Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   5 / 54

12K to 15K   out of 159.5K words

zuwa ya samu Muhammad ya gama shiryawa, shima cikin shirin manyan kaya kamar yanda Abdul din ya saka irin dinkin yan nigeria , shada har da hula kuma du sun karbe su sun fito da su das gwannin sha.awa,

Muhammad ya dube shi da kyau bayan sun gaisa ya ce" yanzu sai ka je daurin auren nan Abdul? Kai wai ina ruwanka ne ma da shiga wannan lamarin? Shi mahaifin nata ba ya san daga inda ya daukota ba? Kuma dai ya san ba zikiri ake a wajen ba abinda ya kaita take yi ba wata damuwa, to yanzu dan zai mata aure fisabililahi Abdul sai ka wani saka mu shiga ta mutunci tamkar zamu je yin abib kirki ?

Abdul ya zauna saman kujera yana dubansa ya ce" Muhammad, Muhammad ya rab, Muhammad kana so kennan mu zuba ido a daura mata aure bayan da dati a jikinta? Ina laifin ta kilace kanta har datin dake jikinta ya barta? Shi kennan dan son kai sai ya rufe ya baiwa wani? Ka ga idan zaka bi ni aikin Allah tashi mu je, idan kuwa tsoron mutanen dubiya ya fiye maka aikin ubangijinka kuma Fine, ai yana kallon ka

Muhammad kam ya shiga cikin tsaka mai wuya, ya dirmiya shi a cikin lamarin shaku kuma ya hada shi da Allah, shi bai san yaya zai yi ba, walahi yana son barin garin aman irin hadarin da Abdul ke shiga ya hana shi motsawa, yanzu mai gaba daya zai dulmiya su a wani lamarin

Turarensa ya kara fesawa, ya gyara zaman hularsa, wato ya kafeta a kansa sannan ya dubi Abdul ya yi gaba ya fara tafia

Murmushi Abdul ya yi ya mike shima ya bi bayansa suka fito gaba dayansu,

Sai da suka fito farfajiyar gidan ya tsaya yana sauraron BS dake masa bayannin an kawo wa.inda zasu dauki wajen bodyguards dinsa da aka harba

Juyawa Abdul ya yi da bakin gilas din idannuwansa ya shiga bin su da kallo,
Wanda aka kawo namijin sosai ya girm8 jibrin, alamun karfi da jajircewa sun bayana a tare da shi, sai macen wata yar dagwas da ita yar kwalisa, duda uban ramar dake jikinta dan kuwa bata da jiki ko kadan gaba daya ta gama horuwa ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ko.inanta ya sabe ya zube aman kyakyawa ce dan lebenta harda dan jan bakinta kalar ja, haka ya kai dubansa wajen jibrin ya ga sai da aka talabe shi du kuwa yanda yake son ya tsaya da kansa ya kasa dan a ciki aka same shi, sai ko Hafsat dake tsaye kikam, ba wata fara.a, ba alamun komai a tare da ita ba zaka gane hallin da take ciki ba, ita dai a tsaye take,
Bin suturar jikinta ya yi da kallo har takalmi sau cikin da ta saka kafin ya maida dubansa wajen BS,
Kai tsaye ya ce" suna iya juyawa da Namijin, aman a bar matan biyu da wanda aka kawo yanzu............................... ya karashe yana mai kara hade girar sama da ta kasa , ya ci wata irin fuska da ta saka bakin gilashin kansa kara fitar da mazakuntar fuskar yana duban BS tsai a gabansa!


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




3??


*Free page*









Koda suka dawo hayacinsu, du sun jigata, domin duka kai sun sha shi, haka suka zuba idon a sake su? Aman shiru,

Wasa wasa suka kwana a gidan nan, nan fa hanali ya fara tashi, cikin gari iyaye na cigiya, cikin police station yaya na zuba ido,

Ba.a wani dauki lokaci ba aka shiga kwasarsu zuwa kotu da su,
Tabas sun ga ikon Allah, ashe sojawa sun biyo wasu yan fashi ne suka fantsama gari, au kuwa yan gari masu zaman banza da neman fitina suka fara jifansu, hakan ya hadasa fada da tashin hankalin da ya si kuwa du suka kwaso su suka zuba gidan kason,

Hankali bai gama tashi ba sai da ta ganta sanye da ancor, an tiso keyarta an sakata a mota,
An gabatar da ita gaban alkali a matsayin daya daga cikin yan fashin,
Bata gama tsurewa da mamaki ba sai da ta ji lauyan nan ya mike ya lauyo karyar wai itace budurwar shugaban yan fashin, dan haka kotu mai adalci ta yanke mata hukunci daidai da laifinta na zama yar fashi a kasa, sanann ta fito da saurayinta,
Gabanta bai buga ba sai da ta yi ido hudu da alkalin da ya dage yana zazago hujojin karya, da nadidiya karyayaki kan ita din muguwa ce ta ga ai mijin kanwar maman Abdul karim ne, innalihi wa ina ilaihi raj.une, mutumen da ta dudurawa ashar dan ya tareta ya tambayeta dan me ta mari matarsa ita da take sarakuwarta? Mutumen da ta yiwa ihun kwarto dan zai wanka mata mari hakan ya saka shi guduwa bai shirya ba, sam ya ki jinnin ganninta ko jin labarinta, yau shi ne tsaye a matsayin wanda zai dulmiyar da ita,

(Bincikena ya nunan cewa tabas kana iya samun kanka a irin wannan prison da ba.a kai kowa sai manyan yan fashi, wa.inda suka kashe mutane, ko wa.inda suke kaso suna karawa cikin babar prison mai cike da rashin tausayi, rashin imani, tsaro na gangariya, rayuwar kunci, irinta ba sai idan mutun ya aikata laifin nan mai muni, ko kuwa wajen sharia *LAUYAN DA ZAI YI JA SHARI.AR YA KASANCE YA YI YANDA YA YI YA NUNAWA ALKALI KAI DIN NAN HAKAN TAKE MAI LAIFIN DA YA CANCANCI WANNAN HUKUNCIN NE* dan haka kana iya riskar kanka a ciki),

Sosai ya saka dukan wata hanyar da zai bi, a matsayinsa na lauyan da ya kware a harkar, ya nunata a matsayin budurwar baban yan fashin, inda aka nemi da ko tana da magana?
Cikin ikon Allah ta budi baki ta nuna shi da yatsa ta ce" ni zaka yiwa shari Kadre? Walahi sai na rama, sai na fadawa Malan, sai na ja maka yaseen!,

Tsawatar mata alkali ya yi, kafin a yanke mata hukucin zaman gidan yari, gidan yarinma *KUTKALE* na tsayin shelara goma, aman idan har ta fido da saurayin nata zata samu sasaucin shekarun, a lokacin shekarunta ashirin,

Wannan shi ne mafarin shigarta gidan yari, wannan shi ne dalilin da ta tsinci kanta a gidan yari,
Gidan yarin da mahifanta basu san tana can ba, domin sun yi cigiyar, su ne har asibiti wajen da ake ajiye gawarwakin mutanen da ba.a ga yan uwansu ba, su ne kauyuka, su ne gidan yarin dake xikin gari, su ne jarda kai karar Abdul karim aman ga dukan bincike bashi da masaniya a lamarin, haka mahaifinta ya daura aurenta domin bai fasa ba, aka ci gaba da nemanta, inda yaron na dagawa a ranar da aka daura auren uwarsa ta saka shi sakin auren domin ba zata aminta a yi mata wannan gangancin ba a aura masa yar da bata san darajar iyayenta ba, dan kuwa du ta samu labarun irin abubuwan da take, a ranar ne wajen daurin aurenta du yan unguwar suka ji ainahin sunanta wato ...............


Ci gaba


Fadan nan bai mutu da dadi ba har sai da aka kuma kiran sojojin nan suka shiga tsakani,

Surfe aka zuba masu na abincin ranar da za.a yi, dawa ce, dan haka du wanda bashi da galihu a gidan yarin ya shiga dukan sirfen ba ji ba gani, ciki harda ita cikin yannayin galabaita aman tana yi dan du wanda ya bari za.a zabga masa bulala ne,

Cikin prison din nan, du wanda ya saki kansa, ko nace du wanda bashi da daurin ginda zai zama tamkar gida, du wani kato na iya shigarsa ya fita son ransa, du wanda ya yarda da haka zai samu kariya da kuma shiryawa da kowa a gidan,
Sannan mata ma tsakaninsu suna watsewarsu son ransu,
Watanta takwas kennan da shigowa gidan, a kulun kiyayarta kara daukaka take domin za.a yi du masifar da za.a yi da ita kan jikinta da kuma zagin iyayenta,


Suna tsakar dakan nan aka shigo aka kirayi sunnanta kamar haka *ZAHRA* ta fito,

Shiru gurin ya yi, wata mai sunnan zahra ta mike dan tafia aman sai aka ce ba ita ba,
Dakan da take ta dakatar ta hanyar cire tabaryar ta daga cikin turmin, hade fuskarta ta yi kafin ta dauki hanyar fita waje dan tafia,

Eliz ce ta ce" yau na ga jaraba gannin idona, yau kuma sunnanki ZAHRA? Ke wai wace irin masiface ta fado mana gidan yari rana tsaka? Ni kam na fara tunanin bakya baiwa yan nan sai yan can, shegiya karuwar sojoji,

Juyowa ta yi ta nuno yatsarta, saka yatsar ta yi a bakinta kafin ta fitar ta ce" kin san bilahilazi, kika kuma ce min karuwa sai na kwakwalo idannuwanki kina barci, kin dai san na san lokacin barcin kowa, kuma ina rigayen kowa tashi ko? To mu zuba , ba sarkin matan prison kike ba, koda kuwa uwar me sai na mayar da ke makauniya!

Ido du suka zaro da mamaki, Eliz dai bagwariya ce da ta fito daga kudu, bata da adini, bata da haramun, ta kasance fitinaniya, masifafiya, ya jaraba, shekarunta uku yanzu a gidan yarin sanadiyar kisan kai da ta yi na mutun biyu a cikin tafiarsu ta hijira dan dauke kudinsu na guzuri inda polisan hanya suka kama su suka kamata da laifin aka so mayar da ita garinta su mata hukunci a can sai dai gwamnatinta ta ce idan an kawotama harbeta ne za.a yi, a niger babu Loi din harbe mutun koda ya yi kisa hakan ya saka suka sakata kaso daurin rai da rai,

Tunda ta zo kason sai da ta san yanda ta yi ta zama shugaba, kowa tsoronta yake tamkar rai, basa haye mata, dan ta fada ta kara kashe wani ba damuwarta bane dama ta shigo ne da niyar a fitar da gawarta bata da matsala da hakan!

Haka aka fitar da ita, aka nufi inda ake son gannin nata, nan ta bar su kowa jikinsa mace dan sun san yau ba su ba barci, za.a sha masifa ta bugu da kari!

Turata ya yi dan dakin sannan ya ja ya tsaya yana muzurai,

Daman ta san shi ne, bata san tambayoyin me yake mata ba, bata san me yake nufi da ita ba,

Tana shiga ta kara kallon yannayinsa, a ranta ta ayana ban taba gannin fuska marar annuri irin taka ba,

Shima dake zaune fuska hade ya mike ya dauki abin auna tsayin mutun ya auna tsayinta,
Hannunsa ya daga a lokacin da take tsaye ya zabga mata wani wawan mari wanda ya sa ta daku da jikin bangon wajen,
Da sauri ta taro kanta sannan ta mike tsaye tana dubansa ido cikin ido,

Dakin take bi da kallo, ba komai ciki sai bindiga daya kwal dake ajiye saman table din da ya tashi daga sama,

Da gudu ta nufi wajen bindigar ta dauka ta saita shi ta firfito da idannuwanta ta daga muryarta da kyau ta ce" kai mahaukaci! Me na maka? Me na maka? Uban me kake zuwa nema wajena? Ko jira kake kaima na daga maka jiki? Kan haka zan iya harbeka dan Walahi malan ba zai yi kukan na rasa mutuncina a waje ba! Koda kuwa gawata zama fitar daga wannan bakin gidan!

Da sauri guard din dake waje ya shigo ya nufeta dan karbe bindigar, ai kuwa ta dana ta kara dana kunamar bindigar, sai dai ba alburushi a ciki,
A haka ya karbe yana mai jin zuciyarsa na bugawa dan kuwa shima bai san ba alburushi a ciki ba, ya dauka ya gama mutuwa kennan,

Datijo ne mutumen da ya gannin nata dan haka ya zagaya ya koma wajen zamansa,

Wayarsa ya ciro ya canza harshe zuwa yaren french ya ce" na yarda da taurin zuciyarta, girman mutun, yannayin fuskarsa, ko karfin mulkinsa ba zai sakata yin dar ba idan ta hado su, tsayinta ya kai daidai a dauketa , bata da kakauran jikin da zai hanata daukan formation, zan saka rana a sakata cikin wa.inda aka dauka,

Shiru ya yi yana gannin yanda take waiwayensa bayan an fitar da ita sannan ya ci gaba da fadin" tabas idan ta samu mugun horo, zata kara tsayuwa saman kafafuwanta, zamu dauketa mu bata horo na wata biyar, zata fito a matsayin *BODYGUARD SECRET* zamu bata horo kala daban daban, zamu bata horo na tausasa murya, zamu bata horo na kalolin yaudara, zamu bata horo na jure azaba komai girmanta, sannan zamu horata da yin biyaya,

Shiru ya kuma yi inda ake masa bayanin an gamsu da kyanta? An gamsu da girman gayunta? An gamsu da girman iliminta? An tabatar tana jin yare biyar *HAUSA, FRENCH, TURANCI, LARABCI, DA ZABARMANCI?*

murmushi ya yi ya ce sunnanta na gaskiya shi ne *HAFSAT MUHAMAD SA.IT*, yare tara take ji, gaba daya kwaya biyu ne na iyayenta, sayran ta koye su ruwa ruwa je a makaranta zama da masu iya yaren, yarinyar kamar computer take, tana dauke abu nan da nan ba tare da ta sha wahala ba, tun da ta shiga makaranta itace ta fari har zuwa faruwar kadararta, gasa ta school da islamiya sai dai idan ra.ayi ya hanata shiga, in dai ta shiga sai ta lashe,
Tana da kakarfar zuciyar da na yi na.am da ita,
Shekara ashirin kennan ina horon sojoji, polisai, guard, Body guards, ban taba tsayuwa gaban mutun mace ko namiji muka kali juna ido cikin ido ba tare da ya sada kansa ba sai wannan yarinyar, zuwan da nake dan duba yannayin mutanen kason dan zaban wanda zan dauka har na isheta yau ta nuna min bindiga danma bana ajiye bindiga da alburushi da ta dana ta harbe Guard dina,

Haka suka gama magana kafin ya fito ya nufi motarsa inda suka sara masa aka ja shi aka fice da shi .......




Wannan kennan .
..


Ku biyo ni ku sha labari....=?
?


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




6??


*Free page*


*SALAM, ZAKU GA WASU ABUBUWA CIKIN WANNAN RUBUTU NAWA, KAMAWA TA YI, WANI ABIN YA ZAMA DOLE NA SAKA SHI, DAN HAKA KU BIYO NI=?O?


Cikin dakakiyar murya ya ce" kafin ku shigo gidan nan kun yi gudu na kilometa 4 a minti talatin, to yau zaku yi 6 a minti ashirin, ba tserere bane, domin so muke ku zo gaba dayanku a tare, kar wani ya rigayi wani zuwa, kar kuma a bar wani a baya, akoy mai tambaya ne?

Shiru du suka yi domin kuwa kida sunada tambayar ba zasu iya yinta a wannan mutumen marar annurin ba, taf idannuwansa kansu wasu jajajir ne kamar an watsa masa barkono, kai ko da hakoran bakinsa ya cikeja ya tada ka tsaye domin dogaye ne, dan haka du suka yi shiru suna tunanin abin,

Kara maimaita tambayar ba mai magana ya yi?

Tsagal ta ce" wani irin mu zo a tare? A tare zamu yi aiki ne? Ko akoy aikin da za.a iya tura mu tare da sharadin sai mun dawo a tare daya ta kula da ran daya?

Datijon nan ne ya saki murmushi yana dubanta kafin ya gyada kansa,
Sai a lokacin ya matso inda saurayin ya dan matsa masa gefe,

Datijon ya dube su ya ce" ya zaku tsaya gaban mutun ya zayano maku maganganu kuna sauraronsa kuma kuna kallonsa, cikin hankalinku, ba maye kuka yi ba, ba duka kuka sha ba, bayan kun san abinda kuka zo yi , horon aikin zama Bodyguard wanda a kaf cikinku za.a dauki mutun uku zuwa hudu, sauran sai dai a yi wani wajen da su, bayan kun zana jarabawa an tabatar maku da abubuwa na wannan aiki, aiki ne na individual (mutun daya), shi ne za.a ce da ku wajen gudu ku karaso tare tamkar tayar mota da aka daidaita wajen hakan sai kawai ku hafiye?
Murmushi ya yi irin na mugunta kafin ya dubi

5 / 54