nufi hanyar fita daga d'akin. Aunty kam sanda ta fita ta barsu bedroom d'inta ta koma ta zauna bakin gado ta yi shiru tana maimaita kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ganin komai take kamar almara,ita gaba d'aya ma bata gane me yake faruwa ba lokacin,Ameerah da ta gani tsaye bakin k'ofa tare da Waleed yana mata magana shi ne dalilin da yasa ko da ta hauro saman tabi bayansa d'akin Hjy Asama'u da taga ya shiga taji me yake faruwa,ko Ameerah ta masa wani laifin ne bai hukuntata ba ya rabu da ita a iya fad'a dan bata ji me suke cewa ba,bisa tsautsayi kuma ko da ta bud'e k'ofar bata kai ga shiga ciki ba ma sai ta tarar da maganar Maman wanda ya ainihin girgiza ta,tsayin lokaci suke zaune gidan suke hak'uri da ita da halinta,duk adadin k'iyayyarta garesu da bata iya b'oyewa ita ko Mother basu tab'a damuwa ba sun fi zaton kishi ke damunta,ashe ita abun dake ranta daban kawai ana zama ne a babu yadda za'ayi, amma ta ciki na ciki,cikin wannan halin Amaar ya turo k'ofar ya shigo da sallama a bakinsa,tsabar yadda tayi zurfi cikin tunani bata ma san ya shigo ba,ya k'arasa kusa da ita ya zauna sanda ya rik'o hannunta cikin nasa ta sauke wani gauron numfashi,a hankali yace "Aunty wani abu ya faru?" K'uri tayi masa da ido ta kasa ce masa komai,hankalin Amaar ya fara tashi ganin yadda take kallonsa tashin hankali kwance k'an fuskarta,a firgice ya jijjigata yace "Aunty please tell me what happened? Me aka miki naga kamar hankalinki a tashe? And yanzun na ga Waleed na yi masa magana bai saurare ni ba ya wuce,na ga kamar kuka yake or something like this,ban dai tantance me yake damunsa ba dan bai ma tsaya ba bare ya kula ni.." Girgiza masa kai Aunty tayi tana sauke wani heavy ajiyar zuciya ta sanar masa kaf abunda ya faru,cikin tsananin tashin hankali Amaar ya fara maimaita kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun.." Tsayin mintuna suka yi shiru babu mai magana a tsakaninsu sai can da Aunty tayi k'arfin hali tace "Amaar zan rok'e ka wani alfarma" ya gyad'a mata yace "ina ji Aunty" a hankali tace "dan Allah ba don ni ba,kamar yadda muka san maganar nan daga ni sai kai,ina rok'onka ka binnesa a zuciyarka,kada ka bari wani mahaluki a cikin gidan nan ya sani.. Musamman kakarku,na tabbatar taji maganar za ta tada rikici a gidan nan,please Amaar ba don ni ba.." Gyad'a mata kai yayi yace "in sha Allah Aunty babu wanda zai sani,na yi miki alk'awari" ta sauke numfashi tana gyad'a masa kai tace "thank u" shiru yayi ya dunga binta da kallo gaba d'aya ita kanta tausayi take bashi yadda yaga ta damu,ina kuma ga Mother idan ta ji? Ita kanta Manar da ba ta da laifin komai cikin abubuwan da suka faru me yasa za'a k'i ta har haka? Shi duk bai tab'a ganin inda laifin wani ya shafi wani ba sai a gurin Mama ita ce kawai ya tab'a ji a tarihi ta k'i wani babu dalili,tabbas ba don ya san Azaan yana son Manar ba,shi a kan kansa baiga dalilin da zai hana baice yana son manar ba,ya jima a d'akin yana kwatarmata hankali kafin ya tashi ya fita yana mai tausayawa d'an uwansa da yake cikin tsaka mai wuyar fita. A b'angaren Waleed kuwa yana fita ya nufi parking space,sanda yake k'ok'arin bud'e motarsa a niyyarsa na barin gidan,yana laluba aljihunsa ya nemi keys d'insa a tare da shi ya rasa,ya waiga yaga ko a hanya ya yar da su amma bai gansu ba,akan ya koma cikin gidan ya duba dan ya fi kyautata zaton a d'akin Mama ya yar da su kawai ya gwammace ya wuce gidan Dadda,sanda ya shiga bai tarar da kowa a parlon ba,ya kwanta kan kujera ya rufe idanunsa,a hankali komai da ya faru ya dunga dawo masa fresh,sai a lokacin yaji zuciyarsa ta karye abunda bai tab'a yi ba tsayin rayuwarsa a hankali yake kuka mara sauti,hawaye suna kwaranyowa daga idanunsa,Manar da zuwa lokacin ta gama gyara jikinta saboda zuwan period d'inta ta fito parlon a niyyarta ta kulle part d'in kasancewar ba'a jima ba Dadda ta fita unguwa y'ar gidan Tasallah k'awarta ta haihu,ta fito rik'e da keys a hannunta tana wasa da su ta gansa kwance kan kujera,ta harari inda yake ta zumb'uro masa baki,har ta d'auke kanta saboda haushin fad'an da ya mata babu jimawa,sai kuma idanunta suka hango mata kamar dai wani abu yana faruwa,da sauri ta sake kallon inda yake kwance,shi kam ko kula da ita ma bai yi ba,ganinsa yana wani irin kuka mai shiga zuciya though babu sauti hawaye kad'ai suke zubowa ta mugun tsorata ta zaro idanu cikin firgici,tsayin rayuwarta da shi bata tab'a ganinsa a irin yanayin ba,da gudu ta k'arasa tana kiransa "Yaya!" Ta tsuguna gabansa da fuskar kuka ta kai hannunta saman fuskarsa tana goge masa hawaye bata san sanda ita kanta ta kece da wani kuka ba,jin sauntinta da k'amshinta a kusa da shi ya sashi zabura ya d'ago yana kallon yadda take kuka ba tare da sanin dalilin kukansa ba,da sauri ya kai hannu ya k'arasa goge hawayensa yana kallonta cike da dauriya yace "me kike ma kuka?" Girgiza masa kai tayi alamun bata sani ba,ya zuba mata jajayen idanunsa yace "tambayarki nake!" Da muryar kuka tace "Yaya nima ban sani ba,gani nayi kawai kana kuka" saurin rik'ota yayi ya zaunar da ita kusa da shi ya kama hannuwanta duka biyu ya k'ank'ame kamar wani zai kwace masa ita,ajiyar zuciya suka dunga saukewa a tare,sai da suka samu nutsuwa kafin da wani murya mai cike da rashin hope yace "Baby kina so na?" Da sauri ta gyad'a masa kai,hawaye suna sake zubowa idonta tace "Ina sonka Yaya,kaima kana so na?" Wani murmushi yayi hawaye sun cika masa ido yace "yeah! I do" b'ata rai tayi saurin yi tana masa wani kallo a shagwab'e tace "me kace?" Bai san sanda murmushi ya kufce masa ba ya zuba mata idanunsa yana kallonta da wani sanyayyan murya yace "ina son ki Baby" murmushin ta mayar masa,yayi shiru sai kallonta yake a hankali ya kai hannunsa ya goge mata guntayen hawayen da suke fuskarta yace "Baby!" Da sauri ta kalleshi bata amsa ba,d'an shiru yayi da farkon kafin ya bud'e bakinsa da kyar yace "ina da muhimmanci a gurinki?" Tace "ehh Yaya" yace "duk abunda nace za ki iya yi min?" Da sauri ta sake cewa "ehh!" Yayi shiru kamar yana tunani kafin yace "da gaske duk abunda nace za kiyi?" Ta gyad'a masa kai cike da tabbatarwa idanunta a kansa,ya sauke numfashi yace "za ki iya killacemin kanki?" Squeezing fuskarta tayi bata gane me yake nufi ba tace "Yaya me kake nufi?" Yayi shiru kamar kada ya fad'a mata because bai san a yadda za ta fahimci maganar ba,and bai ma sani ba ko za ta fad'awa wani,sai da yaji ta d'an girgiza shoulder sa kafin ya dawo hayyacinsa,ta d'aga masa gira tace "mene ne?" Yace "Arhhmm!" Kamar zai fad'a mata kuma sai yace "barshi ma kawai,nan gaba zan fad'a miki" shagwab'e fuskarta tayi kamar za tayi kuka da sauri ya rik'o fuskarta yana girgiza mata kai yace "don't cry.." Sosai tayi fuskar kuka tace "ni sai ka fad'amin abunda kayi niyya" murmushi yayi yana kallon yadda lips d'inta suke fitar da words d'in a nutse ya zuba musu ido yana jin wani abu yana taso masa,waving hannunta tayi a dai² fuskarsa yayi saurin kallonta yana sauke numfashi,ta b'ata rai tace "baka fad'a ba fa" gaba d'aya ya rikice yace "me?" Tace "baka ce komai ba kana ta kallona" girgiza mata kai yayi ya lumshe idanunsa,ta sake tab'a shi fuskarta a had'e tace "ni idan baza ka fad'a na tafi" wani kallo ya mata da har cikin jikinta sai da ta jishi ya mayar da idanunsa ya kulle yace "ina za kije?" Tace "gurin Ameerah za ni,ba zan iya zaunawa ni kad'ai ba" ido d'aya ya bud'e ya kalleta yace "ni aljani ne ko cinye ki zanyi idan kin zauna?" Dariya ta fara masa ya bud'e idanunsa duka ya zuba mata su fuskarsa a d'aure,just in time ta shiga taitayinta,ya girgiza kansa yace "to na sani ko ni ba mutum bane da kike cewa ke kad'ai" d'auke kanta tayi tace "ni dai tafiya zanyi tunda baza ka fad'a ba" yace "me zan fad'a?" Tace "maganar d'azu daka fara" squeezing fuskarsa yayi yace "nace me?" Wani kallo ta dunga binsa da shi ta kasa masa magana,sai da ya tab'ata tayi kicin² za ta matsa daga kusa da shi ya rik'o hannunta,ta kalleshi ta kalli hannunsu da ya sark'e fingers d'insa cikin nata,a hankali yace "don't go.. Stay with me please" b'ata rai tayi tace "ni ka daina min turanci" yayi murmushi yana kallon yadda tayi yace "mene ne matsalarki?" Ta kalleshi tace "haka kace?" Wani dariyar da bai tab'a irinsa ba yayi ta dunga kallonsa ganin how cute he is da yana dariyan,sanda ya daina ta turb'une fuskarta tace "Yaya ka ci gaba" ya kalleta yace "me fa?" Tace "dariyan da kake,dan baka ga yadda ya maka kyau ba" yayi murmushi yace "kina so nayi?" Ta gyad'a masa kai da sauri tace "sosai ma" yace "sai dai ki siya" zaro idanu tayi tace "ni to ina naga kud'in siya?" Yace "ba ki da su?" Ta gyada masa kai,yace "eyyahh! Shi kenan baki da rabon gani" sosai tayi fuskar kuka yayi murmushi yace "ko dai na ranta miki,idan Hjy ta dawo sai ki karb'a ki biyani?" Da sauri tace "eh! Zan karb'ar maka a gurinta" yace "no! Ban yarda ba,kada kiyi min irin nata kice kinci dubu sai ceto" dariya ta fashe masa da shi yace "ohh! Na fad'a dai² ko?" Ta girgiza masa kai tana tsayar da dariyarta tace "aaaaa.. Ni fa ba haka nake nufi ba" yace "ya ya kike nufi?" Tace "babu komai" yace "ban yarda ba" tace "da gaske zan karb'ar maka idan ta dawo" yace "um'um! Sai dai ki yimin labari mai dad'i" da sauri tace "shi kenan ba sai na biya ba?" Ya harareta yace "inji wa yace haka?" Tace "to ai idan nayi maka labari ka ga ba sai na biya ba" yace "a'a za ki biya" da sauri tace "tabbb' d'i ai sai dai idan kaima za ka biya ni shi kenan kaga na samu kud'in da zan biya ka" yace "da gaske?" Tace "ehh!" Yace "ke fa k'anwata ce,sai na biya za ki ba ni labari?" Tace "to ba kaima ka ce sai na biyaka ba?" Yace "shi kenan na yafe ba sai kin biya ba" da sauri itama tace "nima na yafe to" hira sosai suka dunga yi tana bashi labari,wani yayi murmushi wani kuma idan yaga ta yi wauta yayi dariya,sosai ranar ya ba-ta mamaki,ta dunga tuna lokacin baya da suke kamar haka,daga bayan tafiyarsu Saudiyya zuwa yanzun ne kad'ai aka samu canji,sai ga shi yau ya sake dawo mata kamar asalin Yayanta da ba ya kyararta,a hakan Dadda ta dawo ta samesu sai surutu suke,tayi tsaye bakin k'ofa tana kallonsu sanda mamaki ya isheta ta k'arasa shiga tana rik'e chin d'inta tace "me zan gani kuma yau ni jikar laraba?" Dukansu suka juya suka kalleta,Waleed ya d'auke kansa yace "sannu da zuwa" Manar ma tayi mata sannu da dawowa,babu wanda ta amsawa ta k'arasa shiga ta ajiye mayafinta saman kujera ta wuce d'aki tana fad'in "ai shi kenan,ni dai ban san lokacin da kuka shirya da mutumin ba" Manar ta bita da kallo bata kulata ba,tana shigewa tayi saurin rik'o hannunsa a hankali ta rad'a masa tace "Yaya tashi mu tafi" ya kalleta da sauri yace "ina za muje?" Tace "ni wallahi mitarta ne ba na so,ita kuma yanzu sai taita ma mutane fad'a ko basu yi komai ba" murmushi yayi yace "ke da Hjyn kuma zan ji kanku?" Tayi kicin² tace "ni dai idan baza kaje ba zan tafiyata" tashi yayi yace "ina kike so muje wai?" Tace "yawo" zaro idanunsa yayi yace "yawo zuwa ina?" Tace "ko ina ma,muje da sauri ni dai kafin ta fito" jin alamunta tahowarta ta turasa suka yi waje da sauri,suka tsaya balcony ya kalleta yace "Umhn! Ina jinki" tace "ina mukullinka?" Ya watsa mata hannuwansa yace "suna d'akin Mama namanta su" zaro idanu tayi tace "ya akayi ka barsu a can?" Yace "ohoo! Ko zaki ki d'auko mana?" Ta wani zaro idanu a tsorace tace "tabb' d'i wallahi bazan iya ba" yace "saboda me?" Tace "ina jin tsoro" yace "tsoron wa?" Tace "Mama mana" shiru yayi yana kallonta kafin yace "shi kenan sai dai mu hak'ura da fitan" da sauri tace "to Yaya kai kaje ka d'auko mana" ya zaro idanunsa yace "tsoro nake ji nima" tace "tsoron wa?" Yace "Mama" ta kallesa tace "to kai ba Mamar ka bace me yasa kake tsoronta?" Yace "munyi fad'a d'azu" dariya ta fara masa tace "kai Yaya da Mamar ta ka kuka yi fad'a?" Ya kalleta yace "ke ba Mamarki bace?" Ta tab'e baki tace "ni ba Mamata bace ita,mother da Aunty ne mamomina" wani kallo ya dunga yi mata yace "saboda me ita bata zama Mamanki ba?" Tace "to ba ita kullum sai dai tai ta min fad'a ba,kuma ko gaisheta nayi ba ta amsawa,shi yasa nima na daina gaisheta,kuma su Deejah ma ba sa gaida Mother da Dadda shi yasa ni kuma na fad'awa Dadda tace nima na daina gaisheta ai uwa bata fi uwa ba" still yayi yana kallonta kafin ya matso kusa da ita yace "me yasa kike k'in gaisheta?" Tace "to ba su Diyanah suma ba sa gaisar da Mamata ba" yace "amma ni ai ina yi" tace "to ai na ka daban suma nasu daban" a hankali ya rik'e hannunta yana kallon cikin idanunta yace "daga yau za kina gaisheta?" Tayi saurin kallonsa,ya d'aga mata kai yace "yessss! Suma zan samesu,za suna zuwa suna gaida mother" tace "to Hjy fa?" Yace "itama haka" ta tab'e baki tace "tabb'! Baza su zo ba fa" yace "saboda me?" Tace "har Abba fa sai da yace musu amma basa zuwa" yace "yeah! Ni zansa suyi" ta karkace kai tace "tabb' d'i ni dai gaskiya bazan yi ba" ya d'aure fuskarsa yace "ko saboda ni baza kiyi ba?" Ta girgiza masa kai tace "a'a zanyi saboda kai" yayi murmushi yace "thank u" daga haka suka koma parlon suka sake zaunawa suka ci gaba da hira,dukkan b'acin ransa lokaci d'aya ya nemesa ya rasa,tsaf ta goge masa komai daga ransa. Yana barin d'akin cikin tsananin tashin hankali Mama ta fizgo wayarta ta fara dannama Hjy Izzatu kira,bugu d'aya ta d'auka da fad'in "y'ar halak kink'i ambato.. Kin ganni gidan Sahiba" duk da tashin hankalin da take ciki bata fasa tambayarta ba tace "Hjy Baraka?" Hjy Izzatu tace "ehhh! Wallahi yanzun ma maganarki muke tace kwana biyu ai baku had'u ba" ajiyar zuciya Mama tayi tace "wallahi ki bari kawai ina cikin tashin hankali ne" Hjy Izzatu tace "tashin hankali akan me,me yake faruwa kuma?" Mama cikin dauriya tace "maganar ya fi k'arfin muyi shi a waya,ke dai kawai ki samu ki zo ko ni na zo" ajiyar zuciya Hjy Izzatu tayi tace "shi kenan idan na bar gidan Sahiba zan b'illo" Mama tace "da kin taimake ni wallahi,dan yau duka ba na cikin nutsuwa ta" Hjy Izzatu tace "shi kenan sai na shigo d'in,dama akwai maganar da nake son muyi dake ma,kuma sai kika katse min hanzari da wannan maganar,but babu matsala duka idan na zo sai mu tattauna" Mama ta amsa suka yi sallama,tana sauke wayar daga kunnenta ta rushe da kuka tana fad'in "Allah ya isa tsakanina dake Maryam da dukkan zuri'ar ki,in Allah ya yarda bazan tab'a ganin wannan bak'in cikin ba" ana cikin haka Hjy Izzatu ta k'araso gidan,tunda ta shigo suka k'ule cikin d'aki Mama take ba-ta labarin duk abubuwan da suka faru,Hjy Izzatu ta rik'e baki tana jinjina maganar tace "dank'ari! Yanzu shi Waleed d'in ne ya iya kallonki ya fad'a miki wannan maganar?" Mama cikin kuka tace "wallahi Hjy ni kaina sai da naji mamaki" Hjy Izzatu ta girgiza kai tace "a'a wannan dai wallahi kema daga ji akwai makirci ciki,Waleed da ko mai kika ce masa obeying yake bai tab'a miki gardama ba,shi ne har kuna musayar yawu da shi?" Mama tace "ki gane min hanya dai,ni kaina na kasa believing" Hjy Izzatu tace "wallahi da sake.. Wai an bawa mai kaza kai,kin san Allah ba yin kansa bane,dole akwai wata a k'asa" da sauri Mama tace "ko?" Hjy Izzatu cikin tabbatar mata da zancenta tace "ahaafff! Ke dai ki bari kawai amma sha Allahu muka je gurin malam d'an juma abunda zai tabbatar mana kenan" Mama cikin tashin hankali tace "to yanzu ya kike ganin za ayi?" Hjy Izzatu tace "ai yadda za'ayi ki shirya kawai gobe muje" Mama tace "amma ba kya ganin gobe ya yi wuri na sake requesting fita gurin Alh?" Hjy Izzatu tace "a'a wane irin wuri kuma? Ai da zafi² ake bugun k'arfe,ko kuwa dai kin fi so muyi sanya muna ji muna gani a sabautamu?" Mama ta girgiza kai tace "ina fa zan so haka ya faru da raina" Hjy Izzatu tace "atoohh! Idan ba haka kike so ayi ba kuwa ai ya zana dole mu fita goben" da sauri Mama ta jinjina kai tace "an gama ai ko Alh bai yarda bama zan saci hanya na zo" Hjy Izzatu tayi dariya tace "yawwa y'ar gari.. Ni kuwa kin ma katse min hanzari fa!" Mama tace "hanzarin me kuma?" Hjy Izzatu tace "maganar auren da boka yace ki yiwa Waleed nake son tuna miki" wani ajiyar zuciya Mama tayi tace "ki bari kawai sai na nutsu zan waiwayo kan wannan batun" Hjy Izzatu tace "a'ahh! Nima ba nufina kenan ba,na dai gano miki suruka ne a gidan da ya dace" kallonta Mama ta dunga yi bata gane me take nufi ba,tace "fahimtar da ni" Hjy Izzatu tace "y'ar Sahiba na gano yau,kin san ta gama karatun ta dawo k'asar,ni dai wallahi na yi masa