Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   16 / 54

45K to 48K   out of 159.5K words

yi salama,

Ga mamakinta sai ta ga ya matso kusa da ita sosai

Sai da ya daga kansa ya kaleta domin ya matso kusa da ita kafin cikin muryarsa dake nuni da manyantakarsa ya ce" ke kuwa, kin ari musulunci ne ko musulmar ce ke?

Kanta ta sada dan kallonsa da kyau itama kafin ta ce" kama gare su ne musulmai ko salamana ne bai cika ba?

Kansa ya gyada kafin ya juya da niyar tafiyarsa ,
Gane hakan da ta yi ya sakata matsawa da sauri ta ce" dan Allah, ka taimake ni, ina son sannin waye Muhammad bine Abdul Basid Abdallah? Ko zaka iya kai ni inda yake?

Sai da ya kare mata kallo sannan ya ce" ki je dare ya yi, ki dawo zan kai ki wajensa, aman yanzu akoy nisa ga kuma dare

Ta so ta yi magiya ko zai saurareta, sai dai gannin bashi da niyar hakan ya saka ta juyawa ta hau mashin din ta tayar ta dauki hanya wanda a lokacin tuni isha ta kawo kai, a kadan zata iya kaiwa awa uku ko zata isa

Gudu kawai take yi, gashi a lokacin da zata bar gidan Abdul sai da ta ajiye du wani abin aikinta da zai bada damar a san inda ta nufa, ta tabata yanzu an farga da bata nan, fatanta kar ta kai BS bango ya dauki mataki a kanta ya kawar da wani gudun bacin ranta ya saba mata!


Ta jima, ba karamar wahala ta sha a hanyar ba kafin ta karasa anguwar, a haka har ta karasa kofar gidan

Tun daga irin kallon da sojojin ke binta da shi ta dan sha Jinnin jikinta, sai dai bata saka komai a ranta ba ta samu ta shigar da mashin din ta karamar kofar sannan ta sauka ta shiga tura shi ta ci uwar tafia kafin ta karasa farfajiyar gidan

Dare ne, aman ko.ina ya dauka da hasken fitila , hakan ya saka du wani mai motsi ana iya ganninsa da dukan abinda ke tare da shi

Tun da ta shigo gabanta ya yanke ya fadi, dan kuwa du wani bodyguard da ya kwana ya tashi a gidan yana tsaye cirko cirko , BS sai doka waya yake haka kuma sai duba agogo yake, gefe kuwa Abdul ne tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa ya zubawa hanyar da ta fito ido


Turus ta yi da babur din gannin yanda BS ya nufo inda take tsaye gadan gadan ta tsura masa ido sannan ta sadakar cewa idan ya zo yana iya dauketa da mari

BS na karasowa hannunta dake rike da mashin din ya damka yana dubanta ya ce " ina kika je? Ke da wa kuka je? Me kika je yi? Bakya tsoron wata fitina ta same ki?

Idannuwanta ta kikifta tana kallonsa,
A hankali ya sasauta damkar da ya yiwa hannunta ya rage ihun muryarsa ya ce" baki damu da damuwata ba? Ya dace ki damu da aikin ki, dan wanda ya dauke mu ya san takun mu

Yawun bakinta ta hadiye a lokaci guda kuma ta dan leka bayansa,
Ido hudu suka yi da Abdul sannan ya juya ya shige ciki ba tare da ya ce da kowa komai ba

Sai a lokacin ta jinginar da mashin din dake kauri ta ce" BS, ka yi hakuri, na gaji da zaman waje dayan ne, shi yasa na fita na sha iska

Hasana dake tsaye ido ta zaro tare da fadin" me? Ke kina da hankali kuwa? Ke Bodyguard har wani lokacinki gare ki bale muradinki? Ki dubi idannuwan mutane ki ce wai kin tafi shan iska? Ba laifi, tunda kin shawo iska sai ki zo ki zagaye balbalin gidan nan sau hamsin!

A tare suka dubeta, daga BS har Hafsat,

Hafsat kam dukawa ta yi ta kara gyara takalmanta sau ciki sannan ta cira da gudu da daren nan ga tarin gajiya , ga yinwa, ga bukatar yin wanka ta shiga gudun punishment domin kuwa Hasana dai ta isa ta sakata ko ta hanata a bangaren aikinta dan gaba take da ita ya zama wajibi ta yi mata biyaya

Hannun Hasana ya damka ya juya da ita da wani irin karfi ya hankadata gefe inda ba za.a iya hangosu ko a ji maganarsu ba ya ce" ke a wa zaki shiga hurumin da ba.a saka ki ba? Ina ruwanki da amsar da ta bani? Ke idan a halayanki zan bi ki kina tunanin zan bar ki ki numfasa ne?

Bayanta da ya buga da bango ta dafe kafin ta ce" BS , saboda na hora yarinyar dake kokarin rainaka a gabana ne kake wulakanta ni haka? Menene tsakaninka da ita? Wacece ita? Me ya sa na ga du kuna wani rawar kai a gabanta? Idan tana zagayawa da wancen da muke yiwa aiki kaima kwoncin kake da ita ko?

Cikin daga murya ya ce" ki rufe min baki da fadin magangannun da ba tsari a nan,
Kin ga yarinyar can da kika raina? Ni ita nake so, kuma ki daina kokarin zaginta dan ko daya , ba irinki bace, yanda take jana a kas ya saka nake kara mutuwa kanta, ta san ina sonta, har yanzu ta kasa so na, dan haka ki girmamata kar ki yarda ki mayar da ita abokiyar gabanki , dan na rantse maki ta ishe ki tuwo da miya

Sosai magangannun nan sukai mata zafi, tana dafe da bayanta ta ce" aman ka san da ni kake soyaya ko? Kuma ka san aikinka ya haramta maka soyaya da dalibar da ba.a yaye ba ko?

Sai da ya shafa gaban goshinsa da sankon kansa sannan ya ce" to ki tona, ke bari ki ji, abinda zai hana ni samunta daya ne, idan ta ce da ni Bashir ka barni haka, bana son ka!


Yana gama fada ya juya ya fice ya tsaya can gefe yana hangen yanda Hafsat ke gudu tana raba hanya,
Kwarai yana da damar hanawa, ya isa ya hana dan shima yana matsayin gaban Hasana, sai dai ba zai shiga ba ko dan ya kori tsargi sannan ya rike girmansa a wajen yarensa, tausayinta yake ji, kaunarta yake yi, ji yake dama zai karbar mata gudun!


Abdul dake tsaye kusan windows din dakin Muhammad ya rike dan labulen ya tsura mata ido yanda take gudu, Muhammad na yi masa magana shi walahi kwata kwatama bai san me yake cewa ba, a haka ya juyo ya ce" *daga ina take?*

Muhammad dake dana waya yana nuna masa sabuwar motar da kanfanin Helix suka kera wace ke da tsananin tsada ya dago yana dubansa
Sai da ya matso inda yake tsaye ya ce" wa kake tambayar inda ta je?

Sai a lokacin Abdul ya farka, tamkar an dan tsikare shi ya dubi Muhammad da kyau, sai kuma ya shiga takawa ya ce " ina zuwa.......

A wannan dare haka kowa ya yi barci zuciyarsa a cinkushe, tun daga Abdul, Ni.ima, Hafsat, BS , Hasana, da du wani ikon dake gidan wanda sanadiyar rashin gannin Hafsat da tabatar masa cewar ta fita a mashin ya saka tayar masu da hankali da rantsuwar su saurari du irin abinda zai sameta walahi da hannunsa zai masu! Hakan ya saka du suka firgice suna masu jin haushin juna da jin haushin wanda ya ara mata mashin din

Ko da safe ba wanda ya shiga sabgar wani, kowa bakin aikinsa yake tun safe har yama,

Ko da yama ta yi , yauma fitowar ya yi , sai dai yau wani bakin yadi sidik ne ya saka ya fito ya nufi wajen shakatarwarsa

A lokacin da ya zauna ya mike kafarsa ya kali BS dake kai kawo ya ce" ka ce da dayar nan ta fita can baya ku kuwa ku zo kai da wancen ina son gannin ku

A nunin da ya yi, yana nufin a cewa Hasana ta fita, su kuwa ya nuna su zo saman kujerar dake kusa da shi yana son gannin su

Abinda ya bukata BS ya aiwatar, inda suka zauna a kujerar dake gabansa su duka suna kallon yanda ya tsura masu ido ya kalli wannan ya kalli wancen

Sai da Abdul ya gama kallon su sannan ya ce" *wai ku yaushe kuke zance ne? Wace irin soyaya ce kuke haka bakwa bata kulawa? To yau ku yi zance!*

Sai da suka kalli junna sannan suka kale shi a tare tamkar hadin baki,
BS ya dan gyara zamansa yana kallon Abdul,

Abdul ya girgiza kai ya ce" kai yanzu, katoto da kai, kake jin tsoron wannan yar yarinyar? Bashir maza ka rako duniya ko me? Ka fito kace da Hafsat cewa kana son ta aman sai ka ringa hauka har kowa ya gane kana sonta ita ka kasa fada mata kiri kiri?

Sai da BS ya mike tsaye, sai kuma ya koma ya zauna tamkar an dangwarar da shi yana zare ido yana kallon yanda Abdul ke kada kafarsa dake wanke tas tamkar a side,
A haka ya bi shi da kallo har fuskarsa, kai shi ko a lakuru bai ga kwalon dan duniya irin Abdul ba,

Dubansa ya maida wajen Hafsat ya ga ta tabe bakinta ta dafe gaban goshinta, kuma abinda ya bashi mamaki bai ji ta yiwa Abdul ihun kar ya yarda ya kama sunnanta sunnan mahaifiyar malan ce, ohk wato sai su da aka raina ko?

Katse masa tunaninsa ta yi ta hanyar fadin" *ABDUL*

idannuwansa ya dauke daga duban gefen da yake , ya saka cikin idannuwanta har da takabe kumatunsa yana kallon yanda ta kankance idannuwanta wai kennan zata yi jaraba ko?
Dubansa ya kai wajen BS ya ce" Bashir, ko jaraba zata yi kyau take mata, bara ka ga yanzu ta ce" Abdul, menene haka? Ka bar mu mu koma bakin aikin mu....
Sai ta wurgan harara, sai ta mike ta tabe baki kuncinta ya lotsa , sai ta koma bayana ta yi tsaye ta hade rai dan Hafsat bata son raini!


Kallon junna suka kuma yi ,
Nan Hafsat ta lumshe idannuwanta tana son tunanin girman rainin hankalin Abdul,
Sai dai bai bata wannan damar ba ya katse mata tunani da fadin" kina tunanin zan baiwa soja mashin na kasa saka masa abinda zai nunan inda yake shiga?
Hafsat me kika je yi cikin jejin da ba wani mahaluki dake rayuwa a cikinsa a sanina? Kina son na saka maki ido a motsinki ne?

Shiru ya yi, kafin ya ci gaba da fadin" BS nah? Ka tambayi wajen wanda ta je dan ba zan lamunci hakan ba!

Mikewa ya yi ya mayar da bakin gilas dinsa ya juya da niyar tafia,
Sai dai sunnan da Hafsat ta ambata ya kusan tainke masa lumfashi,

Wani irin ja ya yi ya tsaya sannan ya juyo a haukace ya.......


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?







*Free page*

*Alhamdulilah, nan na kawo karshen free page...du mai son ci gaban Kutkale ya garzayo ta hanyar biyan nasa ya samu shiga cikin grup din*


Ta jima tana auna maganarsa, kafin ta janye hannunta tana harararsa,

A dan kufule ta ce" a ina aka taba yi? Dama an tana haka? Wace za.a dauko dan ta tsare lafiarka kace sai an daura maku aure? To danme ma za.a wani aura maka yarinyar? Ka yi yaya da ita?

Kansa ya shafa yana kallon maman basa har ta gama kafin ya ce" an samu ci gaba kala daban daban a duniya Ummih,
Sun buda wannan wajen dan a dauka a kuma biya su,
Akoy damar ka auri mace na adadin lokacin da ka dauketa aiki, su zasu san yanda zasu yi tsarinsu, sannan ni fa ba wani abu nake nufi dan nace a yi hakan ba, halin rayuwa nake dubawa,

Kanta ta dafe da hannunta na dama,
Da na hagu ta yi masa nuni da ya tafi,
Dan haka a hankali ya mike yana mai adu.ar Allah yasa ta ki amincewa, shi fa a gaskiya baya so, baya ra.ayi, haba, ko dan bata san shi nasa aikin da yake yi na biye bane ya saka take takurar kanta haka? Da zata san menene ainahin aikinsa, da bata damu kanta haka ba, somin ya baro saudiya ne bisa dalili kwakwara na kasancewarsa agent mai aiki a boye, ya baro ne dan shima da nasa aikin, kasuwanci da ya karanta shi duniya ta sanshi da aikinsa, idan ba wannan ba ta yaya zai ringa gane abubuwan dake faruwa a tatare da shi? Shi ba aljani ba? Horon da ya samu, ya yi imanin ba zasu taba samun irinsa ba!

A haka ya baro gidan mahaifiyarsa, cikin motar da yake ja da kansa,
Ya yi tuki mai nisa ya ja gefe ya tsaya sakamakon sarawa da kansa ya yi,
Idannuwansa ya lumshe ya shiga karanta du wata ayar da ta zo bakinsa dan neman tsari,
Kansa ya jinginar jikin kujerar da yake tuki samanta,
Gabansa ne ya yanke ya fadi, ya kara yankewa ya fadi,
Da sauri ya dafe daidai zuciyarsa yana mai jin wata irin zufa na karyo masa,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une!
Shi ne abinda ya shiga maimaitawa ba ji ba gani,

Wani irin ribos ya yi da motar ya dauki hanyar gidan mahaifiyarsa, gaba daya jikinsa rawa yake,
Gaba dayansa ya fice a hayacinsa, irin wannan abin ne ya faru da shi, a shekarun da suka shige, shekarun da ya rasa babansa, shekarun da ya rasa kanwarsa, shi ba mahaukaci bane, kudi gata basu saka ya zauce ba.... yana rayuwar sakalci ne bisa dalilai,

Horn din da ya dane ya saka mai gadi mikewa da gudu gudu ya bude masa kofa yana mamakin abinda ya dawo da shi,

Yana shiga gidan abinda ya hango ya saka shi sakin sitiyarin motar ya dora hannayensa biyu saman kansa tare da fasa wani ihu mai taratsin mai fitar da innalilahi wa.ina ilaihi raj.une
Hannayensa saman kansa motar ta je ta daki karfen rumfar ajiye motoci, nan rumfar ta rufto ta rufe motar baki daya, inda da wuta ka yi tunanin idan har za.a iya ciro mutun da rai daga wannan accident

Wannan shi ne farko,
Wannan shi ne mafarin sabuwar rayuwar da zata budewa *ABDUL JABAR*, wannan shi ne duhu, kunci, rayuwar gimgim, rayuwar gimtsewar da zata samu Abdul Jabar, daga wannan lokaci, wannan dan saurayi mai rayuwa cike da sangarta, da garari, ya dawo tamkar kurma, ya dawo wani bahagumen mutun mai wuyar zama,
Ya kai sati kwonce cikin halin rashin sannin inda kansa yake a babar asibitin garin, inda sojoji ke gadinsa ,
A ranar da ya farka ya kai dubansa saman agendar dake dakin makekiya ta shekarar da ake,
Bai gane ranar da ake ba, sai dai awar ta bashi damar gannin kamar ya kwana a wajen kennan?
A lokacin da likita ke cike da murnar farfadowarsa bayan sati daya da sumarsaa ya saka shi jin wani irin bugawar zuciya,

Da kyar ya iya buda bakinsa ya ce" ina Ummih? Ina Ummih?

Gargadin da yarima Muhammad ya yi kan kar wanda ya bashi amsar nan ya saka su kokarin gannin sun masa alurar da zata saka shi baci,
Sai dai ina, a hankali karfin zuciyarsa ya hayo inda ya shiga kokowa da su yana ihun ina Umminsa?

Ta mutu ko? Ta mutu? Ku kai ni wajen gawarta, ku kai ni na ga gawarta, sun kasheta? Ummih, kina fadi sai da suka rufe maki baki?
Daneshi suke son yo aman sun kasa dan haka suka baiwa sojoji biyun da suka shigo waje suka kai shi kasa suka dane kafin ya tsira masa allurar baci,
Shiru dakin ya dauka, dan kuwa sai da ta kashe masa jiki idannuwansa kekashe kafin ta yi masarar daukansa,
........................................


Haushi yarinyar ke bata walahi, bata san yaya zata yi ta taro yarinyar da a haife ta girmeta aman take hauka irin haka,
Dama haka mutanen dake kallonta tana tafka tsiya har wa iyayenta suke jin haushinta? A gaskiya da tana da yancin cewa ita a mayar da ita camp da ta fada domin du wani kokarin nunawa yarinyar shirmenta ya jaza mata tiwa saurayi rashin mutuncin da ya wanka mata mari da ikirarin sai ya tozartata, ta kasa fahimta,

Ko yanzu da suke tsaye, Hafsat din na tsaye bayanta , ita kuma sai hauka take na fadan ita gaskiya dad a rabata da wannan mai biye da bayan nata, haba sai kace jela, wai kayan da ta yi niyar sakawa Hafsat din ta hanata, dama haka ne? Aikinta fa ta bata tsaro a biyata, to na me zata ringa shiga hurumin irin suturar da zata saka?

Maimakun ya tsawatar mata ya nuna mata hanata saka kayan nan damamu shi ne daidai ko dan gudun janyo hankalin mugayen samari kanta, sai ya shiga rarashinta da fada mata ta yi hakuri ya je ya samo wannan Bodyguard din ne dan a samu a kamo yaron da ya daga hannu ya mareta , da barazana kala kala, ko so take sai ya kona mata fuskar?

Jin maganar kona fuska ya sakata girgiza kai a hankali tana mai jin gabanta na dokawa, ina idan aka taba mata lafiyar fuska an gama da rayuwarta, ita dake takama da kyan fuskarta? Ita dake ji du duniya babu abinda ba zata iya sakawa ba dan gannin fuskarta ta kara kyau? Lale wannan saurayin ya aika, gashi tunda hakan ya faru da su tama daina ganninsa a makarantar ko a gida, du

16 / 54