Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   4 / 54

9K to 12K   out of 159.5K words

son yi mata wasu tambayoyi a kan aminin abanta wanda ya yi imanin ta sani dan kuwa akoy sakin baki a wajen uban idan yana cikin farin ciki,

Nan ta nemi bashi wuya, dama baya shiga rigar sai ya yi shiri irin nasu, hakan ya saka shi neman yi mata tijara da kyar dai ta sanar masa labarin , ta boye ne dan ya shafi mahaifiyarta ita kuwa har ga Allah tana jin son mamanta a ranta, harma tana fatan idan ta ga bayan wannan lamari da ranta ta je wajen mamanta ta rungume ta.

Daga rigar ma wajen yan sholishon cikin garin ya koma, saman babur din nan na aro, ya saje da su, ya burmu inda suke burmuwa, dan tabatarwa kansa labarin dan aminin Elhaj, shi ne diler din wato mai siyar masu da kwayar wanda suka haifa da matar Elhaj a lokacin da ya yi doguwar tafia wace ta faukan masa shekara biyu harda yan watani......wannan masifa na tafe da su duka bisa tafkeken laifin da suka aikata, harma sula gayaci wani!

Juyawa ya yi a hankali ya shige wankan,
Wankan da ya daukan masa lokaci, kafin ya fito yana tsane jikinsa

Sai gashi fess ya fito da shi cikin dan kankannin lokaci

Doguwar riga ya saka , ya bude frijj dinsa, nan ya ga an cancanza madarar holondia dake ciki, daukowa ya yi yana dubawa,
Bai sha ba ya mayar cikin frij din ya taka ya fita

Yana fitowa ya ganta tsaye, ba wata walwala a fuskarta irin dai a shirye take shirin aikinta,

Dakin matarsa ya nufa, wanda ya saka mata bugawar zuciya na tsoron kar a je ya kuma abinda ya yi jiya?
Sai dai bata iya cewa komai ba ta bi bayansa suka shiga, suna shiga bata tsaya jiran wani abin ba ta je du ta yi binciken da zata yi kafin ta juya ta fita ta ja ta tsaya kusa da abokannan aikinta,

Yana kallonta ya zo wajen kujera ya zauna, ya dora kafa daya kan daya

Saukowa ta yi daga saman bed, gabanta na dukan tara tara tana adu.ar Allah dai ya sa ba abin nan na jiya ya dawo da shi ba, dan yau da ba dan ta wuni gasa jikinta ba, toh da tabas ba zata iya takawa rasss da kafafuwanta ba,

Zaman da ya yi, yana duban du motsinta har ta karaso kusa da shi ta tsuguna ta gaisar da shi,

Bai amsa gaisuwarta ba ta mike ta zauna a kujerar dake facing dinsa tana sinne kai irin kunyar nan,

Hannunsa ya nuno wajenta ya ce" menene wannan kike yi? Irin wannan sada kan haka?

Daina sada kan ta yi aman bata dago ta dube shi ba, dan haka ya ci gaba da fadin" kin san a tarihin matan da na aura ke ce ta farkon da ta kai warhaka bata mutu ko ta gudu ta bar ni ba? Ke ce wace bayan kin ga girmana har na so sakar maki shi sai dai kika kasa dauka sai hakura na yi dan kina ta ihun da ya saka na ji na daina muradi? Kin san da lale masu baki tsaro sun bada kyakyawar gudunmuwa wajen gannin rass har yanzu kina takawa yanda kike so?

Shiru ya yi gannin ta nutsu harma tana dagowa ta dube shi sannan ta sada kanta, ya ci gaba da fadin" bani da time din da zan auri mace kuma na bata tarbiya! Ki gane bana wulakanta dan adam mai daraja, kar ki yarda ki saba da haka domin kuwa idan har na gane haka ko da cikina a jikin ki na wata tara ina iya salamarki, can ki je ki karata da abinki ki bani lafia ni ba zan so ina ji ina ganni mace ta mayar da ni wawa ba!

Ajiyar zuciya take saukewa na dan kukan da ta fara, dan a fada ta dauki magangannunsa, duda bai yi su a lalama ba, bata wani saurari abinda ya dace ta tsinta ba, sai tsayar da hakan na faruwa ne dan ba soyayarta a ransa, dan haka sai ta ji ta muzanta,

Sai da ya gama ya maida dubansa wajenta, sarai ya lura da yannayinta aman ya basar ya mike ya ja rigar jikinsa ya cire kafin ya koma saman kujerar ya yi wani zaman rashin kunya yana dubanta ya ce" yau fa, sai na shiga, zo ki ja ra.ayina=? ?

Ya karashe yana mai lumshe idannuwansa ,
Sai da gabanta ya fadi a lokacin da ta dube shi, jibgin uwannan kai, haka yake a haske sosai? Haka yake? Waima ya shiga ina? Ta yaya? Yau ta shiga yku ta ga abinda ya fi karfinta, gashi ya yi wani ringeshe wato jira yake ta zo ta yi masa abubuwan nan wanda ta dauka na jar fata ne, sai dai ya yi mata nuni da sunna ce kafin ya nemi darara mata ? Kai ita dai tsakaninta da matan da yake daukowa har suka saba masa da irin wannan rayuwar sai Allah ya isa (=?3? to fa, ke, shi da ya dauko sun fa? Fans kar ku yi mamakin irin yanda zai mikewa mace amarya santaleliya irin Ni.ima cewar ta ja ra.ayinsa, idan baku manta ba Abdul fa namiji ne da ya yi mu.amalar jan ra.ayi da mata kala daban daban, wa.inda suka isa da wa.inda basu isan bama duk suka zube suka ririta shi ya wanke su da dala....hakan ya saka shi gannin wanima ya yi rawa balatana dan makadi, kennan wanima ya ja ra.ayinsa ina ga ta sunna?)

Sai da ta cire rigar tata ta sama ta baci, sannan ta duka gabansa irin yanda ya nuna mata a jiya ta yi tsuru tana kallon sa,

Bude idannuwansa ya yi a hankali ya kai kanta, shi take kallo abinta, kallo irin na san gane abu...
Dagowa ya yi da yannayinsa mai nuni da jarabar ta gama motsawa yana dubanta, a hankali ya ce" yaya sunnan ki na gaskiya banda Baby? (Sunnan da yake ji kennan shi tun da ya santa, ko wajen daurin aurensu shi fa sai ya rantse bai ji sunnanta da kyau ba bai rike ba, =?D?=?D?=?D?, zaka fada ne Abdul)

Idannuwanta ta bude da kyau tana dubansa,
Sunana kuma? Wai dama bai san sunana ba?


Jiki sanyaye ta ce" NNNi.uma,

Hannayensa ya saka ya dagota ya dorata saman cinyarsa, a hankali ya matso da ita zuwa jikinsa , cikin yannayin rada ya ce" Ni.ima, Allah ya sa Ni.ima na tare da ke, ki daina langewa ki bani kulawa kin ji?

Kanta ta shiga gyadawa a hankali, tana jin wani irin yannayi na shigarta na sababin abubuwan da ya shiga yi mata ta hanyar anfani da hannunsa da kuma sajen fuskarsa.......


A yau kam abin ya ja daga, dan kuwa ba shi ya fito a dakin Ni.ima ba sai kusan karfe daya, sai da ya gama mayar da ita cikakiyar mace, wanda shi da kansa ya tausayawa yannayin da ta shiga , ta sha wahala ta kirki wace sai da ya talafa mata lumfashinta ya dawo jikinta, tabas ya san dole sai ta ji jiki, shi din bai taba yi ba, ya bita a hankali aman ya girmeta sosai, shi ya sa ya kasance mai tunanin zama da mace biyu, dan a ganninsa irin wannan fitinar da wuya mace daya ta iya dauka,

Bayan ya gama bai tsaya wani gashe gashe ba, da ta farka, kayanta kawai ya iya zura mata ya kwontar da ita ya ba dakin baya, yo shi ina ya san ana wani gashi? Inama ya san ana wani ririta? Shi fa a sanninsa shikennan kafin safe ta ware, dan haka ya fice yana mai jinsa sakayau kam, (wayo Ni.imana, ashe ke wuni da gashinma ba na dalili bane? Yau kam zaki yi gashi)

Yana fitowa ya tarar da ita dai tsaye,

Gaba ya yi tana biye da shi a baya har suka shiga dakinsa,
Suna zuwa ta kakabe shinfidarsa, ta bude frij ta ciro hollondiar nan biyu da ruwan gora ta ajiye ta juya ta fice a dakin inda ya rakata da kallo kafin ya zarce bayi dan yin wanka........



Kwonci tashi, yau har kwannan su Hafsat goma a gidan Abdul, sun ga fitintunnu da abubuwan mamaki da tarin takaici a tare da wannan bawan Allah,
Abdul, bai taba yin wani yinkuri dan nuna masu yana son kare lafiarsa da ransa ba, bai taba basu damar su fuskanci inda zasu kare ba,
Ya sha dan iya shege su fita ya zile masu du tsaron su, du kulawar su ya dawo gida kawai dan ya saka Hafsat ta yi ta balaki kamar ta kai masa mazga yana zaune yana dubanta yana murmushi, kuma du fitar da zasu yi, Hafsat na kula da takunsa basu taba fitar da ba wani abin mahinmanci na lamarin aikinsa ya fitar da shi ba, cikin dabara take hada abinda ta samu itama har ya zile masu!

Kamar yau ma da karfe biyar na yama ,
Abdul ne ya fito daga dakinsa cikin shiga ta kayan gudu, wato yau dole su yi sports dai?

Yana fitowa bai yiwa kowa magana ba ya dauki hanya ya falla da gudu,
Sai da Hafsat ta dora hannu a ka gannin wani balakin kuma, sannan ta cire rigarta ta sama ta fala da gudu ta bi bayansa hakama su BS gaba dayansu sunna biye da shi da wani irin gudu ,

Sunna shan kwana, kamar daga sama wata bakar mota ta shanyo kwanar a guje ta ........... . ........



*Toh fa, lamarin na Abdul ba sauki>?&?
@&,*

Ku yi hakuri da yannayin rubutuna, ina iya yina dan baku pages mai yawan gaske a hakan, ku min uzuri plz=?O?

>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 2??


Koda Hafsat ta koma dakinta wanka ta shiga ta yi ta fito ta saka wata riga fara dake cikin kayanta ta zauna tana kallon waje guda,
Kwata kwata wani lokacin idan ya yi irin abubuwan nan sai ta ji ta tsani kanta,
Mikewa ta yi ta dubi madubi,
Tabas yannayinta tamkar ba yar musulmai ba, suturar jikinta a kulun ba kamilaliya bace irin ta yayan musulmai,
Gashin kanta rabon sa da dan kwali ya zauna daram a kanta ba lokacin sallah ba tun tana gidan mahaifanta,
Sam aikin zama bodyguard ba aiki ne da zai ja maka mutunci da girmama ba a kasar Musulmai,
Kai dai kulun ka kare a saka wando, da rigar da ba zasu iya hanaka gabza fada ko dankarawa da gudu ba ? Kai dai haka zaka kare a bushe?

Zama ta yi tana mai jin haushin irin yanda yake nuna mata iya shege a fili duda ba shi ne na fari ba, aman nasa na yi mata ciwo, bata san dalili ba, bata san me yasa du idan ya ambaceta da gardi, ko yace da ita a bushe sai abin ya yi ta yi mata yawo a kwonya!

Tsaki ta ja tana zabgawa bed din da zata kwonta harara a fili ta ce" ba dai na shayar da uban ba, aa shima na mayar da shi cikina na haifo shi! Kuma gwarama na bar aikin naka dan banda neman kai ni barzahu ba abinda yake, ga wulakanci! In sha Allah zan tafiata gobe ka je ka zama abinda zaka zama sai me? Idan ban samu incin daga wannan aikin ba sai me? Na yi hakurin duka wannan lokacin dan wannan ba zai kashe ni ba!

Haka ta yi ta magangannun bacin rai, har ta raba dare kafin ta yi kwonciyarta a nan kasa ta nemi rintsawa,

Du irin yanda ta cika dare, kiran sallar farko a kunnenta, dan haka ta ciciba ta mike tana mai jin hannun ya dan yi mata nauyi dan kuwa ko ba komai ciwo ne da ya kwana ya yi tsami bale harbin bindiga

Zuwa ta yi ta yi wanka, ta kiyaye wajen bata jika ba, haka ta gama du wani uzurinta ta dauro alwallah ta fito,
A daidai lokacin da take kokarin tayar da sallah ta ji shigowar mota,
A hankali ta daga labulen dakin tana hange,
Bakar mota ce ta shigo , gannin BS tsaye a wajen motar ya sakata juyawa ta tayar da sallarta, sai da ta gama a nitse sannan ta dauki dogon wandonta baki da riga baka ta saka, rigar mai karamin hannu ce bata dora ta samanta ba dalilin ciwon hannunta,
Bata shafawa fuskarta komai ba, sai harhada kayanta da ta yi cikin yar akeatinta dama kayan ba wasu masu yawa bane sai bindigarta da ta daura a tsatsonta ta ja rigarta ta rufe bindigar,
Wajen madubin dakin ta je ta tsaya, tsurawa madubin ido ta yi, a hankali ta furta" shikennan, haka zaki bar shi tsakiyar wannan tashin hankalin?

Fuskarta ta yatsina ta dubi madubin da kyau ta ce" kwarai, mutuncina, da son haduwa da iyayena ya fi mani aikin nan da kowama, dan haka zan kara gaba!

Murmushi ta yi ta duka ta dauki akwatin ta shiga janta a hankali, kanta bude ba dan kwali sai gashin kanta da ta daure da dan karamin ribom,

A lokacin da ta fito katon falon gidan, BS ne kawai tsaye ,
Ido ya tsura mata, kai yarinyar ta hadu ne, du irin gudun da aka sakata bai saka mazaunanta rage fadi da tudu ba, cikinta kiwa tamkar babu hanji a ciki, fatar jikinta wani urin fresh da ita, domin kuwa mayukan da sabulansu na wanka ba jagaliya bane, sun karbeta sosai, haka kuma gashin kanta baki ne sidik ba yambo ba komai, haka yake halitarsa ce, ga cika ga madaidaicin tsayi, gaban goshinta ya fi cika da suma luflufluf haka yake, girar fuskarta har cajeta take ta daidaita ta yanda take so, hancinta ya ja ya tafi tsuwait har kusan dan karamin madaidaicin bakinta mai dauke da lebunna kalar pink, idannuwanta manya manya ne masu hasken fari bakin cikinsu mai girma ne sannan ko ranta ya baci sai dai su cicika da kwala,

Shi kansa bai san da ya zuba mata ido ba sai da ta zauna saman kujerar zaman mutun daya bayan ta mayar da jakarta gefe ta dan jingina suka shiga zaman jiran fitowar Abdul da ya san da zuwansu tun jiya da sare

A hankali ya karasa inda take zaune ya zauna shima,

Sai da ya hadiyi yawun neman kwarin gwuiwa ya ce" fuahi ake da ni ne?

Bata buda gazar gazar din gashin idannuwanta ba ta girgiza masa kai kawai,

Kyakyawan dogon hannunta fari kal wanda baya dauke da gashi ko dis , damtsen hannun shar da shi du irin formation din da ta samu bai saka ya yi mundil mundil da shi ba, ya dan kara girma aman bai zama wannan kigi kigi din irin na maza ba ya bi da kallo,
Sai da ya karewa wajen kallo sannan ya kai dubansa kan fuskarta, da son samunsa ne, ya watsa mata selfi a ajiye a gaban wayarsa ya ringa kallo idan ya samu lokaci sai dai ya san bama zai samu hakan ba dan haka a hankalin dai ya ce" yaya jikin ki?

A hankali ta buda bakinta ta dane zuciyarta dan kar ta dankara masa magana ta ce" alhamdulilah

Shiru ya yi shima, bai matsa a kusa da itan ba, bai kuma kara yi mata magana ba, yana mamakin irin yanda sam baya gabanta, ba wani ziga kai ba, ba komai ba irin yanda manyan yan matan cikin gari ke binsa yana jan su a kasa yana tafka masu iya shege da yaudarar soyaya sai gashi yana bin yar yarinyar nan tana faman jan sa a kasa, ko yanzu wace aka kawo ta canjeta babar bodyguard ce, kuma ta yi kudi sosai yanzu haka daga america aka daukota aka yo nan da ita, yar kwalisa , yar cakwas da ita, ita kanta soyaya suka yi ya yarda ita daga baya , ko yanzu yace su koma zata yarda da gudu ne, aman ita ga damarta a hannunta tana wasa da ita.

Wasa wasa a nan a zaune sai da suka kai wajen karfe tara da mintuna, suna yi suna kallon agogo, aman ba Abdul ba alamunsa,
Shi dai BS yana zaube bai yi gigin zuwa taso shi ba, hakama ba wanda ya yi gigin hakan domin dai su BS ne mai gidansu, umarnin da ya bada shi za.a bi dole, shi kuwa an fada masa waye Abdul din, dan haka yake kiyayewa

Goma saura kadan alamun bude dakinsa suka bayanna , dan Haka da sauri BS ya mike ya koma wajen kofar ya tsaya hakama Hafsat ta mike tana jiran fitowarsa, inda BS ya shaidawa na wajen cewa zai fito dan haka kowa ya kama kansa

Sai da Abdul ya gama wana kys din kofar sannan ya bude ya fito,
A lokacin da ya fito maimakun ya tsaya ya bi abinda ake juransa dominsa, sai ya shiga dayan lungun da zai sada shi da dakin Muhammad,

BS juyowa ya yi ya dubi Hafsat dake tsaye itama,
Ai kuwa yannayin da ya nuna ita sai ya bata dariya ma, dan haka ta murmusa tana dubansa sannan ta kauda kanta, a ranta kuwa tana ayyana baka san rainin hankalin Abdul har inda ya kai ba kennan, muna iya wuni a wajen nan idan ya yi niya!

Abdul na

4 / 54