suka jiyo muryan Mama na cewa "ana zuwa" wani sanyayyan murmushi Deejah tayi tana lumshe idanu,sanda Mama ta bud'e k'ofar ta d'an lek'o da son ganin waye,suka yi ido biyu da Waleed dake gaban k'ofar,Mama ta saki fuska tana kai hannu za ta karb'i Alhassan take musu sannu da hanya suka amsa,kamar yaron ya santa ya zuba mata idanu but kuma ya k'i zuwa,sai ma wani lafewar da ya k'ara yi a jikin Waleed,Mama ta bud'a baki tace "auu too! Baza ka zo gurina ba?" Deejah ta kyalkyale da dariya tace "Mama ai ba ya zuwa hannun mutane wannan,da dai Alhussain ne ko bai tab'a ganinki ba zai zo,amma wannan kou mu haka yake mana" Mama ta gyad'a kai tace "aatooo! Ya sha zamansa" sai ta mik'a hannu ta karb'i Alhussain,tare da ba su hanya tana fad'in "bismillah! Ku shigo" suka shiga suna yin sallama ta amsa musu,sai da suka shiga kafin ta biyosu a baya suka shiga parlor,Manar za ta zauna k'asa kan lallausan rug,Mama dake shigowa tace "haba Manar mene ne kuma zama k'asa,dan Allah tashi ki zauna sama kar ki b'ata kayanki" cikin jin kunya ta tashi ta zauna kan kujera,Mama tana ma Alhussain wasa tace "sannunku da hanya,kun sauka lafiya?" Suka amsa,Manar tace "ina wuni Mama,mun same ku lafiya?" Mama ta amsa da "lafiya lau alhamdulillah!" Sai satar kallon yadda Manar ta zama uwar mata take,tana tambayarta mutanen gida da yara,while a gefe d'aya sai kallon yanda Waleed ya zama,har wani special k'iba yayi jikinsa luff² kamar ka tab'asa jini ya fito,zara²n gashi a kwance a duka sassan jikinsa,sanda suka gaggaisa Mama ta mik'e ta kawo musu ruwa da lemo then abinci da ta shirya saboda zuwansu,kiran sallah dai ya sa Waleed bai zauna ba yace zaije sallah ya dawo,Mama tace "tou kai da kake bak'o ka san inda Masjeed d'in yake ne?" Yace "bazan rasa sani ba,idan na fita zan tambaya" daga haka ya kalli Manar da ido ya mata alaman sai ya dawo,ta masa murmushi ya juya ya fita,after an fito daga Masjeed ya dawo,yana yin sallama Mama tace "o'o! Kuma ka gane inda Masjeed d'in yake?" Yayi murmushi yace "tou Mama dama ai na fad'a miki" ta gyad'a kai tace "sannu da dawowa" ya amsata then ya koma ya zauna yana tasbihi,Mama ta kallesa tace "a zuba maka abincin?" Yace "ehh! Ba da yawa ba" tace "tou" sanda ya juya ya k'arema parlon kallo,yace "Mama ina suka shiga na ji gidan shiru kamar ke kad'ai ne" Mama tayi murmushi tace "sun shiga sallah ne" ya gyad'a kai ya gyara zamansa,yana cin abincin suka fito,suka masa barka da dawowa,ya gyad'a kai bai k'ara magana ba sai da ya gama,suka d'an fara hira jefi²,can wajen 3pm Azaan ya kirasa,sai da yayi murmushi kafin ya amsa kiran,Azaan yace "haba Malam ina ka shiga yau babu ko d'aga hannu" Waleed yace "wallahi munje gaida Mama ne" Azaan yace "kuma babu sanarwa,ko dan kada muce za muje?" Murmushi still yayi yace "not at all! Ban dai yi tunanin haka bane" Azaan ya gyad'a kai yace "alright! Sai yaushe za ku dawo kuma?" Waleed yace "maybe da dare" Azaan ya gyad'a kai yace "alright! Sai kun dawo,a gaishe da Mama" yace "zan fad'a mata in sha Allah" sanda ya tambayi yaransu kafin suka yi sallama,ba'a jiba sosai kuma ya mik'e yana d'aukan car keys d'insa yace "Mama zanje nan kusa na dawo" cikin barkwanci Mama tace "anya Waleed kai da kake bak'o,kada fa ka b'ata kasa mu daukan mayafi mu fita nemanka" Manar da Deejah suka kyalkyale da dariya,Manar na fad'in "ka ga Yaya kada kasa mu kuka bamu shirya ba" Deejah kam sai dariya take,yayi murmushi yana ma Manar wani kallon k'asan idanu yace "ni da k'asara za'a ce na b'ata cikinta,duka shekara nawa nayi bana nan? Na je nayi shekaru na dawo ban b'ata ba sai yanzu da y'an kwanaki nayi duka?" Manar tayi k'asa da murya tace "wancan zuwan daban,ka sani kou wani abu yasa yanzun ka iya b'acewa" shi dai murmushi kawai yayi bata san ya jita ba ya nufi hanyan fita,yana cewa "sai na dawo Mama" da ido yama Manar alamun ta zo,kwab'e fuska ta fara za ta masa musu,ya juya mata ido tare da nufar k'ofa ya fita da sauri yace "Lily zo nan" kamar wanda aka watsama ruwan k'ank'ara tsabar kunyan da ya sa ta ji,Mama da taga ba ta niyyar tashi tace "tashi mana daughter kuma,ko kunya na kike ji?" Da sauri ta tashi ta biyosa,dai² get ya tsaya ya juya yana kallonta,ta tsaya tana kallonsa tace "ga ni" matsowa yayi daf da ita yana kallonta yace "me ma kika ce yanzu?" Ta juya idanu tana kallonsa tace "yaushe?" Yace "kince sai dai in wani abu yasa nayi me?" Dariya ta kyalkyale da shi tace "auu! Wai ka ji dama?" Yace "ohoo!" Ya rik'ota jikinsa a hankali yana kallon lips d'inta yace "banga abunda zai sa na manta da identity na ba,sai dai kou kece za kisa ni mantawa" tayi murmushi tace "saboda me?" Yace "idan kina ba ni dad'i yanda ya kamata da wuri zan manta da ko ni waye ma bare wata k'asa" dariya ta kyalkyale da shi tace "kai Yaya! Amma tou ya akayi duk garan da ka d'iba a baya baisa ka manta ba idan haka ne?" Yana d'an squeezing fuskarsa yace "maybe saboda baki mayar da hankali bane lokacin amma yanzun idan mu duka muka yi aiki da guminmu sai kiga na manta" wani kallo ta masa tana rufe baki tace "duk abunda nayi a bayan kace wai ban yi ba" ya k'ara d'an tab'e baki yace "ai na fiki aikatuwa girl,kinyi but d'an kad'an ne ba da yawa ba" kallonsa ta dunga yi tana gyad'a kai tace "haka ma za kace?" Ya mata murmushi wanda ya k'ara masa kyau,kyawawan jerarrun hak'oransa farare tas da su suka bayyana,yace "oops! Ba haka nace ba" tayi kicin² tace "tou da me kake nufi? Ni sake ni na tafi" k'ara rungumeta yayi yana mata dariya mai d'an sauti yace "tsaya mana kiji sirri za muyi" tace "ni babu wani sirrin da za muyi,kayi tafiyarka sai ka dawo" da sauri yace "a'a za muyi mana juyo kiji na fad'a maki" a hankali ta d'an juyo da fuskarta tana kallonsa,ya zuba mata idanu kad'an yana kallonta,ganin haka yasa ta d'aga masa gira tace "ya akayi?" Yayi murmushi a hankali ya matso da fuskarsa,ji tayi kawai yayi grabbing lips d'inta yana sha,a d'an tsorace ta bud'a idanu tana son kwacewa,shi kam k'ara rik'ota yayi yana sucking lips d'inta,dan kansa ya gaji ya saketa,ta galla masa harara ta lashe lips d'inta tace "kai ko kunya baka ji a zo a ganmu?" Shoulders ya d'age yace "it's my property fa.. My halal,kema ga shi nan har lashe lips kike saboda zakin da kika ji" dariya ya bata ta girgiza kai tace "yawwa! Master nace please ko za ka barmu mu kwana biyu a nan?" Lokaci d'aya fara'ar fuskarsa ta d'auke yana kallonta yace "a ina?" Tace "a nan mana gurin Mama" da sauri ya girgiza mata kai yace "a'a!" Tace "pleaseee!" Kafin ta k'ara magana ya d'ora index finger sa akan lips d'inta da fad'in "shhhiii!" Dole tayi shiru tana jujjuya idanunta akansa,yace "na barku ku kwana a nan,ni kuma na kwana a ina?" Tace "Master tou ba sai ka koma gida ba kai" yana mata wani kallo yace "kou?" Ta gyad'a masa kai tace "ehh!" Ya gyad'a kai yace "mu bar maganar nan tsakaninmu" tace "saboda me?" Strictly yace "saboda bazai yiwu ba" kallonsa ta dunga yi fuskarta ta yi rau² tace "shi kenan tou" yace "jeki ciki zanje na dawo yanzu" tace "umhn! Allah tsare hanya" ya amsa mata da "ameen.." Ya juya ya fita,jikinta a sanyaye ta bisa da kallo,sanda ya fita ta d'an lek'o sai da taga ya bar line then ta koma ciki. Sai kusan 7pm ya dawo,bayan ya tsaya Masjeed ya yi sallan isha'a ya shigo gidan,ya tarar da Deejah da Manar sai hira suke akan zuwa gidan Diyanah,Mama kuma tana zaune kan rug tana gama yiwa Alhussain wanka tana ciccilasa sama yana b'ab'b'aka mata dariya,Alhassan sarkin k'ulafuci yana lik'e jikin Manar yana ma Mama dariya kamar shi takema wasan,Waleed dake shigowa yayi sallama,suka amsa suna masa sannu da zuwa,bayan ya zauna Mama tace "Deejah kawo ma Yayanku ruwa da abinci" da sauri Waleed yace "kawo min ruwa kad'ai" Mama tana maida hankalinta kansa tace "abincin fa?" Yana kallon Manar yace "ba na jin yunwa" tace "tou ai kuma tun rana fa ina tunanin rabonka da abinci kou?" Yace "Mmm!" Mama tace "ki had'o masa da abincin.. Idan baka ci ba ni da za ka barma nayi yaya da shi?" Yayi murmushi yace "tou ki sa kad'an" Mama tace "wani cin abinci kad'an,kou dai abincin nawa ne bai maka ba? Na ga ka fara tumbi ina tunanin kou abinci ka fara ci da yawa" Manar dake musu dariya tace "har yanzu Mama haka nan yake ba ya son cin abinci,sai dai kayan kwad'ayi" Mama ta bud'a idanu tace "tou! Ashe su suka hurasa yake hawa kaman farashin k'asarmu" Deejah dake fitowa kitchen tace "sharrinta ne Mama babu wani kayan kwad'ayin da yake ci" Waleed dake tankwashe k'afa sanda Deejah ta ajiye masa plate yace "thanks.." Then ya d'ago idanunsa ya sauke cikin na Manar yace "kika sani kou ita take ba ni kayan kwad'ayin nake ci a b'oye?" Mama tayi murmushi tace "atou! Akwai dai lauje cikin nad'i,ya kamata muji inda maganar yake" Manar kam wani zaro idanu tayi ganin yana kashe mata ido d'aya yana mata kiss a b'oye,lokaci d'aya kwakwalwarta ta fassaro mata abunda yake nufi,da sauri ta d'auke kai tana turo baki,yayi murmushi yana kallonta yayi bismillah ya fara cin abincinsa yana sakin murmushi,yana sauraren hiran da suke,har ya gama yayi hamdala,Deejah tazo ta kwashe kayan ta kai kitchen,Manar ta biyota a baya tana harararsa ganin wani mayen kallo da yake mata,Deejah ta had'a kayan za ta wanke Manar ta matso za ta tayata suyi tare,Deejah tace "a'a dan Allah kije ki huta,naga girkinma ke kika yi fa" Manar tayi dariya tace "tou bak'on guri na zo da za ki hana ni yin aiki?" Ta fizge sponge d'in da sauri tace "go gefe madam" da k'arfi Deejah tace "Mama dan Allah ki kira Manar ta kyaleni nayi wanke²n,kin ganta wai lallai ita za tayi" da sauri Mama ta tashi ta nufi kitchen d'in tana cewa "haba Manar ki barta tayi mana,kin hana mu yin girki kuma wanke²n ma baza ki barshi tayi ba?" Manar tana murmushi tace "ki kyaleta kawai Mama na kusa gamawa ma ai kayan ba su da yawa" babu yanda Mama bata yi da itaba amma ta k'i bari,dole ta koma parlor har suka fito,lokacin ana kiran isha'a Waleed ya mik'e zaije sallah yace "get set Lily idan na dawo za mu tafi" ta gyad'a masa kai tace "tou! A dawo lafiya" ya fita yana cewa "Allah sa.." Sanda aka idar da sallah ya nufo gidan,suma lokacin duk sun idar da sallah suna dai zaune parlon suna hira,yayi sallama ya shigo,suka amsa masa,yana tsayen bai zauna ba yace "muje kada muyi dare" Deejah ta tashi tana d'aukan veil d'inta,Manar kam da kyar ta tashi,Waleed yace "Mama za mu koma,sai mun sake dawowa kuma" Mama dake kallonsu cike da alhinin barinta da za suyi,wuni d'ayan da suka mata jinsa take wani so special,saboda yau ta wuni cikin jama'a kuma tana jin gwarancin jikokinta,ba kad'anba kasancearsu tare ya d'auke mata kewa,ta kalli Waleed tace "ayyahh! Waleed baza ka barminsu su kwanarmin ba?" Da sauri ya juya ya kalli Manar kwakwalwarsa tana kawo masa tunanin ko dai bayan fitarsa sunyi maganar da Mama,sai kuma dai ya d'auke kai yace "za mu dai sake zuwa Mama yanzu bamu zo da shirin kwana ba" ta d'an gyad'a kai tace "tou shi kenan.. Na gode sosai,a gaisar da mutanen gidan idan kunje" ya amsa yayi gaba,suka biyosa a baya,sanda ya fita ya bud'e motar yace "oops! Mama na manta da sak'onki a mota" tace "sak'ona in ji wa?" Yana murmushi yace "mazajenki" tayi murmushi itama tace "a'a ni mijina d'aya,da shi kad'ai nake auren tunda shi ya yarda da ni" Manar tayi murmushi tace "ayyahh! Mama shima Alhassan wata rana da kansa zai zo inda kike" Mama ta gyad'a kai tace "tou Allah sa,ya ara mana tsawon rai" suka amsa kafin suka yi mata sallama suka shiga mota,Deejah tace "Mama sai an kwana biyu zan tambayi Abba nazo nayi kwanaki" Mama tace "tou Allah sa Abban naku ya amince" Deejah tace "in sha Allah ma zai bari" suka k'ara mata sallama,bayan Waleed ya shigar mata siyayyan da ya mata d'azu da ya fita,tana ta masa godiya da sawa rayuwarsu da yaransu albarka suka tafi tana d'aga musu hannu cike da kewarsu,direct sanda suka fara sauke Deejah a gida basu tsaya shiga ba suka wuce gida,yayi parking ya fito rungume da Alhassan,ya bud'e mata k'ofar ta fito d'auke da Alhussain suka k'arasa ciki,washe gari suka ma Diyanah zuwan bazata,Manar,Ameerah,Rania da Deejah,sai mazajensu da suka kaisu,ai kam ta ji dad'in ganinsu sosai,ta rasa inda za ta ajiyesu,haka surukanta ma sai nan² suke da su,sun sha hira sosai,a nan Dr Mahfouz sai satan kallon Deejah yake,sanda za su tafi kaf iyalin gidan Alh Baffanyo suka musu rakiya gurin motocinsu,Dr Mahfouz yana ma Waleed tsiya,Waleed yace "ka dai bini a sannu,idan ba haka na zan maka tsiyan da yafi wannan.. Ka san kuma zan iya" da sauri Dr Mahfouz yace "afuwan! Babban Yaya" Azaan yace "a'a nifa ban gane wani babban Yaya ba,muma duka ai yayye ne! Ko dai ko dai?" Akayi dariya,Amaar yace "atou! Ni dama tun d'azun na gano akwai wata a k'asa,shiru dai kawai nayi" a nan ma sanda suka tab'a barkwanci kafin suka yi sallama suka tafi. Wasa² sai da suka samu kimanin sati biyu a Nigeria,sun yi zumunci sosai,ko gidan Mama ma bayan wancan zuwan da suka mata sun koma,sun mata kwana biyu saboda alk'awarin da ya mata,cikin satinsu na uku suka fara shirin komawa India,ranan da za su tafi sanda mutanen gidan suka ji ina ma su zauna kada su koma,but haka nan dai akayi bankwana jirginsu ya mik'a. Bayan watanni biyu da komawarsu soyayya tsakanin Dr Mahfouz da Deejah ba'a cewa komai,dan lamarin da gaske ne,a lokacin kuma tuni ma har an saka ranar aurensu,Diyanah kam babu wanda ya kaita farin cikin za su zauna gida d'aya da y'ar uwarta,ita gaba d'aya ma hidiman ya had'e mata,Afreen k'anwarsu Dr Mahfouz ma da ba ta k'asar tuni ta iso da yaranta biyu maza,nan suka fad'a hidiman bikin babban Yayan nasu,su Manar kam sa cikin satin bikin suka k'araso,nan suka had'u basa nan basa can,tun da aka shiga satin biki,hidima kawai ake a duka b'angarorin biyu,ranan da suka yi dinner kaf d'insu anko suka sha na red d'in lace,mazan suka zuba farin shadda an masu aiki da bak'in zare,ya subhanallah kada kuso ganin wannan family da suka had'e kai,abun har ba'a cewa komai,Mama ma dai ta zo da kyar dan mugun kunyar shiga cikinsu Mother take,su kam a garesu sun nuna mata komai ya wuce,a haka aka yi biki aka watse,satin Deejah d'aya a d'akinta Alh Baffanyo ya shirya musu zuwa honeymoon,lokacin da suka dawo kuma bayan sun huta,ya kirasu yace ya sallamesu kowa ya d'auki matarsa su koma gidajensu tunda yanzun ya fahimci Farhan ya jima da yin hankali,ya daina yawon dare,daga gurin aiki sai gida,ko abokan ma tuni ya watsar da su,matarsa da d'ansa sune abokansa,idan ya taso ya d'auki little Daddy yana masa wasa suna dariya. Su Manar kam sai da suka k'ara sati d'aya bayan bikin su Deejah kafin suka koma India.
*Few years later...*
A hankali rayuwa take sake tafiya,komai yana sake canjawa,lokaci ya ja sosai,yanzun kimanin shekaru goma sha biyu kenan da auren su Waleed,alhamdulillah bayan twins d'inta ta k'ara haihuwan namiji,wanda Waleed ya sama Muhammad Azaan,suna kiransa (Little),cikin burin da Waleed yake ajiye su zuwa yanzun,da yawa daga ciki sun cika,ciki kuwa har da burin sama d'ansa sunan Azaan,for nothing other than ya mayar da irin halaccin da Azaan ya masa na sacrificing soyayyar da yake ma Manar ya bar masa ita,ba tare da ya sani ba ko ya yi shawara da kowa,ai kam ba iya Azaan kad'ai ba,hatta Raj Jarood da Rani Naheed sunyi murna lokacin da suka san sunan Azaan ya sama d'an nasa,wannan dalilin yasa Raj d'in k'ara rik'esu da amana,dan shi dama y'ay'a ya d'aukesu duka,tun ma ba Manar da iyayenta suka mallakawa only brother d'insa ba,komai na masarautar yanzun da shawarar su yake tafiya,saboda gani yake sune matasa wanda dole sai ana tafiya da su ne za'a samu ci gaban da ake buk'ata. Ameerah ma dai ta haihu bayan shekaru hud'u da aurensu ta haifi y'arta mace mai sunan Rani Naheed,sai tsohon cikin da take da shi yanzun,haihuwa yau ko gobe,Rania ma haihuwarta biyu duka maza,Amaar yasa sunan Abba Ibrahim Khaleel,sai na biyun Muhammad Jarood,a gefen mutanen Nigeria kuwa Diyanah ta sake haihuwan yara uku bayan Little Daddy,sun samu Asma'u (Miemie),da Aisha (Aflaha),sai wanda take goyo mai sunan Abba,Deejah ma yaranta biyu duka mata,ta farkon sunan Aunty ne Fatima (Ikhlas),sai ta biyu Maryam (Iftihal) sunan wata k'anwar Alh Baffanyo,amma ita Deejah kullum cewa take sunan Mother ne. Bayan duk wani k'alubale da suka fuskanta a baya,yanzu rayuwa ta inganta,komai ya zo ya wuce kamar ba'a yi ba. Dr Waleed kam da ya k'ara zama babban mutum yanzun alhamdulillah sunansa da d'aukakan da ya samu bai tsaya iya India ba,kusan k'asashen duniya d'ad'd'aya ne bai saka k'afarsa ba,dan ko Nigeria yanzun hospitals d'insa sun kusa zagaye states 36 na k'asar,inda yake da manya kuma k'wararrun ma'aikata,duk inda ka zaga da wahala baka ji ana batun *DR WALEED MAJI DA'DI* ba,da yawa y'an mata sun sha kawo masa tallar kansu yana k'i,saboda shi tun asalinsa bai taso da sha'awar auren mace sama da d'aya ba,a duk lokacin da irin haka ya taso kuwa hak'uri kawai yake basu,wani lokacin wasu y'an matan kance su dai ko amfani da su yayi,sai dai yayi murmushi yace "kuyi