da nan ta fashe masa da kuka sosai,da sauri ya d'ago fuskarta yace "shhhhiiii! Don't cry" ta kasa yin shiru sai sheshshek'ar kuka take,ya kai hannu yana goge mata fuska yace "i said ya isa,kou kina so ki sani kuka ne ehh?" Ta girgiza masa kai da sauri,yace "it's okay tou,ki bar kukan haka,okay?" Ta gyad'a masa kai,ya d'an zubawa lips d'inta da suka yi wani pinkish kaman na jarirai idanuwansa,so yake yayi kissing d'insu but yana gudun abunda zai iya faruwa,yana can duniyar tunani sai jin saukar warmth lips d'inta yayi akan nasa tana tsotsa,yayi saurin kallonta yana k'ok'arin raba bakinsa da nata,da kyar ya iya b'amb'areta yana kallonta yace "me kike yi haka? Baki san ba ki da lafiya ba?" Ta fashe da kuka sosai tace "tou ba kaima kana so ba?" Ya zaro idanuwansa yace "kika ji na fad'a miki haka?" Tace "ai tou ba sai ka fad'a zan sani ba" ya d'an lumshe idanuwansa a hankali yace "kiyi bacci nace,ina jiran Hjy suzo naje gida na dawo" kallonsa ta dunga yi kafin ma tayi magana aka yi knocking k'ofar,suka kalli k'ofar a tare kafin ya fara k'ok'arin sauka daga gadon ya kwantar da ita saboda tun da ya dawo ya kulle,ya k'arasa ya bud'e,da Dadda ya fara yin ido biyu fuskarta a tamke tana mitan tun asuba ya kamata ace an kawota taga jikin Manar d'in amma dan walak'anci ba'a tashi kawota ba,sai da rana ta gama zagaye duniya,ya matsa ya bata hanya yana mata sannu da zuwa,ta amsa ta wuce ciki,ganin Manar d'in ma idanunta a bud'e Dadda ta wani washe baki tace "kaiii! Barka da nazo dai yau na ga idanuwanki biyu ba kamar jiya ba har muka tafi kina kwance kamar gawa" ta k'arasa gaban gadon tana d'an murmushi,Aunty ta shigo d'auke da basket da ledoji a hannunta,Waleed yayi saurin karb'an kayan idanuwansa akan Manar ya ajiye,suka gaisa da Dadda then Aunty,suka masa ya mai jiki ya amsa,sun jima da shigowa kafin yace zai je gida ya dawo,suka masa Allah tsare,ya d'an kalli Manar a hankali yace "bari naje na dawo" ta d'an langab'ar da kai,yace "me zan kawo miki?" Instead of ta masa magana sai ta girgiza masa kai kafin tace "babu komai" ya musu sallama ya fita. Ak'alla sai da Manar ta samu kwanaki biyar a hospital d'in,lokacin su Ameerah har sun zo sun koma,Mommella kawai suka bari,kullum da ita ake wuni a hospital d'in,since that day da incidence d'in ya faru Waleed ya rok'i Dadda akan duk hukuncin da za'a yanke suyi hak'uri har ranar da za'a sallami Manar d'in,da farko Dadda bata fahimcesa ba tace saboda uwarsa ce shi yasa zai ce a bari ba yanzu ba? Sanda ya mata bayani sosai yace shi fa ba yana nufin kada a hukunta Mama bane,jikin Manar d'in yake so yayi sauk'i sosai idan suka daso gida duk za sufi samun nutsuwar fuskarta case d'in yanda ya kamata. Ranan Sunday da yamma suka dawo gidan,motocinsu suna yin parking Mama ta lek'o ta window tana kallonsu saboda har ranar babu wanda ya tayar mata maganar,a tunaninta ma aikin bokanta ne yaci su shisa taji shiru babu wanda yace mata k'ala,tana tsaye tana kallonsu tana tab'e baki suka wuce part d'in Dadda,tana hango sanda Deejah ta fita taje part d'in,sanda take dawowa ta shigo d'akin ta samu Mama tsaye wajen window har lokacin ta kasa zama,ta shigo tace "Mama! Ya kamata ki shiga kiga jikin Manar,ance ta samu miscarriage ki mata jaje" wani uban kallo Mama ta juya ta maka mata tace "to uwar iya,bazan je ba,idan sai na je za ta samu sauk'i daga can ta mutu" Deejah ta dunga kallon Mama ta kasa magana tsabar mamaki,sanda Mama ta mata wani tsawa tace "c'mon get out please idan kin gama kinibibin" jiki a sanyaye Deejah ta fita tana waigen Mama,ita dai duk ta rasa wannan dalilin k'iyayyan na Mama akan Manar,shisa fa ita tun sanda Mama tayi rashin lafiyar nan ta dunga surutai jikinta duk yayi sanyi tun daga nan ta sakko ta daina ma Manar d'in mugun tsanar da Mama ta cusa musu a kanta,lokacin da Deejah take fita ya yi dai² da shigowar Aunty,ta gaisheta kafin ta wuce,Aunty ta tsaya daga door way tana kallon Mama tace "Alh yana son ganinki a can b'angaren Hjy yanzu" sanda Aunty take fad'ar sak'on Abba though cikin Mama yayi mugun juyawa but da yake she's wicked haka ta daure a wani iri ta amsawa Aunty maganar tace tana zuwa,Aunty bata tsaya saurarenta ba ta fita,sanda ta gama nuk'u² da jan jikin kafin ta d'auki hijab d'inta ta fita,gabanta yana fad'uwa ta tsaya balcony d'in gidan Dadda tana kallon rututun takalman dake gurin,ba na mutum d'aya ko biyu ba,Abba ya d'ago a fusace zai magana ya hangota kasancewar k'ofar a bud'e yake aka barsa,fuskarsa a d'aure yana mata wani kallo yace "bismillah Hjy kada ki b'ata mana lokaci ke muke jira" Mama ta kalli yanda Abba yake magana fuskarsa babu fara'a ta k'arasa ciki jikinta a d'an sake,ta nemi guri ta rakub'e tana sunkuyar da kai,taron da ta gani ya sa gabanta mummunan fad'uwan da ta fara jin kamar fitsari yana shirin zubo mata..
#Aasiiif habibtiies! Jiya wallahi i was moody ne shisa ban iya yi muku update ba,rubutu kuma yana buk'atar nutsuwa,so a k'ara hak'uri please.
#Asli Smasher.
[3/4, 10:49 PM] My number 1: 47...
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*
Kaf mutanen gidan taga sun hallara parlon sai k'ananu²n yara irin su Asad ne kad'ai babu,amma hatta su Diyanah da Deejah suna zaune,zuciyar Mama bata k'ara bugawa ba sai da ta kallo kusa da Mommella taga Hjy Sahiba k'awarta da Hjy Izzatu,gefensu kuma ga Afiyah zaune tana mata wani murmushi,wani kallo Dadda ta yima Mama tana girgiza k'afafuwa,Mama ta sake juyawa ta kalli Abba da Daddy da suke zaune a parlon,babu wanda ya kalleta a cikin occupants d'in parlon,Abba yasa Amaar ya bud'e musu taro da addu'ah,kafin ya tambayi Hjy Sahiba abunda ya kawo su,kaf alak'arsu da Mama sanda ta zayyano kafin ta d'ora da batun jan Afiyah gurin malaman tsibbu da Mama ta dunga yi,da gurguwan shawararta wanda yayi sanadiyyar gutsirewar igiyoyin auren Afiyah,sanda ta kai aya ta kalli Afiyah tace "kou ba'ayi haka ba daughter?" Afiyah tace "babu abunda ba'a yi ba a ciki" pretend Mama ta fara tana matsar kwalla tace "wallahi sharri suke min,da girmana me zai kaini shiga al'amarin gidan d'ana?" Ganin kukan da take tana rantsuwa ba k'aramin mamakinta Hjy Sahiba tayi ba,ta kalleta tace "ehh! Lallai Hjy Asama'u ban san ba ki da kunya ba sai yau,ke yanzu dan Allah baki ji kunyar cewa na miki k'arya ba?" Mama ta hayayyak'o mata cikin borin kunya tace "ai dama kin san k'aryan kika fad'a,saboda dai d'a na ya saki y'arki shi ne kika yo takakkiya dan ki watsamin nawa auren" Hjy Sahiba ta dunga kallon Mama wani iri tana gyad'a kai tace "idan ni kince na maki k'arya a maganar da nayi,na san dai kaf nan babu wanda bai san alak'arki da Hjy Izzatu ba,babu wanda kuma bai san aminiyarki ce ita ba" Mama ta kalli Hjy Izzatu da sauri gabanta yana fad'uwa tace "ke dai kawai kice kin d'aukota sojan haya,kin biyata ta fad'i abunda ba'ayi ba" Hjy Sahiba tayi wani murmushi tace "tou alhamdulillah! Tunda kin san ma zan iya d'aukanta sojan haya,amma ba'a kan abunda kike tunani ba sai akan ta zo ta fad'i gaskiyar abunda ya faru" babu wanda ya sa musu baki cikin maganar,sanda Hjy Izzatu ta tona asirin abunda suka dunga yi har dai daga baya sanda Afiyah da Mama suka koma tafiya su kad'ai suka manta da ita a gefe,kallon Mama occupants d'in parlon suka dunga yi suna jira suji ta k'aryata maganar da Hjy Izzatu tayi,but sai kame² take ta kasa magana,Abba ya mata wani kallo yace "Hjy kina da abun cewa ko ba ki da shi?" Mama tace "ina da shi mana" yace "ke muke sauraro" Mama ta fashe da wani kuka tace "wallahi Allah Alh duk abunda suka fad'a na yarda,na san na yi amma kaima shaida ne akan ba haka hali na yake ba" Abba dai ya yi shiru kallonta kawai yake,Dadda tayi zaraf tace "iiiihhh! Wane kuma magane haka? Yo Allah na tuba halinki kuma wanne ne b'oyayye a gurinmu? Ai kaf da kika ga munyi shiru,saka miki idanu kawai muka yi,amma babu halinki da bamu sani ba,sai dai mu bawa wani labarinki" Mama taji wani gumi yana yanko mata,sanda Dadda ta maimaita mata maganar da Waleed ya tab'a mata lokacin akan auren Manar tace idan bai bar maganar ba za ta masa baki,da abunda ya faru a gidan Waleed d'in har ya janyo b'arewar cikin jikinta,gaba d'aya kukan da take ya tsaya cak,Dadda ta maka mata wani kallo tace "tou kuma mutumin da ya aikata wannan laifin ne za'a zo ana bamu labarinsa,ko dan kinga mun maki shiru?" Da sauri Mama ta rarrafa wajen k'afar Dadda za ta rik'eta,Dadda tayi saurin kwashe k'afafuwanta daga k'asan tana nunata da yatsa tace "kul! Wallahi kar ki fara tab'an k'afafuwa,ina zaman zamana lafiya k'alau baza kisa na shiga uku ba,haka kawai mata ki gama yawon bin bokayenki da sab'onki ban san kin yi ba kija fushin ubangiji ya sauka a kaina,ina tafiyata ras a dalilin tab'a ni kisa na gurgunce" Mama tayi turus ta kasa motsi,Daddy ya kalli su Hjy Sahiba yace "za ku iya tafiya mun gode" ba don sun so ba suka musu sallama suka fita cike da jin dad'i,dan ko tantama ba sa yi auren Mama ya k'are daga yau,suna fita Abba ya d'ago cikin b'acin rai ya d'auko takarda da biro zai fara rubutu,Daddy yayi saurin karb'e biron yana girgiza masa kai yace "u have to take it easy,bai kamata ace ka yanke wrong decision akan wannan al'amarin nan ba please,ya kamata mubi komai a nutse" wani kallo Abba ya dunga yiwa Daddy yace "mubi komai a nutse kake cewa Muh'd? Anya kasan what am i going through? Ita wannan matar kake so na sauk'ak'awa gurin hukunta ta? Did u really want me to take a look at that wicked woman?" Dadda dai mamakin Daddy yasa ta hangame baki ta kasa magana,can tana kallonsa kamar wanda akayi playing d'inta tace "Muhammadu billahillaziiy ko ka sakar masa takardan nan ya saketa ko kuma wallahi zan ci maka mutunci yanzu" Daddy ya kalli Dadda yace "dan Allah Hjy kiyi hak'uri ku barta haka.." Wani bud'e baki Dadda tayi ta gwalalo idanuwa tana kallon Daddy kamar a tsorace tace "mu barta kuma? Ta mana me idan mun barta?" Daddy ya girgiza kai zai yi magana,Dadda ta kalli Abba tace "Yaro! Maza sallameta tayi gaba,ni dai banga amfanin da zamanta zai mana a gidan nan ba,da can ma bata amfane ra komai ba sai sharri da take binmu d'aya bayan d'aya da shi bare yanzu,muka san me za ta k'ullo mana kuma gaba?" Daddy zai yi magana Dadda ta had'e rai tana nunasa tace "wallahi ahirr d'inka da sake yin magana akan wannan matar,idan ka ga na kyale Yaro ya barta ta zauna a gidan nan kafura uwata ta haife ni" Abba ya karb'e biro a hannun Daddy ya gama rubutun da zaiyi ya mik'a mata takardan fuskarsa a d'aure yace "daga yau ba na son ki k'ara kwana a gidan nan,na sake ki saki biyu,idan kin had'a da na baya uku kenan,Allah ba mu alkhairi,y'ay'a ne dai da suke tsakaninmu bazan hana ki zuwa ki gansu ba,but ban amince su je inda kike ba.." Kallon hannun Abba Mama ta dunga yi idanuwanta kamar za su fad'o k'asa,zuciyarta tana bugawa da k'arfi dan tsoro,can ta daure ta karb'i takardan da sauri tana kallon content d'in da ya zana,bata san sanda wani irin kuka ya kwace mata ba,tana kallon Daddy hankalinta a tashe ta nufesa tace "shi kenan ya cike sauran sakin,dama igiyoyi biyu suka rage tsakaninmu,dan Allah ka basa hak'uri,kasa baki ya janye ko d'aya ne,wallahi na yarda zan gyara duk kuskuren da nayi a baya" shi dai Daddy bai ce komai ba sai kallon Mama yake,Dadda tayi mitsi² da idanuwa tana kallon Daddy jira kawai take taji ya yi magana ta tsigalesa,Daddy ya rasa me zai ce kawai ya mik'e ya fita daga parlon,Mama ta k'ara fashewa da kuka ta zauna dirshen a k'asa tana kallon yaranta da suke kuka tana fad'in "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,na shiga uku,yanzu shi kenan mun rabu?" Dadda ta kalleta ta had'e rai tace "ni dai ki tashi kiyi tafiyarki inda kika fito,tsakanina dake da muguntar da kika dunga yi mana,da alkaba'in da kika dunga jifanmu da shi sai nace Allah ya isa ban yafe ba,Allah kuma yayi mana tsari da masu irin halinku duniya da lahira,Allah ya saka ma jikana da ya fito ta tsatsonki,ko da yake dai bai d'auko halinki ba ko d'is ni dai na godema Allah ko iya haka ma,kuma tunda yana da mu bazai maraicin rashin ki ba,cutar da kika masa in sha Allahu sai kin gansa a kanki.. Manar kuma tsakaninki da ita,sai dai Allah ya isar mata,dan baza mu yafe miki ba,ni dai ba don wannan mutumi mai baud'ad'd'en halin bama da wallahi kotu ce za ta rabani dake,to ya yi uwa yai makarb'iya ya ce a barki haka nan,wannan dai naji na hak'ura" kuka sosai Mama take yi ta kasa kallon occupants d'in parlon,Waleed kuwa dama tunda Hjy Sahiba ta fara fad'an maganganu akan Mama ya sunkuyar da kai yake hawaye Manar sai kallonsa take sympathetically ta kasa kwakwkwaran motsi,Dadda tayi wani kabbara tana kallon Mama tace "tou Allah na tuba,a zamanin nan mutum ya rik'e Allah ma ya ya k'are bare ya rik'e waninsa? Kaita tafka shirka ba ji ba gani,bare tsoron mutuwa ya riskeka.." A hankali Mother ta mik'e jikinta a sanyaye tabi bayan Daddy,zuciyarta ba k'aramin girgiza yayi ba da maganganun da taji,Mama ta had'a kai da guiwa tana kuka sosai tana maimaita "a yafe mata.." Babu wanda ya tausaya mata halin da ta shiga,ta mik'e ta fita still wiping her tears,kaf cikin yaranta babu wanda yafi ba su tausayi kamar Waleed,shi kad'ai ne bai d'auko mugayen halinta ba,but ko ba komai dai ita tayi silar zuwansa duniya,komai zai faru kuma ba'a tab'a canjawa tuwo suna. Sanda Mama ta fita direct part d'in Mother ta shiga jikinta a sanyaye,tun shigowar Mother daurewa kawai take ba ta son zubar da hawaye,k'arshe kasawa tayi dole ta fashe da kuka tana fad'in "me na tsarewa Hjy Asama'u haka,me y'ata tayi mata da k'iyayyarta zai koma kanta?" Daddy dai sai lallashinta yake ji yake inama yana da halin mayar da komai baya,tabbas da bai bari haka ya faru ba,shigowar Mama tana kuka yasa su yin shiru Mother tayi saurin goge idanunta ta tashi za ta wuce d'aki Daddy ya rik'o hannunta,duk k'ok'arin da tayi na ganin ta kwace bai saketa ba,dole sai da ta koma ta zauna ta sunkuyar da kanta dan ta hana kanta kuka,kallo d'aya Daddy ya yiwa Mama ya d'auke kai,dan baima san me zaice mata ba,Mama ta durk'usa gefe hawaye yana sauka fuskarta cikin rawar murya tace "dan girman Allah da manzonsa,ka ceci rayuwata,wallahi ban san ina zan nufa ba yanzu da yace na fitar masa daga gida,ku shaida ne akan ba ni da inda zanje naji dad'i wanda ya wuce gidan nan,y'ay'ana da komai nawa suna gidan nan,wallahi duk abubuwan da suka faru na yarda na aikata,amma sharrin shaid'an ne da rud'in duniya,ko a kotu ka amsa laifinka ana sassauta maka bare nan,ku yafe min ba dan halina ba sai domin Allah.." Wani kallo Mother ta dunga mata a zafafe tace "kin san da haka me yasa tun farko baki fasa cutar damu ba? Yanzu da kin kashemin yarinya sai kice tsautsayi ne?" Daddy dai kallon mother kawai yake,ganin ya yi shiru ya k'i cewa komai cikin rawar murya Mama tace "dan Allah ku tausayamin ba dan halina ba sai dan darajan y'ay'an da na haifa dan Allah ku yafe min" sai lokacin Daddy ya d'ago ya kalli inda take,sai dai ya k'asa magana,mother dai ganin za su iya yin b'atacciya tayi sauri ta mik'e ta bar gurin,Daddy ya kalleta kawai ya mik'e yabi bayanta zuwa bedroom,Mama tana ganin haka ta k'ara fashewa da kuka dan ta san da wahala su iya yafe mata,can ta mik'e tana waiwayen k'ofar d'akin ta fita daga gidan tana share hawaye. Almost 30 minutes da fitar Mama daga part d'in,Daddy ya fita part d'in ya wuce part d'in Abba,a hankali ya shiga ya zauna yana kallon Abba da yayi shiru idanuwansa a kulle,after few seconds cikin sanyin jiki yace "i'm very sorry about what happened brother,but no one is above mistake,kuskure ne ya riga ya faru,sai dai ko saboda darajan yaranku,ya kamata ka duba abunda zai iya faruwa,i'm really not happy about this gaskiya,ni dai bana goyon bayan ka rabu da matarka,ko ba komai ya kamata taci albarkacin 'ya'yanta,kuyi hak'uri ku barta tayi zaman y'ayanta,we all know sharrin shaid'an ne,babu wanda yafi k'arfin shaid'an ya rud'esa sai wanda Allah ya tsare,ni da iyalina mun yafe mata,na tabbatar basu rik'eta ba,dan Allah ina rok'on ku yafe mata kuma,Allah ya shirye mu gaba d'aya ya raba mu da bin son zuciya da mummunan k'arshe.." Abba ya d'ago ya kalli d'an uwansa cike da k'arfin hali yace "batun aure tsakaninmu ya k'are,igiya biyu da suka yi saura yau na cikasa mata su,babu wani sauran alak'a tsakanin mu kuma,saboda haka ta bar gidana ba na marmari ko son k'ara ganinta.." Shiru Daddy yayi yana kallonsa,jiki a sanyaye ya masa sallama then ya tashi ya fita. Bayan sallar isha'a Mama tana d'aki,har lokacin kuka take tana kallon d'akin ta kasa tafiya,Deejah da Diyanah suna zaune sai kuka suke suna kallon Mama,can dai Mama ta daure tana kallonsu hawaye suna sauka fuskarta tace "i