Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   52 / 54

153K to 156K   out of 159.5K words

yi, ba.a gama halitarsa ba, bai san kalar da zai bada ba, aman ya ji gaba daya jikinsa ya dauka da kaunar abin,
Ji yayi dama kar ta daina haska masa, ji ya yi dama a janyo wata biyar din da suka rage ya taka duniya ya ganshi,
Kaunar abin, wani irin yamyam ya ringa ji inda ya duka yana shafa wajen
Cikin nata ya dan tada , sai dai ba zaka yi tunanin dan mutun bane a ciki sai dai ma ka yi tunanin nrmal haka cikinta yake

Wata kwala ce ya ji ta tarar masa a cikin idannuwan nasa, a hankali ya karasa kusa da fuskarta ya duka sosai ya kama lebenta
Idannuwansa ya lumshe ya tsotsi na kasan cikin wani irin sanyi sannaj ya saki yana kallonta
A hankali ya ce" ina son ki Hafsat, plz ki so ni? Ki so ni tun kafin yarinyar mu ko yaron mu ya taka kasa? Hafsat zaki bani baby

Idannuwanta dake kallonsa ta ji sun mata nauyi cike da hawaye
A hankali ta ce" Abdallah *I LOVE U*

gaba dayansa ya ji kafafuwansa zasu gagara daukansa, hakan ya saka shi zama saman kujerar dake ajiye kusa

Idannuwansa ya lumshe, sai ga wasu hawaye masu dumi
Yau babar rana ce a gare shi, yau ya tashi cike da ni.ima , Alhamdulilah shi ne abinda ya iya fada

Sai kuma tunanin mahaifinsa ya diro masa a zuciyarsa
Dama haka ya ji a lokacin da ya san matarsa na dauke da cikin dansa na farko? Kai, wannan madaukakiyar soyaya ita uba ke ji idan ka ji zaka samu yaro?

Ajiyar zuciya ya sauke suka mike ya kama hannunta dan du yanda ta ki sai da ya riko gam a hannunsa suka fito

Murmushi kawai yake saki, sai ya kaleta, ita kuwa kunya ta cikata dan likitocin nan sun sha dariyar irin yanda ya zaburo ya ringa bata muah du inda bakinsa ya kai cike da murna da farin ciki gabansu ba wani kunya , harma suka yi sabo da doctern inda ya kara fahimtar inda ya nufa harma ya ji ya birge shi

A hankali ya karasa anguwar da malan ke zama ,
Farin ciki ne ya mamaye zuciyarta a lokacin da ta hangi mahaifinta zaune cikin shigarsa ta kamala

Tana kallon yanda Abdul ya duka yana gaishe shi aman Malan ya mikar da shi yana ta doka masa murmushi

Tana kallonsu har suka karaso wajen motar aka bude nan Malan ya yi tozali da yarsa da yake ji tamkar nama daya kwal a cikin miya

Murmushi ta yi hannunta cikin na malan, shima yana kallonta yana mai jin farin ciki a ransa, ko ba.a fada masa ba shi ba yaro bane, koda basu sani ba shi ya fahimta, yarsa ce fa, shi ya raini abinsa, ya gane me ke tare da mamansa, lale ya godewa Allah, murna ce cike da ransa wace ya salame su bakinsa kamar ya kai kunne

Gidan mama ya ajiye Hafsat inda ya ki shiga ya ce da ita zai je wani waje ya dawo

Bai zame ko.ina ba sai kasan wata bishiya mai cike da innuwa sanyayen waje ne mai cike da ni.ima

Zama ya yi waje guda ya dauki wayarsa ya danna kira

Kiran na shiga aka daga


Shiru ne ya dan ratsa kafin a hankali ya ce" ka dawo cikin Gari Abu Abdellah


Da sauri mahaifinsa ya cire wayar ya kali sunnan, ya kuma mayarwa a kunnensa
Bakinsa na rawa rawa a hanklai ya ce""""


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




6?? 9??


A hankali ya ce" Abdu?

Abdul ya yi murmushi mai sauti ya ce" Abih

Ajiyar zuciya ya sauke, da sauri ya ce" dama zan kuma jin sunnan da murmushi a lebenka?

Abdul ya kuma yin murmushi bai dai ce komai ba

Abdul Basitt ya ce" ko yanzu Allah ya amshi raina na cika burina Abdallah, na gode, na gode, baka san irin farin cikin da ka saka ni a yau a yanzu ba, baka san irin yanda na ji a zuciyata ba

Abdul ya ringa sauke ajiyar zuciya shima jinsa yake sakayau, ashe ka riki mutun kanai masa fushi da gabama ba wai wani jin dadi bane sai tarin nauyin fake azuwa saman zuciyarka da faduwar gaba idan ka ji sunnansa? Mahaifinsa ya tafka kuskure a rayuwa, ya aikata laifi mumuna na hanyar saduwa da yar da ya haifa, sai dai hakan ya faru bisa sharin magabata, sharin abokan zama , banzayen abokai masu kai mutun ga halaka,
An kasheta dan a dora masa laifi
Ya yi nesa da su dan tarin kunyarsu, yana jin kunyar haduwa da mahalincinsa a irin wannan rayuwa hakan ya saka shi kauracewa kowa ya kadaice kansa da neman gafarar ubangijinsa da neman zabinsa
Dansa cilo ya rayu cikin kunci da tunanin bayan bata rayuwar yar cikinsa shi ya kasheta haka kuma ya kashe mahaifiyarsa sannan yake bibiyar rayuwarsa dan dukiyarsa

Du irin abubuwan nan suka taru suka saka gaba mai tsanani da rashin fahimta tsakanin dan da uban
Aman da yake buwayi gagara misali ya kaiwa kukansa
Ya duka ya zubar da komai nasa
Ya kasance babu wani abu tsakaninsa da Allahnsa wanda bai fito ya fada ba,
Ya yi kukan jin kunyar ubangijinsa da irin abubuwan da ya aikata
Ya nemawa yarsa da matarsa gafara
Ya kuma roki da ya tausasa zuciyar dansa cilo ya kasance koda shi daya zai wanki gawarsa ya yisa yana mai bi a hankali yana yi masa shinfidar kabari mai ma.ana,
Sai gashi sarkin sarakuna
Mai mulkin da ba algus
Wanda zaka roka ya baka in ka kuma roka ya kara maka ya yi ta baka ba tare da ya gotanta maka ba
Wanda zaka yiwa laifi mai tsanani idan ka tuba ya karbi tubanka harma ya daukaka ka? Mai annabi aban fati ya nuna masa ranar da dansa na cikinsa ya nemi da ya dawo kusa da shi bama a ya mutu ba
Bashi da bakin magana,
Bashi da abin mamaki
Burinsa ya kafaice ya kai sujada
Idan goshinsa a kas yakan ji kansa sakayau ne, yana jinsa a cikin nishadi kasancewa a fadar Allah, zai je ya tsaftace wajen salarsa, ya kara saka turare ya kai goshinsa kasa ya yiwa Allah kirari, ya yabi manzanninsa da sahabansa
Zai rubar da hawayen farin ciki kafin ya tatara ya kaura kusa da shi

Cikin muryar farin ciki ya ce" Abdallah, Alhamdulilah

Abdul kansa dake jin dadi har ransa ya ce" Abih, zan so ka zauna cikin gidana, kusa da mu duka , Abih zan so matana su yi zumunci da soyayar junansu, zan so su zauna da ni da zuciya daya
Abih, basa fada, basa gaba, sai dai basa shiga harkar junna kuma daya bata damu da halin da yar uwarta ke ciki ba

Shiru Abih ya yi , tun da ya ce ya koma cikin gidansa da zama da ta fado masa a rai,
Da gaske ya huce harma zai yarda ya zauna tare da matansa bayan ya afkawa yarsa ta cikinsa????

Abdul ne ya katse masa tunaninsa ta hanyar fadin" yanzu ita Kauriyata dake cikin wannan yannayin idan aka yi katarin tana da wani bukatar ni kuwa bana nan sai dai ta yi hakuri? An ce ba.a son mai ciki ta nemi abu ta rasa, idanma haihuwa ta kamata bana nan yaya za.a yi kennan? Ko hali na rashin lafia?

Wani murmushin ya saki a fili ya ce" inyeh, zan zama papy? Ita maman malan din?

Shiru abdul ya yi, sai kuma ya ji wani yannayi mai shige da kunya ya kama shi,
A hankali ya kashe kiran yana sosa bayan keyarsa yana murmushi,

Message ya shigo masa mai tsayi , budawa ya yi ya karanta kamar haka" kai zaka zama jajirtacen namiji a cikin gidanka Abdu, kai zaka hada kan matanka, sannan ka yi ta adu.a
Zan dawo cikin gari kusa da kai aman ba zan zauna da tsufana da komai a cikin gidanka ba , aa ba zan sakawa yara ido ba, zan dai kama wani gidan da ya fi kusa da kai, sannan ka sani ba zan lamunce su dorawa dana daya cilo hawan jini ba, koma waye zan dauki tsatsauran mataki a kansa ehe!

Murmushi Abdul ya saki, sai kuma ya rubuta
"HARDA KAURIYATA ABIH?

murmushin shima ya yi ya ce" *Eh harda maman malan, kai koda kai da kanka ne*

Jinsa yake cikin nishadi, karshe dai hirar haka ta kare ya dauki hudubar Abansa cewa ya yi masu jan ido idan suka ki shirya kansu, zaman kishi ai ba hauka bane, kuma aure sunnan ma.aiki ce

Hafsat dake gidansu yau ta yi matukar mamakin irin yanda mamanta ta ringa nan nan da ita,
Bata gama mamakin ba aka shigo da kayan kwadayi wai malan ya ce a kawowa mamansa
Ai kuwa ta hau tande tande tana murna dan kuwa azumi tun a wajen likita ya fice domin sai da ta cika cikinta da ruwa kafin a yi mata aikin da farko ta so kiyawa Abdallah ya ce shi ai dama ba da izininsa ta dauki azumi ba, ita dai bata ce da su ga abinda ta kunso ba, kuma bata fahimci sun fahimci hakan ba sai ta dauka dan ta jima basu hadu bane ya saka su yin nan nan da ita
Halayen matan mahaifinta na nan yanda suke, amarya ce ta yi yaji wai malan ya kwashe kayan abinci kaf da dukiyarsa ya aikawa yarsa sai kace ita daya ya malaka wai gara bayan mijinta ya ce ya hutashe shi aman ya cika motoci aka kaiwa maman malan abinda bai taba yiwa wata yar ba dan rashin adalci irin nata bayan malan din bai yiwa mamansa kayan daki ba, wannan din ma fin karfin abdallah ya yi!

Ita dai sha.aninta ta wuni yi hankali kwonce,, nan kafarta ta mike jikintama haka ta samu ta samu walwallah sosai domin kadaici mugun ciwo ne

Sai yama Abdallah ya je daukanta nan ya shiga ya gaishe da su mama cikin jin kunya da girmamawa kafin suke mikewa su fice

Sai da ya yi yawo da ita a garin Niamey har kiraye kirayen sallar magarib ya fara kafin ya dakata wani waje su gabatar da sallah baki dayansu domin nesa suke da gida

Sai bayan sun gama ya dauki hanyar gidansu ,

Yana tafe yana yi mata hira cikin nutsuwa da birgewa suna cikin nishadi har suka karasa gidansu

Yanzunma fitowa ya yi ya bude mata sannan ya kamo hannunta ta sauka daga motar

Rufewa ya yi yana rike da hannunta ya nufi bangaren Na.ima da ita

Ja ta yi da sauri ta tsaya tana kallonsa

Juyowa ya yi shima yana mai jin dar dar dan bai san yanda zai iya tankwasa kansa gaban maman malan ba!

Kallonta ya yi cikin ido ya ce" ya dai??

Hafsat ta kale shi da kyau sannan ta kalli inda zai kaita, a hankali ta ce" nan ba bangarena bane ba fa

Abdul ya lumahe idannuwansa shima cikin nutsuwar ya ce" eh na sani, zamu je ne mu yi zumunci sannan kin ga bata san fitarmu ba

Hafsat ta kara kallonsa da kyau kafin ta ce" aman ai sai ka fada mata ko? Sannan ai zamu hadu bangarenka ba sai mu yi zumuncin ba??

Tana maganar tana kokarin hadiye sauran ne sakamakon wani irin yanda fuskarsa ta fara hadewa tana hade kanta tamkar kashin safe

Takead ya yiwa fuskarsa irin bai taba dariyar nan ba,
Bai bata amsar maganarta ba ya kara jan hannunta suka je kofar fallon Na.ima

Ja ya yi ya tsaya ya danna abinda zai shaida mata da bako bangarenta

Na.ima dake zaune tana jiran lokacin zuwa bangarensa ya yi ta sha kwaliyarta daidai misali ta mike cike da mamakin waye ya zo gidanta a irin wannan lokacin? Yan aiki dai ba shiga wajensu suke a irin wannan lokacin ba, mijinta kuwa bai taba zuwa bangarenta ba bale ta kawo shi a tunanin ko shi ne

A wannan yannayin mamakin ta je ta buda kofar
Sai dai mamakin ganninsa tsaye ne ya kasheta

Murmushin da bata shirya yi bane ya kubuce mata saman fuskarta ganninsa tsaye
Sai dai gannin hannunsa rike da na mace a hankali murmushin nata ya ringa ragewa har ya bace fuskarta ta kasance babu yabo babu falasa a lokacin da ta ga wace ke tare da shi din

Gannin ta yi bake bake a bakin kofar ya saka shi cikin yannayin laushi ya ce" hajia mun zo ziyara ne ko mu juya wannan tsare hanya haka?

Na.ima ta kale shi da kyau, ta kuma kallon Hafsat
Ja ta yi gefe wanda ba haka ya dace ta yi ba a matsayin wace aka zo gidanta

Sai da suka shiga sannan ta bi bayansu jikinta du a mace tana jinsa yana waya da mai kula da harkar girkin gidan

Zama suka yi su duka, ba wace ta gaishe da yar uwarta, shi kuma bai damu ba ya dai shiga jan kowace da hira cikin hikima yake sako daya cikin hirar daya a haka har aka gabatar masu da abinci suka ci a nan bangaren nata

Sai da dare ya kara tsalawa Hafsat ta mike,
Dan murmushin iya lebe ta sakar masu kafin ta ce" Allah ya tashe mu lafia

Na.ima ta kalleta itama murmushin ta sakar mata ta amsa da " asuba ta gari

Abdul ya mike ya kashewa na.ima ido ya ce" Ina zuwa

Fita ya yi ya bi bayan Hafsat ya rakata har kofar dakinta

Gannin zata shige bata ko kale shi ba ya saka shi riko hannunta da yannayin shagwaba irin ta maza ya ce" ko dan muah babu Madame??

Hafsat ta juyo da idannuwanta da sula cika da kwallah ta jin haushinsa ta sauke su a kan fuskarsa
Haka kawai sai ta fashe da kuka ta janye hannunta ta shige bangarenta,
Ita fa kawai ya wulakantata ta, dan me zai fara kaita bayan ita bata taba takowa inda take ba? Me take takama da shi da ita bata da shi? Kallon raini da wulakanci? Dan me zai wani kwasheta ya kaita bangaren macen da bata damu da ita ba?

Abdul dake tsaye ya daburce sai dora hannunsa yake yana shafa kansa,
Tamkar ya fada dakin ya duka ya bata hakuri, sai dai ina, hadewar kansu ya fi masa komai, ya fi masa fushin su su duka

Juyawa ya yi ransa a jagule ya koma bangarensa

Yana zuwa ya tarar da Na.ima ta zo,
Tana ganninsa ta tabe baki a fili ta ce" an bi matar so kennan


Na.ima, bata san dawan garin ba da bata yarda ta yi furucinta ba, bata san a kan tsani yake ba, bata san kiris yake jira ya fashe ba, bata san ta tabo tsuliyal dodo ba sai da ya budi baki bayan ya ja ya toge ya dafe tsatsonsa da hannunsa na hagu ya nunota da manuniyar hannunsa na dama ya kankance idannuwansa ya ce"



>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




7?? 0??


Wato ga sakarai wawa marar hankali
Ga dan iskan nan ya dawo
Ga danki da kika tsana bara ki sauke masa kwondon rashin kutunci
Wato ga shegen nan ya dawo
To Na.ima sai ki mike ki ciro wayar jikin bangon dakinki ki ki lakada min dukan jaki kin ji?

Au, girmama kin da na yi na dauke ta na kaita bangarenki dan ku yi zumunci ne laifina ko me?
Shin ku dukanku marainin ku nine?
To bara ku ji baki dayanku, bilahilazi karya kuke! Ni ba sakaran namiji bane au ku hade kanku au na dauko rigar rashin mutunci na yafa na yarfa maku kalar nawa takun sai a auna a ma.auni idan naku ya fi rinjaye zan sadako! Kan muradina ba abinda ba zan iya yi ba, muradina a wajenku kuwa shi ne ku hade kanku ku yi zumunci! Abdaul jabar nake haihuwar Mina girman maka ni da ku shege ka fasa!


Yana gama fada ya ja tsaki ya juya dan komawa bangaren Hafsar domin ya ga alamun idan har ya yi sanya zasu mayar da shi wani sauna ne zancen ya tafi a shashance


Yana zuwa turawa ya yi ya shige uwar dakanta ba tare da ya nemi izini ko wani

52 / 54