Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   15 / 66

42K to 45K   out of 196.2K words

yi shi kam ya duk'ufa aikinsa,sanda ta ji uwar bari cikinta sai k'ara yake ta tashi da gudu ta shige toilet ya d'aga kansa ya bita da kallo,fitsari tayi ta wanke bakinta da fuskarta ta fito ya d'aga kansa ya bita da kallo,ta d'aure fuskarta ta wuce tana murgud'a masa baki,ta k'arasa gaban table d'in ta kai hannu za ta d'auki ledan yayi saurin d'aukewa,ta kalleshi da sauri tace "ka ba-ni" idanunsa a cikin nata yace "u loose girl.." Ta dunga kallonsa ta kasa sake masa magana,ga shi bata gane me yace ba,nan da nan idanunta suka fara kawo ruwan hawaye ta kalleshi kawai ba tare da ta ce masa komai ba ta juya ta yi ficewarta daga office d'in,saurin tashi yayi ya ajiye ledar ya biyota yaga ta kama hanya za ta bar asibitin da sauri ya dunga nufarta tana tafiya tana share hawaye bata san ya biyota ba sai ji tayi an rik'ota ta juya a tsorace taga shi ne,yana mata wani kallo yace "ina za kije?" Hannunta ta fara k'ok'arin k'wacewa da taga baza ta iya ba tace "ka sake min hannu na tafi" yace "kin yi hauka ne?" Ta fashe da kuka tace "ni ka kyale ni,babu ruwanka da ni,ka barni na tafi gida" juyawa yayi yaga mutane har sun fara kallonsu yace "wuce muje" tace "ni ka kyale ni,bazan koma ba d'in" yin duniya yayi da ita ta k'i yarda su koma,ya shammaceta ya d'auketa ya juya ya nufi hanyar office d'insa,taga idanun mutane sai kallonsu ake da sauri ta kai hijab d'inta ta rufe fuskarta,ya tura k'ofar ya shiga ya k'arasa gurin table d'in ya d'orata a kai ya zauna kan kujeransa,fuskarsa a d'aure yace "bud'e idonki ki kalleni" kafad'a ta mak'ale masa tace "ank'i a bud'e d'in" ya zaro k'ananun idanunsa yace "ni kike cewa baza ki bud'e ba?" Ta d'aga masa kai tace "to ba fad'a kake ta yi min ba tunda muka taho,kuma baka bani abinci na ci ba" yace "na ji bud'e idon" tace "ni ka kyale ni gida zan tafi" yace "ba yanzu ba ki bari har lokacin tashi yayi" saurin bud'e fuskarta tayi a shagwab'e tace "kaiii! Kuma sai nayi ta zama a nan har dare?" Gyad'a mata kai yayi yana kallonta yace "baza ki zauna ba?" Tace "ni dai gida nake son komawa" yace "nan a dawa kike?" B'ata rai tayi ta d'auke kai tak'i kallonsa,yace "tambayarki nake" ta zumb'uro masa baki tace "to ni na san ina ka kawo ni" kallonta ya tsaya yi kamar zai yi magana sai kuna ya fasa yayi k'wafa ya d'auko ledar ya mik'a mata yace "karb'i nan" ta kalli ledar tana yatsina tace "mene ne shi?" A fusace yace "ban sani ba" matsawa tayi gefe ta b'ata fuskarta,ya mata tsawa yace "kin karb'a ko sai na daka ki? Kinga ina biye miki shi yasa za ki min iskanci?" Ta fara masa alamun kuka ya fizgota da k'arfi gaba d'aya ta fad'a kansa ta fasa masa k'ara a kunne,saurin runtse idanunsa yayi duk da ya ji fad'uwarta jikinsa hakan bai hana shi fad'in "ke meye haka?" Tace "ni me na maka?" Ya bud'e idanunsa ya kalleta fuskarsa a d'aure yace "sauka!" Tashi tayi daga jikinsa sum² tayi kamar za ta fita daga office d'in yace "idan kika fita ni da ke" ta tsaya a gurin ta waigo tace "to ni ce maka nayi fita zanyi?" Yace "ohoo miki" ta hararesa da k'arfi ta fizgi ledar ta wuce kan kujera ta zauna ya bita da kallo. Hankalin Dadda gaba d'aya ya tashi ganin wuni guda sur babu labarin Manar,yaran kuma duka sun dawo gida,duk wanda ta tambaya Manar sai yace bai san ina suka tafi ba,Ameerah ce ma ta fad'a mata tace ta gansu a skul d'insu ita da Yaya,rai a b'ace Dadda tace "to kuma daga na masa shiru sun tafi shi kenan sai yak'i dawo min da yarinya har yanzu,ko abinci fa bata ci ba ya d'auketa ya tafi gantali da ita" Ameerah tace "ai dai kin san ba zai b'atar da ita ba" cikin fad'a Dadda tace "ke dai wannan yarinya sam ba ki da hali,ni ina ruwana da bazai b'atar da ita ba? Ni dai gaskiya a yi masa waya ya dawo da ita idan ba haka ba zan je na samu uwarsa ko na d'auki mayafi na bisu" Ameerah tana jin haka ta mik'e tana dariya tace "idan kin san inda suka tafi?" Dadda take "ko ban sani ba sai na fad'awa Yaro yazo muje tare" da sauri Ameerah ta tsayar da dariyarta tace "ni dai kinga babu ruwa na,idan ya dawo kuma wallahi kada kice masa nice na fad'a miki sun je makarantar mu" a fusace Dadda tace "to uwata ba sai ki hana na gaya masa ba" Ameerah dai kamar za tayi kuka ta dunga kallon Dadda ta san tsaf sai ta fad'a tunda tace haka,da sauri ta juya ta bar gidan ranta duk a jagule,wasa² tun Dadda tana sa rai da ganinsu har ta fara cirewa,hankalinta gaba d'aya yana kan k'ofar shigowa duk taji motsi ta baza idanu tana jira taga waye zai shigo idan taga ba su bane sai tayi tsaki,su kansu masu shigan suna ganin haka ba sa zama suke ficewa,after maghreb ta idar da sallah ta tashi a fusace ta fita gidan,tana tafe tana mita sanda ta isa k'ofar gidan bata tsaya kwankwasawa ba ta hankad'a musu k'ofar da k'arfi,Aunty dake zaune parlour ta d'aga kanta taga waye Allah ya so bata yi magana ba ta ga Dadda tana shigowa,ta tashi da sauri tana fad'in "sannu da zuwa Hjy" fuskar Dadda a tsuke tace "Fatima wai ni kam nace kin san inda gantalallen yaron can ya d'auke yarinyar nan suka je?" Aunty girgiza kai tace "Hjy ba dai basu dawo ba har yanzun?" Cikin fad'a Dadda tace "ina fa suka dawo,ni dai da ya dawo min da ita ma hankali na duk ba zai tashi ba,kawai kuma daga na yi masa shiru shi kenan sai yak'i dawo min da ita har yanzu" cikin nuna jimami Aunty tace "gaskiya bai kyauta ba,amma bari na kirasa muji suna ina" Dadda tace "yi sauri dan Allah,ni idan ma bazai dawo ba,to ya dawo min da ita gaskiya" kiran line Waleed Aunty tayi ya d'auka yace "hello Aunty!" Aunty tace "Waleed ina kuka je har yanzu baku dawo ba?" Yayi murmushi ya kalli Manar dake gefensa yace "muna hanyar gida Aunty,yanzun za mu k'araso" ajiyar zuciya tayi tace "alright! Sai kun dawo" ta kashe wayar,idanun Dadda akanta tace "me yace miki kuma?" Aunty tace "suna hanya yace min" Dadda ta gyad'a kai tace "Allah sa da gaske yake" suna cikin maganar Mama ta sakko daga sana ganinta yasa su yin shiru,Dadda ta tashi da sauri tana tsuke fuska tace ma Aunty "to ni dai na tafi,idan sun dawo su same ni can gidan" Aunty ta amsa tace "sai da safe Hjy" Dadda dai tuni ta yi gaba bata tsaya amsawa ba,Mama ta bita da kallo tana tab'e baki,Aunty ma dai bata kalleta ba ta d'auke kanta,ganin babu fuska yasa ta neman guri ta zauna. Sanda suka shigo gidan kowa haushin kowa yake ji,yana yin parking ta bud'e ta fita da sauri ya kalleta yace "waye yaronki da za ki fita ki barma kayanki?" Ta juya ta kalleshi bata dawo ba tayi wucewarta b'angaren Dadda tana k'unk'uni,k'wafa yayi ya bud'e ya fito ya bud'e back seat ya d'auko kayan ya bita da su,yana shiga yaga Dadda a tsaye bai kulata ba ya ajiye kayan ya juya zai fita,a fusace Dadda tace "kai dai wannan mutumi ba ka da hali ko d'is" a fusace ya juya ya kalleta fuskarsa a d'aure yace "na yi miki wani abu?" Fuskarta a tsuke tace "da ka d'auketa ka tafi gantali da ita gidan wace uwar ka kai min ita?" Wani kallo ya mata ya juya yana tafiya yace "ina ruwanki?" Kamar za tayi kuka ta dunga kallonsa har ya kai k'ofa ta d'aga murya tace "ka fad'awa uwarka Asama'u" k'wafa yayi ya wuce ya fita,yana barin apartment d'in ta juya ta shiga d'akin,a tsaye ta ga Manar tana cire kaya sai b'ata rai take,ta bita da kallo tace "kema da yake ja'irar kanki ce ina maki magana kika barni tsaye saboda ga gantalalliya" d'auke kai Manar tayi tak'i kulata ta shige bathroom,haushin rashin maganar da bata yi mata ba yasa Dadda yin k'wafa mai ciwo ta fita. Da safe Ameerah ta fito daga wanka ta tarar Manar bata tashi ba,ta k'arasa da sauri ta d'aka mata duka,Manar ta tashi a tsorace tana sosa gurin,Ameerah tace "dallah ki tashi ke baki san za mu makara ba idan kika ci gaba da baccin?" Manar tace "kuma sai ki dake ni?" Ameerah tace "ni dai ki tashi ki shirya kafin Yaya ya shigo" jin ta ambaci Waleed da sauri ta tashi ta shiga wanka,ta fito ta shirya Ameerah tana tayata,suna gamawa ganin yadda uniform d'in suka mata kyau yasa Ameerah tayi mata pictures suka yi wasu tare then suka fito,Dadda ta d'aga kanta ta dunga kallonsu duk da ta ga kyaun da kayan suka yiwa Manar amma fushin da take yasa bata ce musu komai ba ta mik'e ta fara goge²,Ameerah ta tab'a Manar ta nuna mata Dadda,tab'e baki tayi tana tafiya tace "ina kwana?" Dadda bata kulata ba ta ci gaba da aikinta,Ameerah da neman tsokana tace "Hjy Dadda ana gaisheki" juyowa Dadda tayi a fusace tace "bazan amsa ba" Ameerah ta kyalkyale da dariya ta rik'e hannun Manar da sauri suka fita apartment,Dadda ta bisu da harara tace "kuma ba zance a dawo lafiyan ba" Manar da har sunje balcony ta jiyota ta dawo ta tsaya bakin k'ofa tace "dama waye yace ki kulasa?" Dadda ta juya fuskarta a tsuke tace "nima bazan kula ki ba d'in" Ameerah dai sai dariya take musu da kyar ta janye Manar suka bar gurin,suna tafiya Ameerah ta kalli Manar tace "sis idan munje skul kada ki yi dariya ki kama ajinki ko a class kada ki dunga kula mutane sosai" Manar tace "me yasa?" Da baki Ameerah ta nuna mata su Deejah dake tsaye parking space suna kallonsu tace "saboda wancan" Manar ta kalli inda Ameerah take nuna mata ta tab'e baki,suka k'arasa Deejah da Diyanah sai cika suke,Manar ta d'auke kanta bata kulasu ba suka tsaya jiran driver,ko a mota da suka tafi k'ala bata ce ba har suka je skul,duk yadda su Diyanah suke yar musu magana Ameerah ma bata yarda ta kulasu ba suka musu banza. Sanda suka shiga class gaba d'aya idanun y'an class d'in suka yo kan Manar ta d'aure fuskarta ta k'i dariya a dole sai ta nuna itama tana da aji,sosai bata manta abunda Ameerah tace ba,Ameerah ta rik'e hannunta suka je gurin zamanta suka zauna,wata k'awar Ameerah Nusaiba dake zama bayan seat d'inta tayi murmushi ta mik'awa Ameerah hannu suka gaisa,then Manar da tak'i ko da murmushi,ranar gaba d'aya babu abunda Manar ta gane saboda turancin da teachers d'in suke yi,duk malamin da ya shigo ba ya musu Hausa,shisa har aka tashi cikin k'unci take,da suka dawo gida ma driver yana yin parking ta fice a fusace ta nufi part d'in Dadda,Ameerah ta biyota tana mata dariya saboda ta san matsalarta,itace ma da taga abun ya yi yawa taita rarrashinta tana cewa za ta saba,za ta iya itama idan ta mayar da hankali,Manar a gaba Ameerah tana binta suna shiga Manar tayi cilli da jakarta ta saki kuka,Dadda ta fito kamar an cillota tana ganin Manar tsaya tana kallonta tace "ke kuma lafiyarki za ki shigoma mutane da kuka?" Ameerah dake k'ok'arin zama tace "nima tun d'azu muke yi da ita a skul" Dadda ta kalleta tace "mene ne kuma wani zuk'ul?" Ameerah ta fashe da dariyar da bata yi niyya ba tace ''makaranta fa nake nufi" Dadda ta tsuke fuska tace "shi makarantar ne dan kinibibi baza'a fad'a yadda kowa ya sani ba?" Ameerah dai sai dariya take,Manar ta tashi a fusace ta share hawaye ta nufi d'aki tana cewa "ni wallahi ba zan sake zuwa ba daga yau" Ameerah ta mik'e da sauri tace "wallahi ba ruwa na ke da Yaya" a fusace Dadda tace "ai kuwa tunda ba ta so ba ta sake zuwa shegen makarantar nan,dama shiru nayiwa Yaro ko da yake sanar min zai mayar da ita makarantar yahudawa nan" Ameerah ta zaro idanu tace "ke dai Dadda Allah babu ruwanki ita da Yaya idan yaji" Dadda cikin masifa tace "yaji mana,zai zare mata rai ne?" Ameerah ta fizgi jakarta da sauri ta shige ta barta sai mita take,tana shiga d'akin taga Manar duk ta yi watsi da uniform d'in,ta zauna bakin gado sai kumburi take,ta k'arasa ta tsince mata kayan ta ajiye saman gado,a fusace Manar ta sake watsi dasu k'asa tana hararanta,Ameerah ta sake tattarawa tana kallon Manar tace "sis kada kiyi fushi please!" Kamar jira Manar take ta kulata ta sake fashewa da kuka,Ameerah ta zauna kusa da ita tayi tagumi ta zuba mata ido,can da ta gaji ta mik'e da sauri bata kulata ba ta d'auko wayarta a cikin press da suke b'oyewa,ta dawo ta zauna kusa da ita ta fara kiran Azaan,ba'ayi taking long ba ya katse ya kirata,ta d'auka tana sauke ajiyar zuciya tace "Yaah Azaan ina wuni?" Yayi murmushi yace "lafiya lou Ameerah ya gida da su Aunty?" Tace "suna lafiya" yace "Dadi fa?" Tace "itama haka" Manar dake gefenta tana jin ta ambaci sunan Azaan ta tsayar da kukan,cikin sanyi murya Ameerah tace "Yaah Azaan u know what?" Yace "nope! Sai kin fad'a" ta d'ago a hankali za tayi magana suka had'a ido da Manar da ta kafeta da idanu,harararta tayi da sauri ta tashi daga kusa da ita,Azaan yace "ina baby fa?" Tace "ka ganta nan mun dawo skul wai baza ta sake zuwa ba" yace "saboda mene ne?" Tace "wai kawai dan malaman suna yin turanci ita bata ganewa shi ne tace baza ta sake zuwa ba" murmushi Azaan yayi yace "kyale ni da ita zan kirata yanzun naji matsalarta" Ameerah ta gyad'a kai tace "Allah Yaya kada ka biye mata,ita kullum sai ta dunga biyewa Dadda,bata san ita ce take cutuwa ba,ko fa islamiyya ma bata zuwa,komai aka ce mata sai tace bata iya ba" Azaan ya gyad'a kai yace "alright! Bari na kirata yanzun" Ameerah tayi ajiyar zuciya tace "toh!" Suka yi sallama suka ajiye wayar,ko minti biyu ba'ayi ba ya kira Manar through video,ta kalli wayar da Ameerah ta ajiye mata ta kai hannu ta d'auka sai b'ata rai take..



#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2021.



                    *♡MANAR¸.•💥*
               


*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA  

_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._


                                14.

#Intermission..

     
      A hankali tana kallonsa tace "Yaya!" Fuskarsa a d'aure babu alamun wasan da ya saba mata yace "mene ne matsalarki da yasa kika ce baza ki sake zuwa skul ba?" A shagwab'e tace "to ba sune ba duk sai su dunga yin magana da turanci" yace "ke kuma turancin ne ba kya so,right?" Ta gyad'a masa kai,ya sauke numfashi yace "ba ku da lesson teacher ne a gida?" Ta gyad'a kai tace "to su ba sun iya ba!" Girgiza kansa yayi yace "ok! Zanyi magana da Amaar,idan an nemo lesson teacher shi kenan?" Tayi saurin kallonsa za tayi magana ya katseta yace "ba na son k'orafi,lesson teacher ne matsalarki and na gama da wannan maganar" yana fad'an haka dan kada ta samu damar sake masa magana ya katse kiran,saurin kallon Ameerah tayi za ta fara mata masifa da sauri Ameerah ta fice tana mata dariya. Da dare Amaar ya shigo part d'in ya gansu zaune ita da Ameerah tana koya mata assignment d'in mathematics,ya zauna yana kallonsu idan Ameerah tayi sai Manar tace bata gane ba ta sake mata,Ameerah ta gaji tace "ke wallahi na gaji tun d'azu fa muke yi,amma wai baki gane ba,kawai kin k'i ki nutsu ni sai wahalar da ni kike yi" Amaar dai sai murmushi yake yi,ai fa nan itama Manar d'in ta mik'e cikin fushi tace "kada Allah yasa kiyi d'in baza'a je makarantar ba,daga yau na dena zuwan.." Karaf maganarta sai a kunnen Waleed dake shigowa,wani tsawar da ya mata yasa tayi saurin waigawa,ya kalleta yace "me kika ce?" Tayi shiru tana kallonsa,a tsawace yace "ba dake nake ba?" Zumb'uro masa baki tayi tace "ni fa bance komai ba" yace "really?" Ta k'i kallonsa saboda ta san ba gaskiya ta fad'a ba,idanunsa a kanta ya gyad'a kai yace "Ameerah tell me what really happened kafin na shigo" Ameerah tace "Yaya cewa tayi baza ta sake zuwa skul ba" yace "saboda me?" Ameerah ta kwashe yadda suka yi ta fad'a masa,ya gyad'a kai yace "good! Kada kije kin ji,ba ni za ki yima ba" daga haka bai sake ce mata k'ala ba ya nemi guri ya zauna fuskarsa babu alamun ya san yadda ake dariya,Dadda ta fito d'aki tana binsu da kallo tace "hayaniyar me kuke min kuma?" Waleed da hankalinsa ke kan TV yace "hayaniya kamar wasu k'ananun yara?" Tace "yo da meye ku Allah na tuba?" Wani murmushi yayi ya tashi zai fita ta rakasa da kallo bata ce sai dai komai ba har ya fita,Ameer ya kalli Manar yace "zo ki zauna k'anwata,muga assignment d'in" hararar Ameerah tayi ta k'arasa kusa da shi da littafin ta mik'a masa,ya karb'a yana dubawa ya d'ago ya kalleta yace "ke yanzu mene ne abun wahala a nan?" Tace "Yaya nifa yadda take yi min ne ban gane ba" yayi murmushi yace "ok! Ki maida hankali ki ga abunda zanyi,idan mun gama za kiyi da kanki" ta gyad'a kai tace "toh" tiryan² Amaar ya sake gwada mata yadda za tayi,kafin ma ya tambayeta ta gane tayi ihu tace "wallahi na fi gane naka Yaya" ya sake yin murmushi yace "oyah! Yi na gani idan kin gane da gaske" ta d'auki biro ta fara yi tana masa bayani kamar yadda yayi

15 / 66