Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   10 / 54

27K to 30K   out of 159.5K words

*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4??


*Free page*



Ana mayar da ita cikin kurkukun dakinsu ta ja ta tsaya sanadiyar ganninsu da ta yi fada suke mata kowace na rantsuwar a barya da ita ta koya mata hankali,

Ganninta ya saka suka fara nufota da yannayin izgilanci suna rantsuwar yau sai dai gawarta, bale masu zaune a wajen da nufin daurin rai da rai,

Da gudu ta warci tabaryar da ake dakan da ita, daidai saratu ta karaso wace ta fi kowa rawar kafa dan samun gidin zama wajen Eliz, sai dai me, batai wata wata ba ta daga tabaryar nan ta sheka mata ita a goshi, sannan ta aniya tarban wa.inda basu rigai sun karaso din ba, ja suka fara yi suna tsayawa, kai danma zaman balaki ne zaman kurkuku? Da me zai saka ka tarban gabanta? Mai zai kaika yin wannan kasadar? Bata ji bata gani, idan ta rufe ido kawai a fado a mutu ne,

Cikin hargagi da iface iface suka shiga dankarawa da gudu, wasu na zagayawa suna nufar wajen sojojin gidan,

Sojojin du mikewa suka yi tsakaninsu suna magana, ba wani abu ba suke cewa sai canko cewa da Aljanar prison ne ake fada, harda masu saka kudi, sannan bakin zuwa sun cika da mamakin wai ita haka take?

Da gudu suka shigo da shirin ko ta kwana, gaba daya suka rufta masu suka shiga dukansu, ba ji ba gani, duka kawai suke sha, sai da suka yi laushi sannan aka barsu, aka tiso keyarsu dan dora garin da suka surfa ba wankewa sai fecewa da suka yo suka kuma daka shi ya zama gari suka dora tuwonsa, inda masu tuka tuwon du suka tafi wanke helunan da zasu tuka tuwon da shi,
Can gefe kuwa Eliz ta hasa wuta da itacen mainan da mazan ke yowa a wajen su hura wutar ta dora tankamemiyar tukunya ta kawo tunjumemen ruwa ta maka ta zuba yan kayan miyan da suka samu, ta afka gishiri, sai dakakiyar miyar da suka dakata da kansu bayan miyar ta tashi sosai ta kawo ta kada da katuwar sanda ba ruwanta da wani burkakewa ta kawo dan mai kadan ta afka abinta ta juya ta zauna tana jira ta yi dan kauri a shiga rabo, yau ta yi niya dan ubanta ba zata samu tuwo ba! Zata nuna mata wanda ke iko a gidan!


Sai lokacin rabo ya yi kowa ya zo da robarsa, dominfa wajen nan ba.a kawo masu ziyara bale ka ci abincin gidanki, abincin da kowa ya ci ne zaka ci ko ka mutu,

Nan kowa ya kawo yar robarsa ana zuba masa abincin da daga shi sai kuma gobe, basu da abincin dare ko na kari, aman suma samun isashen da idan sun adana zai masu anfani.

Tana ji tana gani aka hambarar da robarta, aka zubawa ta bayanta,
Hakan ya sa ta mike ta dauke robar ta kai ta adana, dan indai ta harta a nan wani na iya taketa dan kawai ta rasa yar robar cin abincinma,

Waje ta samu ta rakube tana mai jin wata irin juwa, idannuwanta ta rufe ruf kafin wani hawaye mai zafi ya shiga bin gefen fuskarta,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Allahuna ajurni fi masibati, wa khalifuni khairan mine ha, ya Allah na tuba, Allah na tuba Allah,

Allah mamana, Abana Allah, ka sa su yafe min, idan har nan karshena yake Allah ka sa su ga gawata, su yi min adu.a, Allah kar ka basu ikon cin mani, Allah ka wankeni koda kuwa gawata ce, Allah ka yafe min,

Abinda ta yi ta maimaitawa kennan tana istghfari, ita kam ta ga rayuwa, ta ga ilar tsalake maganar iyaye, bata san haka lamarin yake ba, niyarta lokaci ya yi ta tuba wa Allah, niyarta ta tuba idan ta kara girma ta dawo ta shirya da iyayenta, sai gashi, tana raye, suna raye, ta wayi gari, nesa kadan da garin da suke, aman basu san a duniyar take ko ta mutu ba, tana tausayawa mahaifiyarta, tana tuna dumbin kaina da take yi mata koda kuwa tana kokarin boyewa, yau gata a raye tamkar mataciya,
Bata da wani anfani,
Ana yakin kwace mata martabarta, ana yakin raba gangae jikinta da numfashin da take shaka, adininta ya tabu, walwalarta ta gushe, bata da tunanin da ya fi ta budi ido ta ga iyayenta, ta ga farkon wannan ukuba bata san karshenta ba,

Tana nan zaune du suka ci abincinsu, ba wanda ya damu da irin halin da take ciki, kai ba itaba, akoy wa.inda suka fita jigata, suka fita shiga wani halin rayuwa, ba wanda ya damu da su bale ita da ba zaman lafia suke da junna ba,

Sai da tsohuwar nan ta lura da sahun kafa ya dauke, ta lalaba ta ajiye mata abincin nan ta gefen damarta inda zata iya ci ba tare da wani ya kula da ita ba,

Da kallo ta bi matar da kallo,
Tunda ta zo gidan, zata iya cewa wannan matar na bakin kokarinta a kanta, akoy lokacin da ta kwatanta yi mata nasiha kan ta bar kula mutanen nan haka, ta yi hakuri ta daina, aman cikin ikon Allah ta fada mata itafa kan abu biyu ne ba zata iya kawar da kanta ba, darajar mahaifanta, da ita tata darajar dake tare da ita, dan haka indai a kansu ta ga tana fada , karma ta daga dan yatsanta ba zata saurareta ba,

Abincin ta wawura daga gefen nata ta shiga ahawa ba ji ba gani,
Tuwon bashi da wani dandano a harshen bawa, yana gangarawa ne ya je ya dunkule maka a cikin ciki,
Bata damu ba sai da ta cinye shi kakaf sannan ta shiga maida numfashi tana duban yanda ganninta ya fara dawowa,

Godiya ta yiwa Allah da bai barta cikin yinwa ba, ta labe robar tsohuwar sai da ta mike dan gabatar da sallah ta kai mata ta ajiye a boye ba wanda ya kula da an tiso tsohuwar a gaba danme zata hana a yi mata horon yinwa.

Sai da ta zo tsakiyar wajen ta yi tsaye , ta saki murmushin godiya ga Allah, sannan ta bi kowa da kallo, bata da dar, du wace ke jin kanta wata shegiya ce kuwa jiranta take, dan haka a gadarance ta nufi wajen ruwa ta dauka, ruwan da na siyarwa ne ta dawo ta shiga alwallah bayan ta kwonkwada,

Ke ina kudin ruwana?
Muryar mai siyar da ruwan ya daki kunnenta,
Namiji ne , aman kuma dan daudu ne, zamansa cikin prison din ba irin sana.ar da baya yi, shi ke samo ruwansa ta hanyar da masu tsaro suka yarje masa, ba wai babu panpo bane a wajen, da ruwa fa, kawai ana hana su zuwa wajen ruwan ne, sai idan dare ya tsala ake bari, su kuwa da ba abubuwan cika ruwan garesu ba wa zai basu? (Ya Allah ka rufa mana asiri, ka rabamu da kadara muguwar kadara, tabas zaman gidan yari wani nufi ne na Allah wanda idan ya nufi bawansa ba wanda ya isa ya hana, kadarra ce, ya Allah ka kare mu da rayuwar rashin yanci ),

Da sauri ta karasa alwalarta, sosai ta didiki ruwan, sannan tamike tsaye tana dubansa cikin ido yanda yake wani laudi, du fuskarsa ta jeme tsabar shafe shafe da yake dan jaraba a gidan yarinma, sannan fuskar wani tafkekiya da ita da dogayen lebuna da aka kara fitar da su dan dole dan kuwa lankwasa sun da ake ta hanyar sai an yi maganar mata dan dole,

Murmushi ta sakar masa sannan ta ce" kai ko kema sunnan yake, kali sama, rana ta raba, tsuntsaye sun yi shiru, sararin samaniya ya kara haske, wanda ya yika, ya kuma baka ruwan ne zan gaisar, in kuwa baka yafe ba fadi mu ji....

Ta karashe tana harde hannayenta biyu tana dubansa ,

Baki ya tabe kafin ya ce" jarababiya mai bakin uwa (zaginsa kennan sai yace da kai mai bakin uwa, wai nufinsa in ba bakin uwa ba me zai kawo mutun kutkale),

Wartar butarsa ya yi kafin ya zabga mata harara tamkar wata mace, ya ja tsaki ya kuma buga cinya ya juya ya bar mata wajen yana mitar ke kika sani, ah ina dalili ga zafin prison ga na yinwa ga kuma na dambe?, bara in je in yi neman kudina in huta, neman fada ai sai matsiyaci!

Ita dai tunda ya juya itama ta juya dan zuwa ta yi sallah, domin malaman cikin prison din sun yi kiran sallah tun dazu, ( kar ku sha mamaki, kamar yanda na fada, ba abinda babu a gidan yari, )



Gidan Malan Muhammad Sa.it


Sadakar damamiyar madara da kuma abinci dafafe ne ake yau juma.a,

Ko a masalaci da aka gama sallah kamar yanda ya saba, sadaka ya yi sosai, inda shima manyan elhazan nan ke kawonasu gudunmuwar , wasu da sunnan masalaci, wasu kuwa da sunnan malan din da kansa, duda kuwa ya fi karfin hakan, aman ba karamin dadi yake masa ba domin kuwa mutuntawa ne,

Sai da aka watse, ya mike ya gyara salayarsa a ma.ajiyarta yana duba agogo dan karfe hudu yana da wa.azi da gidan tv Tele Sahel,

Abokin shawararsa ne, wato Malan Laminu ya shigo masalacin,

Cikin raha suka gaisa kafin su fito daga wajen sallar suka yada zango a balbalin masalacin wajen shuke shuke na gazon macha Allah,

Dubansa ya yi a tsanake sannan ya ce" yaya karin hakuri? Ya juriya, ya hakurin Matar arziki?

Shiru ya yi kafin ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa ya ce" ka san na shaku da yarinyar,
Kai shaida ne komai nata daban ne,
Inada vidioyinmu inda take tatata, tana yi tana fadin Baba..baba tatata,


Malan laminu ya sauke ajiyar zuciya ya ce" ba kai kadai ba malan, ko ni da ta yi karatun alkur.ani hanuna na sha mamakin lamarinta,
Wai ka san tun kafin ta yi sauka ta taba kamo bata a cikin rubutun litafi da malan salisu yake koyon nan da tadawa? A nan na kara dubanta,
Ka duba ka ga a kusan tare ta yi hardar ahlari, kawa.idi, da alkur.ani, tana gamawa ta shiga damkar litatafan adinin nan, kuma ya shiga kwajwaluwar cikin ikon Allah ya zauna,
*UWATA* raye ko mace?

Malan Muhammad ya ce" na so gannin gawarta, na tabata da na hakura na samu nutsuwar zuciya, man laminu, mutuwa bata boyuwa, gani nake koda a ketare da niger ta mutu zamanin android za.a haskota,
Ina ji a jikina *UWATA* na raye, ina ji a jikina tana wani yannayin rayuwa, mahaifiyarta ke bani labarin mafarkinta, takan yi mafarki *HAFSATU* na miko mata hannu, ko ta yi mafarkinta ta dora kanta saman cinyarta tana shasheka tamkar wace ta yi tsere,
Ya Allah ka kare min UWATA du inda take, idan da kafarta ta gudu dan zan mata auren da bata so, Allah ka shiryeta ka dawo da ita gida, idan kuwa fitar da ita aka yi, Allah ka kare min ita,

Shiru ya yi yana duban Malan laminu daje amsawa cike da girmamawa sannan ya ce" idan kuwa Uwata ta rigamu gidan gaskiya, ya Allah ka jikanta, ka sa tana cikin rahamarka, Allah ka hada mu da wanda koda hoton mutuwarta ne ya gani ya fada mana ko hankali uwar daukan cikinta zai tsaya waje guda, ko zata rage yawan fado mani a cikin zuciya ya Arahaman rahimine

Amsa masa adu.arsa yake, inda suka mike suka rankaya gidan Malan Muhammad din, somin yau juma.a ce, gidan malan na cika ne tun da asuba har wata asubar ana raya ranar sosai,,




Bayan sati biyu

Murkashi take na ciwon ciki, ita daya yashe a rana sai juyi take , abin ne ya hadun mata ha yunwa da take ji, ga rashin bacin kirki , ga damuwa, ga kuma al.adarta da ta risketa cikin wannan halin,
Adu.a take so ta yi aman ina, sosai cikinta ke ciwo tamkar ranta zai fita...................



*Domin Samun kutkale, naira dari biyu ne, Niger kuwa 500 franc ta orang money*


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 5??

*DUNIYA MAKARANTA,*

ASALAMU ALAIKUM




A lokacin da su BS suka cinma wannan mutun, sun tarar da shi yana zubar da wata irin kumfa , wato ya hadiyi poison,

Ba yanda basu yi ba dan gannin bai auna barzahu ba, sai dai ina poison din mai karfi ne,
Wayarshi dake yashe dan nesa da shi suka dauka da sauri,
Bayanta BS ya buda dan cire layin, sai dai wayam ba layi a ciki, ba alamunsa,
Cike da jin haushi ya doka wayar da kasa yana fadin shiiit!
Kafin ya kai dubansa wajen yaren dake tare da shi ya basu umarnin maza maza su duduba layin inda ya jefar da shi,

Hafsat dake tsaye tana kallo ta yi saurin maido baya kadan,
Inda ya yi kamar ya labe fuskarsa ta yi zooming,
Nan ta ga yanda ya yi da layin, wato a bakinsa ya saka shi ya taune shi sannan ya ya hadiye,

Bata san lokacin da ta dora hannayenta biyu saman kanta ba, ta janye atach mai ruwan blue din dake kanta dan bada kama, ta yar ta dan ja da baya irin desespoir din nan,
A hankali jiki a sanyaye ta ce" BS, kar ku ba kanku wahala, ya taune layin kafin ya hadiye shi

Sai a lokacin ta tuna da yana zaune a dakin, sai a lokacin ta kai dubanta inda yake zaune,

Kuri ita yake kallo, tun da ya hadiye layin shi ya gani, kuma ya gane nufinsa, aman kuma ya barsu su yi aikinsu,
Yannayin da ta nuna na tashin hankalin echec din abinda ta saka a gaba ya matukar bashi mamaki,
Menene damuwarta haka a kasan zuciyarta? Ko kashe shi aka yi ita fa bata da asara domin kudin aikinta cas sai an cashe mata su,
Abu biyu ke iya saka ta a wannan yannayi, tana da damuwar kanta,
Ko kuwa ta matukar dauki aikinta da mahinmanci,

Ido cikin ido suke kallon junna,
Kafin ya ga ta mike ta tunkaro inda yake zaune,

Sai da ta zo kusa da shi, irin kusan da babu wani space a tsakaninsu ta saka idannuwanta cikin nasa ta ce" ka bamu damar yin aikinmu yanda ya dace,
Ya za.a dauke mu aiki, ba.a bamu wani cikeken bayani a kan aikin ba, ba.a fada mana girman risk din da muke ciki ba, bamu san komai ba, kuma a ce zamu iya yin wani abin kirki? Ya dace kafin mu hau filin aiki mu san ko kai waye, meye sana.arka, meye tarihinka, me ke yawo da kai haka da za.a farauci rayuwarka daga zuwanmu, kafin mu zo an farauce ka har haka? Kana da wanda kake hasashen shi ke neman rayuwarka?

Duka magangannun nan da take masa , cikin yannayi na daure fuska, da kuma iya gaskiyar abinda take son sani kennan take yi, sannan idannuwanta tsai cikin nasa, ba tare da ta ji wani dar ko wani nauyin saka idannuwanta cikin nasa ba, haka ta kare zanenta sannan ta yi shiru tana mai dubansa , hakan na nufin amsarsa take jira.

Kijerar ya ajiye daga lilon da yake mata, sannan ya mike tsaye, wanda mikewa ta saka kirjinsu kusan goguwa da juna har sai da ta dan ja baya,

Tsayuwar da ya yi ya sakata dan daga kanta fan kar ya ga wasa a tatare da ita ko gazawa a idannuwanta ta ci gaba da kallon nasa wanda hakan shima ya so din,

Idannuwansa ya bude mata baki daya yana dubanta ya ce" wacece ke? Su waye mahaifanki?

Kanta ta dafe da yannayin irin wannan tambayar ta isheta , kafin ta kuma dubansa ta ce" ba shi ne abinda ya kawo ni gifanka ba! Dan me kai ba zaka iya bamu information din da muke so ba?

Idannuwansa ya kankance ya matso kusa da ita domin ta kara ja baya irin suna jin har bugun zuciyar juna ya ce" ban ga dalilin da zai saka na dauki karti biyar na tinga biyansu kudin aiki masu tsokar da ba a gine nake ba sai na girgije dan an wawushe ni, sannan kuma na masu rabin aikin!
Me aikin ki ya kumsa?

10 / 54