Manar Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Fatima Category :  Romance

Chapter   21 / 66

60K to 63K   out of 196.2K words

ta bud'e motar hawaye suna zubowa idanunta tace "thank u" ta juya ta wuce gidan da sassarfa. Jikin Manar ya yi sanyi a hankali ta kalleshi tace "Yaya me yasa za ka sata kuka?" A fusace yace "keep ur mouth shut.. Kada ki dame ni da surutun banza da wofi." Ya tada motar ba tare da ya kalleta ba yayi horn get keeper ya bud'e musu suka fice da mugun gudu a hanya motar ya yi shiru Manar dai bata daddara ba tace "Yaya! Ni dai gaskiya ban ji dad'i ba" without ya kalleta yace "baza kiji ba kuma" ta kalleshi fuskarta a had'e tace "to kai wai Yaya a haka ma za kayi auren kana sa ta kuka?" Tsaki yayi yace "ki rufe min baki kafin na bigeki" ta kallesa tace "dan na ce haka shi ne za ka doke ni?" Ya d'auke kansa bai k'ara kulata ba,ganin ya mata shiru itama sai bata sake ce masa komai ba tayi fushi ta juyar da kanta,suna shiga gidan yayi parking ta bud'e motar ta fita cike da haushi ta wuce part d'in Dadda,ya bud'e motar yana kallonta har ta kusa shigewa yana niyyar fita ya rufe motar wayarsa ta fara ring,ya juya ya d'auka yaga Mama ke kiransa,ya d'auka ya kai wayar kunnensa,cike da bariki Mama tace "Waleed kana ina?" Yace "ga ni parking space wani abu ne?" Tace "har ka dawo ne?" Yace "ehh!" Gyad'a kai tayi tace "ya kuka yi da Afiyah?" Shiru ya d'anyi though jikinsa ya bashi ta san wani abu game da yadda suka yi da ita yace "Mama ta ce miki wani abu ne?" A fusace tace "wane irin magana kenan? Ina tambayarka kana tambayata?" Yayi ajiyar zuciya yace "mun gama magana da ita" Mama tace "ya kuka yi? Nawa ka tura mata kud'in gyaran jiki da k'unshi?" Yayi shiru yace "she didn't told me" tace "saboda me? Ko dai baka je ba?" Yace "not at all Mama yanzun fa na shigo gidan" gyad'a kai tayi tace "kada ka min k'arya yallab'ai,yanzun muka gama waya da ita tace min baka je ba,so kafin ka b'ata min rai maza ka juya kaje ka sameta" yace "amma fa Mama" a fusace tace "but what? Me za ka fad'a min? Halinka yanzu wanne ne bak'o a gurina?" Yana ji yana gani haka Mama ta masa tass a waya,kan dole kuma ba don yana so ba ta sa shi komawa,yana shiga compound d'in gidan ya fito ya jingina da motarsa fuskarnan tamkar hadari,Afiyah da tasa a mata observing idan ya dawo tana jin ance ga shi can tsaye ta buga tsalle taja gyalenta ta fita,tana masa murmushin mugunta ta k'arasa cike da kissa tace "Welcome back D" ya sake d'aure fuskarsa bai tankata ba,ta matso kusa da shi ta tsaya kamar za su manne da juna tace "muje ko?" Ya d'auke kansa yace "fad'i abunda kike son cewa ba ni da lokacin b'atawa" wani dariya tayi tace "no problem! Tunda ka dawo ai bazan ji haushi ba ko me za kayi min" ajiyar numfashi yayi yace "idan ba ki da abun fad'a zan tafi" tayi dariya tace "yadda ka tafima haka za ka sake dawowa" murmushin takaici yayi ya d'auke kansa..




#Share pls.
#Asli Smasher.
[1/23, 9:00 PM] My number 1: 19...





*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*


*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*





Yana kallon wani guri yace "me kike tak'ama da shi?" Tayi dariya tace "kai baka san da me nake tak'aman ba?" Ya tab'e baki suka yiwa juna shiru,shi yana tunanin makomarsa a gurin Mama,ita kuma wani farin ciki ya mamaye zuciyarta ganin Mama ta sa shi dawowa and ba tare da yaran d'azu ba,gaba d'aya ta k'uresa da idanu tana k'ara kallon how cute he is tana hango yadda za ta ja zarenta cikin colleagues d'insu,duka team d'insu y'ay'an manya ne,daga governors,president,ministers sai y'ay'an manyan ma'aikatan gwamnati,kaf babu d'an wani mai k'aramin matsayi a cikinsu,haka samarinsu duka y'ay'an manyan gwasake ne,ita kad'ai ce kusan za'a ce ta fita daban but duk da haka shima ba wai matsayi ne baida shi ba,mahaifinsa ne dai bai taka wani matsayi a gwamnati ba but da yawa sun san wane ne field marshal na wannan lokacin,dole za'a san matsayin Waleed a gurinsa kasancewarsa k'ani a gurin Abbansa,sosai ta shagala da kallonsa sanda yaga ba ta da niyyar magana yayi siririn tsakin da ya dawo da ita hankalinta,fuskarsa a daure yace "ba na son kallo.. And idan za kiyi magana ina jinki if not kuma zan tafi and don't ever think wai ni zan sake dawowa nan,ba Mama ba ko waye za ki fad'ima sai abunda naga damar yi,fahamtiiy?" Dariya tayi tace "yanzun wai sai ka sake tafiya?" Ya mata banza,tace "alright! Bari na fad'a ko kada naita wahalar da angona" kamar ta caka masa mashi haka yaji kalmarta,cike da isa tace "maganar tsare²n biki tunda kai baka ce komai ba har yanzun,and bama ka tab'a zuwa ba bare na san abunda ya dace,that's nace Mama ta turoka muyi maganar because ni ban fad'a musu baka tab'a zuwa ba" ya wani d'age kai yayi fuska kamar ma ba da shi take magana ba,sanda tace masa "yanzun ya kake gani za ayi?" Strictly yace "kinga Malama ba abunda ya kawo ni kenan ba,ina ga ki had'a maganarki guri d'aya ki fad'a amsa d'aya nake tunanin zan iya ba-ki a duka maganar ki,so if u're ready go on.." Wani kallo ta dunga binsa da shi kafin tayi murmushi tace "D duk fa kafin muyi aure ne kake min wulak'ancin nan" shi dai bai tankata ba sanda ya d'auki mintuna biyar,yaga ta k'i magana kawai ya bud'e motarsa ya shiga ya sauke glass d'in kad'an cike da aji yace "idan kina da wani maganar da baki fad'a ba just give me a call ko ki tura min sak'o,ok bye.." Ya mayar da glass d'in ya rufe,tsaye tayi tana kallonsa har yayi zooming off ya bar gidan,yana fita ta kira Mama a waya ta sanar mata ya tafi basu gama magana ba,Mama cikin fad'a tace "wane iskanci kenan haka?" Tace "And he said duk abunda nake buk'ata kada na kirasa na tura masa text" Mama cikin jin haushi tace "alright! Kada ki damu zai dawo ya same ni" bayan sun gama waya,Mama ta fara kiran Waleed but abun mamakin wayoyinsa a kashe,ta gyad'a kai tace "da ni kake zancen za ka shigo ka tarar da ni.." Waleed kam cikin kwanciyar hankali yayi parking bakin get dan ma kada Mama taji alamun shigowarsa ya san dole tana da masaniya akan abunda ya faru tsakaninsa da Afiyah,ya rufe motar ya fito ya shiga gidan da k'afarsa,direct ya nufi gidan Dadda dan can kad'ai yake zaunawa ya samu nutsuwa babu hayaniya babu takura da fad'an Mama,yana shiga Dadda tace "kai kuma fa?" Ya kalleta ya wuce ya zauna kan kujera,sai lokacin yaji zai iya mata magana yace "me ya faru?" Tace "yo na ga kun fita da su sun dawo suna fushi,kai d'in ina ka tsaya?" Ya d'auke kansa yace "ina ruwanki da inda na tsaya? Ko dai kin fara saka min ido?" Harara ta wurga masa ta tab'e baki tace "Allah ga ni.. In ji kishiyar mai doro,kai dai wannan mutumi ba ka da kirki ko d'is,dan ka ga za kayi aure ko,shi ne kake kwab'a min magana,to Allah ya so dai kafin kayi nima na yi auren bare ka gwada min iya shege.." Murmushi yayi bai sake mata magana ba ya d'auki wayarsa da ya jefa flight mode yana kallon pics d'insu na d'azun kafin su fita,sosai ya shagala da kallon pictures d'in Manar da ta fito d'aki tana video call da Azaan ta wuce kan kujera ta kwanta tace "Yaah Azaan Allah ni dai ban yarda ba" yace "yanzun ya kike so ayi?" Tace "kawai ka taho tare da Mommella ni dai ina son ganinka" dariya yayi mai sauti yace "banda ganin da kike min yanzun har wani kike buk'ata?" Ta gyad'a masa kai a shagwab'e tace "ai wannan a waya ne ni dai kawai ku taho tare,ka ji?" Yace "no way Guddi akwai ayyuka sosai gaba na" ta marairaice tace "to ni dai Allah idan baka zo ba zan daina kulaka" ya zaro ido yace "me yayi zafi gemu zai ci wuta?" Dariya ta kyalkyale da shi tace "ba sai asa masa ruwa ba" yayi murmushi yace "ni dai ki bar maganar zuwan nan ba zan samu dama ba" haushi taji sosai cikin muryar kuka tace "to kada ka zo d'in Allah na daina kula ka ma daga yau.." Tana fad'ar haka tayi disconnecting,cike da jin haushi ta jefar da wayar gefenta tana jan tsaki,kamar ance ta d'ago kanta suka had'a ido da Waleed ya kafeta da wani mugun kallo fuskarsa kamar za ta tsage tsabar b'acin rai,ta murgud'a masa baki ta d'auke kanta dan shima d'in haushinsa take ji,bai iya ce mata komai ba ya mik'e a fusace ya fice daga gidan,ta bisa da kallo tana tab'e baki a hankali tace "za kayi za ka gama." Tun daga ranar da ya fita gaba d'aya bata k'ara saka shi idonta ba,ya daina shigowa gidan,kullum suna zuwa skul da su Deejah da yake ba ta kulasu sai ta kasa tambayar yana nan,yayin da a gefe d'aya rashin ganin san yake mugun damunta,har zuciyarta take jin damuwa da rashinsa but duk ta tattara komai ta ajiye gefe,ba ta son kiransa saboda ba ta san uzurin da ya hanasa zuwan ba,ranar alhamis lokacin saura kwana uku bikin wajen 6pm sun taso islamiyya,haka nan ranar suka jin tafiyar k'afa ita da Ameerah suna tafiya suna hira da yake ranar drivern nasu Mama ta aikesa,and su kad'ai ne Deejah basu je ba suna hidimar biki,suna tafiyar motar Waleed ya giftasu da mugun gudu ya wucesu lokacin ko nisa da makarantar ma basu yi ba,bin motar da kallo suka yi Ameerah tace "Laaa! Kinga Yaya ya wuce mu,dama ya tsaya ya k'arasar da mu gida wallahi na gaji" Manar tayi shiru tabi motar da kallo bata ce mata komai ba har suka zo bakin get d'insu suka shige ciki,suna tafiya compound za su wuce gidan Dadda,Manar ta juya ta kalli parking space d'insu Waleed,ai kam nan ta gansa tsaye jikin motar da ya shigo da shi yana waya yana murmusawa,haka kawai taji wani haushi ya sake ciyota a fusace ta wuce bata tsaya ba,da kuka ta shiga gidan ko ta kan Dadda dake zaune parlor bata biba ta wuce d'aki da gudu tana rafzar kuka,Dadda dake hira da Tasallah k'awarta da tazo biki suka saki baki suna kallonta har ta shige,Ameerah ta shigo da sallama bayan ta gaisar da su ta wuce da niyyar zuwa ta cire uniform d'inta tana shiga Dadda ma ta shigo,taga Manar kwance sai kuka take,hankali tashe ta k'arasa tana salati ta d'ago ta a rikice tana tambayarta "me aka maki kike kuka ni jikar laraba? Wani malami ne ya bugar min ke yanzu na d'au gyalena mu koma?" Da sauri Ameerah ta tari numfashinta tace "babu wanda ya doketa fa" Dadda tace "Iiiiiihhh! Idan ba dukanta akayi ba me zaisa tayi irin kukan nan na fitar rai? Ni dai gaskiya ba'a kyauta min ba wallahi sam,haka kawai a dunga sa min yarinya kuka ana cutata,koma uban waye yaje shi da Allah,wallahi ban yafe masa ba.." Ameerah tace "Hjy ina jinfa Yaya da muka gani ne bai d'auko mu ba ya barmu muka taho da k'afa" Dadda tayi mitsi² da ido tace "waye kuma haka?" Ameerah tace "Yaya Waleed" tace "ganinsa kuka yi shi mutumin?" Ameerah tace "ehh! Muna fitowa islamiyya lokacin an tashi shi ne to ina jin da bai tsaya ba,yanzun kuma muna shigowa muka ga ashe gida ya taho,ina jin shi ne dalilin kukan nata" cikin jin haushi Dadda tace "shi Mamman d'in ne yak'i tsayawa ya d'auko min ku?" Ameerah tace "ehh!" Dadda ta girgiza kai tace "ni wallahi ban san yaushe Mamman ya zama haka ba,bak'in ciki da mugun halin uwarsa ban san sanda ya kwafesu ba.. Amma bari naje na samesu har shi har uwar tasa naji ko ita tace idan ya ganku kada ya rage muku hanya" ta fita tana mita,Tasallah dake zaune ta d'aga kai tana kallonta ganin ta nufi hanyar fita da sauri tace "to ina kuma za kije kike sauri?" Dadda ta waigo a masife tace "kyale ni dai naje bin ba'asi,idan ba bak'in ciki da mugun hali ba,wai ace kamar Mamman ne zaiga yaran nan suna tafiyar k'asa ya kasa d'auko su sai dai su zo sugansa a gidan" Tasallah tace "a'a wannan dai ba halin k'warai bane gaskiya,kuma Waleedi dai na san bazai musu haka ba sai dai in zugasa aka yi ya walaak'anta su" Dadda tace "Uhn! Nima dai sai da nayi wannan tunanin,amma bari naje dai naji ko Asama'u ta hanasa d'auko su" da sauri Tasallah ta mik'e tace "ai kuwa dai nima banga ta zama ba wallahi muje kinji mubi ba'asi" suka fita suna mita,Waleed da har lokacin yake tsaye gurin da su Manar suka barsa yana ganin shigarsu Dadda gidansu yace "we'll talk later" ya katse kiran ya wuce gidan Dadda fuskarsa a d'aure,ko da ya shiga bai tarar da su a parlor ba ya wuce bedroom da yake jiyo maganar Ameerah sama²,yana tura k'ofar suka waiga tare idanun Manar sunyi ja tsabar kukan da tayi sun d'an tasa,Ameerah ta gaisheshi ta nufi k'ofa ta fice,tsaiwa yayi door way yana kallonta,ta d'auke kanta tana sake share guntayen hawayen da suke mak'ale idonta,a hankali ya kalleta yace "me aka miki kike kuka?" Ta masa shiru ta k'i ba shi amsa,yayi k'wafa yace "ba dake nake ba?" Tashi tayi za ta shige bathroom ya fizgota da k'arfi sai da tayi k'ara ta turesa cikin b'acin rai tace "ni ka sake min hannu,ina ruwanka da ni?" Wani kallo ya mata yace "stay still.. Magana za muyi" da muryan kuka tace "ni bazan yi magana da kai ba" sosai yake kallonta da mamaki yace "me yasa baza kiyi magana da ni ba?" Cikin kuka tace "ba dan ka ga za kayi aure shi ne ka daina kula ni ba,kuma ko ganinka ma ba ka bari nayi" yayi still yana kallon yadda take kuka bil'hak'k'i ya zuba mata idanunsa jikinsa duk ya yi sanyi,sanda ya gaji da sauraron kukanta ya kai hannunsa ya mata whipping tears d'in a hankali yace "shhhiii! It's ok.. Kukan ya isa haka" duka ta kai masa a k'irji tace "ni ka kyale ni,kayi tafiyarka ba ruwana da kai" yace "i said ki bari haka,ko kina so muyi fad'a?" Ta girgiza masa kai da sauri,ya matso kusa da ita a hankali yace "Oyah! D'auko hijab muje,idan mun dawo sai ki fad'amin laifin da na miki kika ce baza ki kulaki ba" ta kallesa da sauri tace "ina?" Yace "kin manta?" Ta gyad'a masa kai,yace "kayanku fa a gurin tailor" zaro ido tayi tace "Yaya na manta" yace "ni ban manta ba,maza yi sauri muje" k'aton hijab ta d'auko har k'asa tasa akan riga da wandon uniform d'inta gudun kada ta b'ata masa lokaci suka fito,a hanya suna tafiya shi da ita yace "Uhn! Me ya faru kika ce kin daina kula ni?" Ta zumb'uro masa baki cike da shagwab'a tace "ba ka ce nice babban k'awarka ba?" Yace "yeah!" Tace "to kuma shi ne za ka daina zuwa na ganka?" Yayi shiru yana sakin murmushinsa ta kalleshi fuskarta a tsuke tace "dariya ma kake yi ko?" Yayi saurin had'e fuskarsa ya girgiza mata kai yace "nope! Ba dariya nayi ba" tace "ai na ganka kana yi" ya sake girgiza mata kai yace "no! Ni banyi dariya ba kece dai kika ga kamar na yi dariya" k'wafa tayi ta d'auke kanta,ya d'an kalleta ta gefen idonsa yace "to wai ba shi kenan ba yanzun na zo kin ganni,ko akwai wani abu kuma?" Ta girgiza masa kai,yace "mene ne? Fad'i naji" ta d'aure fuskarta tace "Yaya ni dai ka fasa yin auren nan ka ji?" Saurin kallonta yayi yana tsayawa,ya juyo yana kallonta yace "me yasa?" Tace "ni dai ba na so kayi" d'an murmushi yayi yace "no way Baby" ta tsaya kallonsa cikin jin haushi tace "to ai sai kai tayi,kuma wallahi ba zanje gidan ba" dariya sosai ta bashi yace "saboda me baza ki ba?" Tace "to ba matar ta fini matsayi a gurinka ba,kuma ita ai baka mata rowan ganinka ba sai ni" yace "waye ya fad'a miki haka?" Tace "ai haka ne" ya girgiza mata kansa yana kallonta yace "ba haka bane" kamar za tayi kuka tace "ni dai bazan yarda ba ko me za ka fad'a" duk yadda yaso ya mata bayani k'in saurarensa tayi dole ya hak'ura ya kyaleta ya fita ya karb'o musu kayan ya dawo ya tada motar suka juya gida,har suka k'arasa gidan bata sake masa magana,yayi parking bakin get yace "Uhn!" Ta juya da sauri ta kallesa tace "me yasa ka tsaya a nan?" Yace "magana za muyi" wani had'e rai tayi tace "ni fa bazan yi magana da kai ba" yace "why?" Kai tsaye tace masa "Z" yayi murmushi yace "alright! Duk sanda kika shirya magana da ni ma yi" ya bud'e motar ya fita,ganin ba ta da niyyar fitowa ya lek'a kad'an yace "get down" ta wani had'e ranta tace "me yasa?" Yace "akwai inda zanje" tayi sauri ta kallesa fuskarta a d'aure tace "gurinta za kaje ko?" Yana mata wani kallo k'asa² yace "ehh! Ko kada naje?" Haushi ne ya kuma kamata a fusace ta bud'e motar ta fita,ko rufewa bata tsaya yi ba tayi gaba,yana kiranta ta d'auki kayan bata ko tsaya ba tayi shigewarta ranta duk babu dad'i,ya girgiza kansa cike da farin ciki ya d'auki kayan ya biyota,dai² tana shiga part d'in Dadda taji muryoyi da yawa a parlon ta k'arasa da sauri hango Waleed

21 / 66