su d'in ne sa'annin juna,lokacin ko da mother ta yaye Manar Muh'd ya sanar mata zai bawa k'anwarsa Hafsah,Maryam ta yi farin ciki duk da Manar itace y'arta ta fari,amma ta sadaukar da ita ma k'awarta for nothing other than zumuncinsu da zai k'ara k'arfi,and kaf gidan babu wanda yayi tunanin bata d'ansa duk da rashin haihuwar da bata yi ba,a ranar da aka yaye Manar Muh'd ya d'auketa ya kaima Hafsah,da yake mata bayani dalilin kawota Hafsah ta yi kuka sosai ta dunga yima y'an uwa waya tana fad'a musu abun alkhairin da d'an uwanta ya mata,tun daga lokacin rainon Manar da komai nata ya koma hannun Hafsah wanda yaran gidan suke kiranta Momellah (meaning-Small Mom) Manar tana barin gidan shima Azaan ya tattara ya koma gidansu,sai da su Mommella za su koma India shekaru hud'u baya Mama azumi da Azaan yake cema Dadaji (grandma) lokacin Manar tana koyon magana ta mayar mata Dadda shi kenan duka yaran gidan suka koma fad'an haka,tana jin maganar da Mommella keyi akan tafiyarsu da Manar wata k'asa ta fututtuke ta hana tafiya da ita a cewarta baza a kai mata jika wani k'asa a lalato mata ita ba,wannan shi ne ya zama sanadin rabuwar su Momellah da Manar,by then kuma lokacin Dadda za ta Saudiyya ta tafi da ita..
*Back to story...*
Da yamma lokacin Amaar ya dawo daga aiki ya shiga apartment d'in Dadda ya tararta ita kad'ai tana mitar b'ata mata d'aki da su Manar suka yi suka fita without sun gyara,yayi murmushi ya k'arasa shiga yayi sallama,bata amsa ba ta d'aga kai ta kallesa ta d'auke kai,murmushi yayi yace "Hjy Manar fa?" Wani kallo ta masa ta d'auke kai ta ci gaba da sakace hak'orinta,bai damu ba ya sake cewa "Hjy ko sun miki laifi ne kika k'i kulani?" Kamar ya tsokanota tayi k'wafa cikin jin haushi tace "idan ba ma sun raina ni ba dama su b'ata guri kuma su tafi su barshi haka kaca²,yanzu ni suke nufi zan sake gyara musu?" Amaar ya girgiza kai yace "a'a gaskiya basu kyauta ba" ta gyad'a kai tace "yara sai k'azantar tsiya malam,su dai babu daman suga guri tsaf² sai sun k'azancesa" Amaar kamar zai yi dariya saboda yadda take kambama maganar,ya juya da sauri yace "Hjy bari na turosa su gyara miki gidan" ta d'aga kai ta bisa da kallo,har ya kai bakin k'ofa ta tab'e baki ta d'aga murya tace "dama baka wahala ba,wad'annan sakarkarun babu abunda suka iya,sai shegen surutu malam kamar sun ci aku.." Dariya ce ta kwace masa yayi sauri ya k'arasa fita yace "bari dai naje na dawo Hjy" ba tare da ta tankasa ba ya fice,apartment d'in Mother ya tsaya yayi knocking Ameerah ta bud'e k'ofar,tana ganinsa tace "Yaah Amaar sannu da dawowa" ya gyad'a mata kai yace "Manar fa?" Juyawa tayi bata bashi amsa ba ta k'walama mata kira,Manar dake zaune tace "mene ne wai?" Tace "kizo inji Yaah Amaar" da murnanta ta taso ta k'araso gurin tana washe masa baki ta gaishesa,ya d'aure fuska yana kallonsu yace "maza ku wuce muje" kallon juna suka yi kafin Manar tace "ina za mu Yaya!" Ya juyo ya kalleta yace "cewa nayi ku wuce ko na ce wata tayi magana ne?" Sum² suka wuce forefront ya kallesu yace "kun san inda za ku da kuka wuce?" Suka tsaya suna kallonsa,ya maka musu harara ya fara wucewa forefront suka bisa a baya,suna shiga suka ga Dadda zaune a parlor sai kad'a k'afa take,Manar ta d'aure fuska itama Ameerah tayi kicin² tak'i kallonta,Amaar ya nemi guri ya zauna in a serious note yace "maza ku d'au tsintsiya ku gyara gidan kafin na b'ata muku rai" sum² suka yi suka wuce kitchen suna hararan Dadda da tak'i kallonsu,yana zaune suka gama sharar suka goge,duk da yana musu wasa amma idan ya had'e rai bala'in tsoronsa suke,suna gamawa ya mik'e zai fita yace "Hjy sai da safe" d'aga kai Dadda tayi ta kalli parlon da yayi k'al² sai k'amshin room freshener yake tayi wani murmushi tace "to d'an fodiyo,sannu kai dai ka ji,Allah maka albarka" ya amsa yana murmushi ya nufi k'ofa,har ya kusa fita ya kira Manar,she thought ko zai sake sa su wani aikin kuma bata iya amsawa ba kawai ta fashe da kuka tace "Allah Yaya na gaji" saurin juyawa yayi yana kallonta tana matsar idanu,sanda ya gama k'are mata kallo yace "dallah rufewa mutane baki,kin ji na ce kiyi min wani abu ne da za ki b'arewa mutane baki?" Da sauri Dadda ta kallesa fuskarta cike da damuwa tace "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Haba d'an fodiyo,me kuma tayi za ka kwad'a mata tsawa haka?" Ba Amaar kad'ai ba hatta Manar da Ameerah sai da suka kalleta,Amaar yayi squeezing fuskarsa yace "me ya faru kuma?" Cikin fad'a Dadda tace "yo wannan uban tsawan da kayi ko ni sai da y'ay'an cikina suka juya bare Manar da take k'aramar yarinya,irin haka ai babu dad'i,kuma ni sai naga jarumtarta da ta tsaya iya zubar da hawaye kad'ai" Amaar ya dunga kallonta mamaki ya hanasa sake mata magana,Dadda tace "ni dai idan ba abun arziki ya kawo ka ba dama ka fitar mun daga gida Allah tashe mu lafiya" gyad'a kai yayi ba tare da ya ce komai ba ya juya yana tafiya yace ma Manar "idan kin gama kukan ki zo ki karb'i sak'onki da Azaan ya bayar a kawo miki" ya k'arasa maganar yana ficewa daga apartment d'in,tana jin ya ambaci Azaan da sauri ta biyosa ko jira bata yi taji abunda Dadda za ta ce ba Ameerah ta rufa mata baya,a parking space suka gansa yana bud'e motarsa,suka k'arasa suka tsaya ya d'auko ledan dake ajiye d'aya kujeran yana mik'a mata ya rufe motarsa ya bar gurin,Ameerah ta karb'a ta bud'e taga sak irin wancan da Waleed ya k'wace colour d'in ne da bambanci,cikin tsananin murna suka juya zuwa part d'in Dadda,suna shiga cikin karad'i Manar tace "Dadi kinga sabon wayana da Yaa Azaan ya sa a k'ara.." Bata k'arasa ba suka yi ido hud'u da Waleed dake zaune,babu shiri ta had'iye sauran maganarta,Waleed ya zuba mata ido yana kallon yadda take tafiya hannunta a b'oye a bayanta tana zumb'uro masa baki,Ameerah ma tana ganinsa ta juya za ta fita ya mata tsawa yace "idan kika sake k'afar ki ya fita daga gidan nan ni da ke ne" babu yadda za tayi ta dawo ta tsaya,Manar za ta shiga d'aki ta b'oye wayar kafin ta kai k'ofar bedroom yace "kema idan kika bari k'afar ki ya taka cikin d'akin nan jikinki zai fad'a miki" saurin juyowa tayi ta kallesa ta kalli Dadda da tak'i musu magana,bai kalli inda take ba yace "me Azaan d'in ya bayar aka kawo miki?" Tayi shiru tak'i cewa komai,ya mata tsawa yace "ba dake nake ba kika min shiru?" Kuka ta fashe da shi ta juya da gudu ta shige d'akin,ya gyad'a kai ba tare da ya kalli direction d'in Ameerah ba yace "mene ne take fad'a?" Ameerah cikin tsoro tace "Yaya nima ban sani ba fa" yace "k'arya kike" da sauri tace "believe me yaya ban san komai ba" wani kallo ya d'ago ya mata yace "ba tare na ganku yanzu a parking space ba?" Tayi tsuru² tana in'ina,ya sake mata tsawa yace "za ki fad'a min abunda ya faru ko sai na zaneki?" Hawaye suna zubowa idanunta tace "waya ya bayar a kawo mata" still Waleed yayi yana kallonta kafin ya maimaita "waya?" Tace "ehh" ya gyad'a kai yace "je ki karb'o ki kawo min" bata masa musu ba ta wuce tana shiga ta samu Manar tana rusa kuka,kaf maganar da Waleed yayi babu wanda bata ji ba,cikin kuka tace "ni to me na masa da zai na kwace min waya?" Ameerah tana share hawaye tace "kiyi hak'uri Sis kawo na kai masa in yaso sai na baki na wajena kiyi amfani da shi" Manar ta girgiza kai tace "ni dai bazan bada wannan ba" Ameerah tace "please ki kawo zan d'auko miki wancan d'in na wajena kinji?" Manar tace "ni wallahi bazan basa ba" yana jiyo rigimar su ya taso da kansa ya bud'e k'ofar yana kallonsu ya tsaya bakin k'ofa bai k'arasa shiga ba,fuskarsa a d'aure yace "d'auko ki kawo min" da farko k'in kai masa tayi sanda taji ya ce "idan kika bari na tako nan na sameki jikinki zai fad'a miki" babu yadda za tayi ta d'auka tana zuwa ta tsuguna ta ajiye masa a k'asa,ya mata tsawa yace "nan nace ki ajiye?" Ta zumb'uro baki ta d'auka ta mik'a masa,ya zuba mata idanu yace "daga yau duk wanda ya kuskura cikin ku na k'ara ganin waya a hannunsa.." Bai k'arasa ba ya gyad'a kai ya juya,kai tsaye ya wuce zai fita daga apartment d'in Dadda da tun d'azu ta zuba masa idanu tak'i ce masa komai ta kada baki tace "Afff! Ka mance baka karb'e na gurin Ameerah ba ai" wani juyowa yayi yana kallonta ta tsuke fuska tace "meye kake kallona ai tuna maka nayi ni" wani murmushi yayi bai ce komai ba ya juya ya fita daga gidan,tun da Manar ta tabbatar ya tafi mata da wayarta take kuka,ko cikin dare ta farka tana tunawa sai ta fashe da kuka,ranar gaba d'aya ta hana Dadda da Ameerah sukuni,kafin safiya ciwon kai mai tsanani da zazzab'i mai shegen zafi ya rufeta..
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2021.
*♡MANAR¸.•💥*
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA
_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._
_Bestowed to Fateema Abdulmajid._
11.
#Forbidden..
Tun gari bai gama yin haske ba Dadda ta fita hankali tashe ta isa part d'in ta dunga knocking kamar za ta cire k'ofar tana k'walama Abba kira,haulatu mai aikinsu ta bud'e mata k'ofar,da sauri Dadda ta wuce tana ci gaba da kiran "Yaro!" Jin shiru a fusace kaman za tayi kuka tace "to wai ko Yaron baya jina ne yayi min shiru?" Ta wuce za ta yi sama suka had'u da Abba yana sakkowa cikin sauri sanye da jallabiya,da sauri ta taresa hankali tashe tace "Yaro! Zo maza² muje kaga abunda yake faruwa" shi kansa Abba hankalinsa bai kwanta ba saboda yanayin kiranta da ya jiyo,ya bita da sauri yana tambayarta "Hjy lafiya?" Dadda tace "ina fa lafiya,zo dai muje ka ganewa idanunka" suka fita tare Aunty ta sauko za ta bisu,Mama da ta jiyo kiran ta fito itama tana murtsika idanunta ta tarar Aunty za ta fita tace "lafiya naji muryar tsohuwar nan a nan?" Aunty dai ta yi hanyar fita tace "wallahi ban sani ba,zan je dai na gani" tab'e baki Mama tayi ta nemi guri ta zauna tana jiran su dawo taji kanun labarai. Tsabar saurin da Dadda take har kamar za ta kifa Abba yace "bi a hankali Hjy" bata tsaya kulasa ba ta wuce,suna shiga part d'in ta nufi d'aki Abba yana biye da ita,dai² lokacin sun shigo Manar ta hantsilo daga kan gado,idanun Dadda kamar za su fad'o k'asa tace "A'uzhubillahi! Mene ne haka kuma?" Kafin ta k'arasa Manar ta fara kwara amai,Aunty da tayi shigowar k'arshe ta k'arasa kusa da ita da sauri ta rik'eta tana mata sannu,sympathetically Abba da yayi tsaye bakin k'ofa ya dunga kallonta yana mata sannu,sanda ta gama Aunty tana shafa mata baya tace "sannu daughter" wani kukan ta sake fashewa da shi muryarta ko fita ba ta yi sosai tsabar kukan da ta kwana yi,Aunty ta d'agata tana rarrashinta suka wuce bathroom ta wanke mata jiki,Ameerah dai na gefen gado ta buga tagumi da hannuwa biyu idanunta suna fidda k'wallar tausayin halin da Manar ke ciki,kafin Aunty ta fito da ita Abba ya kalli Dadda yace "Hjy me yake damunta ne?" Da wani muryar takaici Dadda ta fara masa magana "kai dai Yaro wallahi tunda na haifeka baka tab'a zuwa ka d'auko min magana ba,amma wannan d'an naka kullum ne Allah ne da kullum sai ya zo nan ya sa ni dogon magana" Abba dai sai kallonta yake yace "kiyi hak'uri Hjy zan masa fad'a" a fusace ta masa wani kallo tace "wane irin za ka masa fad'a kuma Allah na tuba? Sau nawa yake zuwa ya sani magana,idan naje na fad'a maka a banza,ko sau d'aya ni dai ban tab'a ganin ka zaunar da shi ka masa fad'an ba sai yau ne za kace min haka?" Aunty ta fito da Manar dake kuka har sannan muryarta a dashe ta kaita kan gado ta kwantar da ita,za ta juya Manar tayi saurin rik'o hannunta,kallota Aunty tayi tace "ina zuwa daughter bari na gyara gurin da kika b'ata na dawo" ta gyad'a mata kai a hankali wasu hawayen suna zubowa daga idanunta tace "sss..sanyi nake ji Aunty" k'aton duvet d'in dake kan gadon Aunty taja ta rufeta da shi fuskarta kad'ai ta bari a bud'e,Manar ta k'arasa jan bargon ta rufu dukanta,Aunty ta kalleta cike da tausayi ta wuce ta fara gyara gurin da tayi aman,sanda ta gama tana kallon Dadda tace "Hjy wai me ya sameta haka lokaci d'aya?" Bud'e bakin Dadda maimakon ta musu bayani sai ta rushe musu da kuka,Abba dai duk ya kasa magana sai kallonta yake,Aunty tayi k'arfin halin fara rarrashinta tace "dan Allah Hjy ki daure ki mana bayani mu san halin da ake ciki" ta kama gefen zaninta tana share fuska kafin tace "fisabilillahi dama ya lafiyar giwa bare ace tayi hauka,kuna kallo dai ba'a yima yarinyar nan wani abuba ta yi kuka bare anyi" Abba ya daure yace "me aka mata?" Kamar mai jira nan Dadda ta fara rattabo masa bayani "nake fad'a maka Yaro jiya da dare yarinyar nan ta shigo min da murnarta tana fad'a min an kawo mata wayar salula.. Kafin ma nayi magana kawai mutumin nan ni dai muna zaman² lafiya ya shigo min ni na d'auka abun arziki ya kawosa,ai yana jin zancen an kawo wa yaran nan waya shi kenan karka dad'a karka raga mutumin sai cewa yayi lallai illalla sai ta kawo masa" Abba yace "waye ya bada wayar?" Dadda tace "wancan yaro dai d'an uwanta na gurin Hafsatu" Abba ya gyad'a kai yace "Azaan kenan?" Dadda tace "shi fa dai nake nufi,to fa shi kenan tunda ya karb'e ya tafi da waya take ta ratatun kuka,daren nan gaba d'aya abunda taita yi kenan,ni dai ina ga bata ko runtsa ba.. Yo Allah na tuba muma bata bari munyi ba bare ita da take da dalili,shi kenan kuma sai ciwo ya rafketa" ran Abba a b'ace ba tare da ya jira ya gama sauraronta ba ya juya da sauri zai fita,Dadda ta bisa da kallo tace "ina kuma za kaje Yaro?" Bai tsaya ba yace "ina zuwa Hjy" ya fita da sauri daga gidan,Aunty ta kad'a kai tace "sha'anin yaran nan sai dai su d'in" Dadda tayi k'wafa tace "ai karma wancan mutumi yaji labari,ni dai da za'a yarda da abunda zance da sai nace kwata² Yaro yasa ya daina zuwarmin tunda babu arziki,kullum yazo sai ya sa ni yawan magana" Aunty ta d'aga kai ta kalli Dadda tana sakin murmushin tsokana tace "haba Hjy Waleed ne fa" a fusace Dadda tace "shi d'in Allah na tuba Waleed d'in na farko ne?" Aunty ta girgiza kai tace "a'a amma dai a gurinki shi ne na farko" nan da nan Dadda tayi mitsi² da idanu tace "Fatima.!" Kafin tayi wani magana tuni Aunty ta yi sauri ta fita,Dadda tace "wallahi ki fita idanuna na rufe,bar ganin ina d'aga maki k'afa,duk ranar da kuka k'ure ni Allah mutum bazai ji da dad'i ba" Aunty dai tuni ta fice tana murmushi ta wuce kitchen,tana shiga ta zuba ruwa cikin kettle ta jona tana tsaye ya tafasa ta juye cikin flask,ta d'ebo potatoes tana ferewa. Tare Abba suka shigo da Waleed dake binsa a baya,suna zuwa Abba yace "wuce ka dubata kamin bayanin abunda yake faruwa" wani b'oyayyar ajiyar zuciya yayi ya k'arasa inda take,a hankali ya kai hannu ya yaye bargon,ya dunga kallonta da mamaki ganin yadda ta k'udundune jikinta,Abba dake tsaye bakin k'ofa ganin Waleed ya kasa tab'a ta yace "ko dai mu tafi asibiti?" A hankali ya girgiza kansa yace "A'a Abba" ya kai hannunsa goshinta da nerves d'inta suka fito b'aro² then ya kai hannunsa kan wuyanta,har bacci ya fara d'aukarta taji ana tab'ata a hankali ta bud'e idanunta da suka kumbure,tana ganinsa ta janye jikinta za ta matsa ya mata wani kallo a d'an tsawace yace "stay still" sheshshek'ar kuka ta fara ya bita da kallo cikin tsare gida yace "ina ke miki ciwo?" Ta masa banza tak'i cewa komai,ya gyad'a kai k'asa² yadda ita kad'ai za ta ji yace "saboda na kwace wayar kike ciwo?" Still tak'i kulasa,Abba dake tsaye yana jiran yaji ya yi magana yace "ko dai sai mun je asibitin Muh'd?" Waleed ya girgiza kai yace "a'a Abba ba sai munje ko ina ba,zazzab'i ne kawai a jikinta" kafin Abba yayi magana a fusace Dadda tace "A'uzhubillahi! Zazzab'i kuwa ai ba kawai bane,matar da ta kwana kuka shi ne za kace zazzab'i ne kawai" ya juya ya kalleta ba tare da ya yi magana ba ya nufi k'ofa zai fita Abba yace "where are u going?" yace "zanje na siyo medications" Abba ya gyad'a kai ya ciro ATM a aljihunsa yace "karb'i nan kaje da shi" da sauri Waleed yace "no Abba zan siyo na dawo" ya wuce ya fita,Dadda ta tab'e baki ta k'arasa kusa da ita tace "sannu takwara kinji,Allah zai saka miki" parlor Abba ya koma ya zauna yana jiran dawowar Waleed. Almost 10 minutes ya dawo da leda a hannunsa ya shigo da sallama,Abba dake zaune ya amsa Dadda dai