k'ara godema Allah a fili,fuskarsa ta kasa b'oye how happy he is,ranan yau jinta yake kamar an masa gafara,da Afiyah ya fara gamuwa za shi parking space,tayi masa murmushi tace "good afternoon D" bai ko tsaya bin ta kanta ba ya wuce ya bud'e motarsa ya shiga zai rufe ta rik'e murfin motar tana kallonsa tace "D wai me yake faruwa,na shigo nake jin rumors kamar wai ko an fasa auren,what's happening?" Bai tanka ta ba ya sake kai hannu zai janyo murfin motarsa,da sauri tana binsa da wani kallon mamaki tace "me kake wa murna haka D?" Murmushin da bata tab'a ganin ya yi ba ya sakar mata a hankali yace "kije ciki babu komai,i'm going out for a little bit" sosai taji dad'in murmushin da ta gani kan fuskarsa because tun da suka yi aure bata tab'a ganin murmushinsa kamar haka ba sai yau,sanda ta fara mayar masa da murmushin kafin tace "toh dear! But akwai bikin ne har yanzu?" Ya d'an gyad'a mata kai kafin yaja murfin data sakar masa ya rufe ya tayar da motarsa ya fice daga gidan,haka nan bayan fitarsa yaita zaga garin yama rasa ina zai nufa,Afiyah tabi motarsa da kallo tana murmushi then ta juya tana d'aga shoulder ta wuce cikin gidan dan amsa kiran da Mama ta mata,kafin ta k'arasa ta hangota tana tahowa hankalinta kamar baya jikinta,a rikice Mama take kallonta tace "Afiyah shi kenan asirinmu ya tonu.. Mun shiga uku mun lalace.." Da mamaki Afiyah take kallon Mama tace "lafiya? Me yake faruwa?" Gaban Mama sai fad'uwa yake,tayi still tana kallon Afiyah zuciyarta yana bugawa,Afiyah ta sake cewa "wai me yake faruwa ne,kimin bayani?" Cike da k'arfin hali Mama tace "sun munafurcemu wallahi.." Sai kuma ta sake fashewa da matsanancin kuka cikin tashin hankali tace "wallahi bai isa ba.." Ta juya da sauri ta koma cikin gida tana goge hawaye bata saurari Afiyah ba,tana shiga bedroom d'inta ta fara kiran Waleed jikinta sai b'ari yake,Waleed dake driving ya kasa controlling tears dake zubowa fuskarsa saboda farin cikin da yake ciki ya kalli wayarsa,ganin Mama ke kiransa ya d'an yi murmushi ya d'au wayar duk da yanda gabansa yake fad'uwa bai hanasa ya kashe phone d'in gaba d'aya ya ajiye ba,hannunta yana rawa ta sake kira sai dai wayan ya sanar mata a kashe,wani zaman y'an bori tayi ta d'ora hannuwanta aka ta kurma uban ihu,dai² lokacin Aunty tana haurowa saman fuskarta a washe ta k'arasa da gudu ta bud'e d'akin ganin Mama a zaune k'asan tiles tana risgar kuka Aunty bata san sanda ta fashe da wani dariya ba,Mama ta juyo a razane tana kallonta ta kasa daina kukan tace "Allah ya isa tsakanina da ku,duk kune munafukan da aka had'a baki da ku aka lik'ama d'ana auren yarinyar can,wallahi bazan tab'a yafe muku ba.. Ko zan yi yawo tsirara kuma sai na ga bayan auren nan tsinannu matsiyata annamimai.. Allah ya isa na ban yafe muku ba,wallahi Waleed d'ina bazai zauna da ita ba,sai na san yanda nayi na rabasu" Aunty dai da taga kaman Mama ba ta cikin hayyacinta juyawa tayi ta rufe mata k'ofan tana fad'in "ta Allah ba ta mutum ba wallahi,da yardar Allah sai kinji kunya,sai ubangiji ya nuna maki k'arshen ki a kusa,banza jahila mai jayayya da hukuncin ubangiji.." Daga haka ta wuce bedroom d'inta tana jan lafiyayyan tsaki. Dadda dai da ta san komai haukan da Mama ta dunga yi ne ya hanata magana,sanda ta fita ta bar parlon ta kalli su Abba tace "kada wanda yace mata k'ala,ku zura mata idanu ku dai,zanyi maganinta da kaina,duk haukarta kada wanda ya tanka mata.. Ku tashi kuje ku dai,Allah ya maku albarka.." Suka amsa duka suka fice,da farkon duk tunaninsu kukan da take ko maganar ne bai mata ba,sai suka ji sab'anin haka daga gareta kuma. Cikin rawar jiki Mama ta k'ara d'aukar wayarta tayi dialing number Hjy Izzatu ta kai kunne,Hjy Izzatu tana d'agawa Mama ta sakar mata wani kuka da k'arfi tace "k'awata duk inda kike kizo gidana maza²,ina cikin tashin hankali wallahi,dan Allah kizo da sauri,ni dai da nasan za'ayi haka da na bar yaron can ya aureta,dan Allah kizo yanzu mu koma gurin mutumin ya warware komai,wallahi na hak'ura duk abunda tayi min ita da uwarta na yafe musu duniya da lahira,ni dai a warware auren da Waleed d'ina kafin na had'iye zuciya na mutu,kina wa Allah da manzonsa kizo yanzu mu tafi kafin ajalina ya riskeni ban shirya ba.." Cikin mugun tashin hankali Hjy Izzatu tace "Waleed kuma? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,Waleed dai na mu d'anki na cikinki?" Mama dai sai kuka take tana gyad'a mata kai kamar tana gabanta tace "shi dai k'awata,shi nake nufi,ban san da yanda zan fad'ima Afiyah maganar ba,da wannan al'amarin dake faruwa wallahi da ma mutuwa nayi kafin ace haka ya faru,zama bai ganmu ba k'awata ki hanzarta kizo dan Allah" da kyar Hjy Izzatu ta lallab'ata tayi shiru,tace ga ta nan a hanya za ta k'araso su wuce yanzu,ta katse wayar ta ajiye tana juya kai tana fad'in "wai.. Wai.. Waiii Allah.." Tana tunawa da Afiyah sai taji zuciyarta yayi rauni sai ta k'ara fashewa da kuka,ta had'e kai da guiwa tai kuka tai kuka,can ta sake d'ago kanta ta d'aga hannuwanta sama tana kuka tana cewa "ya Allah me na maka kasa abubuwa suke faruwa dani haka marasa dad'i,Allah ya Allah kasa mafarki nake ba'a zahiri abun nan ya faru ba,ya Allah ka warware auren nan kafin na mutu,wayyo! Allah ka dubeni da idon rahama" kamar mahaukaciya sai kuma ta mik'e ta shiga dudduba d'akin can ta hango hijab ta d'auka ta saka ta d'auki mask tasa ta fito kanta a k'asa tana tafiya buzugur² kamar sabon kamu ta fice daga gidan ta nufi titi,tana tafiya tana sharar k'walla tana cewa "in sha Allahu sai an warware auren nan,na hak'ura ba gidan sarautan duniya ba koma masarautar aljanune a kaita,wallahi na hak'ura na yafe mata komai ya wuce.." Bayan barin Mama a gidan sabon walima aka tashi yi a gidan,bayan malaman da Aunty ta gayyato sun gama yi musu lectures akan zaman aure da rayuwar gidan miji,lokacin bayan an tashi,can k'arshen d'aki Manar suka k'ule ita da Ameerah,Ameerah sai kuka take saboda ita dai wannan auren ba zatan bata ma san da yaya za ta fassara shi ba,but yaya za tayi tunda iyayenta sun yanke hukunci akanta,dole haka za ta karb'i mijin har sanda za ta koyama zuciyarya sonsa,bayan sallan isha Mama suka dawo gidan a mugun jigace,dan ko ruwa bata shaba wunin ranar tun fitarta daga gidan,bayan Hjy Izzatu ta tafi ba k'aramin kuka tasha ba haka nan ta hak'ura dan mutumin ya fad'a musu aure bazai rabuba,ya ga rabo mai k'arfi a tsakani yana tunkarosa,haka nan dai tai shiru amma da zaran gyangyad'i ya fara d'aukanta sai tayi sauri ta farka,yaranta duk sun zagayeta sunyi zuru² dan yanda al'amarin ya kad'a musu ciki. Yunwan da ya damesu yasa Manar fitowa daga d'aki,dan yau kukan da suka yi ba kad'an bane duk da tana son Yayan nata,amma yanda al'amarin yazo dole ta girgiza,tana fitowa Dadda dake zaune parlon tun d'azu da ta gama kiransu suka k'i fitowa,ta zauna tayi jigum kamar wanda aka yima mutuwa ta rafka tagumi da hannu biyu,jin motsin bud'e k'ofa Dadda ta juya da sauri ta kalli Manar dake wucewa hanyar kitchen,ta bita da kallo jikinta a sanyaye tace "Manar!" Manar ta juya tana kallonta a sanyaye idanunta sun kumbura,Dadda ta yafitota da hannu tace "zo ya ki,ina ita y'ar uwar taki?" Manar tace "tana d'aki" Dadda tace "zo maza ki zauna kinji magana za muyi" a hankali ta k'arasa ta zauna jikinta a mugun sanyaye ta kasa kallon Dadda,Dadda ta kamo hannunta ta rik'e k'am² tana kallonta tace "ki gaya min gaskiya takwara,auren ne baki so,ko shi Mamman d'in ne bakya ra'ayi nasa ya sawwak'e maki?" Da sauri Manar ta girgiza mata kai tana turo baki tace "a'a" Dadda tace "to me yake damunki?" A hankali tace "babu komai" Dadda dai bata yarda ba sai kallonta take tace "anya kuwa?" Manar tayi saurin kallonta tace "babu komai fa" Dadda tace"ko dai haukar da uwarsa tayi ne yake baki tsoro?" Da sauri Manar ta gyad'a mata kai tana share hawayen da suka ziraro mata,Dadda tayi murmushi ta dafa kanta da muryar lallashi tace "ina so ki kwantar da hankalinki,babu abunda ta isa ta maki wanda Allah bai k'addaro faruwarsa ba,ki dauka da ita da duk maganaganunta shirme ne,kada ma ki fara bari su dameki har ki kasa yiwa mijinki biyayya kinji kou?" Manar ta sake gyad'a kai a sanyaye tace "tou Hjy" Dadda tayi murmushi tace "tashi ki shiga ciki ki kwanta abinki ki huta kinji,Allah ya maku albarka ya baku zaman lafiya" d'an murmushi tayi sai kuma ta kasa tashi,Dadda ta gwalo idanu tace "au bazaki tashi ba?" Manar ta turo baki tace "yunwa fa muje ji" Dadda tace "dama ai dole kuji yunwa,tun rana kuka kulle kanku a d'aki,nayi bugun duniya kuka ki kula ni,sai ki tashi kije zan kawo maku abincin yanzu da kaina kuci tunda na damu lallai sai kun ci.." Ta k'arasa maganar tana k'ok'arin tashi daga kan rug ta kamo hanunta tace "muje ki jira ni a ciki kada d'an banzan ya faki idona ya shigo.." Sanda ta kaita d'aki ta janyo musu k'ofar ta wuce kitchen ta d'ebo musu abinci cikin cooler da Aunty ta kawo mata d'azu,ta wuce bedroom d'insu ta samesu kwance,ta shiga da sallama fuskarta da fara'a tace "toh maza ku tashi kuci,kada a kaiku gidan mazajen su ganku da k'ashin wuya.." Kallon juna suka yi kafin suka sakko k'asa Dadda ta ajiye tray d'in ta fita tana fad'in "bari na kullo mana gidan kada gardi ya shigo mana" ta fita tana y'an maganganu,suna gama cin abinci kwanciya suka yi akan gadon suna kallon juna da tausayi within 20 minutes bacci yayi gaba da su,Dadda dake kishingid'e a parlor kan lallausan carpet taji ana k'ok'arin bud'e k'ofar parlor da sauri ta tashi ta zauna da kyau tana gwalo idanu tace "waye a nan yake tab'a min k'ofa?" Waleed ya shigo sanye da wani bugaggiyar shadda sai k'amshi yake ya d'aure fuska yana mata wani kallo yace "ina matata?" Ko kallonsa Dadda bata yi ba taja pillow ta k'ara kwanciya tace "je ka tambayi uwarka Fatima ko Hafsatu,basu fad'a maka ba yau za'a kai amare ba? Kuma ita Manar ma daga yanzu a nan gidan za ta zauna,tunda y'ar uwarta za ta bar garin sai ta je rakata har d'akinta idan sun dawo ta tare a can gidan,dan bazan yarda na bada ita yanzu ka hanata zuwa ba,haka kawai in tafi in barta nan a hannun zabiyar matarka ta cutar min da jika" takowa ya dunga yi yana kallonta yace "ni da mata ta kice ba yanzu ba? Idan ta zauna nan amfanin me za ta miki?" Ya wuce yayi hanyar bedroom d'insu,da sauri Dadda ta mik'e tsaye ta sha gabansa ta rik'e k'ugu,dole yaci burki yana kallonta cike da b'acin rai,fuskarta a d'aure ta rik'e hab'a tace "mara kunyar banza,zo ka fitar min daga gida tunda ba kai ka ginamin ba,ko naje na had'aka da ubanka Yaro" ganin ta dage babu alamun wasa ta wani rik'e k'ugu yasa ya juya ya fita daga gidan ransa duk a b'ace,Dadda ta rakasa da mugun kallo ta maida k'ofarta ta rufe harda saka makulli ta juya inda take kwance tace "fitinannun yara" kwanciya tayi abunta ranta fes tace "d'an kan uba yo ni za ka ma iya shege? Ka san kana son yarinyar ka kasa fad'a tun wuri,yanzu da na aurarta ga wani ai sai kasa Allah ma ya tambayeni.. Da ni kake zancen sai na wainaka sannan zan baka ita,idan ma na bari ka k'ara sata a ido ba suna na Azumi ba" ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya. Direct part d'insu ya wuce duk ranshi a dagule,kafin ya shiga yaga Amaar da Azaan tsaye a balcony suna magana,suna ganinsa suka gimtse dariyar da suke dan duk abunda ya faru tsakaninsa da Dadda suna jinsu,ko kallonsu bai yi ba ya shiga gidan ya haura sama ya shiga bedroom d'in Aunty,ya tarar da ita da Mommella suna magana,ya k'arasa shiga yaje kusa da Mommella a hankali ya kwanta a jikinta,Mommella ta juyo ta kalleshi tana shafa kansa tace "ya akayi Son? Did anything happen?" Da kyar ya iya d'ago idanunsa da suke cike da damuwa yace "Mommella please kisa baki Hjy ta ba ni ita mu tafi..."

#Hhhh! Angon zamani..🧗

#Asli Smasher.
[2/22, 3:47 PM] My number 1: 38...





*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*


*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*





Kallon² akayi tsakanin Mommella da Aunty,kafin Mommella ta zaro idanu tana kallonsa tace "ka rufa min asiri son so kake na tafi inda na fito ban shirya ba?" Ya d'an marairaice fuskarsa yace "to Mommella cewa fa tayi wai ba yanzu ba,sai ta raka Ameerah sannan za ta tare gida na" dariya Mommella ta guntse tana shafa kansa tace "to kayi hakuri mana har mu tafin,it's just one week fa kad'ai" d'ago kansa yayi da sauri yana kallonta sai kuma ya mayar da kansa ya kwantar a kan thighs d'inta,ji yake kamar ya fashe da kuka tsaban yanda yake jin wani jaraba na jagorantar duk wasu sassan jikinsa,yau kad'ai da yaji Manar ta zama mallakinsa duk wasu gab'b'ai na jikinsa da suke tabbatar masa da lafiyarsa suka motsa,jinsa yake wani iri,idan har bai samu abunda yake so ba yana ji ne kamar zai iya mutuwa kafin wayewar gari,d'an lumshe idanunsa yayi yana sauke ajiyar zuciya soundly,Mommella ta kalli Aunty itama ta kalleta tana girgiza kanta tana sakin murmushi,har bacci ya fara fizgarsa a kan k'afafun Mommella ya zabura ya tashi,Mommella tayi saurin rik'esa tana fadin "a'uzhubillah minash'shaid'inir rajiim.. What happened son?" Sauka yayi daga gadon jikinsa yana rawa yace "nothing Mom.. Sai da safe" Mommella ta bisa da kallo cike da tausayi tace "okay! Allah bamu alkhairi" har ya kai k'ofa zai fita ya waiga yaga duk shi suke kallo,ya b'ata rai ya turo baki a shagwab'e yace "ba dai kunk'i kusa baki ta bani matata ba.. Shi kenan" ya k'arasa fita,Aunty da Mommella me za suyi banda dariya,Mommella ta kalli Aunty tace "wannan yaron naki fa baida kunya" Aunty tace "haba Mommella kuma dai wannan ai jan rai ne ku basa matarsa mana idan lokacin tafiyan ya yi ai bazai hanata zuwa ba,ko bai bari ba ma idan an kwana biyu ai za suje ko?" Mommella ta d'auke kanta tana dariya tace "no my water inside,kije ki sa baki,ke da Hjy ba zance komai ba ni.." Yana fita bedroom d'in ya sakko k'asa a hankali yaga Amaar suna magana suna ganinsa suka d'auke kai suna dariya k'asa²,k'wafa yayi ya wuce zai fita yana hararansu,suka bisa da kallo suna k'us² ya d'an tsaya jikin k'ofa ya d'ora hannunsa kan handle ya kasa bud'ewa yana saurarensu,wani juyowa yayi da sauri suka d'auke kai,yayi k'wafa ya dawo idanunsa sun d'an canja sun k'ara shigewa saboda damuwa da baccin da ya fara,sosai suka k'ara masa kyau idan ba ka sani ba sai ka fassara sa da wani abu daban,ya zagaya ya zauna kad'an yana hararansu yace "kuyi dariyanku,ai lokaci zai nuna ku ne,duk sai na rama abunda kukemin... Gara ma ni kunga kalar nawa jaraban,wa yasan ku me za kuyi.." Ya d'auke kai yana d'an danna wayarsa daya ciro a pocket,Azaan ya kallesa yana masa murmushi yace "a'a kai dai daka san dad'in abun shisa ka kasa hak'urin yau.." Saurin kautar da wayar yayi yana kallon Azaan yace "uhn! Baza ku gane ba,ni kad'ai nasan what i'm going through,da wancan matar gara ace ma mutum a gwaurosa yake har yanzu" d'an zaro idanu Azaan yayi yace "kamar ya?" Amaar dai ya yi tagumi yana kallon Waleed yace "to kai bros idanu kasa mata ne?" Waleed ya kallesa yace "bazan sa mata idanu ba? Me zan mata tunda ba ta so,am i going to force her sai ta bani kanta?" Ya d'an girgiza kansa kad'an yace "no!³ I'm not that type,ni bazan takura mace ba,macen ma wanda ba

39 / 66