Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   37 / 54

108K to 111K   out of 159.5K words

ya zo sannan suka sake shi bayan ya bada umarni

A hankali suke takawa GN da shi, cikin yannayin mamaki GN ya ce" yaya aka yi ka kawo kanka wajen nan?

Abdul ya kale shi ya ce" a ranar da aka maida mu tare da mahaifiyata, tun a ranar na saka maku abinda zai nunan inda kuke dan tsaro,
A ranar na san inda kuke ba.a dai yi falilin da zan zo bane sai yanzu

GN ya jinjina kai yana kallonsa, wato dai shi bai yarda da kowa ba?

Abdul ya ce" waye BS? A ina iyayensa? Ta yaya ya zo base? Menene halayensa?

GN gabansa ne ya ji ya fadi yana kallon Abdul,
Tsoro ne ya ji ya kama shi kar a je BS ya janyowa kansa wani balakin?

Abdul ya juya ya fuskanci GN da kyau , ya yi masa wani kallon dake nufin shi yake sauraro

GN ya sauke ajiyar zuciya ya ce" BS, bazabarme ne, domin ni ne mahaifinsa, mun same shi ne da mahaifiyarsa a lokacin muna soyaya, Allah bai yi zan aureta ba aka aura min wata

Abdul ya kafe shi da ido cike da mamakin wai ashe BS dansa ne? Aman yaya aka yi bai amsa sunnansa ba? Duda ya ji ya ce ba da aure ya same shi ba,
Kansa ya girgiza ya furzar da wata iska daga bakinsa, shi kam bai san me ke damun mutane ba, ya sani akoy kadara aman wai har wata kunya yake ji a yanzu ko me?

Tsaki ya ja a fili ya ce" yaya aka yi ya ci jarabawar zuwa wajen nan, harma ya zama Bodyguard soldier? Shin takardubsa suka bashi dama ko babansa?

GN ya kali Abdul ido cikin ido, sam bai ga tsoro ko alamun zai risina masa ko dan ya girme shi, dan haka gwara ya fito a mutun ya bashi du wasu informations kan questions dinsa, fatansa dai ba wani laifi ya yi ba

Bakinsa ya buda ya zayanewa Abdul du wata tambaya tasa a nan a inda suke tsaye dan GN ya so su karasa su zauna abdul ya ce sauri yake

Sai da ya gama Abdul ya gyada kansa ya ce" masha Allah

GN ya ce" aman, sire wani laifi ya aikata ne?

Abdul ya kale shi, sai da ya gama nazartarsa sannan ya daga kafadunsa duka biyu ya ce" bai aikata ba tukunnan, ka bashi sako yarinyar da yake neman aurenta idan har da agske yake mahaifinta ya ce ya fito a cikin satin nan a yi komai a gama, idan kuma ba da gaske yake ba, abinda nake so da shi shine ya janye a hankali, ba tare da ta zubar da hawaye dalilin hakan ba, dan na tabata zata samu wani idan shi baya yi

Yana gama fada ya mikawa GN hannu suka gaisa sannan ya sakar masa fuska suka yi salama tare da mutunta junna suka rabu

Abdul bai koma gidansa ba masalaci ya je, yana zuwa ya tarar da Malan zaune da jama.a ana ta karatu dan haka ya gaishe su kawai ya juya ya koma gidansa

Da dare bayan salar isha.i suka shigo da malan, sai da suka zauna Abdul ya fadawa malan cewa ya je, ya binciko, in sha Allah ya fadawa mahaifin yaron idan har sun tashi auren da gaske to su fito

Malan kam godiya ya ringa yiwa Abdul, wace har sai da ya gaji da amsawa

Sun jima zaune suna hira jefi jefi, sai malan ya ji Abdul ya ce" wani abu ya faru da ita ne?

Malan ya kale shi, sam bai gane wa yake nufi ba, aman gannin ya yi jim ya saka shi cewa" wa fa?


Abdul ya dago yana kallon malan, shi fa gaskiya ba zai cewa Hafsat wai mama ba, shi kuma ba zai kama sunnanta kiri kiri gaban malan har a je ya daina gannin mutuncinsa ba, dan haka sai ya ce" ita wace za.a yiwa auren

Malan ya kada kansa yana murmushi ya ce" Abdallah, bana son yaro ya ringa yi min dogon zance a gida, ai kawai idan yi yake ya fito a yi a gama, idan kuwa ba shi ne rabon ba sai ya bada waje ko zata sami wani ya aureta itama ta je ta raya sunnar ma.aiki

Abdul ya gyada kai sannan ya kawar da dubansa, wani haushi ne ya ji yana ji, wai ko ta samu mai aurenta, Hafsat din rasa mai sonta zata yi ne? Yarinyar mai daraja mai hankali mai ilimi mai kyau? Me ta rasa a jikinta na mace har da malan ke son saka gagawa a lamarinta?

Yau bai cika dare ba ya yiwa malan salama,

Yana saukowa ya hadu fa ita tana shanya saman igiya, ita daya ce kwal a tsakar gidan da yake lokacin kamar da sanyi sanyi kowa yana daki ya labe, itama wankin kayanta irin dogon wando ne ya sakata yi da dare sannan ta kwashe da wuri dan basa barin kananun kayansu na shawagi a tsakar gidan, wannan mahaifiyarta ce ta yi mata wannan horon

Tsayawa ya yi ya harde hannayensa duka biyu yana kallon yanda take dukawa ta matse kayan sannan ta mike ta shanya saman igiya, har dira take dan ta gyara shanyar da kyau

Idannuwansa ya lumshe a hankali ya furta" ANGEL

Hafsat dake shanyarta bata ma san yana wajen ba, sai da ya ga hakan ba gyara shi zata yi ba da sauri ya matso inda take ya tsaya a gabanta tana shanya kayan tana juyowa suka kusan hada kirji

Da sauri ta ja baya tana kallon sa

Murmushi ya sakar mata a hankali ya ce" wanki kike ne? Ina mai wankin ki?

Kin bashi amsa ta yi , saima juyawa da ta yi ta dauko wata shanyar zata shanya

Kara matsawa kusa da ita ya yi ya ce " wai fushi ake da ni ne?

Hafsat ta tsaya da shanyar tana kallonsa,
Abdul ya saki murmushi ya ce" yi min murmushi kin ji?

Hafsat ta zabga masa harara tana kallonsa sannan ta shanya kayanta

Zuwa ta yi ta dauki bokicin karfen ta zubar da dan sauran ruwan cikin bokicin sannan ta juyo da niyar tafiarta

Da sauri ya kama kunnayensa ya ce" na tuba, dan Allah ki min magana ko daya ce Hafsat

Hafsat ta kale shi sama da kasa sannan ta juya ta yi shigewarta cikin dakinta

Ji yayi gaba daya hankalinsa ya tashi, a hankali ya lalubi kofar ya fita ya shiga motarsa ya ja,

Tukin dai kawai yake, aman gaba daya kunnayensa sun rikice, bukatarsu shi ne su ji muryarta, idannuwansa kuwa su ga murmushinta,

Hannun nasa da ya mareta da su ya kara kallo, sai kawai ya kai yatsarsa guda wajen bakinsa da niyar cizawa
Ko me ya tuna, ya fasa ya ci gaba da wani irin tuki har ya karasa gida

Yana shiga gidan wayarsa ya dauka a cikin motar ya shiga kiranta,
Tun yana kirga kiran da yake mata tana reject har ya daina irgawa ya zauna kawai bakin bed dinsa ya cire belt din wandonsa ya bale mabalin rigar ya dan sasauta wandon kasa ya dafe gaban goshinsa da hannunsa yana kara gwada kiranta hankalinsa a kanta gaba daya

Can ta daga, cikin wata irin murya mai cike da kasala da sangarta ta ce" Abdul, ka barni na yi hira da mijina mana, yaya ina waya da shi kana kirana sai titit yake ya kasa jina yanda yake so

Idannuwansa ne ya lumshe, a hankali yake jin maganar na girmama a zuciyarsa, kamar da wasa ya ringa jin maganar tamkar ta zagi mahaifiyarsa , wani irin dacin maganar yake ji,
A kasan ransa ya maimaita" *tana hira da mijinta?*

Zuciyarsa ce ya ji ta wani irin bugawa, a hankali ya ce" ki yi hakuri kin ji? Ki daina fushi da ni Hafsana

Ita kanta yannayin yanda muryarsa ta fito sai da ta ji gabanta ya fadi, a hankali ta janye wayar a kunnenta ta duba shi dai ne,
Mayar da wayar ta yi a kunnenta ta yi shiru tana sauraronsa, sai wata irin ajiyar zuciya take saukewa wace ke sauka da lumfashinta tana dirar masa har kahon zuciyarsa

Ji ya yi idannuwansa sun yi masa wani irin nauyi, a hankali ya ce" ba zan kuma marinki ba, kar ki hora ni da fushin ki Hafsat

Sai da ta ja numfashi kamar wanda ya toshe mata lumfashin nata ta ce" ba dukan da ka yi min ya tsorata ni da kai ba Abdul

Abdul ya yi saurin cewa" menene?

Hafsat ta ce" irin yanda ka nuna rashin damuwarka a halin da zan shiga da kuma mamana bayan na fada maka bana jin dadin hakan,
Abdallah, ka san girman matsayinka a wajena? Kai yayana ne, abokin sirina, aminina, Abokina,
Abdallah ina jinka a raina sosai, ni ba zan yarda na saka ka a damuwa ba, aman kai sai ka saka ni ka yi tafiarka, ka san halin da nake ciki a gidanmu ne?

Ji yake harta gaban jikinsa sun yi masa nauyi, du wani furuci nata sai ya kayar masa da gaba, wai me ya sa ne ta kasance mai karfin ruguza shi, sannan mai karfin saka shi risinawa? Shin me ya sa take da madaukakin iko a kan muradinsa da akasinsa?

A hankali ya buda bakinsa ya ce........




Hapoy sallah yan uwana,

Allah ya karbi ibadun mu, ya maimaita mana


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4?? 9??



A hankali ya kuma iya daga bakinsa ya ce" Hafsat... ..


Wani irin jan sunnan ya yi, ya karasa shi da ajiyar zuciya wanda ya hakan ya saka Hafsat rungume fillow din dake kusa da ita ta lumshe idannuwanta baki daya ta shiga neman saisaita lumfashinta, domin gagarar buda bakinta bale har ta iya amsawa ta yi

A hankali ya ce" bani da uwa, mahaifina yana jin kunyata da ba zai iya kuma rayuwa tare da ni ba,
Na tara dukiyar da ni kaina ban san adadinta ba,
Ina kwana da sannin ni ba kowa bane dare daya mala.ikan mutuwa zai zare raina na zama gawa

Shiru ya yi kafin ya ce" a da na zauna zaman ni sai na ga mace an min asiri, ko wata rana sai na ga wani kalar tsiraicin daban bayan na kwana da sannin mai kallon tsiraici baya tsufa da ido, tun a gidan duniya bare irin girman hukuncin da zan tarar aman haka nake tafe watara na hadu da yarinyar da na haifa da cikina, wata rana na hadu da wace ta haife ni da cikinta aman da yake aikin shedan ne haka zan zauna na bita da kallo har ta gama karanta min karatun nata na zubar da najasar tawa a kasa kusa da abin wankana!
Hafsat, sai da kika zo rayuwata na fara fahimtar eh lale idan da asirima to ni kaina na baiwa abin gaskiya,
Hafsat ke ce ta biyu bayan mahaifiyata da nake jin kunyar ki kama ni ko ki san irin halin da nake ciki daga bakin lokacin da na fahimci kina tare da ni da zuciya daya da niyar gama aikin ki lafia ki yi gaba abinki
Hafsat ba irin kalar iskancin da ban nuna maki ba aman sai ki juya abinki ko idan abin ya yi maki tsauri take kike wanke ni tas bakya raga min harma ki zubar da hawayenki dan takaicina
Ina sane, ina sane da dukan motsin ki,
Hafsat, ba zan iya hadiye abu a kanki ba, ba zan iya kawar da kai a dukan wani wanda zai cutar da ke ba,
Ban san dalili ba, har ji nake lumfashina zai tsaya idan na ji ki a damuwa,
Abin haushinma sai kawai kike son canzawa daga matakin mai kare yancin kanta ki koma wata mau tsoron mutun, ban kai hanuna fuskarki ba sai tukukin haushin kin kirayi kanki da muguwar kalma, Hafsat, koda a ce haka kike ina nufin kalmar nan ke din ita ce ta haramta ga kowani mutun ya fade ta, ina iya soya masa idannuwa dan ubansa!

Wani irin tsam tsam tsam ta ringa ji a gaba daya jikinta, lale ta yarda da maganar nan cewa a duniya ka ji a damu da kai ba karamin jin dadi bane bare ka gani da idannuwanka,

A hankali ta ce" kai mafadaci ne Abdallah

Murmushi ya yi, wanda bai yi shirin yinsa ba, wai Hafsat ce ke cewa wani yana da fada

Sai da ya gama murmushin ya ce" takura maki ake a gidan nan ko? Me suke maki ne? Wa da wa ke maki?

Ta so sakin baki dan fada masa , sai dai a likaci daya kwakwaluwarta ta tina mata wanene shi, da kuma magangannunsa ba cika baki bane yana iya aiwatar da alkawarinsa ko furucinsa,
Dan haka sai kawai ta ce da shi" ba wani abu ni dai ka taya ni da adu.a samun saukin rayuwa

Haka suka yi ta tautaunawa har kusan raba dare, sai da ya ji yannayin saukar numfashinta ya canza, a hankali ya ce" baci ki ka yi?

Shirun da ya ji ne ya saka shi sakin murmushi a fili ya kai dubansa agogo, karfe biyu har da rabi, adu.ar baci ya yi mata wato ta tsari daga wayar da niyar Allah ya kai mata domin suna tsakar hirar bacin ya yi awon gaba da ita ta gaji ainun gashi ya tsareta har wannan lokacin


Da duku duku, da duhu duhu kamar yanda ya saba jiransa har ya karaso yau har tarbo shi ya yi

Tun da ya hango shi ya tabata akoy abinda ke faruwa dan kuwa mahaifinsa nasa na kiyaye a ganshi tare da shi ko dan kar a san a yanda ya same shi ya jaza masa matsala a ma.aikatarsa

Motarsa ya bude ya shiga , kafinma ya gaishe shi sai ya ji ya balbale shi da fada kamar haka" lale lale Bashir kana wasa da wuta! Tun lokacin da ka je yi masa aiki na gargadeka cewa wannan mutumin da kake gani basaja yake dan kar a gane meye asalin aikinsa, na bayana maka ko waye shi mai gidan mai gidanka kuma ubanka ne shi! Aman da yake cikin kwakwaluwarka majina ne cike shine har kake son sako shi a lamarinka? Har ya kasance shi zai yi bincike kan yarinyar da kake so kuma? Yaushe zaka daina zuwa gidajen yan mata kana nuna kana so ? Nawa ka saka har muka je tambaya ka dawo ka fasa? Nan yarinyar nan har ciki kuka zubar kuna soyaya daga baya ka watsar da ita da ka gama samun abinda kake so, shine yanzu tsautsayin tozarci ya kai ka ga afkawa wajen da zaka tonawa kanka asiri ka tona min? Waima yar gidan wa ka je ka saka kanka a ciki da har ya saka shi tasowa da kansa da niyar yin bincike a kanka?


Haushi, takaici hadi da kishin lamarin abdul ne ya turnike BS, haka kuma haushin mahaifinsa ya kama shi, shi ya san du abinda ya saka babansa a taro a taro din nan dan baya so duniya ta san ya haifi dan gaba da fatiya ne, aman ba komai zai nuna masa shi din ya iya iskanci

A dake ya ce" yarinyar nan ce da ka kawo daga prison *KUTKALE* na horata ta zama bodyguard

Da sauri ya kale shi,
Kansa ya girgiza sannan ya ce" lale a mahaukatanma kai baba ne, ka san da shugaban kasar nan ya yi kira cewa a kurce sunnanta a matsayin mai laifi ko mai bashin kasa a kanta? Yarinyar da ta gagari yan ta.adar Kutkale? Yarinyar da ta fito lafia daga kutkale? Ta zo nan ta zama zakararsu? Yarinyar da ta tsare mutuncin kanta take adu.ar Allah ya tsareta?

BS ya ce" wannan abinda take nuna mana kennan! Ni kaina da farko na dauka hakan ne, aman daga bakin lokacin da ta fara yiwa Abdul aiki na gane cewa itama watsatsar ce sai dai bata haraka sai da manya, yarinyar da ta bi Abdul kuma ta kare da abokinsa? Idan ba aikinta ba ta ya ta gane shi ne mai neman rayuwar Abdallah? Idan ba kwaratanta ba ta yaya muka tarda ita a yannayin da muka tarda ita? Ta raina arzikina ne, bata san ba wanda ta gama watsewar da shi ba aurentan zai yi ba! Eh na je gidansu, kuma ina son aurenta dan haka a aura min ita ba ruwan kowa

Ikon Allah kawai yake kallo kafin ya ce" ka sani, ni kaina mai tsayawa shara.a da kai ne idan ka cutar da rayuwar yarinyar nan, bare na tabata ba za.a rasa mai iya wujijiga namanka ba, dan ka sani *yar kamilin datijo yar kuma baban gida ce*, yanzu fice min a motar nan tun kafin ka hadasa min wani ciwo!


Bakinsa ya tabe, sannan ya fice a motar, yana kallo babansa ya shige cikin gidan horon da motarsa sannan ya kara tabe baki a fili ya ce" idanma iskanci ne ai gado na yi, kuma yan mata yanzu na fara haye ruwan cikin du wanda ta dagan buje! Itama wancen tunda na lura ba zan samu dan arzikina ba zan aureta na haye ruwan cikinta na ga meye banbancin sa da na sauran da har ake min iskanci a kansa, dama dama ni na zubar da cikin ban bari ta haifo min

37 / 54