Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   19 / 54

54K to 57K   out of 159.5K words

rufe bakinsa,
Ya rintse idannuwansa yana sauraron yanda zuciyarta ke dokawa,.....
Tabas jaruma ce, sai dai boyayiyar jaruma,

Da sauri ya yinkura ya cireta a jikinsa da niyar mikewa sai dai ta kara damke hannunsa da yannayin tashin hankali ta ce " ka daina yannayin masu kudi ko sangartatu ka gane rayuwarka ke hatsari ka duka, kar ka mike, domin ba.a ga wanda ya yi harbin nan ba!

Yannayin yanda ta yi magana murya a kausashe, da irin yanda ta bashi ordre ya saka shi yin dan tsai yana kallon fuskarta, kafin ya bi hannunta da kallo,

Da sauri ta cika hannun nasa tana mai kara tamke fuskarta , tana kallo ya mika hannu ya dauki jalabiyarsa, ya dan tsurawa Ni.ima ido sannan ya juya ya fice,

Kuka Ni.ima dake dukunkune waje daya ta fashe da shi tana mai bin hanyar da ya fice da kallo,
Shikenan , ta shigo rayuwar hadari, ashe da gaske dai neman ransa da du wani wanda ke tare da shi ake? Yanzu da an same shi, da shikenan har an mayar da ita karamar bazawara?

Da sauri Hafsat ta kawar da kallonta saga kan Ni.imar ta bi bayansa,

Dakinsa ya je, kai tsaye ta ratsa ta shiga inda ya shiga,

Tsayuwa ta ja ta yi dan ta gane wankama shi ya shiga,

Tana nan tsaye ya fito da tawul daure a kugunsa hakan ya saka ta kawar da dubanta daga wajensa,
Ikon Allah ita bata taba gannin bakin namiji mai cikar gashi a fatar jiki irin wannan ba, dama ba sai larabawa, buzaye , fulani, da dai sauransu keda irin wannan izgar gashin?

Hankali kwonce ya cire tawul din, ba tare da damuwar tana dakin ba, ya saka wandonsa na ciki, sannan ya dora wani wandon baki,

Rigarsa ya saka irin mai lafewa a jikin mutun din nan du tana kallon wajen da ba wajensa ba,

Bata tashi juyowa da sauri ba sai da ta ji wani kara yannayi na gyaran bindiga,

Da sauri ta juyo tana mai zaro ido tana kallon irin yanda ya saka kartushi a yar karamar bindiga ya ja ta ya gyarata da kyau sannan ya yi mata kyakyawan ajiya a kugunsa, irin ajiyar da idan ba karantun hakan aka koya maka ba , ba zaka taba iyawa ba,

Bata gama mamaki ba sai da ta ga ya dauko computernsa ya kunna ya ajiye saman table din dake dauke da turaruka shi kuwa ya dora hannunsa na hagu dake jimke saman table din, na daman kuwa ya shiga dadana computern kamar wanda shi ya kirkiri abinsa,

Bakinta da hancinta gaba daya a bude suke tana mai binsa da kallo, har ya gama nuno waje waje a jikin computern dake nuna ciki da wajen gidan, abin mamaki har benen da aka yi harbin daga shi gashinan waje waje radau ya fito a sama

Sai da ya yi wani recherche sannan ya dora wata hanya, wace ke nuna wani mutun tsaye yana ta waige waige bayansa goye da wata jaka sannan kunnensa yana waya da alama wayar a hanzarce yake yinta,

A tare suke kallon mutumen, kafin ya dago da dubansa ya dora saman kanta, irin yanda ta matse masa waje ita kanta bata kula ba, ta raja.a tunaninta da hankalinta kan mutumen nan,

Yannayin kallonsa ya shaida mata yana nufin wannan shi ne, dan haka da sauri ta je dora hannunta saman computern dan gannin hawa na nawa ne, da yannayin da zai kara tabatar mata da wajen,

Da sauri ya tare hannunta, domin gaba daya computern na anfani da emprinte din yatsutsansa ne, dora hannun wani na iya tayar da karan laluwar da ya saka gaba daya a cikin gidan,

Fitar mata da abinda ya tabata take son gani ya yi, yana mai dan kara yarda da yannayin aikinta , domin da wanda bai san aikinsa bane yana iya fita da gudu ya shaidawa mutane ai yana nan, a fantsama a yi ta hauka ba.a samu mutumen ba,

Maimakun ya ga ta fice da gudu sai ya ga ta kara dan abin hannunta ta ce" BS, suspect din mu na hawa na biyu wajen matatakala yana kokarin saukowa, sanye da bakin jeans da riga baka mai dogon hannu, fari ne kar bayansa dauke da jaka baka mai dauke da bindigar,
Yana waya, ku kula yana waya, kar ya jefar da wayar .....

Shiru ta yi ta tsurawa screen din ido , inda shi kuwa ya tsura mata ido yana kallonta,

A sakalce ya ce" ke, yo ke bakya zuwa ne? Kin wani sakani gaba kina kale min na.ura?

Bata daina kallon computern ba ta bashi amsa a takaice cewar" eh!

Murmushi ya yi ya juya ya zauna saman kujera ya daga hannayensa ya dora bayan sumar kansa ya dan daga kujerar daga gaba ya watsa kafafuwansa yana kai kawo yana duban yarinyar,
Bakinsa ya tabe , ya so ta bara masa dakin, shima ya fice ta inda zai gyara shi ko zai damki wannan wannan mai harbin, aman ta wani zauna , shi kuwa ba zai yarda saboda haka wannan yar yarinyar ta gane menene aikinsa har ta falasa shi ba!


A hargitse mutumen yake doka waya wa wanda ya bashi wannan mission din,
Ana daga wayar aka ce da shi" ka tabatar ka yarda layin nan ko ka hadiye shi, sannan ka san yanda zaka kubuce masu, idan kuwa aka kama ka, ka san ko rayuwar wa ka saka a hatsari!



To fa........., shin za.a kama wannan mutumen kuwa?
Yaya tafiar wannan aiki tsakanin Hafsat da Abdul?
Ni.ima fa?
Bs Fa?


Na ji dadin comment din ku sosai wollah,
Ban bayar da amsa ba domin ban zauna ba,
Ina biye da ku kamar yanda kuke biye da ni makaranta *KUTKALE*

>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




3?? 5??




Ki zzo gare ni Hafsat,
Ya karashe yana mai dafe kansa da dukannin hannayensa kafin yake mikewa kuma da wani irin sauri

Fita ya yi ya nufi dakin da computersa ke girke,
Yana shiga ya kunna ya kamo ya shiga bi yana kallo daya bayan daya

Ba abinda ya gani sai duhu ridim , wato wanda ya dauki Hafsat ko waye ya san inda camerorin suke dan kuwa baki daya sai da aka rufe su aka hana gannin abinda zai wakana

Gaba daya Abdul ya fita a hayacinsa, du wani abinda zai tunkara dan gannin ya sameta, ya ganta ya duba , ya bincika aman babu, babu ita babu alamunta

A hankali ya ringa jin wani irin zazabi na son rufe shi, hakan ya saka shi neman magani ya hadiya kafin ya juyo inda ya tara gaba daya mutanen dake cikin gidan, wato du wanda ya kwana ya tashi a gidan nan in dai mutun ne dan adam yana halarce a tankamemen falon Abdul du suna zazaune kamar yanda ya umarta shi kuwa yana tsaye dafe da kansa, ciki kuwa harda matarsa ta sunna da kuma Furaira

Sai da ya gama saisaita kansa sannan ya shiga bin kowa da kallo,

Sai fa ya gama kare masu kallo kafin ya hadr hannayensa cikin wata murya mai nuna tsantsar tashin hankali ya ce" koma wanene a wannan waje, na roke shi da ya saketa ya kama ni,

Na yarda, ya gane menene lagona ya kuma dakan harbi a lokacin da nake barci,
Ina mai rokarsa, idan har da dan sauran imani da kuma sannin zai yi kwonciyar kabari ya sakar min ita ta yi tafiarta nesa da ni, nesa da hargitsin rayuwata,

Ya karashe yana mai kara bin su da kallo,
Gaba daya, yana iya cewa gaba daya sun nuna fuskar basu san abinda yake nufi ba, kai ko wa yake nufi gaba dayama, dan haka ya kara gyara tsayuwa ya ce" daya daga cikin ma.aikatan gidan nan aka dauke, wace ke gadina mai sunna Hafsat, mun wayi gari babu ita ba labarinta, ba kayanta sama ko kasa,
Sasauta muryarsa ya yi irin na wanda ke azabtuwa da lamarin ya dube su duba irin na neman agaji ya ce" shin , da wanda ya ga Hafsat?

Kallon kallo suke yiwa junna, aka dauke wata? Mai bashi tsaro? Aa, kuma? Hankali nan ya fara tashi, da yawa suka shiga mikewa ana mayar da su zaune, inda Ni.ima ta kure shi da kallo, Furaira ta dafe kunci cike da mamakin wannan gida, Muhammad kuwa ya karasa kusa da amininsa ya shiga tausar sa yana bashi hakuri

Abdul ya gyada kansa sannan ya ce" ban so mu shiga fannin neman juna ido rufe ba, ban so mu shiga fannin da zan fita farautar mai farautana ba, walahil azim idan ban kashe shi da hannuna ba sai dai karfin ikon Allah, *tunda ya yi gigin taba min ita* nima sai na taba shi!

Abdul na gama fadar haka ya juya ya shige dogon lungun daka iya kai shi dakinsa yana mai jin wata irin juwa na neman dibansa ta kayar

Da sauri Muhammad cike da tausayin aminin nasa ya dafa kafadarsa hakan ya saka Abdul rage saurin tafiar da yake

Muhammad ya ce" Abdul, menene kuma? Me ke damunka haka da yarinyar kuma? Eh tabas dole hankalinka zai tashi da wannan sabon lamarin, to aman sai na ga abin na taba ka sosai, ko da wani abu tsakaninka da ita ne?

Abdul ya tako da sauri inda Muhammad ke tsaye ya kama hannunsa da karfi kafin Muhammad ya ankara ya dora hannun daidai wajen zuciyarsa,
Sai da ya furzar da huci ya ce" ta bani tsaro fiye da tsaron kanta ne? Dalilin ta dauki harbina ne? Ta iya zama da ni ne? Ko dan na ga tausayina na zahirin gaskiya a fuskarta ne? Tun da abokin aikinta ya fado dakina gudun zuciyata ya ki komawa yanda yake da, kuma yana yi gabana na faduwa ne,
Muhammad, nawa suka kashe? Nawa suke son kara kashewa? Ni na san ba son kashe ni suke yi ba, dan walahi da son kashe ni suke son yi na san da tuni sun cin min, Muhammad so suke su haukata ni? So suke na zama dan gidan su? Ko takarduna suke bukata? basu da wasa Muhammad, basu da wasa......


Ya karashe yana mai dora hannunsa ya share zufar da ta zubo masa

Muhammad dake kallon sa da yannayin tsoron yannayinsa ya ce" Abdul, soyaya kake da ita ko kwonci?

Abdul ya saki hannunsa ya ce" ba zaka fahimta ba,
Ita din ba zata kwonta da dan iska ba, bata taba yarda na rike hannunta a yannayin lafia ba bale har a zarfe wani waje da ita ba,

Shiru ya yi yana kallon kasa , sai kuma ya yi murmushi ya ce" so? Soyaya? Ina na ga halin yin soyaya ni? Ta ina zan soma? Ko daya , ba wannan wasan tsakanina da ita, soyaya suke da mai gidan su, wato BS

Ya karashe yana mai duban gefensa sannan ya saki murmushi ya daki kirjin Muhammad ya ce" zan iya hakurin rashin da aka rigaya akai min, bana jin zan kuma iya rintsa ido idan bamu yi fada yau ba

Nan ya bar Muhammad tsaye ya shige ya saka suturar kirki ya fito ya haye mashin ya bar gidan

Wasa wasa haka ake neman Hafsat tamkar ana neman zinari, ba inda basa dubawa, ba wanda ke zaune, du wanda ke gidan nan hankalinsa a tashe, GN da kansa ya tako ya zo ya kuma bada gudunmuwar neman Hafsat,

Abdul du ya wani firgice, harda lokacin da Muhammad ya tirke shi kan wai me yake haka? Ya fita lokacin da ya yi niya ba tare da an san fitarsa ba , a yi ta nemansa a rasa, baya tsoron masu farautarsa su samu galaba a kansa, baya gudun wani mugun abin ya same shi,?
Sai kawai ya karewa Muhammad kallo ya ce" da sun kasheta, da sun kawo gawarta kamar yanda suka saba, tana raye, yau kwananta hudu tana raye a hannun makiyana

Muhammad ya ce" ka tabata makiyan naka suka dauketa? Yarinyar da ta saba guduwa abinta ta yi tafiarta? Yau aka fara tsayuwa nemanta? Shaidar basu kasheta ba zai nuna maka cewa kawai ta yi tafiarta ne

Abdul ya kare masa kallo kawai ya sa kai ya barshi wajen tsaye

Yau an tashi lahadi, kwanan hafsat biyar kennan rabonta da gidan Abdul, ko yau tsaye ya kwana yana kaiwa Allah kukansa

Safiya na yi Ni.ima ta fara shigo masa daki, cikin shiga ta abaya a jikinta
Waje ta samu ya zauna bayan ta gaisar da shi tana kallon sa,
Sai da ya shafa fatihar azkhar dinsa ya kai dubansa wajenta sannan ya amsa gaisuwar tata ,
Yana kallonta ta ce" me ke faruwa haka ne? Kwana biyar kennan baka waiwayi inda nake ba, baka neme ni a komai ba, wani abin ne?

Tsuru ya yi yana kallonta cike da mamaki, kai kwanansa biyar bai nemi mace ba? Ikon Allah, dama akoy damuwar da zata gigita wannan bukatar har ta daina hayo masa a lokacin da ta yi niya?

Yawun bakinsa ya hadiya kafin ya yi mata nuni da ba komai

Kukan dake cin ranta ta hadiye sannan ta mike da niyar yi masa salama,
Har ta fara tafia ta kuma dawo ta duka tana kallon zara zaran yatsutsan kafafuwansa masu dauke da gashi baki sidik sun kwonta luf luf a yatsar ta ce" Abdul, ina son ka, sonka ya saka ni makancewa na bi ka, bani da jiyar gudun ka komai wuya Abdul, kar ka juyan baya dan kuwa a irin take take da kuma yannayinka da na karanta na girgiza na kasa baci, ni ban hanaka kara aure ba, dan kuwa ina son abinda kake so

Tana gamawa ta mike ta fice a dakin, inda Abdul ya bita da kallo a wajen a zaune tamkar mutun mutuni

Mikewa ya yi ya shiga wanka ,
Yana fitowa ya saka manyan kaya harda hirami saman kansa ya fito ya nufi dakin Ni.ima

A lokacin da ya shiga tana kwonce saman bed tana ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????aikin, wato kuka

A hankali ya karasa inda take da irin kwonciyar da ta yi ya saka hannunsa ya dagota zaune,

Ido ya dan tsura mata kafin ya ce" ba kyau kwonciya saman ciki,

Kanta ta gyada tana kallonsa tamkar ta dauke abinta ta mayar cikin cikinta ko zata ji sasaucin zafin kaunar da kishinsa da take

Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" kin san wani abu? Kyautatawa na saka so koda babu shi,
Ki lalubi sauran kyautatawar zaman aure, ki rike a hannun ki, ina mai baki albishir din tabas zan maki hira

Shiru ya yi cikin jan aji da jan maganar da ya yi sannan ya ce" ban san me yasa kowa ke gannin nuna damuwata wa batar yarinyar da ta damu da ni *So ne*, shi dama ba.a shakuwa sai soyaya? Na shaku da ita, ina walwala da ita, ta iya hira da ni
Wannan shi ne kawai tsakanina da ita,

Yana gama fada ya mike ya mikar da Ni.ima dake jin wani irin kaunarsa da kara shiga ranta da yake da irin yanda yannayin jan ajinsa da kwaliyarsa ke kasheta ,
Cikin yannayin nutsuwa ya kai lalausan lebensa wajen goshinta ya mana mata kiss, sannan a hankali ya ce" Allah ya maki albarka

Bai tsaya ya kuma kara wani zama ba ya fice a dakin ya fice tare da masu bashi tsaro ba tare da ya fada masu ga inda zasu je ba, haka kuma bai yiwa Muhammad salama ba suka dauki hanya cikin tukin garari kamar yanda suka saba har suka dangana da aeroport

Jirgi na daukan su sai da ya kawo su Niger, ya sauka a Niamey

Suna sauka wasu motocin suka shiga wa.inda BS ua tanada ,

Tafia suka yi mai tsyain gaske, dan a kadan sun yi awa daya da minti talatin sunna tafe a cikin banban birnin kafin su karaso anguwar

A lokacin da suka karaso masalacin da akai masa kwatance da shi ya saka su karasawa direct har kofar tankamemen gidan

A lokacin da Abdul ya fito ya yi tsaye yana bin anguwar da kallo haka kawai murmushi ya kubce masa,

Salamar da ta doki dodon kunnensa ta saka shi saurin juyowa,

Yau gashi ga kamilin datijon, datijon da yake jin muryar sa a waya,

A lokacin da malan ya karaso inda Abdul ke tsaye kasa tsayawa kikam ya yi a gabansa kamar yanda ya saba, dan kuwa wani irin ni.imtacen kanshi ne yake bazawa gashi cikin wata farar shada an yi mata baban dinki gari da yar ciki, kansa da hula da carbinsa madaidaici a hannunsa mai kyan gaske, sai walwali yake na annuri yana karawa

Gaba daya Abdul ya kai kasa dan gaisar da Malan, hakan ya sa sauranma zuba masa ido da mamaki, dan basu taba gannin haka ba, du girmanka har sai ya wani karkace zai maka gaisuwar raini sai gashi yau ya dukawa wani datijo

Malan kam da ido ya bi shi yana murmushi, sai da ya amsa gaisuwarsa sannan ya mika masa hannu ya taso su kai musabaha ta kirki kafin Malan ya ce"


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA

19 / 54