Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   23 / 54

66K to 69K   out of 159.5K words

3?? 7??



*DUNIYA, ABAR TSORO CE, KANA TAFE KANA YIWA KANKA MAKIYA A LOKACIN DA KAI KANKA BAKA SANI BA, FATAN RABIH YA SA MU GAMA DA DUNIYA LAFIA=?O?




A wannan rana Sun wuni tare da Malan da Abdul, dan kuwa sallah kawai ke fitar da su, sun tatauna sosai, hankali malan ya kwonta ya kuma fada kan adu.ar Allah ya kubutar da ita,
A haka suka yi masa salama da yama suka kama hanyar garin Minna


Tun da ta ji motsin an shigo dakin ta yi tsai tana sauraro
kamar yanda aka saba aka so aka bude wajen da zata ci abinci aka saka mata mesa aka dudura mata abincin da sam babu dadin dandano sannan aka barta aka rufe mata bakin aka fita

Idannuwanta dake rufe cikin bakin kyale ta lunshe wasu irin hawaye suka bi tsuman suka jika, nan ta shiga buga hanci dan kuwa muguwar mura ke damunta na irin azabar da ake gana mata

Mamake take, irin yanda ba.a fita da ita a mota ba an fai ja ta an yi tafia mai nisa da ita a lokacin da aka rufe mata idannuwanta da bakinta aka kuma daureta aka durfafi wajen da ba zata ce ko ina ne ba aka kawota aka daureta saman kujera ake gana mata azaba kala daban daban dan kuwa namiji daya ne ke azabatar da ita sai ta fadi inda ta saka wayar da ta hada da computernta take sharing du wasu informations dan kuwa wannan dalikin kawai ya hana a kawar da ita aman mirsisi ta ki fadi, du ta fice a hayacinta ta zama wata iri sai karbar azaba take ko abinci sau daya ake bata wani irin damun da bata san ko meye ba a bata ba wani da yawa ba shikennan sai kuma gobe, ta yi ta yi ta kwonce daurin da sukai mata aman ta kasa san ba komai a jikinta wanda zai saka ta iya kwoncewar, so take a mayar da ita azabar tsoma kanta a cikin ruwan da aka yi ko zata samu ta damki wani abin da zai bata damar kubuta

Tarin tashin hankalinta shi ne
Bayan masu son ran Abdul ma tare da shi, tayi imanin kuma *A CIKIN GIDANSA NE AKA DAURETA* dan kuwa ta ina za.a bi a fita da ita a irin mugun tsaron da gidan ke samu? Idan sun jirge camera ai ba zasu jirge sojoji da su BS ba, ba zai yiwu duda dare ne a fita da ita a kafa a yi nisa da ita ba, in dai an fitan da ita to fah ana kusa!
Kai, irin girma da lungu lungu sako sakon gidan nan, ta fara tunanin ko dakin horon Abdul ne?

Motsin da ta ji an buda dakin da wani irin karfi ya saka gabanta yankewa ya fadi

Muryar da ta ji sama sama ana fadin magana kamar haka" *banzan sonta yake! Sonta yake, kuma ya iya fita da bada sau! Ka san irin yanda yake da mugun naci a kan abu, ina jin wannan yarinyar idan muka kasheta mun idasa tunzura shi! Damuwarta ya hana shi bin matan da wadincan sakarkarun suka hada shi da shi fa? Dan haka ka bude mani idonta idan har bata fada min a inda ta saka wayar nan na harbe banza a kai masa dakinsa a ajiye masa ya dawo daga inda ya je din ya tarar da gawarta mu ga abinda zai yi* !


Das das das das das shi ne abinda gaban Hafsat ke yi,

Wani irin mugun tausayin Abdul, da tata rayuwar ne suka kamata,
Shikenan,
Shi ne abinda ta iya fadawa zuciyarta

A hankali ta shiga neman taimakon Allah har ta ji an kama abin bakinta an vire shi da mugunta hakan ua sakata jin wani irin zafi

Bata gama jin zafin ba aka cire abin da ya rufe idannuwanta
Tar hasken wajen ya sakata saurin rufe idannuwanta dan wani irin dukanta abin ya yi a idannuwanta

A hankali ta ringa buda idannuwanta tana gannin dishi dishi da kumburariyar fuskarta har ta idasa buda idannuwanta saman fuskarsa

Ido cikin ido suke kallon junna, a hankali ta buda baki ta ce" *WHY? WHY? Kai ne wanda ya fi kowa kusanci da shi, kai ne wanda ya fi kowa sannin sirrin sa, kai ne wanda ke yi masa fada kan ya bar desir na vengeance ku juya gida, kai ne wanda a duk lokacin da aka kawo masa hari ka fi kowa rikicewa da shiga tashin hankali, aman ka san kai ne ka shaka masa abu da kanka a wajen auren yar gidan aminin mahaifinsa? Bashi da baban abokin shawara sama da kai, ka kasance mai yi masa fada a kan banzan burin daukan fansa da nacin zama a wajen da ake son gannin bayansa! ME YA AIKATA DA GIRMA DA KUMA ZAFI HAKA DA HAR KA ZABI ZAMA MAKUSANCINSA MAFI KUSANCI SANNAN MAKIYINSA MAFI GIRMA A DORON KASA? KA MIN ALFARMAR SANAR DA NI WANNAN DALILI NAKA KAFIN KA KASHE NI=?O?

Gashin kansa ya shafa cike da dumbin mamakin yanda aka yi a kankanin lokaci, kwanakin da basu fi wata uku ba yarinyar karama ta shigo ta gane abubuwan da sauran mutanen basu gane ba, wato cewar banda bin bayan Abdul na son kashe shi da yake shi ne ya kashe mahaifiyarsa da hannunsa, ya kuma saka aka kashe kanwarsa? Kai wannan yarinyar dole a yau a yanzu ya kasheta dan kuwa yana gannin take takensa da dukan jama.ar dake tare da shi, a kowani lokaci suna iya gane wanda ke saka su a rudun rayuwa su kashe shi kafin shi ya kashe shi!


Kafarsa ya dora daya saman abin kujerar yana kallonta ya ce" dalilinsa hukuncin sare kai ya hau budurwata wace tun da aka haifeta nake son ta tamkar raina, ina ji ina gani ta afka soyayarsa a lokacin da muka tasa dan ya fito a matsayin zakaran da ya zarce kowa ya ci aikin baban bodyguard na kasar *SAUDIYA*

Mun kasance mun fi karfin a kiraye mu aminai , sai dai yan uwa
Ni ke zuwa gidansu hutu a lokacin da ya je aikin da take takamar shi rikeken dan bincike da kuma gane mai laifi ne,

Tabas na san dukan abubuwan dake faruwa tsakanin mahaifinsa da yar da ya haifa, na kuma san du wani shirye shiryen uban ,

Mahaifinsa ya dauke ni kamar yanda ya dauke shi, dan kuwa har shi kansa bai san ainahin waye ni ba , bai kuma san na yi alkawarin karar da danginsa ba!

*Hasina* ta kasance mai son bakin namiji jarumi dan kuwa muguwar harija ce a tana kananun shekarunta ma na san da haka dan wani lokacin sai na taimaka mata nake samun lafiarta,
Tun da ta yada ido ta ga Abdul, ta shiga tarda shi ni tana kewaye ni,

Abin ya zama jaraba ta tsane ni tamkar ranta, shi kuwa ya tsane ta tamkar mutuwarsa!

Takan tarda shi du inda ta san zai je, ya wulakanta ta ko a gaban waye ya taketa ya yi tafiarsa,
Gana da kanai ciki akoy wace sak irin halayanta ne da ita dan kuwa itama nunawa ta yi tana son sa,

A lokacin shi harkar mata bata gabansa, ni kuwa ina bibiyar kanwarsa jira kawai nake ya yarda ya so Hasina ni kuwa na bi kanwarsa dan kuwa cikin ma.aikatan gidan na samu mai bin mani du wani motsinta

Ke bara na takaice maki, dan ya kori Hasina sai ya fara kula kanwarta a lokacin ya dawo ya zama cikeken sojan boye, yana shirye shiryen zuwa gida wajen iyayensa wani lokaci aka wayi gari Hasina ta Kashe kanwarta da hannunta , binciken da ya yi ya gano ita ce ya fakasata aka kawot tsakiyar gari aka gile kan Hasina ina tsaye ina kuka ina magiya ina kallo ya gurgura gangar jikinta ta fadi gefe

Daga wannan ranar na zama makiyin Abdallah, ke ko raina zai shiga sai na ga Abdallah na kukan jini yana magiyar a yi hakuri a kashe shi dalilin bakin cikin rayuwar da yake gani kala daban daban kafin na kashe shi da hanuna

Hafsat kyam shi take kallo, kafin ta ce" *tabas, mutuwarsa zata fi zuwan masa da sauki da jin mumunan labarin cewa kai MUHAMMAD kai ne bakin kumurcin dake bibiyar rayuwarsa cikin innuwa yana kasara shi, na baka albishir din a lokacin da zai san da hak, abinda zai hana zuciyarsa bugawa to fa lale baban abu ne mai girman sauran kwanakinsa a duniya, kuma tabas na yarda da maganar cewA......makashinka yana tare da kai, ko ba komai na gane cewa duniya sai Allah*

Irin yanda take hawaye yake kallo kafin ya yi wata yar karamar dariya yana kallonta ya ce" na kasa gane shin son ki ne ya saka shi a wannan halin ko shakuwar ce da yake fada? Dan kuwa a yanzu ina cikin tsakiyar abu biyu, ban taba gannin ya yi rikicewar da ya yi sai da na dauke ki! Shi kashe ki zai idasa haukata shi ko kuwa cire maki kayan jikinki nake, na mayar da ke matata na tsayin wata guda, gefe guda shi kuwa ina kara tunzura shi, sai na maki ciki , cikin ya fara fitowa sannan na cire maki kai na dora masa a kofar dakinsa a lokacin da zai fito ya yi tozali da ke? Kin ga an yi dai dai,
Taya ni gannin shawarar da ta fi dacewa?

Ido Hafsat ta rintse tana adu.a a cikin zuciyar, ba wata adu.a take ba sai rokon Allah kan kar Allah ya bashi damar taba jikinta da mugun nufinsa,

A firgice ta buda idannuwanta sanadiyar jin ya.......





Comment comment commetn=?-?=?-?=?-?=?-?=?-?=?-?=?-?=?-?



>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




3?? 6??


Tunda Malan ya saka Abdul a gaba da ido yana kallonsa cike da al.ajabin labarin da ya bashi nasa na ainahin waye shi dala dala har ya dire malan kallonsa kawai yake

Mikewa ya yi ya dauko goron ruwa ya mika masa tare da fadin " Sha

Bismillah Abdul ya yi ya sha ruwan nan sannan ya kokarta ya mayar da damuwar dake tare da shi ya dubi malan dake kallonsa zuru, sak irin idannuwan Yar malan

Malan ya lumshe idannuwansa sak irin na Hafsat kafin ya dan gumtse bakinsa sai kuma ya saki ya ce da Abdul" Sannu


Abdul ya yi murmushi ya sada kansa, dan shi wani irin nauyin Malan yake ji sosai,

Malan ya ce" bawa na haduwa da jarabawa kala kala yaro,
Tabas jarabawarka mai girma ce, ba kamar gannin gawar mahaifiyarka da harbi a goshinta,
Tabas Allah ya san da zamanka dan ka rayu cikin jarabawa Alhamdulilah,

Sai dai maganar da batai min dadi irin yanda kake magana da sunnan mahaifinka a cikin lamarin nan, ba zan so ka yanke hukunci a kansa ba, ba zan so ka zama mai fushi da iyayenka ba, ko mai ya yi zan so ka saurare shi sannan ka yi maza uzuri, jarabawar rayuwa ce shi kansa ta same shi, muguwar jarabawa ce mai saka bawa kauracewa mutane, kai wannan mahaifin naka yana da zuciya mai kyau da abi saka rayuwarsa a hatsari ba, ina nufin ya kashe kansa, ko ya idasa lalacewa ya shiga wata muguwar hanyar daban

Abdul ya sauke ajiyar zuciya yana sauraron Malan,

Malan ya ci gaba da fadin" sai maganar da muka yi da kai cewa an ce da kai makashinka na tare da kai, gashi an harbi tsohuwar matarka kuma an sace mai baka tsaro ko?

Andul ya tsura masa ido yana kallonsa,

Malan ya ce" in sha Allah, tunda har suka kai haka, zan iya ce da kai wata hanyar ce ta samun nasara, tabas ka sakawa ranka cewa za.a iya dacewa a kowani lokaci gaskiya na iya bayana,

A hankali Abdul ya ce" ta kasance mai kwana da tashi da sunnanka,
A kan dalilinta na ta dawo wajen iyayenta ta tarbi harbin da zai same ni ya sameta, fama take, ta shure makudan kudadan da take iya samu dalilin aikin da aka bata ,

Tsai malan ya yi da jan carbin da yake ya tsurawa Abdul ido

Abdul dake zaune saman abin salaya mai laushin gaske , ya kara tankwasa kafarsa yana kallon malan ya ce" ba zata gudu ba, ba kuma ta wulakanta kanta ba, rayuwar tsayaya da ta yi halitarta ce, iko ne daga Allah,
Ta kasance mai tsare kanta, mai tsare mutuncinta, mai hanawa a kama sunnanta kai tsaye dan malan, mai kuka da hawayenta tana kitan sunnan malan,

Carbin hannun malan ne ya kubuce ya fadi daga hannunsa yana kallon Abdul, unda hannunsa ya shiga rawa rawa haka kuma ya kasa magana ya kuma kasa motsawa

Mikewa Abdul ya yi daga inda yake ya matsa kusa da shi ya zauna sosai kusa da malan ya ce" na taso daga kasar Minna a irin wannan lokaci dan na kasa dangana,halayanta na gari sun saka na shaku da ita, na zo da kokon barana a kama mana da adu.a, Allah ya kuma fitar da ita da hannun da ta shiga, dan kuwa wasu na zargin ta tafi da kanta ne, ni na san ba zata tafi da kanta ba, dan kuwa tun fitar higar da ta yiwa gidan nan ta yi alkawarin za.a san da tafiarta in dai mai daukan lokaci ce

Idannuwa Malan ya lumshe a hankali, wasu hawaye ne suka zubo daga gurbin idannuwansa, kafin ya budi baki a hankali ya ce" *Uwata*

Abdul ya kali malan, sai da ya ji tsigar jikinsa ta mike gaba daya, dan kuwa karara tsantsar tsabar soyayar Hafsat ne ta bayana a fuskar mahaifinta, ya bashi magana a baibai bai shaida masa ko da wa yake ba, dan kuwa duniya ce mai cike da girma da kuma fadi, tabas ana iya samun masu halayenta birjik, sai gashi daga jin yannayin, makamancin halayenta ya zubar da hawaye, tsabar ya yi missing din gudan jinninsa, hakan na nuni da du irin wahalar da ta gana masu suna kwana suna kuma tashi da ita a ransu a tare da su ko?

Ji ya yi ba zai iya boye masa kamar yanda ya zo da niya ba, ya zo ne da niyar saduwa da shi ya bashi labarin kansa ya kuma roki alfarmar a kama masa da adu.a a taya shi kan Allah ya bayana Hafsat dan kuwa idannuwansa sun rufe, ya kasa gannin komai, ya kasa fahimtar du wa.inda yake tare da su bare har ya ware daya ya bibiye shi, sai gashi datijon ya canza masa abinda ya yi niya

A hankali Abdul ya fuskance shi ya ce" a lokacin fa ta fita daga gidan nan, ta hadu da kadara wace ta yi sanadiyar zamanta a gidan yari na tsayin watani, kusan shekara,
Bayan wannan gwamnati ta dauketa ta horeta zama cikakiyar mai baiwa mutane tsaro wato Bodyguard, sai dai mutanen manyan mutane wasun bama a cikin kasar niger ba, ta haka na dauketa aiki, ita ce wace muka baiwa juna labarin juna

Malan ya miko hannunsa ya riko na Abdul, wanda hakan da ya yi ya saka Abdul bin hannayen nasu da kallo,
Malan ya ce" yaro, kana nufin...UWATA na raye a doron kasa? Uwata na tine da mu har tana faman zuwa garemu? Yaro kana nufin Uwata ta nutsu har tana yi mana adu.a? Yaro wai Uwata ce ta zama mai baiwa mutane tsaro? Yaro ita fa? Uwata mace ce, Uwata yarinya ce, ita ce ta yi kaso? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,

Abdul ya jimke hannun Malan yana kallonsa sai dai bai ce da shi komai ba

Malan ya sauke ajiyar zuciya sai kuma ya saki wani murmushi ya ce" tun da na ga na kasa dangana cewa ta mutu na yi hakuri na bar tunaninta zuciyata ta aminta da tana raye,
Sai dai sake sake ba wanda ban yi ba, dan Uwata ta nuna cewa idan ta bale ba zat yi mana da dadi ba,

Abdul ya saki murmushin shima a hankali ya ce" bata jin magana

Malan ya kale shi da kyau ya ce" Uwata? Bata san mene jin magana ba, Alhamdulilah, Allah ya kara shiryar min da ita,

Abdul ya amsa da amen,

Malan ya ce" ka san meye? In sha Allahu zata fito, ba abinda adu.a ta bari, hakuri da adu.a su ne makamin bawa

Abdul ya gyada kansa har zuwa wannan lokacin hannunsa da na malan na cikin juna,

Malan ya kali hannayen shima sai kuma ya kara yin murmushi, wato da ka karanci datijon zaka gane yana cikin wani irin farin ciki dan kuwa sai sakin murmushi yake duda an bashi abin a dunkule an kuma bashi labarin tana wani hannun mai hatsari, aman da yake mutun be mai tawakali, sai ya saki du wata damuwa ya ringa barin zuciyarsa na turo masa da sakon murmushi yana karba yana yi yana karawa,

Malan ya ce" ka san da sai da na daurawa Uwata aure?

Abdul ya kafe malan da ido, dan kuwa ya san da maganar an daura mata aure, aman ce masa aka yi mijin ya saketa, kar dai malan ya fadi abinda ba haka ba,

23 / 54