Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   16 / 66

45K to 48K   out of 196.2K words

mata,tana gamawa yayi mata tafi yace "ashe dai akwai kan hankaline baki mayar ba" tayi dariya ta juya ta kalli Ameerah ta harareta tace "Yaya itama fa dan bata min kamar yadda kayi ba shi yasa ban gane ba" Ameerah tace "wallahi k'arya kike yadda yayi nima ai haka na miki" Manar ta harareta tace "Hummm! Ba wani nan" Ameerah tayi dariya ta tashi tace "ke kika sani gobe ai sai kisa Yaah Amaar d'in a jaka ku tafi skul tare" Manar tace "ehh za muje d'in ina ruwanki" gwalo Ameerah tayi mata tace "woooo! Slow leaner" haushi Manar taji ta tashi a fusace Ameerah tana ganin haka tasa gudu suka fara zagaye parlon,Amaar dake zaune yana danna wayarsa ya musu banza bai kulasu ba sai da suka dameshi ya musu tsawa,duka suka zube suna haki Manar sai hararar Ameerah take daga k'arshe tayi k'wafa tace "ai dai za mu had'u" Ameerah ta mata gwalo tace "mu had'u d'in na zane ki" dariya Manar ta fashe da tana nuna Ameerah tace "ni za ki daka? Lallai ma yarinya jikinki zai yi tsami na kama ki" wani kallo Amaar ya musu yace "baza ku min shiru da bakunanku a nan ba" suka yi tsit babu wadda ta sake cewa k'ala har ya fita. Ranar alhamis da yamma Amaar ya kaita islamiyyar su Ameerah,da yake tsarin makarantar alhamis da jumu'a da yamma,Saturday and Sunday kuma da safe shi ma dai da kyar aka kaita ajin su Ameerah saboda sunyi kusan izu 30,sai da malamin yaga tana kuka wiwi sannan yace a kaita amma idan yaga bata yi k'ok'ari ba a jarabawar k'arshen term za'a mayar da ita ajin k'asa tayi tsalle ta dire tace ta amince,ranar saturday da yamma lesson teacher da Azaan yasa a nemo mata ya fara zuwa,suna kan yin lesson Waleed ya shigo gidan,ya gansu ita da Ameerah zaune balcony d'in gidan Dadda ana musu lesson ya kallesu ya d'auke kansa ya wuce bai musu magana ba,sanda ya sake fitowa sun gama lesson teacher har ya tafi,cikin isa ya shiga parlon yayi sallama a k'asan mak'oshi,Ameerah dake kwance tana game da wayarta ta amsa,ya kalleta fuskarsa a d'aure yace ke "waye na ganku da shi?" Ameerah tace "lesson teacher d'inmu ne" ya kalleta da kyau yace "waye ya d'auka muku lesson teacher?" Tace "Yaa Azaan ne.." Wani kallo ya mata yace "Azaan?" Ta gyad'a masa kai "ina Manar?" Ya tambayeta fusakarsa a d'aure har ya fi na lokacin da ya shigo,a tsorace tace "tana ciki" wucewa yayi hanyar d'akin gadan²,Ameerah tana ganin haka bata tsaya shawara ba ta shafawa kanta lafiya ta bar gidan kafin ya juyo kanta. Manar ta fito band'aki d'aure da towel ta zauna bakin gado tana yatsina fuska,gaba d'aya bata jin dad'i,tun shigowarsu take jin kamar something is about to happen,tayi shiru tana tattab'a cikinta zuwa mararta da ta rasa gane asalin inda yake mata ciwo tsakanin gurare biyun Waleed ya bud'e k'ofar d'akin,footsteps d'insa da ta ji suka sa ta d'ago kanta a hankali ta bisa da kallo,cikin fushi bai ko kula da yanayinta ba ya fara mata fad'a "uban waye yace ma Azaan ya d'aukar muku lesson teacher?" Kawar da kanta tayi tak'i masa magana,haushin yadda ta masa yasa shi fizgota da k'arfi yana huci yace "ba magana nake maki ba za ki min shiru saboda kin raina ni?" Kuka ta fashe masa da shi ta fara ture shi,ya rik'eta sosai yana mata wani kallo yace "stay still kafin na gaura miki mari" da muryar kuka tace "ni ka kyale ni bani da lafiya" wani kallon karki raina ma kanki hankali ya mata kafin ya bud'e bakinsa yace "me yake damunki?" Hannu ta watsa tace "nima ban sani ba" ya mata kallon rainin hankali yace "baki sani ba?" Ta gyad'a masa kai tana share hawaye,ya tab'e baki yace "ke kika sani" fizge jikinta tayi za ta koma kan gadon ya rik'o arm d'inta da k'arfi sai da ta saki k'ara,cikin shagwab'a tace "Yaya meye haka wai?" Ya juyata ta fuskancesa yace "waye ya ce ma Azaan ya d'aukar muku lesson teacher?" Tace "to ni nace masa?" A fusace ya doke mata baki yace "amsan abunda na tambayeki kenan?" Sheshshek'ar kuka ta fara tace "ni wallahi ka kyale ni na kwanta" yace "idan nak'i fa?" Cikin kuka tace "zan fad'awa Dadda" sakinta yayi ya koma gefe yana kallonta yace "Oyah! Je ki fad'a mata" ta murgud'a masa baki ta koma ta zauna tana share hawaye,yayi k'wafa cikin kaushin murya yace "daga yau kar na k'ara ganinsa a gidan nan,idan ya zo gobe ku sanar masa ba kwa buk'ata,kin ji me nace?" Saurin d'ago kanta tayi ta kallesa tace "to saboda me?" Yace "ban sani ba" tab'e baki tayi cikin k'unk'uni tace "a'a wallahi ni dai muna so" a fusace ya mata tsawa yace "ba shawarar ki na nema ba,umarni na bayar" da muryar kuka tace "ni wallahi bazan ce ba" mamaki shimfid'e a fuskarsa yace "ni kike fad'ima haka?" Tace "to ba kai bane kace muce bama so" kansa ya gyad'a ya wuce yana fad'in "kada kuce kinji,ki bari na sake ganin ya zo kiga yadda zanyi da ke a gidan nan" yana gama fad'a ya wuce ya fita,k'unk'uni ta fara masa tana ganin ya tsaya kafin ya waigo da gudu ta shige toilet ta kulle k'ofar,ta jingina jikin k'ofar ta murgud'a baki tace "kuma baza'a ce d'in ba" ficewa yayi gaba d'aya daga gidan ransa a b'ace,ya wuce apartment d'insu yana shiga yayi sama,yayi knocking d'akin Aunty Ameerah da ta gudo nan ta b'uya ta yi zaton Manar ce ta biyota ta tashi tana fad'in "ke wallahi kar kizo ki shafan kashin kaji" ido biyu suka yi da Waleed dake tsaye gurin fuskarsa a d'aure ya watso mata tambayar "waye yace ma Azaan ya d'aukar muku lesson teacher?" Tambayar ne yasa tsoro ya kamata ta fara in'ina,ya mata tsawar da sai da hanjin cikinta suka juya a tsorace tace "Yaya nifa" ya mata tsawa yace "idan kika sake kika min k'arya jikinki zai yi tsami" hawaye suna sakkowa fuskarta tace "Yaya ba ni bace" a kausashe yace "waye?" Ta fara in'ina tace "yay... Ya shi ne fa ya d'aukar mana" yace "ko kuka ce masa kuna so ko?" Ta girgiza masa kai da sauri tace "a'a Yaya" ya d'aure fuskarsa yace "Uhn! Waye yace masa kuna so?" Tayi shiru tana matsa fingers d'inta ya mata tsawar da yasa Mama fitowa daga d'akinta ta tsaya bakin k'ofa tana kallonsu bata ce musu komai ba,Waleed yace "za ki fad'a min gaskiya ko sai jikinki yayi tsami?" Girgiza masa kai tayi da muryar kuka ta fara magana,ya mata tsawa yace "idan kika bari naga drop d'aya na hawaye a fuskarki sai na fasa miki jiki" ta dunga k'ik'k'ifta idanuwa tana mayar da su tace "Yaya wallahi ba mu muka ce masa muna so ba" yace "Uhn! Waye yace masa?" Tace "babu kowa" yace "k'arya kike.. Cikin biyu dole za'ayi d'aya,ko dai ke ko Manar wata ta fad'a masa" saurin girgiza masa kai tayi tace "a'a Yaya" ya kalleta yace "ya akayi ya sani idan baku fad'a masa ba?" Tace "Yaya maganar Manar ne fa da tace baza ta sake zuwa skul ba shi ne ya sani,ya tambayeta me yasa tace haka,shi ne ta fad'a masa ita ba ta gane turanci,shi ne ya tambayeta ba mu da lesson teacher a gida tace masa ehh,shi ne sai yace zaima Yaah Amaar magana,jiya kuma shi ne kaga ya zo" ajiyar zuciya yayi yace "daga yau ku fad'a masa kada ya sake zuwa gidan nan" tace "Yaya" a fusace yace "ba shawararku na nema ba,umarni na bayar,idan ba'a ji ba kuma toh!" Ya mata wani kallo ya juya zai bar gurin idonsa sai cikin na Mama da ta kama k'ofa ta rik'e tana kallonsu,d'auke kansa yayi zai bar gurin cikin gadara tace "dawo ka zo" tsayawa yayi a gurin yace "Mama ina da wani uzuri yanzun" a fusace tace "ba shawararka na mema ba,zo ka wuce muje" babu musu ya wuce cikin d'akinta ta mayar da k'ofar ta rufe,tana jifansa da wani kallo tace "meye ruwanka a cikin maganar da naji?" Ya d'ago da sauri ya kalleta yace "Mama" tsawa ta masa "dallah rufe min baki.. Munafiki kawai,kullum na maka magana akan yarinyar nan sai kace min babu komai,yanzun uban me ya had'aka da shiga shirginsu uban iya?" Yace "Mama ba fa wani abu bane kamar yadda kike zato.." Kyakykyawan mari ta d'aukesa da shi,cikin fushi tace "wallahi Waleed ka fita idona na rufe,ina fad'a maka ba ka ji ko? Billahillaziiy yarinyar nan ko tare aka haifeka da ita sai ka rabu da ita,idan ba jaraba irin naka ba,mene ne had'in kifi da kaska? Ina ruwanka da shiga abunda bai shafeka ba?" Shiru yayi ya sunkuyar da kansa zuciyarsa sai tafasa take,Mama tace "na rantse da ubangijin al'arshi mad'aukakiya idan baka rabu da yarinyar nan ba zan ci ubanka da gaske,zan nuna maka other side of me dan ka gane ba kai ka haife ni ba" bai sake cewa komai ba sai ajiyar zuciyar da yake saukewa mai cike da b'acin rai,tace "ka ji na fad'a maka ko? Daga yau kuma daga yanzu babu ruwanka da yarinyar na,kai ko wuta kaga za ta fad'a ka kauda idonka,ban yarda ka taimaka ba ka kyaleta ta fad'a" saurin d'agowa yayi idanunsa sun yi wani irin jaa mai ban tsoro yace "Mama wannan wane irin k'iyayya ne haka? Me yarinyar nan tayi miki kika tsaneta? Mama Manar fa jinina ce me yasa kike son lallai sai mun rabu? Mama ki fad'a min me yasa ba kya son alak'ata da ita?" Cikin fushi tace "Waleed ni kake ma wannan tambayoyin?" A zuciye yace "me yasa bazan tambayeki ba? An tab'a k'i babu dalili? Haba Mama me yasa za kina haka? Idan da kara Manar y'a ce a gurinki kema fa saboda y'ar k'anin mijin.." Kafin ya k'arasa ta sake d'auke shi da mari,ya d'ago ya kalleta yana sakin mata murmushi mai ciwo yace "Mama saboda wannan maganar kika mare ni?" Cikin hayaniya tace "idan ka sake min maganar yarinyar nan zan maka abunda baka yi zato ba" yayi murmushi yana shafa cheek d'insa da ta mareshi har sau biyu yace "u know what Mama?" Ta masa banza bata kulasa ba sai kallon da take jifansa da shi,yace "Mama akan d'an wannan maganar kin mare ni,idan kuma kika san *INA SONTA* kuma fa? Za ki kashe ni kenan?" Mummunan fad'uwa gabanta yayi ta runtse idanunta cikin tsawa ta kira sunansa "WALEED!" Bai fasa mata murmushi ba ya gyad'a mata kai yace "k'warai Mama ina son Manar,aurenta nake son yi,na ajiyeta k'ark'ashin inuwata" tsawa ta sake masa idanunta suna fidda hawaye tace "Waleed ni kake cema aurenta kake son yi? Yarinyar da ta gama gantali da yawon bin kwararo,mazan larabawan nan duk sun gama k'wak'wuleta,wane ne bai san abunda kakarku ta kaita tayi ba kenan,irin wannan matar kake ik'irarin za ka auro min matsayin suruka? Wallahi in har ina raye baka isa ka auro min jinin Maryam ba,matar da ta yima y'ar uwata bak'in ciki ta kankane komai,ta hana k'anin ubanka auren Rabi k'anwata,wane soyayya ce za ta had'a ni da ahalinta? Wallahi baka isa ba Waleed,ka ji na rantse maka matuk'ar ina raye baza ka tab'a auren jinin Maryam ba,kai ko wanda suka santa baza ka aura ba bare tsatsonta.." Murmushi yayi da ya bayyana hak'oransa duk da ba ya cikin mode d'in yin hakan yace "Mama kada kija da hukuncin ubangiji,wallahi za ki iya mutuwa ayi auren.." Mummunan damk'ar da ta kaiwa wuyansa da hannuwanta biyu ta shak'esa yasa shi yin shiru,cikin gushewar hankali tace "na rantse da zatin Ubangiji baza ka aureta ba,kai ko mutuwa za kayi wallahi sai ka rabu da karuwar yarinyar nan" yana mata murmushi yace "karuwa Mama? Kina da shaidar cewa ta tab'a karuwanci? Mama ki fad'i abunda ko gaban ubangiji kika tsaya za ki iya kare kanki,kada ki fad'i abunda zai zama hujja akanki" sake shak'eshi tayi tace "dan kutumar ubanka ni kake fad'i ma haka?" Duk da yadda ta shak'e masa wuya bai hanasa zaro ido ba,yace "Mama zagi?" Cikin hayaniya tace "na yi d'in dan ubanka! D'an iskan yaro kawai,billahillaziiy zan d'aga maka nono,akan yarinyar nan ban k'i na tsine maka kabi duniya ba idan yaso kowa ya rasa.." Sosai kalamanta na k'arshe suka ba shi tsoro suka girgiza gobensa,a hankali wasu hawaye masu cike da k'unci suka fara zubowa daga idanunsa yace "Mama akan maganar za ki tsine min" ta hak'ik'ance tace "wallahi Waleed zan iya tsine maka muddin baka bar maganar nan ba" hankalinsa idan ya yi dubu ya gama tashi,ganin Mama yake kamar ta samu matsala a cikin kanta,ya daure yace "Mama kuma kina cikin hayyacinki kika fad'i haka?" Tace "hauka nake dan ubanka.." Kallonta ya dunga yi hawaye suna zubowa daga idanunsa,lokaci guda ya daina ji ya daina gane komai,duniyar kanta ji yake ta tsaya masa cak,ya zube kan k'afafunsa ya rik'o k'afafunta cikin firgici yace "Mama dan girman Allah kada kiyi min haka,wallahi idan kika ce na rabu da ita zan iya rasa numfashi,Mama ki sassauta min dan Allah wallahi dan ni kad'ai aka halicci Manar,Mama kada ki janyo abunda zaisa ki rasa ni" hankad'esa tayi daga jikinta cikin bak'in ciki tace "wallahi sai dai ka mutu Waleed,amma idan kaga ka auri yarinyar nan ba na numfashi a doron duniya.." Daga bayanta taji ance "Wannan kalmar ta ki dai² yake da na jahilin da bai tab'a shiga aji ba,bare ya zauna gaban malami,shin za kiyi jayayya da hukuncin ubangiji ne..?" Gaba d'ayansu suka juya suka kalli Aunty dake tsaye bakin k'ofar,cikin tsananin tashin hankali Waleed yace "Aunty dan Allah kisa baki ta barni na aureta.." A fusace Mama tace "na rantse da Allah baza ka aureta ba,idan ka dage kuma sai dai mu raba hanya ni da kai,daga ranar da ka aureta na yafewa duniya kai.." "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Aunty take fad'a tana jijjiga kai,cikin tsananin mamaki da tashin hankali take kallon Mama,though ta san wace ce kishiyarta amma bata fasa fad'in "yanzu Maman Waleed akan wannan maganar kike ik'irarin yafe d'anki wa duniya.? Ba-ki fa kike nufin za ki masa?" Mama ta juya ta kalleta tace "na rantse da Allah Fatima zan yafesa wa duniya muddin bai bar maganar ba.." Shiru d'akin ya d'auka tsayin wani lokaci banda kukan AC babu abunda kake iya ji,Waleed kam tuni yayi suman zaune kalaman Mama sun girgiza shi ba kad'an ba,babu abunda yake ji a cikin kansa face kalamanta da suke masa amsa kuwwa a cikin kunnuwansa,addu'ar ma bakinsa ya kasa kama kowacce iri saboda tsananin firgicin da ya shiga,a hankali Aunty dake ma Mama kallon ta tab'u ta k'arasa kusa da Waleed tana kallonsa da tausayawa tace "Waleed!" Ya d'ago kansa da sauri ya zuba mata idanu kukan ma ya tsaya ya kasa yi,Aunty ta dafa kansa cike da lallashi tace "ka yima mahaifiyarka biyayya Waleed iya yadda za ka iya,ina maka umarnin cire tunanin Manar a ranka wata rana idan da rabon ta zama mallakinka sai kaga cikin sauk'i ubangiji ya dawo maka da ita.." Kasak'e ya mata yana kallo ta ya kasa cewa komai,Mama dake gefe tana musu wani kallo banda cika babu abunda take kalaman Aunty sun mugun k'ona mata zuciya amma sam ba ta shirya kulata ba saboda ba ta da lokacinta...

                  *#Turk'ashi... Wannan shi ake kira tashin hankali wanda ba'a sa masa rana.* 😢

     #Alhamdulillah alaa kulli halin! My habibtiiys as u all know my book is not for free y'an amanata wanda suke shirye su bini i'm done with free pages cikin hukuncin mai duka,kamar yadda nasan sauran novels suna fita,mine will go round as usual and i can't prevent that,but if u should come across it it's not for free,ki biya kafin ki karanta because ba zan yi muku Allah ya isa akai ba,if u want any favour pertaining to the book ki neme ni muyi magana ta digit d'ina,my book is 200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank. And then u contact me through my digit 08165726609 to be added in the paid group. For those da suke ganin za su samu a bati kuma i call upon u ku sani ba'a banza yake ba,i repeated my book is not for free,idan kin karanta baki biya ba ke kika sani muddin ba daga gurina yake ba,billah u'll prove a inda baki ba zai iya shaidanka da komai ba..

#Share pls.
#Asli Smasher.
[1/19, 6:29 PM] My number 1: 15...



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA


*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's 200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*




Aunty tana gama fad'a masa haka ta juya ta fita cike da jimamin hali irin na Hjy Asama'u,Mama da ta rakata da mugun kallo tayi tsaki ta juya ta kalli inda yake durk'ushe har lokacin cikin rashin tabbas,da kakkausar murya tace "ina fatan ka ji duk maganganuna kuma ka haddace su,kada kayi zaton wasa nake maka,ya zama dole ka rik'e shi a cikin kanka.. Idan har ni na haifeka ba kai ka haifi kanka ba laazim kayi min biyayya.. If not kuma ga fili ga mai doki,ni da kai zan ga wanda zai yi nasara" tana gama fad'a itama ta juya a fusace ta fice had'e da banging masa k'ofar,runtse idanunsa yayi da k'arfi,gaba d'aya ji yake duniyar ta masa zafi,he only wish mafarki yayi duka maganganunta yana farkawa ya fad'a mata tace ta amince,sanda ya bud'e birkitattun idanunsa ya sake tabbatarwa kansa da gaske al'amarin ya faru,da kyar ya d'ago hannuwansa ya rufe fuskarsa da su,ya shafe ak'alla mintuna talatin zaune a gurin ba tare da ya iya motsin kirki ba bare ya san abunda ya kamata yayi,sanda yaji bud'e k'ofarta yayi k'arfin hali ya tashi ko gabansa ba ya iya gani ya

16 / 66