Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   34 / 54

99K to 102K   out of 159.5K words

muryar Abdul ta dawo da shi cewa" Aba,
Dama amini na zama makiyi? Aba dama alkhairi na jazawa mutun kiyaya? Aba, shin a gabanan zan iya yarda da wani dan adam komai kusancina da shi kuwa?

Aba ashe aminina ya kashe min kanwata? Ya kashe min mahaifiyata? Ya kashe mutanen dake tare da ni? Du dan ya kai ni ga ciwon hauka kafin na bar duniya? Aba........zuciyata sai nake jin tamkar ba zata kuma gannin haske ba, ji nake tamkar na gama da farin ciki, idannuwana na gannin kowa da fuska biyu, *ABA, shin me zai saka na yarda da kai kanka?*





Halin rudani na rudar da zukatanmu a likacin da wani lamari ya dake mu=??, sauki na Allah ne


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4?? 7??





Jikinta ne ya dauki rawa gannin mamanta ta nufo motar,
Kanta ta sada da sauri ta shiga murza yatsutsanta, ta saka a ranta ne tata ta kare, sai da ta yi mata nasiha, sannan tun da ta dawo kulun famanta nuna mata ta karyata abinda ake fadi a gidansu da kuma anguwarsu

Shirun da ta ji ne ya sakata dan dago da kanta,
Tsai ta tsayar da dubanta ga al.ajabin da take hange,
Malan ne da amininsa ladan, da kuma mama a gefe tana amsa gaisuwar Abdul da ya duka har kasa kansa a kas yana gaisheta,
Malan ne da kansa ya yi kiranta ta fito su gaisa da mutumen da Hafsat ta yiwa aiki

Ita kanta tamkar wani sirikinta sai kara gyara zumbulelen hijabin jikinta take tana amsa masa cikin nutsuwa inda kunyarsa ta lulubeta dan ba karya abdul akoy cika ido da siffar kamilin mutun

Sai da suka gama gaisawar Mama ta yi ciki kusa da yan uwanta, nan malan ya fara shiga ya ga kowace da shigar kamala ba wace ta yi shigar da zai ji kunyar nunata dan haka ya kara yiwa Abdallah iso ya shige suka shiga saman malan
Gannin har an fito a sallar magariba sun kasa bata waje ko zata fito ya sakata ziro kafarta a hankali ta fita a motar da lipton din malan sai yar pos dinta

Bata kula kowa ba ta shige bangarenta ta nufi dakinta

Tana shiga ta fada bayi ta zauna ta shiga kuka, ita kanta bata san kukan me take ba, mari dai a gidan duniya ba kalar wanda bata sha ba, ta sha dukan balakima bare wani mari can?

Sai da ta ji muryarta na shakewa sannan ta sasauta ta kunna ruwa ta wanke fuskarta ta dauro alwallah ta fito a dakin

Sallah ta tayar cikin nutsuwa ta gabatar sannan ta mike saman bed ta kashe wayarta gaba daya ta shiga neman hutu

Abdul kam sai da matan malan suka hau da kansu daya bayan daya suka gaisa, ya gabatar da shi a matsayin wanda Hafsat ke gidansu
Ido ido suka ringa yi kowace na ciki na ciki har malan ya salame su suka fito a dakin

Sai da Abdul ya kusan raba dare dan kuwa sun jima da malan suna tataunawa kan lamarin duniya, kafin ya mike ya sauko bayan sun yi salama da malan ya roki da ya yi zamansa ba sai ya raka shi ba

A lokacin da ya sauko ya dan jima yana kallon kofar da ya tabata ita ce ta mama, kuma a ciki dakin Hafsat yake,

Sai da ya ga daren na kara yi sannan ya juya ya fice a gidan ya tarda direban da ya kawo masa wata motar har ya fara baci bawan Allah ya tashe shi suka tafi

Ko da suka karasa gida wanka kawai ya yi, ya gabatar da shafa.i da wuturi, ya gama adu.o.insa, har ya zo shafawa ya lumshe idannuwansa, wata adu.ar ya yi kamar haka" ya Allah, ka kare ni da mugayen mutane, Allah ka bani amini mai tsoronka wanda zan shiga aljanah dalilin zumuntar mu, Allah ka raba ni da mugayen mutane

Bugun zuciyarsa ne ya ji na neman canzawa sakamakon kokarin tuno irin abinda ya faru tsakaninsa da Muhammad da kuma irin hukuncin da ya yi masa, da sauri ya dauki carbinsa ya shiga jan salatin annabi *MUHAMAD SALALAHU ALAIHI WA SALAM*, yi yake ba kakautawa, a hankali ya ringa jin nutsuwa na ratsa masa zuciyarsa har ya nemi damuwarsa ya rasa
Bai tashi a wajen ba sai da ya rokawa malan gamawa da duniya lafia, domin shi ya bashi sirrin salatin annabi, da ba dan ya riki sirrin nan ba da bai san idan ransa ya baci ina zai tsoma ransa ya ji dadi ba

Sai da ya kwonta saman bed dinsa, yana rintse ido ya ji passsssss
Karar marin da ya sakar mata,
Da sauri ya buda idannuwan nasa,
Hannunsa ya daga yana kallo, hannunsa na dama wanda da shi ya mareta,
A hankali ya mayar da hannun ya ajiye a fili ya ce" aman me ke damun zuciyarki Hafsana? Me ya sa kika zuran ido baki ce da ni komai ba? Na mare ki, na yi maki ihu a kai duka kina kallona baki bani amsa daidai da ni ba? Da gaske sunna mugun takura ki a gidan nan? In dai dalilinsu kike cikin yannayi na rashin walwala zan saka a yi maza a yi aurenki ko na maido ki nan a matsayin bodyguard dina har a maki aure ki yi tafiarki gidanki,

Wayarsa ya dauko yana kallo, sunnan BS dake cikin wayar ya kurawa ido,
Ya so ya rubuta masa message sai kuma ya fasa,
Juyawa ya yi ya gyara kwonciyarsa da niyar idan ya kai gobe lafia zai nemi BS, zasu yi da wajewa idan ya auri Hafsat ya wulakanta masa ita walahi sai ya yi shara.a da shi! Dan rainin hankalin banza dan rainin hankalin wofi, dalilin wulakantata da Muhamad ya yi ba zai yarda kowani kato ya wulakantata a gidan aure ba, idan da hali zai saka camera dan gannin irin zaman da suke dan kar ya je ana cutarta a yanda ta zama lusarar nan yanzu ta rufe ta kasa fadi!!!!!!!!! (Sannu baba)


Sai da mama ta gama salolinta ta shiga dakin Hafsat, nan ta tarar da ita ta yi wani kwonci a takure tana baci sai sauke ajiyar zuciya take

A hankali ta shafi gefen fuskarya da ya tasa kadan, ya kumbura irin an daketan nan, kura mata ido ta yi cike da tausayawa , ko wa ya dake ta? Me ya hada su?

Ledar Boutik din da ta je ta buda ta ga Lipton din da ta siyo,
Murmushi ta yi ta mayar mata da kayanta ta mike ta fita a dakin tana mai yi mata fatan alkhairi a kasan zuciyarta


Bayan Hafsat ta yi sallar asuba wanka ta kuma yi ta canza kayan jikinta na baci, ta saka hijab dinta na sallah ta dauki ledar lipton din malan da canjin jika biyun da ya bata na taxi ta fito

Daya daya cikin yaran gidansu ke wulgawa jifa jifa domin safiya ce karfe bakwai da wani abu gashi ba makaranta,
Da ido suke binta, ba wanda ya gaisheta cikinsu dan kuwa iyayensu sun fada masu daga yawon banza ta dawo kar wanda ya girmamata, gashi dama ta girma fiye da yanda malan ke barin yayansa mata su kai bai masu aure ba, hakan ya sa du suke mata wani gani gani sannan suka yarda da maganar iyayensu

A hankali ta karasa kofar dakin mahaifinta, hannunta ta saka ta tura kofar da salama a bakinta
Tana shiga ta ringa jin maganar hajia, uwar gida kennan ran gida , matar malan ta farko tana magana kamar haka" aman malan yaya zaka ringa nuna rashin adalci a tsakanin yayanka kiri kiri? Nan Zakari tafia ce ya yi neman kudi dan ka hana shi da ya dawo ba irin abinda bai gani ba da ni kansa mahaifiyarsa,
Aman malan ita yar gwal din shekararta nawa bata gida ba aure akai mata ba ba karatu aka kaita ba ba dawan makaranta aka kaita ba? Rana tsaka a dawo da ita cikin yayanmu kananu a shigo da ita cikin gida gaban kowa a ringa yi mata oyoyo ana murnar dawowarta ana rungumarta ana nuna mata farin cikin ganninta , malan baka tsawata ba, baka tara yayanmu baki daya ka yi fada ka hukuntata ba, baka nuna wani bacin ranka ba, hasalima kilaceta ka yi ka yi mata dinkuna, bata yi mana aikin fari bare na baki a cikin gida tana nade a daki tana cin abinda ta yi muradi, tana shan abinda ta ga dama, karshe malan da girmanta shekara kusan ashirin da biyu har damar ta zauna tanai maka zance a cikin gidanka da wani kato wanda ba tsaresu ake bare a san me suke yi ko suke cewa ba, malan a jiya a kawo mana wani gabjejen katon da bashi da fara.a ya zo ya tsaya a gabanmu kikam yana harararmu wai a gidansu ta zauna, a fadi haka a gaban yayanmu warwararu da kananu, malan ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kwakwaluwar yara me ake so su dauka? Me zai hana su suma gobe su tafka tsiyar da ta tafka su kuma dawo mana gida kai tsaye? Koda yake su sun san ba yayan so bane ba zasu yi hakan ba, aman gaskiya malan korafinmu kawai a san abin yi, idan da hali a fitar da ita a kaita can wajen dangi har a yi mata aure, ko a maida ta gidan su yaron da ya zo jiyan muga idan shi iyayansa zasu aminta anai masu irin haka a cikin gida ba aure ba komai!

Malan dake zaune, tun da ya bata damar magana shiru ya yi yana sauraronta har ta gama,
A hankali ya shiga bin sauran matan da kallo, kowace na zaune kusa da ita da alama shawara aka yi na abinda za.a fada masa , sai aka baiwa wace ta fi kowace tsaurin ido da rashin tsoron zuciya ta fada masa,
Dubansa ya kai kan matarsa, mahaifiyar Hafsat, kanta a sade yake, ko daya ba.a gannin fuskarta bare a gane yannayin da take ciki, sai yatsutsanta da take ta murzawa tana karawa tamkar wa.inda take son canza masu kalar fatarsu dake jikin hannun nata,

Dubansa ya kara kaiwa kan matarsa, wace ita ce ya dace ta zama mai datako, mai tsawatarwa mai tausasa muryarta mai nasiha gare su da shi kansa, aman kananun sun turota ita ce yau ta buda baki, ta daga muryarta sama da tashi, ta gaigaya masa magangannu irin haka a kan *Uwa*, shi da yake rayuwa a takure , yana boye nuna soyayar mamansa a gaban yan uwanta dan a zauna lafia ashe bai tsita ba? Shi da yake nuna kowani da da ya haifa daya ne a wajensa ashe ba tsira ya yi ba? Me ya ragi yayansa da shi? Bukatunsu, tarbiya, ilimi, ko walwalarsa? Ba wada ya hana masu, kowane ya basu wadatace kuwa,
Me suke so da shi ne? So suke ya rufe Mamansa da duka kan laifin da bata aikata ba? Ko a kan zarginsu suke so su dawama harma suke ikirarin ya fitar da ita daga gidansa ? Mamansa? Mamansa ce suke so ya wulakanta haka?

Ajiyar zuciya ya sauke mai karfi wace ta saka mama dago da kanta a hankali ta saci kallonsa idannuwansa sun kada sun yi jajir, tausayinsa ne ta ji ya kama ta, haka kuma sai ta ji haushin Hafsat din, tun tana karama ake irin haka a kanta, a da yana da karfi da yarinta a yanzu da ya fara manyanta ma ba zai huta ba? A bar mata mijinta ya huta haka, in dai a kan Hafsat ne in sha Allah idan bata samu miji bama ita zata kaita inda ta kaita, in sha Allah zata samu ya yarje mata ta kaita nesa da gidan ko kowa zai kwontar da hankalinsa a kan kishin zamanta a gidan da suke, kallonta ta kawar, idannuwanta je suka sauka kan kwalin lipton din nasa da ta ajiye ta juya,
Gabanta ne ta ji ya fadi, kar dai a je ta ji? Dama akoyta sabkon zuwa wajensa su yi karatu kafin su yi ta hirar duniya, yakan yi mata labarai su sha dariya, yakan yi mata bayanin dukiyarsa , kai harma da shawara,

Kanta ta sada, sai kuma jin muryar malan ta yi ya ce"


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 4??



Cikin nutsuwa malan ya yi gyaran murya ya shiga labartawa mama duka kaf abubuwan da Abdul ya fada masa, da kuma gannin idonsa da ya yi, harma ya tina mata lokacin da ya zo ya fada mata a yau mamansa ta ziyarce shi, mamansa na raye dan kuwa a masalaci ya ji a jikinsa ita din ce

Idannuwanta cike da hawaye ta kai dubanta wajen da Hafsat ke zaune a saman cafet ta sada kanta sai zubar da hawaye take,
A hankali ta ce" Allah ya kara shiryar da ke, ya maki albarka, ya baki miji na gari

Hafsat ta dago kanta da sauri ta saka idannuwanta cikin na mahaifiyarta, gaba daya maman nata ta yi wani irin sanyi bata zaci zata zama haka ba, tana shashekar kuka ta ce" mama, uncle din Abdul aziz ne, shi ne ya kai ni gidan kason gagan yan daba dan kawai na mari matarsa, mama ba zan taba yafe masa ba, ya wulakanta ni, ya tozarta ni, ya kai ni gidan halaka wanda Allah kawai ya fitar da ni

Mama ce ta gala mata harara ta ce" ko komawa zaki yi ki kara daukan fansa?
*UNMIH* ba zan so ki koma irin rayuwarki ta da can baya ba, kin ga taurin kai, jayaya, masifa, raina maganar manya sun bada gudunmuwa wajen saka ki a wannan jarabawa, shiga gidan kaso na abin kunya bane dan kuwa kadarar bawa ne baka isa ka kauce masa ba, sai dai abin lura me kika koyo a can? Yaya kike son tafiar da rayuwarki a yanzu? Mace kike, rayuwarki kadan ce, kar ki yi tsamanin kyan nan naki zai yi ta karuwa ne, daidai da gashin kankin nan zai ringa ja baya a hankali a hankali ne har ya dawo kadan, fatar jikinki zata janye, idannuwanki zasu jeme, furfura zata yi maki salama idan har kin dace! Ki rufa bakin ki, babu rufin asirin da ya kai na kariyar da Allah ya baki, Allah ya baki kariya Unmih ke kin sani...nima na sani...nan gaba kowa zai sani, kar ki yi garajen da Allah zai barki ya ga yanda zaki yin! Tashi malama ki fice min a daki ga kys din dakinki an gyara , je ki zan neme ki!


Jiki a sabule ta mike ta karbi kys din dakin a hankali ta shiga takawa tana kuma waiwayen malan aman ga mamakinta bai daka tsawar kar a yi mata fada ba, saima kawar da kai da ya yi tamkar baya wajen
Bakinta ta zumburo ta daga kafa ta fice a dakin tana fadin lale malan ya daina son ta

Tana fita malan ya kurawa mama ido yana kallonta,

Kanta ta sada kafin take kamo dan yatsarta ta shiga dan ja,

Malan ya ce" to a huce a kaina mana da za.a saka min uwa gaba daga dawowarta a fara yi mata ihu ana fitar mata da ido? Ni madame me ya sa karfinki kike nuna shi a kan UWATA NE?

murmushi ta saki a hankali, ta dago da idannuwanta da sukai jajajir,
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta fashe masa da kuka marar sauti

Murmushi malan ya yi yana kallonta ya ce" menene na kukan kuma?

Sai da mama ta yi dan kukanta wanda tamkar na shagwaba kafin ta sasauta tana kallonsa ta ce" tsoro nake ji, du wannan rayuwar da Anmih ta gani bai saka ta daina fada ba, ji fa ita nan har tana gannin ramuwar da zata yi ta huce? Ramuwa

34 / 54