tare.. I'm coming home" da sauri tace "a'a ni bance ka fasa ba ai" yace "kin hak'ura naje ni kad'ai?" Ta gyad'a kai tace "ehhh!" Yace "thanks" yana d'an murmushi,tace "bari na kyaleka kayi driving,sai ka dawo?" Yace "in sha Allah" tace "ka gaisheta tou" suka yi sallama,dai² nan ya tsaya wani super market yayi mata siyayyar kayan amfani sosai kafin ya tada motar ya d'auki hanyar da za ta kaisa gidan. Sanda ya k'arasa unguwar da Abba ya sanar masa ya bata gida ta zauna halak malak,yayi parking dai² k'aramin get d'in gidan,unguwar shiru da yake sabon guri ne,ya d'an jima a mota yana studying arean kafin ya fito ya rufe ya k'arasa bakin get yayi knocking,daga ciki ya jiyo muryar Mama tana tambayar "waye?" D'an shiru yayi,a hankali sanda yake jin footsteps d'inta kusa da k'ofar yace "Waleed ne" ita kanta Mama jin muryarsa sai da ya ba ta mugun mamaki,ta bud'e k'aramar k'ofar jikinta a mugun sanyaye kanta a k'asa kamar surukinta tace "sannu da zuwa" ya amsa yana kallon yanda ta zumbulo hijab har k'asa tace "shigo" tana basa hanya,yace "thanks" then ya shiga,ta mayar da k'ofar ta rufe tana juyowa ta gansa a tsaye yana kallonta,ta d'anyi k'asa da kanta tace "mu shiga ciki" ta fara wucewa yabi bayanta zuciyarsa a mugun raunane saboda yanda yaga Maman ta koma wata quite kamar wanda akayi sabon version na ta,suka shiga parlor ta nuna masa gurin zama,a k'asa kan carpet ya zauna yayi flexing legs d'insa ya gaisheta,ta amsa bata yarda sun had'a idanu ba ta koma kan darduma ta zauna,tace "ya mutanen gidan da aiki?" Yace "alhamdulillah,duk lafiyarsu lau" tace "ya iyali fa?" Shi dai kallonta kawai yake kamar zai mata hawaye tsabar ramar da yaga ta yi da duhu,yace "lafiya lau tana gaisheki" tace "ina amsawa,ya k'annenka da kakarku?" Ya d'an sauke numfashi kafin yace "basu san ma zan zo ba" tace "Allah sarki" daga haka suka yi shiru,can ta tashi tace "ina zuwa" yace "toh a fito lafiya" ta wuce hanyar kitchen,ya bita da kallo cike da tausayi,tsakanin d'a da mahaifi sai Allah,duk abunda ta masa da yake mugun jin haushinta lokaci d'aya tausayin halin da ya ganta ya shafe komai,yana zaune ta kawo masa jellop d'in taliya da taji kifi da kayan lambu,da sanyayyan sob'o ta ajiye masa tace "bismillah ga abinci" d'an murmushi yayi mata yace "na gode" ta koma ta zauna tayi shiru,shima shirun yayi yana d'an kallonta,sun kusa 30 minutes a haka shi bai ce mata ba itama haka,can ta d'an d'ago taga bai ci abincin ba tace "kaci abincin mana kar yayi sanyi" yayi murmushi bai ce komai ba ya d'auki fork d'in data saka masa ya fara ci,bai wani ci da yawa ba ya ajiye cokalin ya tsiyaya lemon ya sha,ta kalleshi ganin ya ajiye cokalin yana danna wayarsa tace "ba dai ka k'oshi ba?" Yace "alhamdulillah na ci ai da yawa" tayi d'an murmushi tace "ko dai bai maka dad'i ba na dafa maka wani abun?" Ya girgiza kansa yace "a'a haka ma na gode,sauri nake zan koma gurin aiki" tace "tou Allah tsare hanya,na gode sosai da ziyara,a gaida mutanen gidan da iyali" yace "in sha Allah" ya tashi zai fita sanda yaje kusa da k'afarta ya sunkuya ya ajiye mata 50k yace "kiyi hak'uri zan dawo in sha Allah,ko rik'e wannan a hannunki" hawaye suna sauka fuskarta tace "na gode sosai Allah saka da alkhairi yayi albarka" ya amsa ya fita ta tashi ta biyo bayansa da niyyar ta rufe k'ofa,yana jin takun tafiyarta a bayansa ya kasa juyawa saboda ya ga kuka take tun kafin ya fito,da zai fita yace "bari na d'auko sak'o a mota" tace "tou" ta d'an tsaya daga ciki ya fita ya bud'e booth ya fito da manyan ledoji da cartoons d'in spaghetti,macaroni,couscous hatta su maggi sai da ya siya mata da ruwa da drinks,yasa almajiran da yaga za su wuce ta line suka shigar mata da kayan,sanda suka gama kwasar kayan ya rufe booth d'in ya zagaya ya bud'e motarsa ya shiga,Mama ta k'araso inda yake tana kallonsa tace "na gode sosai Waleed,dan Allah idan ka je gida ka k'ara yima mahaifinku godiya sosai" yayi mata murmushi yace "in sha Allah" tana tsaye sai da taga ya bar line kafin ta shiga gidan ta kulle k'ofarta,ranar Mama kwana tayi tana kuka,sosai ziyaran da Waleed ya kai mata ya tuna mata abubuwa da yawa daga rayuwarta,bata tab'a zaton zai zo ba saboda abubuwan da tayi masa a matsayinta na mahaifiyarsa. A nasa gefen shima tun da ya bar unguwar jikinsa ya k'ara yin sanyi da al'amarin,tun a lokacin kuma ya d'auki alwashin zai dunga zuwa yana dubata lokaci² ko dai bai samu ya je kullum ba zai yi k'ok'arin ganin ya je duk ranar Friday,a haka ya koma hospital,sai da lokacin barinsa asibitin yayi ya kama hanyar gida,a hanya sanda ya tsaya ya siya mata apples da yawa because ya san abunda take mugun so kenan kafin ya k'arasa. Sanda yayi parking ya fito ya d'auki ledar daya ajiye d'ayan seat d'in ya fito ya wuce ciki,ya bud'e k'ofa ya shiga da sallama,sanyayyan k'amshin dake tashi gami da sanyin AC daya kai ma hancinsa da gangar jikinsa ziyara yasa shi lumshe idanuwansa a hankali yana sauke ajiyar zuciya,then ya fara bud'esu a hankali,a kanta idanunsa suka sauka tana tsaye a kan staircase ta d'an karkace ta side d'aya ta rik'e waist tana masa wani kallo mai tsuma zuciya,tun d'aga k'asa ya fara kallonta sanda ya kai kan k'ugunta da yake nan fam kamar zai fashe ta cikin creazy jeans d'inta,yabi fresh skin d'inta da yake hangowa ta wajen thighs da kallo yan fesar da wani iska,ya k'ara yin sama da inanunsa sanda ya kai k'irjinta bai san sanda ya fara tafiya ba ya nufeta,gaba d'aya ta gama tafiya da shi,ji yake idan bai rab'a jikinta a nasa ba sam ma ba zai samu nutsuwa ba,tsayawa tayi a matakala ta uku har ya k'araso,kafin ya hauro tayi saurin tahowa kamar za ta fad'o,da sauri ya saki ledojin hannunsa ya tarota,yana kallonta a tsorace yace "why Lilac kike son min wasa da abu mafi tsada da muhimmanci a rayuwana? Idan da kin fad'o fa kin ji ciwo sai kice min tsautsayi ne ko?" Dariya ta kyalkyale da shi tace "ai na san kana nan shisa,and baza ka tab'a bari wani abu ya same mu ba" ya zuba mata idanu yana sauke ajiyar zuciya can ya juya ya kalli yanda tasa ya b'arar da komai,then ya kalleta yace "kinga kinsa na zubar ko?" Ta kalli gurin tana dariya tace "sai ka kwashe ni ai bance ka zubar ba" yace "ohh! Ba ke kika sa na zubar ba ma?" Ta gyad'a masa kai a shagwab'e tace "ni ba ni bace" ya gyad'a kai a hankali ya saketa ya tsuguna ya fara tsincewa,tayi dariya ganin yana kwashewa baice komai ba ta tsuguna tana tayasa. Da dare lokacin suna kwance taji har sannan baice mata komai game da zuwansa gurin Mama ba,ta daure tace "Master! Ya ka baro Mama?" A hankali yace "tana lafiya,ta ce a gaisheki" ta dunga kallonsa ta kasa yarda wai Mama ta ce a gaisheta,ya kalleta jin ta yi shiru,da sauri kuma sai ta waske tana d'an murmushi tace "ina amsawa ka sameta lafiya?" Yace "alhamdulillah!" Tace "maa sha Allah" daga haka sai bai sake ce mata komai game da abunda ya shafi Maman ba,har suka gama budurinsu suka yi bacci,itama kuma bata damu kanta ba bare ta masa tambaya kan al'amuran Maman. Washe gari Friday around 7am Deejah ta kirasa hankalinta tana kuka tace "Yaya dan Allah kazo gida yanzu" yace "lafiya?" Dan shi bacci ma yake kiranta ne ya tashesa,tace "please kazo dai dan Allah yanzu" ya amsa mata,yana d'an tab'e baki ya juya ya kalli side d'in Manar,ya yi zaton tana kwance sanda yaga wayam,da sauri ya sauka daga gadon ya fad'a bathroom yayi wanka ya fito ya shirya a gurguje cikin manyan kaya kasancewar jumu'ah ya fito daga d'akin ya nufi downstairs,a kitchen ya sameta tana had'a musu breakfast ta d'aure hancinta da handkerchief,ya k'arasa shiga yana kallonta yana cewa "aikin kamar ya zama wajibi kiyi?" Ta waigo da sauri tana sanye da riga oversized da short nickers,ta d'anyi maea murmushi tace "dole ne mana" ya girgiza kansa yace "a'a bai zama dole ba tunda ina nan" ta sake masa murmushi tana kallonsa tace "waye ya tasheka na san sanda na fito bacci kake?" Yace "Deejah ta kirani wai naje yanzu,so ban san me yake faruwa ba bari naje naji" gyad'a masa kai tayi tace "za ka dawo ne idan ka fita?" Ya d'an girgiza mata kai yace "i don't think so" kallonsa ta dunga yi kafin tace "tou kayi breakfast kafin ka wuce" yanda yaga tana kallonsa yasa shi cewa "noo! Na kusa makara,idan kin gama ki bayar kawai zan wuce ina sauri" wani kallo ta dunga masa baki bud'e ta kasa cewa komai,kawai hawaye suka fara biyo idanunta,da sauri ya k'arasa kusa da ita ya rik'ota yana tambayarta "me ya faru?" Fizge hannunta tayi ta bud'e hancinta cike da masifa tace "na hana idanuna bacci na maka breakfast d'in shi ne za kace na bayar?" Yana k'ok'arin sake rik'eta tace "ni karka tab'a ni,tunda baza ka ci ba jeka kawai Allah tsare hany.." Bata k'arasa fad'a ba warin gas da ba ta so yasa ta fara yunk'urin amai,ya matso da sauri zai rik'eta ta turasa da k'arfi ta nufi hanyar fita da gudu tana toshe bakinta..
#Afuwan dearies yau bamu samu NEPA ba suna gyara,kuyi hak'uri please..
#Asli Smasher.
52...
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*
Saurin biyo bayanta yayi yana tambayarta lafiya? Bata tsaya basa amsa ba ta nufi wani bedroom a nan k'asan,kusan tare suka shiga d'akin ta fad'a bathroom,tun bata k'arasa ba aman da take yunk'urinsa ya fara zubowa,ya k'arasa kusa da ita da sauri ya rik'eta,sanda ta amayar da kaf abunda ke cikinta kafin ya wanke mata baki da jikinta ya cire mata rigan ya d'auki towel ya d'aura mata,har wani hazo² take gani lokacin ya d'auketa suka fito,sama ya wuce da ita ya bud'e bedroom ya shiga ya kwantar da ita kan gado yana mata sannu,ita dai tunda ya kwantar da ita tayi shiru sai numfashin da take saukewa,ya zauna kusa da ita yana kallonta yace "kina jin wani abu ne?" Ta girgiza masa kanta a hankali tace "um'um! Babu abunda nake ji kawai jiri ne" yace "sannu! Allah kara sauk'i" zai mata magana wayarsa ya fara ring,ya kai hannunsa ya d'auko a aljihu,yana dubawa yaga Deejah ce take sake kiransa,d'an siririn tsaki yayi then ya d'auka ya kai kunne,da sauri Deejah dake kuka tace "Yaya baka zo ba kuma" yace "yeah! Yanzu zan zo,what happened?" Kasa magana tayi duk ta rud'e sai kuka kawai take yi,da sauri yace "I'm coming in sha Allah" ya fara katse wayar,ya kalli Manar dake kwance har lokacin idanunta a rufe ya mik'e yace "Lilac tashi mu tafi" d'an bud'e idanuwanta tayi tace "kaje ka dawo na ji sauk'i fa" wani kallo ya dunga mata yace "bazan yarda na tafi na barki ba,get up na shiryaki mu tafi" duk yanda ta so ya tafi ya kyaleta sanda taga ya dage akan bazai barta ba,dole ta tashi ta zauna tana kallonsa,ya bud'e press ya d'auko mata lightweight kaya,ya dawo yasa mata then suka fito yana rik'e da hannunta,da suka sauka downstairs,ya barta a parlor ya shiga kitchen ya had'a musu kayan breakfast d'in a basket ya d'auko ya fito,a kwance ya sameta a kan kujeran da ya zaunar da ita,ya dunga kallonta sanda ya k'arasa kusa da ita yace "tashi muje" d'an bud'e idanunta tayi ta kalleshi a wahale kafin ta fara k'ok'arin tashi,duk aman da tayi ya sa ta zama wata sai a hankali,ya dunga kallonta sanda suka fito,suka k'arasa parking space ya bud'e mata mota ta shiga,ya shiga yaga ta jinginar da kanta ta kulle idanunta kamar mai shirin yin bacci,yace "da haka kike so na tafi na barki?" Ta d'an bud'e idanunta ta kallesa tayi murmushi k'arfin hali bata dai ce komai ba,ganin yanda tayi ko magana ma ta kasa yasa ya kwantar mata da seat d'in then ya tada motar suka tafi. A hanya babu mai magana har suka k'arasa gidan,yayi horn get keeper ya bud'e masa ya wuce ciki yana d'aga masa hannu,yana yin parking ya d'an juya yana kallonta kafin ya bud'e motar zai fita,ta bud'e idonta a hankali da suka fara canjawa saboda baccin da ta fara,ya zagaya side d'inta ya bud'e mata yana kallonta,ta sauko k'afarta a hankali ta mik'e,da sauri ta koma ta zauna tana rik'e kanta,yayi saurin sunkuyawa kanta yace "what happened?" Bata d'ago ba tace masa "jiri nake gani" ya mata sannu kafin yace "let me help u" ya janye hannun rigarsa ya d'auketa,ya tura murfin da k'afa ya rufe then ya nufi b'angaren Dadda,da ya shiga bai ga Dadda ba ya kwantar da ita kan kujera yana kallonta yace "I'm coming,okay?" Ta gyad'a masa kai ya juya ya fita,sanda ya kawo mata basket da ya had'a musu kayan breakfast ya ajiye ya had'a mata komai yace "kiyi breakfast in zuwa" tace "okay!" Ya fita ya wuce b'angaren Mother,da yayi knocking yaji shiru ya wuce b'angarensu,yana bud'e k'ofa Dadda ya fara hangowa tana share fuska,gabansa ya fara fad'uwa,a haka ya daure ya k'arasa shiga yayi sallama a hankali kamar yana jin tsoro,yana sake bin occupants d'in parlon da kallo,Aunty da Mother suka amsa masa da fuskar damuwa,ya shiga ya zauna ya gaishesu,Dadda dai bata amsa ba sai kukan da ta sake kecewa da shi,ya kalli Aunty jikinsa a sanyaye yace "me yake faruwa?" Aunty dai kallonsa take ta kasa magana,kana ganin idanuwanta za ka san ta ci kuka har ta godema Allah,Dadda ta d'aga murya tana share hawaye tace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Um!³" sai gyad'a kai take ta kasa cewa komai,Waleed ya sake tambayar lafiya? Dadda ta fyace hanci tace "ai kai dai Mamman muna cikin gagarumin tashin hankali wallahi" yace "tashin hankali akan me?" Tace "iiiihhh! Idan ba tashin hankali ba me za'a kira wannan abu da ya faru? Irin wannan babban masifa da Halima ta d'auko ma kanta" jikinsa har tsuma yake yace "ki min bayani dan Allah,na kasa gane me kike nufi?" Dadda har da gyara zama tayi tace "tou ni dai dama kaje ka d'auko uwar taku,tazo taga abunda y'ay'an so suka aikata" ya fesar da wani iska yace "ni kink'i ki min bayani,kin tsaya rarraba magana" Dadda dai daga haka ta k'i ce masa komai,sanda ya fusata kawai ya mik'e ya nufi sama,ya tura k'ofar bedroom d'insu Deejah yayi sallama a ciki,Deejah ta d'ago da sauri jin maganarsa,suna had'a ido ta kece da wani kuka mai ban tausayi,ya shiga yana kallonta a d'an tsorace,kafin yayi magana idanuwansa suka gano masa jariri kwance cikin zani an nad'esa fuskarsa a waje,kyakykyawan gaske kamar jinin larabawa,idanuwansa kamar za su fad'o ya dunga kallon jaririn dake bacci,kamar wanda aka sarewa k'afafu ya dunga tafiya ya nufi yaron,ya tsaya daf da shi jikinsa was vibrate,ya nuna yaron yace "wannan fa a ina aka samosa?" Deejah sai kuka take ta kasa magana,wani tsawar da ya mata yasa ta nutsuwa,ba ita kad'ai ba hatta Diyanah dake toilet sai da kayan cikinta suka hautsina tsabar tsoro,ta dafe k'irjinta wasu hawaye suna saukowa fuskarta,taji ya sake ma Deejah tsawa yace "ba dake nake ba kika min shiru?" Jikinta yana b'ari tace "Yaya ba nawa bane fa" wani zaro idanuwansa yayi yace "na waye?" Tace "Diyanah!" Saurin matsawa yayi ya jingina da bango yana fad'in "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. allahumma ajirnii fiiy musibatii wa'aklufnii khairan minha" Deejah ta rik'e kanta sai kuka take,da sauri ya sake matsawa kusa da yaron ya zuba masa idanu,ya kai hannunsa yayi sauri ya d'aukesa,wasu irin hawaye masu d'umi suna saukowa fuskarsa,ya jima sosai yana kallon yaron kafin ya ajiyesa ya fita,Diyanah tana jin fitarsa ta bud'e k'ofar ta fito,da ya sauka downstairs bai iya yima kowa magana ba ya fita daga gidan ya wuce b'angaren Dadda,ya samu Manar kwance tana bacci ko abincin bata ci ba,yanda ya ajiye mata haka ya tarar da shi,kasa k'arasawa kusa da ita yayi ya juya ya fita da sauri,ya tsaya balcony ya kira Mama a waya,a hankali yace tazo gida yanzu inji Dadda tana son ganinta,ta dunga tambayarsa lafiya,yak'i fad'a mata yace kawai shima haka tace masa ya kirata amma bata fad'a masa dalilin ba,duk da jikin Mama ya bata ba lafiya ba,ta daure tace tana hanya in sha Allah yanzu,ya katse wayar yana sauke numfashi,then ya juya ya koma parlon. Kafin yamma maganar ya isa kunnen duk wanda ya dace ya sani,Mommella,Amaar,Azaan,tare da Ameerah da Rania har sun sauka k'asar,Mama ma tuni ta zo aka labarta mata abunda ya faru,suka kuma gani da idanuwansu,Ameerah dai babu hawaye ko d'is a fuskarta dan a lokacin da suke zaune parlon Dadda ma da taga Manar tana kuka,kallonta kawai ta dunga yi kafin ta tab'e baki,tun da taji abunda ya faru ta d'agama kanta hankali,Ameerah da ta gaji da kallonta tace "dan Allah malama ki mana shiru haka,haba da Allah ke yanzu har kin manta abunda suka dunga fad'a akanki? Shi ne kuma za ki damu kanki? Wane magana ne basu ce ba sanda Hjy ta d'aukeki kuka je Saudi? Cewa fa suka dunga yi karuwanci tasa kiyi,ta fake da neman kud'i ko har kin manta?" Karaf maganar ya sauka kunnen Dadda da Mommella da suke shigowa side d'in,Mommella ta kunduma wani zagin da basu tab'a jin ta yi ba,ta shigo a fusace tana kallon Ameerah tace "me yasa baki fad'amin ba tun lokacin da akayi?" Ameerah tace "Mommella lokacin fa tun da suka dawo ne akayi" Mommella cikin tsananin b'acin rai tace "ko yaushe