Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   25 / 54

72K to 75K   out of 159.5K words

tarin gajiya, karshe dai ya mike ya kara dangana kansa da darduma dan kara fadawa Allah ya kare mutuniyarsa a samu yar mutane lafia ya shige gaba kan matsalarta na kaso a wanketa tsaf ya mayar da ita wajen iyayenta lafia idan ya so ya daga ya yi tafiarsa shima saudiya tare da amininsa!


A lokacin da ya gama shafa fatiya wayarsa message ya shigo,

Hannunsa ya saka ya shiga message din dan kuwa yanzu baya sake da du wani abinda zai shigo masa dan gudun ya taka kaya ya bar abinda zai kai shi ga Hafsat

Yana dubawa message ne kamar haka" *Ba.a gane mahinmancin abu sai yana nesa da kai, yanda kake ji, haka nake ji ba dare ba rana tun daga bakin lokacin da na shiga jirgi da niyar yiwa yarona daya kwal da matata karyar na mutu, Abdallah damuwa ta hana ka baci ne? Rabona da baci tun lokacin da aka kashe min yarinya,.........BA NI BANE*

Tsaki ya ja ya jefa wayar saman bed dinsa ya mike ya fice a dakin a lokacin karfe hudu ne na dare dan kuwa ko kiran sallar farko ba.a yi ba

Ky din wajen sa ya saka ya buda dakin ya shiga, yana shiga ya zarce inda yake kwonce ya saka hannunsa ya dada masa wani duka mai karfi wanda ya saka shi mikewa tsaye a firgice yana kallon Abdul

Abdul ya kura masa ido kafin ya nuna shi da yatsa ya ce" kai, wace irin rayuwa kake son shiga? Daga ina kake dazu? Ina ka hadu da ita? Ina ka kai ta?


Wani irin faduwar gaba da ta ziyarci zuciyar Muhammad, lokaci guda kafafuwansa suka kwashi rawa , wata irin zufa ta shiga zubo masa a fuskarsa,

Da sauri ya kalli bayan Abdul ya ga shi daya ya shigo a wannan lokacin, gaba dayansa a hargitse, yannayin Abdul ya mugun tsorata shi dan kuwa a lokaci daya abinda ya fado masa a rai shi ne asirinsa ya tonu, lokaci daya ya fara jin wani abu na bi masa kafa kamar wanda fitsari ya kufce masa fan ya sani, ya fi uban kowa sani in dai har asirinsa ya tonu ne walahi sai dai a banbare gawarsa ko yace abinda ya yi saura a gangar jikinsa daga hannunsa,

Hannayensa ya hade yana son yin magana, lokaci daya kuma yake son amayar wa da abdul cewa eh shi ya yi, shima dan ya raba shi da budurwarsa

(Allah kennan, wato shi mugun abu , ita mugunta idan kana aikata ta du dadin da kake ji bai kai fargabarka da tashin hankalinka ba, dan kuwa kai kulun jininka a akaifa yake, baka da nutsuwa a komai! Cin amana? Du mai yi bashi da nutsuwar zuciya, haka kuma ka mace ka je ka tarar da Allah)

Kafin ya yi magana Abdul ya sasauta muryarsa ya ce " Haba, Haba , Haba Muhammad, me ya yi zafi da zaka saka rayuwarka a kazamar rayuwa irin wannan , kar ka manta fa, kai ke min fada kan rayuwar zina, kar ka manta tashin hankalinka ka ganni ina rabawa mata ruwan jikina, ka fi kowa sannin ba shigar mace nake ba aman a wancen din ma adu.arka Allah ya shirye ni, sai yanzu da na shiryu na canza na daina kai zaka afka? A inama ka ga yarinyar da har ka yi kusancin da ya hada hannunka da gashin kanta?

Wata wawuyar ajiyar Zuciya Muhammad ya sauke yana mai matse kafafuwansa tare da neman zama saman bed din dan kar Abdul ya fahinci abinda ya aikata a jikinsa,
Sai da ya zauna sosai sannan ya saka hannun nasa cikin gashin kansa yana shafawa a hankali kafin a ransa ya ayanna' tabas zan yi gagawar kawar da ke a doron kasa kafin sanadiyarki asirina ya tonu, idan na mutu a yanzu yanzu ban ga anfanin rayukan da na yi ta dauka ba, dan kuwa du irin mutuwar da akai masa kala daban daban bai saka shi ya rasa imaninsa ba, haka kuma bai zauce ba! Burina na ga Abdul na sakin magangannun haukacewa, kafin na kai shi gidan mahaukata a ringa tsira masa alurar mahaukata mai karfi tana cinsa a hankali tana azabtar da shi har lumfashinsa ya bar gangar jikinsa, daga nan na tabata na ci galaba a kansa!


Abdul ma ya zauna irin zaman fa ya yi ya ce" mazinaci, mazinaci, bashi da wata daraja da ta rage masa a duniya, karshensa ya mutu babu ido, ba abin hannu, ba iyalin da zasu talafe shi, ba mutunci a idannun kowa, dan kuwa yaro karamima zai taka shi ya fice idan bai tuba ba wa Allah ba.......wannan shi ne nasiharka gare ni

Muhammad ya gala masa harara ya ce" yanzu saboda wannan abin ne ka biyo bayana kai jarababe da tsakiyar daren nan Abdul kake kokarin sakawa jinina ya hau? Ni ba tsoro na ji ba kar a je mugayen anamiman masu biyar bayan naka ne suka kuma kawo mana farmaki da tsakar dare haka? Gaba daya ka saka na firgice na fita a hayacina bayan ni na sayi abin gashin dan ya birge ni?

Sai a lokacin Abdul ya yi tsai yana mai karewa yannayinsa kallo,
Dariya ce ke son kubuce masa dan kuwa walahi ya bashi dariya du ya yi tsuru tsuru da shi,
Hannunsa ya matso kusan sa ya ce" Muhammad, wai tsoron mutuwa kake?

Muhammad ya tsura masa ido bai bashi amsa ba, ya nuna yannayin irin ya kufilan nan

Abdul ya yi murmushi ya dan daki kafadarsa ya ce" to dan me ba zaka juya saudiya abinka ba Muhammad? Ka koma gida ka huta zan biyo bayanka in sha Allah

Muhammad ya sauke hannun Abdul a kafadarsa ya ce" kana tunanin zan iya barinka kai daya tsakanin masu harin rayuwarka? Rana tsaka fa wata aljanar yarinya ta zo wai yayarka ce, kai kuwa ka bata wajen zama , idan fa ita ke harin rayuwarka? Abdul bana samun isashen baci dan yawan tunani, a ina tare da kai idan na koma yaya kake so na samu nutsuwa?

Abdul ya koma ya zauna a hankali yana kallon sa ya ce" *MUHAMMAD, MAKASHIN MAZA AI MAZA KE KASHE SHI*
Na yi imanin ko irin yanda mai bibiyar rayuwana ke hana aminina sukuni Allah ba zai barshi ba,

Muhammad, hakurin da nake yi, ahi zan ci gaba da yi, na tabata Adu.a bata faduwa kas,
Ban san tsayin lokacin da zan kara dauka ina cikin wannan rayuwar ba, aman na san lokacin da Allah ya diban mata zai zo zata kare,

Muhammad....mai bibiyar rayuwana na kusa da ni, tunda Allah ya saka hijabi tsakanina da shi na kasa gane shi du irin yanda na kware a harkar bincike, nasa ya zame min a cikin duhu ..... to kawai na barama Allahn, na tabata ya bashi dama ne ya gama rawarsa kafin ya daga shi sama ya kuma dada shi da kasa,

*MUHAMMAD, IN SHA ALLAH, ALLAH SAI YA SAKA MIN KAFIN YA BAYANA SHI KOMA WANENE*

Muhammad dake binsa da wani irin kallon da ba zan iya gane ko na meye ba, cikin wata irin murya mai rawa rawa ya ce"......


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 4??



Cikin nutsuwa malan ya yi gyaran murya ya shiga labartawa mama duka kaf abubuwan da Abdul ya fada masa, da kuma gannin idonsa da ya yi, harma ya tina mata lokacin da ya zo ya fada mata a yau mamansa ta ziyarce shi, mamansa na raye dan kuwa a masalaci ya ji a jikinsa ita din ce

Idannuwanta cike da hawaye ta kai dubanta wajen da Hafsat ke zaune a saman cafet ta sada kanta sai zubar da hawaye take,
A hankali ta ce" Allah ya kara shiryar da ke, ya maki albarka, ya baki miji na gari

Hafsat ta dago kanta da sauri ta saka idannuwanta cikin na mahaifiyarta, gaba daya maman nata ta yi wani irin sanyi bata zaci zata zama haka ba, tana shashekar kuka ta ce" mama, uncle din Abdul aziz ne, shi ne ya kai ni gidan kason gagan yan daba dan kawai na mari matarsa, mama ba zan taba yafe masa ba, ya wulakanta ni, ya tozarta ni, ya kai ni gidan halaka wanda Allah kawai ya fitar da ni

Mama ce ta gala mata harara ta ce" ko komawa zaki yi ki kara daukan fansa?
*UNMIH* ba zan so ki koma irin rayuwarki ta da can baya ba, kin ga taurin kai, jayaya, masifa, raina maganar manya sun bada gudunmuwa wajen saka ki a wannan jarabawa, shiga gidan kaso na abin kunya bane dan kuwa kadarar bawa ne baka isa ka kauce masa ba, sai dai abin lura me kika koyo a can? Yaya kike son tafiar da rayuwarki a yanzu? Mace kike, rayuwarki kadan ce, kar ki yi tsamanin kyan nan naki zai yi ta karuwa ne, daidai da gashin kankin nan zai ringa ja baya a hankali a hankali ne har ya dawo kadan, fatar jikinki zata janye, idannuwanki zasu jeme, furfura zata yi maki salama idan har kin dace! Ki rufa bakin ki, babu rufin asirin da ya kai na kariyar da Allah ya baki, Allah ya baki kariya Unmih ke kin sani...nima na sani...nan gaba kowa zai sani, kar ki yi garajen da Allah zai barki ya ga yanda zaki yin! Tashi malama ki fice min a daki ga kys din dakinki an gyara , je ki zan neme ki!


Jiki a sabule ta mike ta karbi kys din dakin a hankali ta shiga takawa tana kuma waiwayen malan aman ga mamakinta bai daka tsawar kar a yi mata fada ba, saima kawar da kai da ya yi tamkar baya wajen
Bakinta ta zumburo ta daga kafa ta fice a dakin tana fadin lale malan ya daina son ta

Tana fita malan ya kurawa mama ido yana kallonta,

Kanta ta sada kafin take kamo dan yatsarta ta shiga dan ja,

Malan ya ce" to a huce a kaina mana da za.a saka min uwa gaba daga dawowarta a fara yi mata ihu ana fitar mata da ido? Ni madame me ya sa karfinki kike nuna shi a kan UWATA NE?

murmushi ta saki a hankali, ta dago da idannuwanta da sukai jajajir,
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta fashe masa da kuka marar sauti

Murmushi malan ya yi yana kallonta ya ce" menene na kukan kuma?

Sai da mama ta yi dan kukanta wanda tamkar na shagwaba kafin ta sasauta tana kallonsa ta ce" tsoro nake ji, du wannan rayuwar da Anmih ta gani bai saka ta daina fada ba, ji fa ita nan har tana gannin ramuwar da zata yi ta huce? Ramuwa ta fi ta barwa Allah ya saka mata?

Sai da ya lakaci hancinta yana kallonta ya ce" shekarun ki arba.in da bakwai da wata hudu da kuma kwana ashirin da biyar yau maman Uwata, aman har yanzu akoy rigima.........
Ki kwontar da hankalin ki, adu.ar nan dai da muke yi in sha Allah ba zata kuma ba, ai yanzunma Allah ya dawo mana da ita lafia ba karfinmu ko dabararmu ba ko?

Kanta ta gyara a hankali sai kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya

A kadan dai sai da Malan ya jima dakin mama yana ta yi mata nasiha sai da hankalinta ya idasa kwontawa sosai sannan ya mike ya kalli agogon hannunsa ya ce" yau ban ga ana shirin zuwa turakata ba

Murmushi ta yi tana rufe idannuwanta irin ta ji kunyar nan, hakan ya saka malan kara sakar mata murmushi ya juya ya fice a dakin, har tsakiyar ransa yana so ya je ya ga kar a je fadan da mamanta ta yi mata tana can tana kuka, kai a duniya da ake cewa ko cikin yaya Allah na saka maka kaunar wani ta fi ta wani, haka yake jin kaunar mai sunnan mamansa har baya iya boyewa, dalilin wannan ne ya saka shi daukan damarar boyewa ko a gaban mahaifiyarta ne bale a cikin yan uwanta da sauran matansa ko za.a shafa mata lafia


Bayan kwana hudu.....

Hafsat a kilace take cikin gidansu, an yi gumurzun an kare an yi rigimar da tashin hankalin an kare, an yi yawan maganar da tsegumin du an lafa, masu jiran su ga ta tsiro da dabanci kala daban daban sun ga shiru, Abdul aziz ya yi sau ya fi a kirga bai ga ko kalar mai kama da ita ba bale ya ganta, kai hasalima ta zama kawar mamanta da kuma yayarta

A yanzu du zama da tashinta tana lure da kyawawan dabi.un mahaifiyarta, idan aikin mamanta ne takan shiga ta zabga masu girki na ji na gani mai dadin dandano a zuba kowa ya ci da sabon taste wa.inda ta koya a wajen Formation na zama bodyguard

Bata da waya, bata damu da rikewa ba , ita ta kanta take sai a yamacin yau mahaifiyarta ta mika mata wayarta ta da wace masoyinta na da wanda sanadiyarsa ta afka tashin hankalin rayuwa

Ta jima tana juya wayar kafin ta kai ta saka a caji ta ci gaba da sha.aninta

A rana ta shida mai dinki wato hajia Farida ta kawo dinkunnan da mama ta bata ,
Ai kuwa dinkuna ne masu shegen kyau rufafu tsararu sannan na gayu masu tsadar gaske,
Ba karamin farin cikin kayan nan ta yi ba, haka ta hau sama wajen mahaifinta dan yin godiya, tana zuwa ya kara mata abayoyi kala biyar masu shegen kyau na yayi dukansu masu botira da mayafansu bakake masu tsari

Kanta kawai ta sada ta rasa bakin magana, a hankali ta dago da idannuwanta sai ta ga mahaifin nata na kallonta yanai mata murmushi, ba komai yake jin dadinsa ba sai yannayinta na yanzu, wai mamansa ce ke nuna farin ciki dan an saya mata sutura, yarinyar da a da hayowa zata yi, ba ruwanta da neman izini sai dai ta afka idan a gaban wa sai dai ta fadi muradinta na kudi ta karashe da fadin" kuma a bani ko na je saurayina ya bani!
Sai gashi yanzu a gidan duniya Allah ya nuna masa ita tana godiya harma ta rasa bakin godiyar

Hannunsa ya daga mata dan ya tabata tana iya yi masa kuka a gurin , shi kuwa baya so , dan haka ta mike har ta kusa fita ta tsinkayo muryarsa ya ce" su ABDALLAH zasu dawo gari da zama karshen satin nan, kwana biyu ina tsaye kan saukar alkur.ani a gidan da zai zauna , kulun muna zuwa a sauke a yi sadaka dan gudun fitinar zamani

Sai da gabanta ya fadi, a ranta ta ayanna me kuma zai dawo da shi kasar Niger?

Kafadunta ta daga a lokacin da ta tuna asalin dan niger din ne shima fa, haifafan garin ne, haka kuma dangin da suka rage masa yan nan ne wato matarsa da kanwar mamansa

Bata baiwa Malan amsa ba sai karasawa da ta yi da murnarta suka dadaga kayan da mahaifiyarta kafin su shiga yi masu turaran wuta da adu.ar Allah ya sa a mora lafia


Bayan kwana goma

Kwonce take tsakar dakinta wajen karfe biyar na yama, juyi kawai take tana tunanin wai yau zata yi zance, zancen ma da BS, zuwansa biyu sai yau Malan ya bashi damar ya zi su gana

Mikewa ta yi zaune tana kallon madubin dakinta mai tsayi, kanta ta girgiza ta koma ta kwonta gashi har karfe bakwai din ta kusa,

Tana nan kwoncen har karfe shida ta buga, buda kofar da aka yi ne ya sakata mikewa zaune tana kallon yayarta da ta shigo da yaronta da ya fara rarafe yana yawonsa ko.ina

Bayan sun gaisa ne yayar tata ta bita da kallo,
Can ta ce" Maman malan, ni ba bako aka ce zaki yi yau ba?

Hafsat ta dubeta ta ce " eh

Yayarta ta ce" to ya haka baki shirya ba

Hafsat ta kaleta da mamaki ta ce" shiryawar me kuma auntu ? BS ne fa??

Sai da ta rike habarta sannan ta yi dariya ta girgiza kai ta ce" dan BS ne shine ba zaki kimtsa jikinki ba? Oya tashi tashi malama

Mikewa Hafsat ta yi tana kallonta kafin ta shige ciki ta dauko abaya daya daga cikin abayoyin Aba ta saka abinta a nan sannan ta shiga saka turarukan wutar da ta miko mata

Tana kokarin yana mayafin dan kwalin ta tsayar da ita ta zauna ta dan gyara mata fuska da kwalinta sannan ta yana mata dan kwalin a kanta

Tsaf hafsat ta fito tamkar ba ita ba, wani irin kyau ne ya bayanna a tare da ita wanda ita kanta sai da ta shafa gefen fuskarta sannan ta yi murmushi


Ana fitowa sallar magariba aka suka zauna tsakar gida inda malan ya basu minti talatin su gana

A zancen nan Hafsat banda tambayoyi a kan aiki ba abinda ta tsare BS da shi, shi kansa sai ya kasa wani yi mata zancen soyaya sai da ya tashi tafia ne ya ce da ita" Hafsat, ina son na turo a yi komai da wuri a gama, dan kin ga malan baya son dogon zance

Sai da ta ji gabanta

25 / 54