Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   9 / 54

24K to 27K   out of 159.5K words

hoda ta kara janye fuskarki, kin zagaye lebe ya zama dan dagwas, da a duhu zaki zo mini shikenan kin ribace ni?
Duba ki ki ganni, fatar jikinki ta fara janyewa irin alamun shekaru sun tarun nan aman dai har yanzu wannan bata isheki ba?
Ya fada yana mai nuna .....dinsa,
Manyan idannuwansa ya daga sama kafin ya maido kanta ya ce" da yarintata yanzu ni hariki ta yiwa wulakanci na kale tsohuwa tas har ina shirin mika mata abuna ta yi wasa!
Gaskiya baki yiwa bariki adalci ba,
Ki saka kayanki kin ji? Ba zan iya rike wannan takalman ba,
Ya fada yana mai nuna kirjinta,

Gaba dayanta ji ta yi ta muzanta, so take a hakanma ta kara jan ramayinsa, sai dai ina, ba wani hayanniya ya yi mata ba, aman tana tsoron ta ga hayanniyar tasa,
Dan haka ta mike jikinta na dan rawa ta saka bras dinta, ta nufi wajen kayanta tana faman du ta maida , ta tsinci muryarsa ya ce" menene kika zuba cikin kofin maltina na?

Gaba daya jikinta ya dauki rawa, inda ta juyo a firgice, gabanta ya yanke ya fadi, gaba daya ta rasa bakalin kwarewa a barikin da ta yi, gaba daya ya wani hautsina mata lisafi ita dake dakon wannan ranar bisa biyanta da aka yi kan ta cin masa, sai gashi kamar da wasa gawo na son juyewa da mujiya, yana son karfi da yaji sai ya ladaftar da haukanta a nitse,

Inda inda ta fara, kafi ta sakar masa murmushi ta nufi wajen kofin ta dauka ta ce" oga, abin karin karfi ne na zuba maka dan mu ji dadin rayuwa, tunda ka fasa shikennan,

Murmushi ya yi yana shafa gemun gayun da ya ajiye yana dubanta a takaice ya ce" to shanye,

Me? Ta fada tare da zaro ido a lokaci daya kuma ta saki kofin gaba daya maltinar ta zube kasa,

Da ido ya bi farin tiles din dakin nasa da kumfar Maltina ke ta yi kafin ta farfashe sai ruwan maltinar, a hankali ruwan ya dan gangara hakan ya sa ake gannin color din maltinar daga maroon mai duhu ya dawo wani jajaja ,

Kallonsa ya kai kanta, ya girgiza kai, ya ce" dauko abin gogewa a wancen wajen,

Wajen da ya nuna mata ta je da sauri ta dauko abin gogewar,
Karba ya yi a hannunsa kafin ya duka da wani dan kofi ya dibi kadan, sai kuma yace goge,

A tsorace ta goge tana hankalce da na hannun nasa,

A hankali, cikin sanyin murya ya ce" ki goge da kyau, bana son kazamta ni, ki kwontar da hankalinki, ji ba zan iya kisan kai ba, wannan laifin bana so na tafka shi gaskiya,
Ke yanzu dan rashin imani kashe ni ne kika zo yi, da maganin da ake zubawa bera? Ina laifin ki kasheni da abu mai tsada tunfa dai kin ga mai tsada ne ni, kuma fisabililahi dan rashin tausayi mutuwarma a gabanki kike so na yi? Wannan fuskar taki mai shige da ta dan iskan bunsuru kike so ina kallo har raina ya fita? Ina wa laifin ki turo yar yarinya wace komai ya ji, na more idan na gama sai in mutu ina kallon jan lebe da gira mai kyakyawan gashi? Aman kuri da ido ya na yan shaina kike so ina kallonki har na daina motsi? To ta Allah ba taki ba, tashi ga kudinki ki tafi kin ji? Ki canza sa.a tun kafin ki karasa zama karyar yan bariki.

Ita kam zuwa wannan lokaci lamarinsa ya girmami tunaninta, da sauri ta gama gogewa da hannunta , sannan ta dauki takardar da ya ajiye mata na kudin da zata dauka, jikinta na bari sannan sanyi kalau ta fice daga gidan wannan bawan Allah mai cike da abin mamaki, tabas da wuya a cin masa, ya kasance wani irin mutun mai wasu halaya masu wuyar fasara, ingarma ne, tsayaye ne mai sanyin magana, hutu ya saka shi abin tashin hankalima shi a shanshakai yake dubansa, ashe du haukan da take ya ganta?

Wayar da aka kirata da ita dan bata kwongilar kashe shi ce ta shiga kara,
Sai da gabanta ya fadi a lokacin da ta ga kiran,
Sun bata rabin kudin aikin zasu cika mata rabi idan ta gama, da sharadin ta kuka da kanta idan sunnansu ya fito ko ta kasa cika aikinta,

Jikinta na rawa ta wurga wayar cikin kwondon shara ta canza hanya tana yi tana dudubawa kar a cin mata..... wannan kennan

Ya jima tsaye jikin window din dakinsa na baci,
Tsakar gidan kawai ya tsurawa ido yana hangen mai baiwa fulawowin gidan ruwa da kuma daidaita su,
A ransa yake ayyana shi kam wannan hankalinsa kwonce, ba zai kwonta da tunanin kudi ya kuma tashi da tsoron fita ba, bashi da wata damuwar da ta fi ya samu yan na kashewarsa ya kashe ya baiwa matarsa , burinsa na gaba daya tsayin rayuwarsa basu fi adadin sadakar da yake badawa ba,
Gashi saboda *Kudi* yana haduwa da abubuwan rayuwa kala kala,
Menene na gagawar? Dan adam, menene na zakuwar?
Ya aka yi baya iya hadiye zalamarsa?
Mutuwa ai mai zuwa ce, idan ka yi hakuri zan mutu....koda kai baka ci ba sai ka yi iya yinka iyalinka su ci ko? Tunda ka rantse sai ka ci haram,
Idan ka yi hakuri, shekara talatin ai an raraka, me ya yi saura? Idan na jima na kara saba.in a kai...
Wani murmushi ne ya saki kafi ya shafa kolon dake kansa tal tal ba digon gashi a sama ya yi baya baya ya fada saman bed dinsa ya lalubo wayarsa ya shiga duba hotunna a Instagram, ua ga wace ta masa, ya tura mata adireshinsa kawai, koda ba yar kasar bace ta biyo jirgi, dan kuwa ba zai iya rintsa idannuwansa mararsa da wannan nauyin ba, shi kuwa ba zayana didikar mqgani ba har ya je ya bata mararsa! ......(ALLAH YA SHIRYE MU)



Da wani irin gudun da ta jima bata???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yi ba, gudun ceton rai ta bar wajen,
Tana zuwa kofar dakin Madame Bilkiss ta ja ta tsaya tana maifa ajiyar zuciya,

Kyam ta yi tana duban waje guda, gaba daya du wani huja dake tatare da ita ne take hadawa kafin ta bi Joli da kallo har ta shigewa ganninta

Ajiyar zuciya ta sauke , ta ci gaba da aikinta kafin lokacin da ya dace ta kwonta ya buga, sai dai ina , bata tunanin zata iya rintsawa a wannan lamarin!


Washe gari bayan Madame bilkiss ta shiga office dinta ta gama caje komai ta fito ta nufi bakar motar dake jiranta,

Tana shiga bata yi magana ba sai takarda daya da ta mika masa,

Ya jima yana duba takardar sannan ya dago da wanni yannayi ya ce" menene hujarki ta fadin wannan gagarumin abin? Kin san da idan har ba haka bane, hakan na nufi da ja da kungiyar lauyoyin garinnnan? Da masu kare mutuncin su, da dukan wani mai nuna tausayinsa kansu? Kin san da bamu da karfin ja da su a haka?

Kai tsaye ta ce" huja kake so? Bani da ita GN, bani da hujar da zan daki kirji na nunota a fili, sai dai ina so ka taimaka kamar yanda na roka, wannan number, itace ta karamar wayar da na samu a dakinsa boye cikin karamin wandonsa,
A saka a cire layi daga cikin layin layikan da ba za.a iya jin hirarsu ba, sannan a saurari abinda suke fada,
Zuciyata ta bani amanar hakan, na yarda da hakan, kuma in sha Allah gaskiyar lamari na cikin nan,

Number dake saman takarda rubuce ya bi da kallo, kafin ya bi bayanta da kallo har ta bacewa ganninsa, ta koma bakin aikinta,

Jujuya takardar yake a hannunsa, cikin zuciyarsa ya kasa yarda da irin girman abin da ta kawo,
Sai dai me, ba zai yar ba, zai saka a bi a boye , idan har hakan ne shikenan, duniya ai ba abinda bata gada ba.

Bayan kamar kwana biyu,
A lokacin , a lokacin har an gama shari.ar an yanke hukunci daidai laifi,
Suna zaune a fallo suna shirin cin abincin da Joli ta girka da kanta, sai zumudi uwar take cikin murnar jolinta ta fara shiga kicin da kyau,

Har an zuba abincin za.a fara ci , Hafsat dake tsaye tana kallonsu Joli ta duba ta ce" wai Mam, ba kun gama shara.ar ba, me kuma wannan abin ke yi tare da ke gar yanzu?

Uwar ta kai dubanta wajen Hafsat, ta ga tsaye kawai take, yau ba gilas din, aman duda haka wani sirri ke tatare da yarinyar, wanda tana so ta san menene shi, tana son sannin wacece yarinyar da du abin shagalta baya dadata da kasa, menene duhun da ya mamaye mata ranta bayan gata yar yarinya, yar karamar attajira , domin a wannan aikin kadai da ta yi ta tara kudi na mamaki, idan aka cire percentage din ma.aikata wanda zai zama nata ba kadan bane, ko tunanin wannan baya sakata irin ka ganta tana ta murna,

A hankali hafsat ta matso sosai kusa da Madame bilki dake son kai abincin nan bakinta ta ce" ashe shi mai bincike, idan ya tashi idonsa na kasa gannin amsar da yake nema a gaban idonsa?

Dago da kanta ta yi tana duban Hafsat, ta sani ne, farin sannin cewa, bata maganar da bata da ma.ana ko wace bata shafi aikinta ba, tunda suka hadu, kusan wata hudu kennan, bata taba koda wasa shiga hurumin abinda bai shafeta ba, du irin cin kashin da joli ke mata kuwa bata taba koda nuna ta san da ita a wajen ba, aikinta ta zo yi, tana kamanta yinsa da dukan gaskiyarta, dan haka maganar da ta fada ya saka madame Bilkiss cikin dan gajeran tunani,

Kasa gane komai ta yi, ta kuma dauka da niyar kara kai abincin bakinta,

Da sauri ta ce" idan kika ci abincin nan, zaki tashi normal ki je dakinki, harma zaki yi wankan minti goma, shafa.i da wuturin minti goma sha biyar , shirin bacin minti biyar, ki kwonta ki fara baci, cikin bacin da bai fi na minti ashirin ba zaki ji gaba daya an hade hanjin cikinki,
Zaki farka da sauri domin takurewar ba ta wasa bace, zaki nemi mikewa ki sha ruwa,
A lokacin da kika sha ruwa, dan lokacin karasawarsa cikin cikinki wajen wannan shinkafa da kika hadiya zai dauki second biyar *kacal*, daga bakin wannan lokacin numfashinki zai nemi gagararki, a hankali a hankali zaki fara fitar da wata kumfa mai kalar shudiya, a haka zaki ringa kaiwa kasa har ki zube kina ihun kiran Bodyguard, aman muryarki bata fita dan ya ci karfinta, cikin haka zaki tafi ta hanyar birkidodoniyar da zata goge kumfar da kika zubar da kashin da za.a dauka du na zafin fitar rai ne, a haka zan shigo na tarar da gawarki, wanda zata nuna min maganin hawan jinin da likita ya rubuta maki a kasar faranc me kika sha mai yawan da ya hadasa maki haka har kika rasa ranki a lokacin da ni sauna nake kofa tsaye dan zama mai kare lafiyarki..........


Gaba daya wajen, su su uku ne dama, domin Boy bai fito ba tukunnan yana daki, wajen gaba daya tsit ya yi kafin cikin matsanancin faduwar gaba madame bilkissu ta saki cokalin tana dubanta ta mike tsaye ta ce" ke, me kike nufi haka? Me menene wannan din kuma?

Hafsat ta yi murmushin da har cikin ranta yannayin da ta nuna ya bata dariya, bata son mutuwa wai ita wannan? Ikon Allah, yanzu ita bata so ta mutu, so take ta yi ta rayuwa cikin jin dadin nan har yaushe? Har a busa kaho ko me?

Murmushi ta kuma yi ta ce" aa, bafa mutuwar bace Madame,
Wai yanda aka tsara lamarin karshenki ne na baki a takaice,

Wata irin tsawa ce ta daki kunnayensu daka wajen matatakala, ashe Boy ya sauko yana sauraro,
Jikinsa na rawa ya karaso yana dubanta ya ce" kashe mini uwa zaki yi? Wannan wani irin banzan zance ne? Tunda kika zo gidannan dai abincin oder ake ci dan kin kori yan aiki na odernma ke ke kawowa dan baki yarda da kowa ba, idan kika fadi haka, wannanma na yau ke kika kawo shi, kennan kece zaki kashe min uwa ko me?

A nitse ta ce" aa dan jaririn mamansa, ba.a kai ga wanda na kawo din ba kennan,

Ni ne jaririn? Ni ne jaririn? Ya fada da hargowa yana dubanta yana matsowa da niyar kai mata duka

Da sauri madame bilkissu ta tare shi ta riko hannunsa ta maido shi kusa da ita tana duban yannayin Hafsat ta ce" ki bani haske kan maganarki , a kan aikinki kike kar ki manta,

Hafsat dake sauraron maganar su BS da suka karaso da police ta kai dubanta wajen Joli dake tsaye itama gaba dayanta, du wani alama na rashin gaskiya ya bayana a tatare da ita ta ce" bomb da aka saka a motarki, ta sayeta ne da makudan kudin da kike sakar masu a acct, ta hanyar kawarta dake da yaya dan fashin boye, wanda yake harkar miyagun makamai a boye ,
Bata cinma burinta ba na kashe ki ta hanyar bomb, ta siyi dan sholisho kan ya soka maki wuka, wanda mun fito daga alimentation ya shigo mu da gudu da wuka na karbe, wannan ma bai mata ba, ta so ta buga zuciyarki ta hanyar kiranki tsakiyar dare ta fasa maki kuka dan ta san kinada mugun hawan jinnnin da tabas damuwarta na iya tada maki ita.......
Wannanma ba.a samu galaba ba, shi ne aka gwada ta jus jus, shima du na canza su, yau aka gwada ta hanyar yin Fride rice, abincin da kika fi so,

Wai wai wa kike nufi? Ya zaki ringa magana kina duban Joli? Me kike nufi?

Karan laluwar da ya karade anguwar harma dake nuni da cikin gidan yake nufowa ya saka Joli sakin marfin glass na kwannon cin abinci ta juya da gudu ta nufi waje da niyar neman inda ta tsere,
Wata irin juwa ce ke neman kayar da ita, nan da nan boy ya tareta a jikinsa, jikinsa na rawa da mamakin wai da da gaske da take cewa zai zama nata niyarta ta kashe matar da ta dauketa ta mayar da ita mutun?

Magani ta balo wanda dama ta san a rina ta mika masa ya saka mata a baki , aka bata ruwa sannan aka jinginar da ita inda gidan ya rikice da hayaniyar kama Joli,

Idannuwanta da sukai mata nauyi ta daga ta dubi boy, muryarta na rawa ta ce" Boy, kace min karya ne ka ji? Kace min ba haka bane, me me ya sa ? Me yayi zafi Boy? Ashe dama makashina na tare da ni? Me na yi da zafi haka boy?

Boy ya sada kansa yana kuka kamar yaro gannin yanda mam dinsu abu ke cinta har zuciyarta,

Wani abu Hafsat ta ji a ranta, tausayin matar, tabas ita fa a matsayin yayanta na cikinta ta dauke su, idan kuwa har haka ne dole ta ji mugun mikin da zai yi barazana wa numfashinta,
A hankali ta matso kusa da ita ta tsaya ta ce" ke fa lauya ce hajia, kin yi shara.ar da ta fi haka gigita, dan yau ya zo a kanki idan har kika yi hakuri zaki bada exampl wa duniya,
Ke kika bani kalmar dan adam mugun ice ne,
Ni kuwa zan kara maki kalmar Allah na jarabtar bawa da abubuwa da yawa, ciki kuwa harda raba bawa da abu mafi soyuwa a ransa, yaya ne, iyaye ne, kudi ne, mata ce, ko miji ne...da dai sauran su,
Da ciwo, aman kar hakan ya zama sanadiyar rugugewar tsayayiyar lauya mai kare yancin matan garina=?O?
Kallonta kawai suke gaba dayansu, har BS ya shigo falon,
Nan ta mike ta sara masa tana dubansa har ya bata izinin tana iya sauke hannunta,

Likitan da aka zo da shi ne ya karaso aka kama Madame bilikiss aka dora gado na turawa aka fita da ita,.a takaice dai kafin su bar gidan sai da suka daidaita komai, suka kwashe komai na dakin joli dan karin bincike suka bar gidan tare da Hafsat

Sai da ta yi wanka ta mike saman gadon dakinta da aka maida su masu gadaje ta lumshe idannuwanta,
Maganar BS ke dawo mata, ashe zasu shirya da shi? Lale duniya, .........




Ummih, bafa zan zauna kato na take min baya a dukan motsina ba, haba ummih ba zaki bar maganar nan bane?

Zama ta yi kusa da shi tana dubansa ta ce" kana so na mutu?

Da sauri ya dago da dubansa kanta shima yana dubanta , murmushi ya sakar mata, sak yanda take masa yana yaro idan ya ki yarda abu, tsoron hakan ke saka shi amincewa da koma menene, shine yanzuma zata yi masa,

Hannayenta ya riko yana dubanta , ya ce" idan kin amince da abu daya, zamu je tare da ke, a bani na zaba, aman fa mace, a bisa sharadin zamu baro wajen da sunnan matata take, dan kin ga zata zame min karfen kafa, du inda na shiga zata ce sai ta shige itama, zamu ringa kwana gida guda.......
Ni ban ce zan yi wani rayuwar aure da gardi irina ba, dan kuwa du macen da ta san ciwon kanta ba zata dauki kafa wai ita ta je ta yi gudu ta shiga duniyar mazajen daga tace itama yar dagan ce na iya kallonta ba, aman saboda irin rayuwar da ake a nan, da irin yanda aka cakulu ake cakuda abubuwa, ga auren nan da kika saka a yi na yarinyar nan, kin ga zan so ta bata tsaron, aman wai ba ni ba, aman kuma a matsayin wace zata fito a Bodyguard kuma matata




*Wannan cakwakiyar fa? Mai yiwuwa ce? Yan matan Bodyguard, damar au yi auren ana nufin irin wannan ko me? Idan irin wannan ne daman ana iya aure haka? Aure dai ai aure ne, ana iya rayuwar aure da su normal ko yaya? Irin matarka ce idan ta raya maka matarka ce?..............mu je zuwa karatun Kutkale*


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA

9 / 54