Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   24 / 54

69K to 72K   out of 159.5K words

kai lale da ba.a kyauta ba, da aurenta tana irin aikin nan?

Muryar malan ce ta katse masa tunani inda ya ce" sai dai yarin ya ki yin hakuri, da yake Allah bai yi ba sai zigar mutane ta yi tasiri a kansa ya haye ya zauna ya mayar min da Uwa bazawara

Wani murmushi ne Abdul ya sake saki sai kuma ya yi gagawar rufe bakin nasa ya daina murmushin, aman a ransa has??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????asowa yake inama inama tana nan aka fadi maganar nan, yana kuma nan, da zai mike ne ya kali tsakiyar idonta ya ce da ita" *kauriyata, bazawara!*

Wata zuciyar ce ta ce da shi" kai Abdul, tana fa iya baka kunya ta ki tankaka, ta yi tafiarta abinta ta bara maka wajen,

Sai wata ta kuma fadin" kai ina, ba zata iya ba, sai ta tsaya ta kama tsatso ta ce" *kai=?D?, ni ce Bazawarar? Ka daina bana so Abdellah*


Haka Abdul ya roki Alfarma wajen malan cewa, ya rike bakinsa, dan kuwa yana son koda Allah ya yi an ganta a wanketa a wajen gwamnati na irin wahalar rayuwar da ta gani har ta rayu a *KUTKALE*

malan sai da ya zabura ya saki hannun Abdul ya ce" bawan Allah, *KUTKALE?* gidan kason nan da ake fadi a gari,? Gidan yarin da sai ka giga ake kai ka? Me Uwata ta yi da zafi haka ta shiga gidan yarin nan da ake fada a cikin gari? Wanda baki da yawa ke fadin irin hatsarinsa? Wani irin rike mutunci neza.a iya yi a wajen da ba mai hanawa ko mai sakawa? Mai karfi shi ke mulki, ga Uwata yarinya? Wace kake nufi a tsare mutuncin?


Abdul ya sauke ajiyar zuciya yana kallon yanda datijon ke jefo masa tambayoyi, a ransa ya ce" ku ji fa, shi da ya dace ya yi ta murna, aman da yake ya shafi Mamansa du ya rikice abinsa, dan Haka Abdul ya ce" ai ina ga a yi murna kawai tunda ta fito a raye,

Jikin malan kam ya yi kalau da shi, a haka har Mama ta zo da kulolin abincin da aka dafa dan kuwa sun tarbi Abdul yanda ya kamata ya fado ranar aikinta ne, ita da kanta ta yi girkin ta hada komai ta shigo da zumbulelen hijabinta wanda ya rufe mata kafafuwanta ba.a ganninsu ko kadan sai fuskarta da hannunta

Gaisawa suka yi da Abdul cikin mutunci kafin ta juya ta tafi bayan ta ajiye komai da komai bata tsaya zubawa ba dan kuwa malan da kansa yake zubawa baya so matansa su tsaya wajen da ya yi baki , sam baya son matansa su kasance a wajen da maza ke wajen, hankalinsa baya kwonciya da hakan....................................................................................


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?



3?? 0??



*KU YI HAKURI DA PAGE DIN YAU DAN ALLAH, KU MIN UZURI, INA CIKIN SHIRIN TAFIA NE, KU MIN UZURI =?O??&?
@&>?&?
@&>?&?
@&, zan fanshi kaina in sha Allah ta hanyar sambado maku pages biyu zuwa gaba*





A lokacin da ya fito, ya fita a gidan a matsayin kuku mai dafa abinci,
Ta gaban hasanar kuwa ya bi ya fice, bata yi tunanin tun da ta zo bata ga wani mai dafa abinci ba, bata tsaya ta kula da kyau dan gannin ko waye ba, bata ga shigarsa dakinsa ba , aman ta zura ido ya fice ta gabanta da plat din abincin da ya dafawa kansa ya fice a falon

Hanyar baya ya sanda, wace ya kwashi minti talatin yana gadinsu har sai da sallah ta tayar da su ya fice a gidan

A lokacin da ya zo bakin gari tuni kusan karfe shida na yama ne, ba wani haske sosai sai na Allah, wato wata dan kuwa idan ka yanki cikin gari duhu ne sai fitilun da aka kukuna a gidajen mutane

Mashin din ya karewa kallo, sannan ya duba yar karamar wayarsa wace BS ke kiransa , ya samu numbersa ya privet ce a jiya da suka nemi Hafsat,
Tsaki ya ja, ya rasa ko ya gane baya nan ne ko me? Yana ta kiran wayar dai dan haka sai ya kasheta ya saka aljihunsa ya haye mashin din

Tuki yake na garari, wani irin gudu yake yana duba JPS din dake hannunsa sannan yana duba agogo ya mika hannunsa ya laluba yar karamar bindigarsa da ya sakawa abin hana a ji karan harbi ya mayar da hannun ya ci gaba da gudu tamkar zai tashi sama

Kai da ba dan muguwar wutar dake cin zuciyarsa ba da ya juya da wannan tafiar mai mahaukacin wahala dan kuwa wani rami da ya afka sai da mashin din ya yi cili da shi, Allah ya taimake shi kwakwaljewa ne kawai ya yi, haka ya mike ya tayar da mashin din ya kuma daukan hanya

A lokacin da GPS din ke nuna masa cewar ya zo wajen, a lokacin ya kashe babur din ya nemi waje ya ajiye shi da adu.ar Allah ya sa ya tardo shi, dan kuwa jejin nan ba za.a rasa barayi ba

A hankali yake tafe yana sandar wajen bakinsa dauke da adu.a, hannunsa kuwa dauke da yar karamar fitila ta haskawa mai duhun haske,

Wajen shiru, shiru ne gaba daya wajen a haka yake kara shiga cikin jejin yana mai baza kunne yana sauraron du wani motsi


Motsin da ya ji a bayansa ne ya saka shi dukewa cikin ciyayin dake wajen ya tsurawa wajen da ya ji motsin bayan ya dane hasken fitilar

A hankali mitsin ke kara matsowa kusansa, har ya kasance an matso sosai kusan shi

Ido ne ya zaro a lokacin da ya ga mai motsin,
Kai, me?

Mikewa ya yi da sauri ya fito ya karaso wajenta, wada itama motsin da ta ji ya sakata aniyar labewa

Hannunta ya damko ya juyo da ita da karfi , hakan ya sakata zazaro ido tare da jan a.uziya ta kurawa wanda ya damki hannunta ido da taimakon hasken watan da ya raba tsakiya ya haske wajen tar,
mutun mai sanye da wani gajetan wando da riga marar hannun kirki da hular kuku, sai dai kuma fuskar Abdul ne,

Gabanta ne ya fadi a lokacin da ya ce" ke, baki da hankali ne? Me ya kuma fitar da ke a wannan tsohon daren? Bayana kika biyo dama? Ke bakya gudun wannan jejin? Wai wa ya saka ki a sha.anin rayuwata ne da kike daukan irin wannan garajen?

Ajiyar zuciya ta sauke, dan kuwa ta yarda ba aljani nane ya yi kama da shi, shi din dai ne, kennan da ya fito nan ya yo? Au , kennan ya dilmiyar da ita ne? Haba gaske a lokacin da ta so bara masa dakin ya yi gagawar dawo da ita? Ikon Allah zuwa ya yi kennan ya kashe mutumen ko me? Wani haushinsa ne ta ji lokaci guda, shi kennan baya jin bari? Ba zai daina wannan banzan kudurin ba?

Hannunta ta yarfe wanda ya rike mata ta ce" ni ba kai na biyo ba malan, tafiata daban, kuma kar ka kuma rike min hannu, a kan aikina nake

Wani takaicinta ne shima ya ji ya rufe shi, wai aikinta, to ubanwa ya dauketa aiki irin wannan?
Haba sai yanzu ya gane kiran da BS ke masa, wato dan ya fada masa ne ta kara fita ko? Lale yanzu ya yarda da irin taurin kanta, yanzu ya yarda lamarinta sai ita, idan ba kasada ba , mace, ita daya kwal da ranta, ta tashi ta wani dadame da wani shegen wando ta daure gaban goshinta da wani dan siririn gyale ta dunkule gashinta ta shigl jejo yamkar zaTa yi farauta?

Tsaki ya ja a fili ya ce" to sai ki kama hanya ki koma inda kika fito

Hafsat ta dube shi da kyau ta ce" mu juya dai

Ke ni sa.an ki ne wai? Ya ina baki umarni kina kokarin takewa who are u? Umarni na baki ki juya ki koma gida

Hafsat ma ta yi tsaye gabansa, ya kasance suna facing din juna ta ce" idan muka yi fita ta ni da kai, na zama a karkashin, ina matsayin malakar ikonka, a yanzu ka bar uwar malan a daki tana baci!

Takaici ne ya saka shi dafe goshinsa ya nufi Hafsat da niyar nuna mata ya fita iya tsayaya, sai dai wata murya ce ta ce da shi" *kul Abdallah* dukan mace kuma ka koma?

Wani irin tsayawa ya yi, lokaci guda gabansa ya fadi,
Da wani irin sauri ya juyo dan gannin wanda ya yi maganar,

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,

Tsaye mutumen yake, ya ja rawanin da ya yiwa kansa ya sauka hakan ya bada damar gannin fuskarsa dake dauke da gemu da saje mai tsayi tamkar tun da ya fara fitar da gemu bai taba askewa ko ya gyara fuska ba
Du irin karancin hasken wajen ba zai taba bace masa ba, du irin yanda ya fito a gabansa ba zai bace masa ba,

Gaba daya jikinsa ne ya kwashi rawa, da sauri ya saka hannunsa jikin wandonsa ya janyo bindigarsa da niyar karasawa wajen mutumen dake tsaye kikam ya ki motsawa ko ya gudu kamar yanda ya yi wamcen karron

Da wani irin gudu ta sha gabansa, ta yi tsaye a gabansa sannan ta nuna masa bindigar dake hannunta gaban goshinsa, cikin karaji ta ce" *walahil azim kafin ka yi harbi zan harbeka Abdul Jabar!*

Sai da ya fan dakata yana kallonta sannan ya yi wani murmushin gefen kunci ya ce" *a kan wannan kudurina kashe ki ba wani abu bane, idan har kin yarda kar ki kauce ki ban hanya!*

Gadan gadan Abdul ya nufo Hafsat dake tsaye tsakaninsa da wannan mutumen dake tsaye shima ya harde hannayensa



Yana zuwa ya danna alburushin bindigarsa ya........





*Ya Allah, shin wa Abdul ya gani haka? Kar kuyi gagawar yanke hukunci fa? Kar ku manta Abdul na tsakiyar makiya kala daban daban,*

*Ya Allah Shin Abdul harbe Hafsat din ya yi?*

Ina muka dosa ne?

*KUTKALE.....KUTKALE...KUTKALE*




>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




3?? 8??




Wani irin shake gashin kanta dake baje ne ya yi, hakan ya sakata buda idannuwanta ba shiri sai kuma ta mayar ta rintse,
Walahi da za.a tona zuciyarta da an ga rubutacen abu cewa taba fatar jikinta da ya yi a yanzu ya fi mata ciwo fiye da azabar dukan da yake gana mata,

Murya na shake mata ta ce" Ta yaya zaka yi tunanin muna soyaya da shi bayan ba wani abu makamancin haka da ya taba hada ni da shi?

Kara matsa fuskarsa kusa da tata ya yi sosai sannan ya ce" irin alwashin da ya ci a kan du wanda ya dauke ki na shi ne ajalinsa da hannunsa kadai ya isa ya shaida cewa kina zuciyarsa,

A kan ya ci alwashin kake son halakani?

Yana shirin bata amsa wayarsa ta dauki ruri,

Da sauri ya rarumo abin rufe bakin ya rufe bakinta sannan ya saita kansa ya daga wayar

Yana dagawa ya ce" Abdul, ina ka je kuma? Ina ka je? Kana ina ne? Shin yaushe zaka daina tayar min da hankali idan kana fita? Yaushe zaka san ciwon abubuwan dake faruwa ka daina fitar nan da kake har sai wani abu ya same ka? Sai da na tashi na neme ka ban same ka ba shin yaya kake so hankalina ya kwonta?

Abdul ya yi murmushi ya ce" Muhammad, gani fa na dawo kai ne nake nema ban gani ba, ka yi hakuri nima kana raina, na je wani uzuri ne

Muhammad ya yi gagawar kashe wayar ya koma wajen Hafsat dake binsa da kallo , da yatsarsa ya yi mata nuni da zasu sake haduwa ne, sannan ya juya da sauri ya fice ya bar mata dakin, wanda yana fita mai tsaron nata ya dawo ya rufe mata idon ya ci gaba da gadinta

A lokacin da Muhammad ya koma ya tarar da Abdul zaune a falonsa,

Sai da ya kimtsa yannayinsa sannan ya karasa wajen Abdul fuskarsa na nuna tsantsar damuwar halin da yake ciki,

Yana zama ya kura masa ido kafin ya ce" yaushe zaka cire damuwar yarinyar nan a ranka ne? Kana abu cikin yannayin da kai kanka baka sani ba, nace da kai kaunarta kake ka kamu da son macen dake baka tsaro, wace aka bata horo irin na gardawa aman ka musa min?

Abdul ya girgiza kansa ya mika masa hannu ya ce" kai kuwa yaushe zaka daina dirowa wajen mutun ka rufe shi da fada da accusation ne? Asalamu alaika

Muhammad ya mika masa hannun da ya shaki gashin kan Hafsat sukai musabaha kafin su ci gaba da tataunawa suna musun da suka saba a haka har ya mike ya ce da shi zai je ya watsa ruwa

Da ido Muhammad ya raka shi har ya shige kafin ya bi masu bashi tsaro sai shawagi suke a wajen,

Murmushi ya yi kasa kasa sannan ya mike shima ya nufi dakinsa

A lokacin da Abdul ya shiga dakinsa tubewa ya yi ya dauki tawul ya nufi bayi da niyar yin wanka
Tsayuwa ya yi kasan shower rufa na sauka jikinsa ba tare da ya goga sabulu a jikin nasa ba,

A hankali ya kawo hannun da sukai musabaha da Muhammad da shi ya saka wajen fuskarsa yana share ruwan dake rubar masa a fuskar

Tsai ya yi da hannun, inda gabansa ya wani irin bugawa,
A hankali ya maida hannun wajen hancinsa da kyau dan kara shakar kanshin turaran gashin matan da ya shaka wanda ya tabata da turaran gashin mata ne dan kuwa a da mamansa ke anfani da shi sai kuma da ya ji shi wajen Hafsat dan kuwa irin yanda ake zama na matsewa junna waje dole a ji iskar kamshi ko warin da jikin mutun ke iya fitarwa, dan shinema ya saka GN basu kulawa dan kiyaye fitar da warin jiki

Tsai ya kurawa pampon ido kafin ya mika hannunsa ya dauko sabulu ya shiga gogawa,

Wankan ya yi ya gama ya dauro tawul ya fito ya tsaya gaban gadonsa yana kallo,
A fili ya furta" aa, Ni.ima da na shiga dakinta bata kanshinnan, hasalima ban taba jin kanta na kanshi ba sai dai abin ruwa ko kanshi kanshin man gashi hade da warin ruwa,

Tawul din ya yar ya mika hannunsa ya dauko jalabiyarsa zai saka ya kuma juyowa ya ce" aman, malan kawai na yi musabaha da shi a fitan da na yi, me zai hada hannun malan da kanshin turaran ruwa na gashin mata?

Yarfe hannunsa ya yi kafin ya kara kai hannun wajen hancinsa ya sinsina, wankan da ya yi da sabulu ya saka babu kanshin,

Dan tsaki ya ja ya shinfida salaya ya tsaftace tunaninsa ya gabatar da sallah

Yana gamawa ya shiga jan carbi yana mai kallon waje daya, ya jima yana adu.a kafin ya shafa ya mike ya cire rigar daga shi sai wandon cikin ya kwonta saman bed dinsa

Shiru ya yi yana mai jin tunanin turaran nan na dawo masa,

Mikewa ya yi ya zauna, a ransa yake ayanna bayan malan sai Muhammad da muka yi musabaha da shi,

Muhammad? Ya Salam, me ya hada Muhammad da turaran gashin mace wanda hakan na nunin ya taba gashin ne? Shin Muhammad ya saka kansa a harkar bin mata ko meye?

Saurin rintse idannuwansa ya yi, dan ba zai yarda yana ji yana gani ya kyale Muhammad ya saka kansa a muguwa kuma lalataciyar rayuwa irin ta bin mata ba, rayuwar da idan kana yi baka da mutunci a idannun al.uma? Ita kanta abokiyar watsewar naka ba mutuncinka take gani ba, a wajen Allah baka da rabo, haka a duniyar du abinda ka taba sai dai ya ringa yin baya? Ina ba zai bari amininsa ya saka kansa a wulakantaciyar rayuwa irin wannan ba

Waje ya samu ya kwonta aman fir baci ya ki zo masa, haka ya yi ta juyi yana tunane tunane ga

24 / 54