Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   21 / 54

60K to 63K   out of 159.5K words

ya dan saki wani dan karamin murmushi ya sakata cikin jikinsa ya bata kyakyawar runguma

Ajiyar zuciya ta sauke ta yi luf a kirjinsa tana shakar kanshin turaransa mai dadin gaske,

Bakinsa ya kai daidai kunnenta, wanda du bawan da ya ga haka zai dauka wani kalaman soyaya ne yake shirin rataba mata dan har dan rausayawa kadan yake da ita a cikin kirjinsa

A hankali ya ce" me kika zo yi gidana ne Bahija?

Bahija da ta lumshe ido tana jin wani irin mugun kaunarsa a ranta a hankali ta amsa shi da" na yi missing dinka ne, ka yi hakuri

Abdul ya dan saki murmushi ya ce" kin min laifi ne?

Kanta take gyadawa a hankali a jikinsa sannan ta ce" ban gujeka da son raina ba, na gudu ne dan tsoro Abdul Jabar

Abdul ya lumshe idannuwansa irin kalamanta sun masa dadin nan, sannan ya ce" ba laifi, *Bahija, ni Abdul Jabar mijinki, na tsinke igiyoyin auren da aka daura min da ke saki uku bisa dalilina na bin maza da kike, daga yanzu idan kika samu miji zaki iya aure, ban lamunce maki zaman minti daya a gidana ba, sannan idan na sake ki abu daya zai hana ni damun rayuwarki, ina nufin bin rayuwarki na tagayara ki shi ne ki mana min kiss a kuncina ki juya da niyar kin tafi ki dawo, idan kika kuskure da nu kike magana!*


Gaba daya jikinta ne ya kwashi rawa, tana so ta dago da mugun firgicin da ya daketa sai dai ta kasa hakan ya sakata yin wani irin lakwas tana limshe idannuwanta da suka cicika da kwallah,

A hankali ta ce" Abdul,

Abdul ya ce" shuiiiiiiiiiiiiiiit


Idannuwanta ta lumshe ta kuma budewa ta ce" *ABDUL, MAKASHINKA NA TA...*

ABDUL ya kuma wani irin matseta a jikinsa ya kara cewa" i said .....Shuittttttttttttttt

A hankali ya sasauta rikon da ya yi mata ya saketa baki daya yana sakar mata murmushi, sannan ya saka hannayensa ya share hawayenta a fili murya a dan dage ya ce" to meye na kukan? Ba gashi kin dawo ba? Ki je gidan zan zo
Ya karashe yana kashe mata ido daya

Murmushi ta kakaro itama ta matso jikinsa sosai ta yi dadage saman dogon takalmin dake kafarta ta mana masa kisss a kuncinsa kamar yanda ya umarta mata ta juya ta nufi motar da suka zo da ita cike da faduwar gaba da fatan Allah ya fidata lafia daga gidan

Hafsat dake tsaye a hankali ta jinginar da bayanta jikin garun wajen ta lumshe idannuwanta tana mai jin zuciyarta na wani irin dokawa tamkar zata ballo kirjinta ta fito


Abdul dake tsaye ya kuma mayar da dubansa dakin da aka kai yarinyar wace ta yi ikirarin ita yayarsa ce wato yar Abdul Basid, a hankali ya kara satar saitin tagar dakin Ni.ima, nan ya ga bata wajen, dubansa ya dan saci kallon dakin Muhammad,
Tsai ya tsayar da idannuwansa wajen, kallon wajen yake sosai inda kansa ya sara,
Dubansa ya kara maidawa dakin Huraira,

Juyawa ya yi ya koma cikin dakin inda su Hafsat suka bi bayansa gaba dayansu

Sai da ya kama kofar zai shiga ya juyo ya yafito Hafsat da hannunsa guda sannan ya juya ya shiga dakin

Hafsat sai da gabanta ya yanke ya wani irin faduwa kafin ta daga kafarta da kyar ta kawar da dubanta daga hararan da Hasana ta gala mata ta juya ta shiga dakin itama

A lokacin da ta shiga dakin yana zaune saman kujera ya janye jalabiyar nan sosai ta yi sama hakan ya bayanar da cinyoyinsa fili cike da gargasar gashi kwonce lufluf a jikinsa, hannunsa dauke da waya da kuma irin abin sauraron nan dake bada damar a ji inda mutun yake din nan

Takunta ta kara daukakawa ta karasa inda yake zaune,

Bakinta ta buda da niyar yin magana sai dai saurin kallonta da ya yi , ta kuma nuna mata abin hannunsa ya sakata yin gum, haka kuma ta ki yin wani motsin da zai saka a gane ko da mutun ko babu

Wayar dake hannunsa ya mika mata
Tana dubawa ta ga message ne rubuce saman screen din kamar haka " meye dalilin ki, una son sannin hujarki na cewa ba Abdul basid ke neman rayuwana ba,

Sai da ta kalli fuskarsa sannan ta saki murmushi hadi da ajiyar zuciya,
Waje ta samu ta zauna ta rubuta masa message kamar haka" *SHI NE DA KANSA YA FADA MIN*

Cikin sauri ya yi mata typing din cewa" ya dauki shekaru yana zaune da Ummih cikin karya da ha.inci, ina son sannin a matsayin girman aikin ki, kin yarda da maganar da ya fada ne?

Da sauri ta gyada kanta a lokacin da ta karanta tana kallon cikin idannueansa

Shima wani irin tsai ya yi ya zubawa kwayar idannuwanta ido,
Su kansu basu san sun jima sunna kallon cikin idon juna ba har sai da ta ji idannuwanta na neman bushewa da ruwan cikin ido ya sakata lumshe idannuwanta tare da dan gumtse bakinta kadan

Hannunsa ya dora saman screen din ya fara typing din message kamar haka" *kina da kyau Hafsat, ina sha.awar kasancewa a haka da ke*

Hannunsa ya tsurawa ido gannin yana ta rawa rawa , a hankali ya shiga bin harufan daya bayan daya da kallo kafin ya saka hannunsa ya shiga gogewa cikin sauri,
Sai da ya gama gogewar ya kuma kallonta ya ga ta kawar da kallonta kwata kwata daga kansama, haka kawai ya ji ba dadi, ta daina kallonsa dan me?

Message ya rubuta cewa " *Budurwar BS, na kara shiga duhu, tsohuwar matata ta dauko kalmar cewa Makashina na tare da ni, hakan na iya nufin ke ce, bs ne, Mubarack ne, Hasana ce, Ni.ima ce, bakuwar da ta zo yanzu ce, ko cikin sojojin dake gadin gidana?*

Da maimaita maganar ya fi a kirga sannan ta dago ta dube shi,

Mayar da yatsunta ta yi , jiki a mace ta saka" *INA TA JE NE? A ZANEN DA KA YI KA MANTA MUHAMMAD.*

da sauri ya dago ya dubeta, mikewa ya yi ya nufi bayi da sauri ya nitsa abin cikin ruwan wanka hakan ya saka ya daina aiki, fitowa ya yi ya yi tsaye gaban Hafsat yana kallonta tana kallonsa,

Sai da ya hadiyi wani irin yawu ya ce" kina tunanin, Muhammad, dan uwana, yaron da muka girma tare, muka yi karatu tare, muke kwana muke tashi tare, zai nemi dukan wannan lamari da ni ne Hafsat?

Hafsat ta girgiza kai tana kallonsa sannan ta ce" ban ce ba, na ga kana zane ne ya saka ni tina maka sunnansa dan kar ka maanta kowa,

Abdul ya gyada kai yana kallonta , dan sam bai karanci abinda take nufin nan da gaske bane, dan haka ya dan kankance idannuwansa yana kallonta

Murmushi ta sakar masa sannan ta dan matso kadan kusa da shi ta ce" *ka bani dama mana, dan Allah ka bani dama na shiga cikin lamarin, ina son binciken nan a kusa da ku, ina son binciken kowa ciki harda ni kaina*


Fuskarta ya karewa kallo yana jin yanda wata irin zufa ke son keto.masa, tamkar wanda ya yi gudu,

A hankali ya kai dubansa wajen kafadarta inda aka harbeta,

Hannunsa ya kai da niyar taba wajen sai dai tuna cewar hakan na iya bata mata rai ya saka shi jimke hannunsa a hankali ya tsura mata ido,

Hannunsa dai ya kuma dagawa ya kai wajen goshinta ya dan dora yatsar wajen gashin gaban goshin da ya yi luf luf da shi a hankali ya fan shafa shi sai kuma ya janye hannunsa,

Tsura mata ido ya yi yana kallon yanda take kallonsa tana jira ya bata amanar shiga dumu dumu cikin harkar hargitsin dake tare da rayuwarsa,
A hankali, cikin wata irin murya ya ce" wanda kika yi na jiya da shekaran jiya, ban so ba,
Sai dai na yafe maki Hafsat,
Ifan kika kuma saka kanki cikin wannan lamarin, Ba zan iya yafe maki ba Hafsat,
Ba zan iya kuma shakar numfashi ba idan har ya kasance wani abu ya same ki,

Idannuwanta da ta lumshe tana kallon cikin idonsa ne ya saka shi cewa" ba zan iya kuma walwalaba idan har wani abu ya kuma samun wani ta dalilina ba ke kadai ba Hafsat!

Hafsat ba zan iya jura ba a ce wa......

Ihun da suka jiyo daga tsakar gidan ne ya saka su gaba daya kallon kofar,

Da wani irin sauri ya daga kafarsa da niyar zuwa hakan ya yi daidai da itama ta damko hannunsa tana girgiza masa kai ta ce"""""""""


Comment jama.ata na tuba>?#?>?#?>?#?


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 5??

*wannan nvl na kudi ne, idan kin biya kin shiga na roki alfarmar dan girman Allah ba dan ni ba kar ki fitar min da shi ki yi hakurin har na gama shi sai ki fitar da abinki ki yi yanda kike so da shi bani da matsala da hakan, dan Allah idan kin san dan fitina, ko dan ki wulakanta min kika shigo ki min magana pc daga ni sai ke na biya ki kudinki wato naira 200 ta hanyar accnt din ki ko kati, dan alfarmar soyayarku da annabi muhammad kar ku fitar min da novel, ku bari na gama shi, in sha Allah ba mai tsayin da zai saka ku gajiya da jira bane=?O?


Sai da ya fara tafia ya nufi wajen gadon da Abdul.ke kwonce kafin ya juyo cikin tsawa ya dubi Hasana ya ce" zaki je ki saka matarnan ta daina mana ihun batancii a wajen nan ko sai na wanka maki marin da zai dauke jin ki ne BD?

Da sauri ta kame masa sannan ta juya ta fice dan fitar da Ni.ima a wajen nan

Bayan fitarta tsayuwa ya yi gabansu yana dubansu daya bayan daya,

Shi bai ga wani allamu na rashin gaskiya a tatare da su ba, aman du da haka sai ya ce" bafa za.a shiga ambulance da shi ba, zan tuka motarsa na kai shi asibitin naku , ku ban kwatance

Muhammad ya dafe kansa cike da takaicin wannan lamari ya ce" wani irin kai zaka kai shi? Kai a wa? Ni na fi kusanci da shi a wannan lokacin, rayuwarsa ita ta fi min komai mahinmanci , dan me zaka ce kai zaka fita da shi? Bayan ka ji bayanin likita cewa dole sai an bashi taimakon oxcygene a tsayin tafiarsa?

Kansa ya girgiza ya matso sosai kusan Muhammad ya dube shi ya ce" kai ka san ko waye shi, nima na san hakan, an bashi horon nitsewa cikin ruwa tsayin minti ashirin tare da rike numfashinsa, ya yi kuma ya ci,
An saka shi a rami an rufe irin na gawa sai dai fa ransa kuma a zaune, sannan ramin mai dan fadi ne aman ba oxygene, haka yana shakar oxygene dinsa har ya kare a hankali ya silale ya tafi duniyar suma

Kai ka san me da me da me ya gani wanda mu fada mana ne ake cewar idan muna son zama irinsa sai mun je mun ga wannan rayuwa,
*Mutuwa* ina jin ba yau ba yake gwadata, idan har ya mutu a yanzu a hannuna, toh fa ba wanda ya isa ya tado shi, aman ba zan yarda a fita da shi a wancen motar mai kuka ba! A matsayin na shugaban masu bashi tsaro ina da dama da ikon yanda za.a yi da shi, kai harta likitan da zai ganshi ina da damar zaba, dan haka na yanke hukunci!

Muhammad ya girgiza kansa cike da tashin hankali ya ce" to sai dai idan da ni zamu je, ba zan yarda a yi wasa da rayuwarsa ba, !


BS ya daga kafadunsa sannan ya juya wajen da Abdul yake, sai da ya saki wani nishi dan walahi a dazuma da bai idasa fita a hayacinsa ba sqi da suka kama sannan suka iya shigowa da shi, to ina da yanzu da ya gama ficewa a hayacinsa lumfashi kawai yake ja aman jikinsa du ya mace sai bin mutane yake da ido kuri .......Abdul an ji jiki.

gannin docter bai ce komai ba ya daka shi janyo gadon mararsa lafian ya kama Abdul ya dora shi da kyar ya gyara kafafuwansa ya kare masu kallo ya ce" kar wanda ya fito sai nan da minti biyar, Muhammad ka same ni cikin motar

Shi kam Muhammad bai san me zai ce ba, hankalinsa du ya dagu, kar dai a je likitan nan da ya kirawo mai cutarwa wa lafiar Abdul ne? To aman ai likitan mahaifin Abdul din ne, wannan shi ya ci gaba da duba lafiar Ummih wato mahaifiyar Abdul har ta rasu, shi bai san wani likita dabana da zai iya kirawowa Abdul, aman gashi yana tsaye sai wani abu ke faruwa,
Dubansa ya kai wajen Hafsat dake summe, hakan ya saka shi bufar frijj neman ruwa ya watsa mata ko zata dawo hayacinta ta fada masa abinda ke faruwa? Gasbi BS ya fice tun tuni, docter kuwa sai duba agogo yake


BS na fita da gadon nan maimakun ya bi hanyar da zata fitar da shi tsai sai kawai ya juya ya canza hanya ya shige ta kicin ya tafi,
Ya jima yana ta fama dan hanyar sai da ya yi da gaske gadon ya ratsa domin kuwa dan lungu ne ke raba shi da hanyar ya shige ya samu ya fitar da gadon ya isa har bakin titi ta wata hanyar daban ba hanyar da kowa ka iya ganninsa ba sannan ya dakata ya samu ya ciciba Abdul ya riko kafadunsa ya sauke shi a saman gadon ya dora hannunsa na dama saman kafadarsa ya talabe tsatsonsa sannan ya shiga dan tafia da shi a haka har ya kawo bakin titin da ya tsayar da taxi ya shige ya umarce shi da fara biyawa islamic kems kafin yaa sada shi da dan karamin asibiti habo dan uwansa ke yi

Shi dai dan taxi tukinsa ya yi normal, yana gannin yanda BS ke ta faman gyara Abdul, aman bai wani yi jayaya da hakan ba har ya kai shi bakin kasuwa,

Bs kam da kokari kara ciciba Abdul ya yi ya je ya siyo abin bukatarsa ya dawo cikin motar da shi, sai sakin nishi yake, haka kuma kafadunsa jinsu yake wani iri, sun kage tun ba.a je ko.ina ba

Tuka shi ya yi ya sada shi da asibitin gwamnati , suna zuwa kudin da BS ya bashi ya bashi mamaki, domin kuwa a aljihun Abdul na wandon dake jikinsa dan gajere ya laluba cikin sa.a ya samu kudinmu jika goma goma ya ciri daya ya mikawa dan taxi ya fice ba tare da ya kula da canjinsa da dan taxin ke kokarin bashi shi dai yana tunanin me Abdul zai yi da kudi ya saka su a kanfai? Kanfai mana har cikin karamin wando?

Sunna shiga BS ya zarce Urgence,
Yana zuwa ya ajiye Abdul nan dandar kasa ya je da sauri wsjen likitocin cikin yannayin hadewar fuska ya tambayi docter
Kun san halayar manyan, sai sukai kuri sunna kallonsa, wasu har suna kokarin zilewa dan kiran masu tsaron kofa a fitar da shi dan sam yannayinsa ya basu tsoro, tun bama kansa dake aske tall yake kyali tamkar wanda ya shirbine shi da man gyada na goma

Ciro baje dinsa ya yi ya mikawa wanda da alama shi ne responsable dinsu yana kokarin karantawa ya shiga kara masa haske da nuna Abdul da fada masu cewar yana daf da mutuwa!


Da sauri ya mike ya shiga fada masu abubuwan da zasu kawo , shi kuwa ya saka aka kawo gadon asibiti mutun hudu suka ciciba Abdul suka dora saman gadon aka tura shi aka shiga dakin aiki da shi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? inda BS ya kasa ya tsare a cikin dakin, su kuwa suka kasa fitar da shi dan kuwa shima a kan aikinsa yake

Gannin mutumen dan gajere fari na kokarin fara duba Abdul BS ya matso ya ce" bawan Allah bafa kai zaka duba shi ba, docter nace a kira min

Hannayensa ya dan watsa kafin ya ce" ai ni din ne, ban yi magana bane dan ana iya zuwa nemana dan cutarwa,

BS ya dubi gaban rigarsa, sai yanzuma ya ga rubutun sunnan mutumen sannan ya ja baya yana jin haushin tsoro irin na mutumen, to sai me? Idan an zo nemanka ba sai ka kwaci kanka ba?

Du abinda suka san zasu yi sun masa,

Ya kawo hankali, ya dawo daga duniyar suman, aman wata irin juwa yake tamkar zai koma duniyar summan domin komai kankantar jinni ya fita daga jikin mutun sai ya juyaka bale fa Abdul ya zubar da jinni sosai, dan kuwa jikinsa ba riga haka BD ya bi duniyar nan da shi gaban kirjinsa du abin jinnin ne, shi kansa BS din jikinsa ya taba bale kuma Abdul din

Sun shiga rudu, dan har haskawa aka yi aka duba ba.a ga wani lamarin da zai mayar da jijiyar wajenta,

Docten ne ya dubi BS ya ce" daman yana irin wannan abin ne? Me kuke masa ya tsaya? Wani abin ake saka masa bayan wa.inda muka yi? Ana iya bamu traitement din sai

21 / 54