tace "ina kuma za ki?" Juyowa tayi tace "ke ni rabu da ni,wancan mutumin zanje nema,yau sati d'aya kenan ban sashi a idanuna ba" yamutsa fuska tayi tace "wane mutumi?" Dadda tace "Waleed mana.. Ko kin gane min shi?" Girgiza kai tayi saurin yi tace "a'a! Nima rabona da shi tun ranar da ya shigo kika samesa kitchen" Dadda dai kamar za ta fashe da kuka tace "to wai ni me na masa da zafi da zai d'auki gaba da ni,ya daina shigowa?" Manar tace "to ba ke kika koresa ba?" Zaro idanu tayi tace "yau naji jaraba.. Ya za kuna cewa ni nace ya daina zuwa,fisabilillahi Yaro yaji ai ba zai ji dad'i ba,ta ina ma zance ya daina zuwa?" Manar tace "to ba ke bace dai kika faffad'a masa magana,ai dole ya daina zuwa,kuma yanzu sai ki zo kina neman sa?" A fusace Dadda tace "ni dai yau na shiga uku,wane magana zan fad'a masa ni kuwa? Bayan duk cikin jikokina na fi sonsa!" Wani had'e rai Manar tayi ta harareta cike da jin haushi tace "to tunda kinfi sonsa ba sai ki tafi ki nemosa ba da kanki ki daina tambayar mu" Dadda tace "yanzu kuwa y'ar nan.. Bari ki gani" ta mik'e da hanzarinta,har ta yi gaba ta waigo tace "ko za ki zo muje tare? Kinga dare ne bana fita ni kad'ai ba" Manar dai bata kalleta ba tace "tsoro kike ji ne?" Da sauri Dadda tace "haba dai.. Wane mutum,me jiya tayi ma balle yau? Muda muke keta daji da talatainin dare" Wani dariya Manar ta saki babu shiri tace "ke dai Dadda idan tsoro kike ji ki fad'a sai na taso na raka ki" harara ta maka mata ta yi gaba tana mita "kuji min yarinya,Allah na tuba sanda muke k'auye muke gane² bamu ji tsoron komai ba sai yanzu da duniyar tayi lafiya,su kansu jinnun ba ganinsu aka cika yi ba saboda addu'ah da ilimin da ya ratsa mutane.." Dariya Manar ta dunga yi har da fad'owa k'asa bayan data tabbatar Dadda ta fita,ta tashi ta biyota lokacin har ta yi nisa,Dadda tana zuwa ta dunga bubbuga k'ofar apartment d'in da k'arfi,Mama tasa Deejah taje ta ga waye a gurin,tana bud'ewa taga Dadda ta bita da kallo bata yi magana ba,Dadda ta wuceta ko kallo bata isheta ba,tab'e baki Deejah tayi ta biyo bayanta,tun kafin ta k'arasa inda Mama take ta fara magana "Asama'u! Ni kam ina Muhammadu ya shiga duk kwanakin nan ban sashi a idanuna ba?" Waigawa Mama tayi da sauri,ganin Dadda yasa ta fad'in "sannu da zuwa Hjy" Dadda ta saki baki tana mata wani kallo kafin ta kyab'e baki tace "yau kuma ni kike ma sannu da zuwa?" Mama ta sunkuyar da kai ba don ta-ji kunyar abunda Dadda ta ce ba,Dadda ta tab'e baki tace "ni dai in dan ganin idona ne yasa kika ce min sannu da zuwa dama ki rik'e abunki,ni ba sannu da zuwanki na zo amsawa ba,tambaya ce dai na zo yi dama ina Mamman ya shiga?" Mama bata d'ago ba tana b'ata rai tace "bai dawo ba" Dadda ta k'ureta da ido tace "yana garin ne?" Mama tace "ehh yana gurin aiki" hangame baki Dadda tayi tace "Auuu! Da gasken dai ba k'arya aka masa ba yana nan,amma dan iya shege shi ne ba ya zuwa inda nake? Ince dai ke kika masa khud'ubar tsiya kika ce masa ya daina zuwa gaishe ni?" Saurin d'ago kai Mama tayi za tayi magana ta hango Abba yana sakkowa shi da Aunty dake bin bayansa,ba dan ta shirya had'iye maganar ba tayi shiru tak'i cewa komai,k'asan ranta sai suya yake mata,ta so ace Abba bai fito ba ta kwab'awa Dadda maganganu,Abba ya k'araso cikin parlon yana kallonsu d'aya bayan d'aya,yace "wani abu yake faruwa?" Da sauri Dadda ta kallesa tace "yawwa! Yaro gwanda da Allah ya kawoka,gara ayi komai akan idanunka" kallonta Abba ya ci gaba da yi bai yi magana ba,Dadda tace "ka ga wannan k'atuwar matar taka,wallahi ba ta da tsoron Allah ko kad'an" Abba ya kasa daurewa yace "me ya faru Hjy?" Dadda tace "idan banda rashin tsoron Allah ni ba ni na haifeka ba?" Abba ya gyad'a kai yace "ke ce Hjy" tace "to ita matar ta-ka bata san da haka bane ko dai mancewa tayi?" Abba ya kalli Mama da ta had'e rai yace "ta sani Hjy" Dadda tace "a'a bata sani ba" Abba dai ya kasa gane me Dadda take nufi sai kallon Mama yake yace "i made sure ta sani Hjy,ta san matsayinki a gurina" girgiza kai Dadda tayi da sauri tace "a'a Yaro kada ma mu fara jayayya da kai,da ta san irin matsayin da nake da shi a gurinka da bata k'i zuwa duk safiyar Allah ta gaishe ni ba,kana ganinta nan dai a haka kamar mutuniyar kirki,amma ni ban isa taje ta tsuguna ta gaishe ni ba,ko da muka zo garin kaf gidan nan babu mahalukin da baije yayi min sannu da zuwa,ya tambaye ni mun zo lafiya ba,amma ita da y'ay'anta kaf ni banga k'eyarsu ba,shi isa nima ko da na tashi rabo na ban babu su ko abun share hanci ba.. Aaahhh tooooh! Maganar gaskiya fa kenan,wanda yayi da kai ai kaima sai kayi da shi,wanda kuwa yace baya yi da kai sai kaima kak'i yi da shi,amma dai maganar gaskiya ka ja mata kunne,idan ta hana wad'annan gantalallun zuwa su gaishe ni sun bi maganarta,bata isa hana Mamman zuwa inda nake ba saboda ni naci wahalarsa,komansa ni ce dan me kuwa za ta dunga k'ok'arin shiga tsakanin mu?" Wani kallo Abba ya dunga jifan Mama da shi har Dadda ta dasa aya,Abba cikin tsananin b'acin rai yace "Asama'u! Maganar da Hjy ta fad'a akanki da yaranki haka yake bakwa zuwa gaisheta?" A fusace Dadda tace "o'o! Ban gane haka maganar da na fad'a yake ba? Kana nufin da girma na zan yiwa matarka k'arya?" Saurin girgiza kai Abba yayi yace "a'a Hjy ko kad'an ba abunda nake nufi ba kenan,ina dai son ta tabbatar min ne da bakinta,saboda na san irin hukuncin da zan d'auka kansu" Dadda ta gyad'a kai da sauri tana washe hakor'in makkanta tace "Uhumn! Ko da na ji,na san dama baza ka bari a wulak'anta ni ba.. Kai dai Yaro Allah maka albarka ya kyauta bayanka" Abba yace "ameen" kafin ya juya ya sake kallon Mama yace "Hjy Asama'u dake nake baki ba-ni amsa ba?" Mama cikin had'e rai tace "haka ne" Abba ya dunga kallonta yana gyad'a kai cikin tsananin b'acin rai yace "ita uwar tawa ce baki ga damar zuwa ki gaisar ba kenan?" Mama dai ta yi shiru sai b'ab'b'ata rai take,a fusace Abba yace "da kika ki zuwa su kuma yaran fa? Wane dalilin yasa kika hana su zuwa?" Nan ma dai tayi shiru,cikin fushi Abba yace "Tambayarki nake?" D'auke kai tayi tak'i cewa komai,yana gyad'a kai ya kalli Deejah dake rab'e gefen k'afar Mama yace "je ki kiramin y'an uwanki duka yanzu kuzo ku same ni" tashi Deejah tayi da sauri jikinta yana b'ari tayi sama,ba'a jima ba suka dawo tare da su Ameerah da Diyana,suka nemi guri suka zauna kawunansu a k'asa Abba ya fara fad'a yace "wane iskanci yasa bakwa zuwa gaisar da Hjy?" Ameerah ta d'ago da sauri tace "Abba wallahi ni dai ina zuwa" Abba ya mata tsawa yace "rufe min bakinki a nan" da sauri Dadda tace "a'a Yaro banda takwarata cikin marasa zuwan,ita kam kullum sai taje gaishe ni safe da dare,wani lokaci ma can take wunarmin idan ba su da makaranta" Abba ya kalleta yace "su waye basa zuwa gaishe ki?" Da baki Dadda ta nuna su Deejah tace "ga su nan zaune gabanka gantalallu masu kamar an tada akuya tsaye" Abba ya kallesu yace "ashe ba-ku da mutunci? Ita Hjyr sa'ar ku ce?" Suka yi shiru,tsawa ya musu yace "sa'ar ku ce nace?" Da sauri suka girgiza kai,Abba yace "mutanen banza mutanen wofi,ni za ku gaishe ni uwata ce baza ku gaisar ba?" Suka yi shiru,fad'a sosai ya dunga yi daga k'arshen yace "duk ranar da ta sake kawo k'orafin kunyi wani abu na rashin da'a ranku sai ya yi mummunan b'aci zan sab'a muku sosai a gidan" a fusace yace "baza ku iya bada hak'uri ba?" Da sauri suna had'a baki suka ce "kiyi hak'uri" Dadda ta kau da kai tana tsuke fuska tace "shi kenan Yaro ya wuce,ni dama buri na har kullum bai wuce ace zuri'arka sun samu shaidar k'warai ba kamar yadda ka samu" Abba ya gyad'a kai ransa a b'ace yace "kiyi hak'uri Hjy in sha Allah haka bazai kuma faruwa ba" Dadda ta washe baki tace "to shi kenan,ai ya wuce ma" ta mik'e tsaye tana karkad'e jiki Abba ya bita da kallo,tace "to ni dai na tafi tunda wanda na zo neman baya nan" da sauri Abba yace "waye kike nema?" Tace "Mamman nazo nema,shima yau sati guda kenan ban sashi a idanuna ba,daga yin y'ar magana ya d'auke ni da gaba ya daina zuwa gaishe ni,ni dai ban san wane irin laifi nayiwa matarka ba da ta k'ullace ni take min haka" ran Abba ya kuma b'aci ya dunga kallon Mama ya kasa yi mata magana,Dadda tayi masa sallama ta juya ta nufi hanyar fita tana mita,tana bud'e k'ofa suka kusa yin karo da Manar dake tsaye jikin k'ofa ta kasa kunne tana sauraren abunda suke cewa,da sauri Dadda tayi baya kad'an ya rage bata zura da gudu ba,Manar ta fara b'ab'b'aka dariya tana rik'e ciki,wani irin kallo Dadda ta dunga binta da shi kamar za tayi kuka,can kuma sai ta d'auke kai tana tsuke fuska tace "ke kuma me kike yi a nan?" Manar ta juya tana dariya tace "biyo ki fa nayi na ga kina jin tsoro" wani kallo Dadda ta maka mata,cikin jin haushi tace "kin fad'awa uwarki Maryam haka" da sauri Manar ta b'ata rai tace "ke wai daga an miki wasa sai ki fara zagin mutane" a fusace Dadda tace "to ko za ki rama?" Harararta Manar tayi tayi k'wafa,Dadda ta wuce fuuu ta barta a gurin kamar za ta tashi sama,Manar ta zumb'ura baki tak'i binta ta wuce apartment d'in mother. Tun da Dadda ta tafi Abba yakewa Mama fad'a ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba sai da ya mata tass²,Mama dai tak'i cewa komai,yanda tayi masa ya sake k'ona masa rai ya dunga kallonta bai dai ce mata komai ba,ya d'auki waya ya fara kiran Waleed,Waleed dake driven ya d'auka yayi sallama,Abba ya amsa kadaram kadahan,kafin yayi wani magana Abba yace "where are u Muh'd?" Waleed yace "i'm on my way back home" Abba ya gyad'a kai yace "alright! Idan ka dawo ka same ni ina son ganinka" amsawa yayi yana duk'ar da kai kamar yana gaban Abban,in less than five minutes ya k'araso,yayi parking ya fito ya rufe motar gabansa sai fad'uwa yake ya bud'e k'ofar ya shiga da sallama,d'ago kai Mama tayi ta bisa da kallo tana had'e rai,and ta k'i amsa sallamar da yayi,sure ba don Abba dake zaune ba baza ta tab'a bari ya zo ba,tun yana hanya za ta masa waya ta hanasa k'arasowa,da kallo ya dunga bin occupants d'in parlon,Abba ya kallesa fuskarsa babu fara'a in a serious note yace "get seated my friend" guri ya samu ya zauna kansa a k'asa ya gaisar da Abba then Mama da take aika masa mugun harara,Aunty kam da fara'a sosai a fuskarta ta amsa masa har tana tambayarsa aiki,da yake kansa na k'asa bai san ma abunda Mama take yi ba kasancewar tun shigowarsa bai yarda ya kalleta ba,Abba yana kallonsa yace "Muh'd! Me ya had'a ka da grandma d'inku?" K'asa ya sake yi da kansa ya kasa magana,Abba yace "am i not talking to u Mr man?" Wani ajiyar numfashi yayi kafin yace "nothing Abba" tsabar mamaki yasa Abba couldn't stop looking at him,then ya maimaita "babu komai kace?" Yayi shiru ya kasa amsawa,gyad'a kai Abba yayi yace "this will be the last time da za'a kawo min k'aran ka,kai ne babba duka gidan amma kuma da kai ake complaints,wane irin shirme ne wannan?" Shi dai bai iya cewa komai ba har Abba ya gama fad'an yace ya tashi ya bashi guri,hak'uri ya fara bawa Abban kafin ya mik'e zai bar gurin,Abba ya bisa da kallo yace "make sure ka je ka bata hak'uri kafin safiya if not kuma ranka zai b'aci" shiru yayi ya juya ya nufi hanyar fita,kusa da apartment d'in su mother yana k'ok'arin wucewa aka bud'e k'ofa,ya waiga a hankali ya kalli gurin suka yi ido biyu da Manar dake fitowa,d'auke kai yayi ya ci gaba da tafiya,Manar tana hangosa ta kwalo masa kira "Yaya" bai tsaya ba ya ci gaba da tafiya,ta biyosa da sauri tana zumb'ura baki tace "shi ne baza ka kula ni ba ina maka magana?" Still ya k'i tanka ta,haushin yadda yayi mata yasa ta sha gabansa ta koma tafiya da baya²,ganin fuskarsa babu alamun wasa tace "Yaya me aka maka?" Wani kallo yayi mata a fusace yace "kauce ki ba-ni hanya kafin na mare ki" nok'e kafad'a tayi a shagwab'e tace "ni dai sai ka fad'a min abunda aka maka" wani kallo ya maka mata bai ce da ita komai ba ya ratseta zai wuce tayi saurin rik'o hannunsa.
#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2021.
*♡MANAR¸.•💥*
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA
_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._
_Bestowed to Fateema Abdulmajid._
05.
#Phone call..
Wani irin yammm yaji jikinsa yana yi,da sauri ya fizge hannunsa,ta sake kawo hannu za ta rik'esa ransa a b'ace yana mata wani kallo a kausashe yace "don't dare touch me!" Rau² idanunta suka yi da muryar kuka tace "Yaya!" Tsawa ya mata "be quite!" Jikinta har b'ari yake tsabar tsoron da maganarsa yasa taji,tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya ta juya da niyyar barin gurin yayi saurin fizgota,k'ara ta fasa ta k'ank'ame jikinta she thought ko zai daketa ne,da sauri ya waiwaya yana kalle²,kafin tayi wani maganar tuni ya jata da sauri ya nufi backyard,a jikin apartment d'in Dadda ya tsayar da ita yana mata wani kallo ransa kamar a b'ace yace "me zan miki?" Sheshshek'ar kuka ta fara tak'i masa magana,sanda tayi mai isarta kafin tayi shiru,ya nad'e hannunsa a k'irjinsa ya zuba mata idanunsa da suka fara juyawa,sanda ta fara gajiya da tsayuwar a hankali ta zumb'uro baki still kuma bata da niyyar cewa wani abu,almost 15 minutes suna ta tsaye babu wanda yace da wani k'ala kafin Manar ta shawaran tafiya ba tare da ta yi masa magana ba ta fara k'ok'arin barin gurin,saurin rik'ota yayi ya dawo da ita,fuskarsa babu alamun wasa ya zuba mata idanunsa masu cike da kwarjini fuskarsan nan a daure still kuma har lokacin bai ji zai iya yi mata magana ba,idanunta ta d'aga tana kallonsa a shagwab'e tace "Yaya!" Yace "Uhn!" Ya d'aga mata girorinsa,ta k'ara narke murya tace "ina son tafiya" wani kallo ya mata yace "na ba-ki izini?" Ta dunga kallonsa kamar za tayi kuka tace "to ai na gaji da tsayuwa" kamar bai gane me take fad'a ba ya sake d'aga mata gira,kuka ta fara yi mara sauti sanda ta shammacesa tayi wuf za ta gudu,taji ya rik'o arm d'inta da k'arfi ya dawo da ita,fuskarsa a d'aure yace "u have nowhere to go girl!" Kuka ta fashe da shi bata gane me yace ba,da wani braking voice tace "to ni fa na gaji,kuma kak'i bari na tafi" wani murmushi yayi ya d'aga gira yace "hukuncinki kenan" saurin kallonsa tayi tana tsayar da kukan tace "ni me nayi maka to?" Yace "u have no idea?" Ta zuba masa idanu tak'i cewa komai,a d'an tsawace yace "ba dake nake ba?" Zumb'uro baki tayi tace "to ni na ji me kace ne?" Ya bud'a idanunsa yana kallonta yace "baki sani ba?" Ta gyad'a masa kai,gyad'a kai shima yayi kafin yace "wancan ranar me ya had'a ku fad'a,da zan aika a kiraki kik'i zuwa?" Squeezing fuskarta ta fara kafin ta b'ata rai tace "to ba su bane dai daga zuwa suka fara fad'a mana magana" idanunsa akanta yace "suka ce me?" Tayi shiru tak'i cewa komai sai da ya mata tsawa,a shagwab'e tace "kawai daga na tambayi Ameerah lokacin ba da su nake ba na ce har ta dawo? Ameerah tace kai sis mun dad'e fa a skul d'in tun 7am muka fita,na san time d'in ma ko juyin farko baki yi ba shi ne wannan Deejan ta tab'e baki tana mana kallon banza tace ya ma za'ayi ta sani tunda babu fuss! Ita kuma Diyanah tace dama tunda an fi ganewa a tafi wani duniyar karuwanci a b'ige da karb'an sabil ana cewa sana'a ake ai baza'a san komai ba,haka za azo a koma cikin duhun jahilci shi ne suka dunga mana dariya,sai ita Deejan ta sake cewa ai ko yanzu ma sis Diyanah kada ki fitar da tsammanin kamosu aka yi aka dawo da su,basu yi niyyar dawowa ba shi ne Diyanah ta dunga dariya har tana rik'e ciki tace wai kina nufin sun zama *TAKARI?* Shi ne dan Ameerah tace musu wannan ai ba yi bane,me yasa za kuna fad'an irin maganganun nan? Shi ne Diyanah tace an fad'a d'in ko akwai abunda za kiyi? Da Ameerah tace babu abunda zanyi zan dai fad'awa Abba muddin baku daina ba,shi ne Deejah tace ai dama dole Ameerah ta tare min,tunda an tab'a k'anwar uwarta,shi ne dan Ameerah tace mata a'a Deejah kada mu kai nan,duk abunda za ku fad'a ya tsaya iya kanmu,amma kada ki kuskura ki k'ara saka iyayen mu,shi ne ita Deejan a tsiwace tace idan an tab'a me za ki iya yi? Ameerah tace sai kin gwada zan nuna miki abunda zanyi suka yi dariya su biyun suka tafa Diyanah tace kin ji fa sis kamar za ta iya mana wani abu,duk fa kwad'ayi ne yasa ta shiga maganar itama