Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   29 / 54

84K to 87K   out of 159.5K words

ya san me ake yi a cikin dakin, basu da katabus sai ido, dan kuwa rabonsa da ya je dakinta tun da ya mayar da ita cikakiyar mace, ya kasance ita ke zuwa kowani lokaci ya bukaci hakan bisa abinda ya dora mata

A lokacin da suka ji karan buda kofar kowa ya kawar da kansa sannan ya kimtsa kansa,

BS kuwa murmushi ya sakarwa Hafsat yana mai yi mata nuni da ba ta gani ba?

A lokacin da Ni.ima ta fito daga dakin ta yi gaba suka bi bayanta Hafsat ta mike ta nufi dakin da niyar shiga,.

Damtsen hannunta BS ya rike ya saka idannuwansa cikin nata ya ce" zaki je ki wanke abinda baki saka bane ko zaki je ya gama koshi? Ki farka, ko aure yake ba zai aure ki ba!

Hannunta ta fuzge daga rikon da ya yi mata, ta zabga masa wani harar tsana zata yi magana kennan idannuwanta suka sauka saman Abdul dake tsaye yana hangen su,

Kwafa ta yi ta nufi dakin da niyar idan ta fito zata kirta masa rashin mutuncin da ba zai taba mantawa da ita ba

Tana shiga ta rufe dakin ta yi tsaye gabansa,
Da alama bai jima da fitowa daga wanka ba dan kuwa jalabiyar jikinsa na like masa a jikin,

Kawar da fuskarta ta yi dan ita ta tsani wannan kallon rashin kunyar da yake yiwa mutane, sam bai iya kallon adini ba!

Ba wani kwane kwane ta ce" *Abdul, ka hana a tafi da ni gobe, dan Allah=?O?
Dan karamin tawul din da yake tsane kansa ya dan yarfe ya matso kusa da ita a hankali ya ce" kin shaku da dan baiwa Abdul ne kema? Wai ya aka yi mata basa son yin nesa da ni ne?

Bata san lokacin da ta dawo da dubanta wajensa ba, kai wannan mutun idan da asirima to walahi da hali,
Kanta kawai ta iya girgiza masa kafin ta yiwa fuskarta kalar kaucona ni Hafsat,

Abdul ya dora mata tawul din mai dan lema lema wanda ya gama gogo ruwan kansa a kafadarta ya yi gaba ,

Janye tawul din ta yi ta ajiye nan tana yatsina fuska ta juya inda ya nufa ,
Gani ta yi ya ciro karamin wando yana kokarin saka abinsa bayan ya san tana dakin
Da sauri ta juya gaba dayanta, inda ya saci kallonta ya yi murmushi tare da girgiza kansa,
Wandon ya saka sannan ya mike da kyau ya nufi wajen bed dinsa ya zauna,
Fuskarsa ya talabe da hannu daya yana kallonta kafin ya yi gyaran murya

Idannuwanta ta bude a hankali, ganninsa zaune ya sakata sauke ajiyar zuciya,
Wajensa ta nufa, ta samu waje ta zauna tana dubansa a sace sannan ta ce " dan Allah, ka yi min alfarmar nan,

Abdul ya saki talabe fuskar tasa da ya yi ya ce" dalili?

Hafsat ta tsayar da dubanta kansa ta ce" savoda ina son na gama aikina daga nan lafia, ina son inci,

Abdul ya tabe bakinsa sannan ya kuma dubanta ya ce" ke yanzu kina mace har wani inci kike tunanin samu? Tafia ta yi tafia fa aure za.a maki, ki je ki yiwa mijin bauta, yi na yi bari na bari, ki masa girki, ki yi shara, ya maki ciki ki haihu ki shayar da su daga shi har yaron ki rin.....

Dan Allah ya isa, wai kai da kowama haka kake magana marar da.a ko nice kake yiwa kallo mn yar bariki? Ka je ka yiwa matarka mana? Sai ka 2ani saki baki kanai min magangannu mararsa da.a? An gaya maka ni yar iska ce?

Kallon da yake mata ne ya sakata tunawa da a gaban wa take,
Hakan ya sakata yin sororo, tsawa fa ta daka masa, ta yi masa tsawa , bayan yana mai gidanta kuma ta zo neman alfarmarsa ne?

Nan da nan idannuwanta suka ciko da kwala,
Juyawa ta yi ta shiga tafia a hankali tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki,
Har ta kusa fita ta ja ta tsaya tare da juyawa ta dube shi , a hankali ta ce" ka manta abinda na zo nema, dan ban ga anfanin karasa aiki a cikin irin wannan rayuwar ba,

Hawayen idannuwanta ne suka zubo daga kwarmin idon, muryarta ta shiga rawa ta bude dakin ta dago da idannuwanta ta dube shi ta ce" *ni ba yar iska bace Abdul*

Sakin kofar ta yi ta fice a dakin da saurin gaske, inda ya mike da sauri ya sauko daga saman bed din da niyar bin bayanta, sai dai me ya tuna, me ya hana shi? Ya dakata ya dafe goshinsa da yake jin ya wani irin sara masa,
Hannunsa ya kai wajen madubin dakin nasa ya daka da mugun karfi kafin ya saki ihu mai cin rai

Idannuwansa ya dago ya kai dubansa wajen madubin, yana mai jin zuciyarsa na wani irin tafarfasa, jajayen idannuwansa ya kai wajen da ta tsaya a hankali ya ce" ba zan kuma yarda na saka rayuwar wani a hatsari ba Hafsat, ki gane.....ni kuma ba mahaukaci bane soyaya aka hana min yi karfi da yaji..............

Wani murmushi mai kama da na yake ya yi mai ciwo sannan ya ce"
*kWANA goma sha uku kacal, kwana goma sha uku kacal kina faman tarwatsa ni? Ba zan baki wannan damar ba, na fi kowa sannin ke ba yar iska bace Hafsat! Aman zan je da ke a yar iskana=??*


=???

>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4?? 3??


Jiki a sanyaye ta ce" idan zaka iya aurena a yanda nake, ka zauna da ni a haka, ni me zai hana na amince da soyayarka?

Daidai sun karaso aeroprt kennan ya ja ya tsaya yana kallonta,
Wani murmushi ya sakar mata kafin ya ce" da Sire ya salame mu, zaki gan ni, zan zo neman aurenki, zan koya maki so na domin kuwa a yanzu ba sai an fada min ba, ba soyayata a tare da ke, bana son ki amince min dan kina tunanin na cancanci haka, ina so ki so ni dan na cika namiji

Shanyayun idannuwanta ta lumshe sannan ta bude motar ta fita

Nan wajen motar suka zauna har aka kawo malan cikin wata motar harda masu yi masa rakiya

Suna sauka basu jima sosai ba jirgi ya sauka , man ya kara kwasar yan Niger suka daga

Malan da Hafsat sai dai su sakarwa junna murmushi lokaci zuwa lokaci

A lokacin da jirgi ya sauka motoci ne suka zo daukan su wa.inda ta yi mamakin hakan,
Sai dai a lokacin da suka zo shiga ta gane daga abdul ne domin mai jagorar motocin ya shaidawa Malan daga wajen Oga Abdul Jabar ne

Shiru sukai cikin motar mai sanyi ga kamshi su duka,

A lokacin da aka shigo anguwarsu sai ta ringa jin gabanta na matsananciyar faduwa,
Du masu zazaune da ido suka ringa bin motoci ukun dake shigewa da matsiyacin gudu har suka ja suka tsaya kofar gidan malan

Dubansa ya kai kan Hafsat da ta yi tsuru da ita, gashi wando dogo ne a jikinta sai dan kwalin da ta yane kanta da riga mai dan dogon hannu aman kuma bata da wani tsayin a zo a gani
A hankali ya ce" bakya murna ne???

Da sauri ta kai dubanta kansa, sai kuma ta sada kanta,
Tunaninta idan ta fita a irin wannan shigar da wannan yannayin me mutanen anguwar nan zasu kaleta da shi? Ta tabata koda za ta bi layin da ihun rantsuwar ba daga yawon bariki take ba, ba wanda zai yarda sai dai ma a kara tsanarta

A hankali malan ya ce" menene mamana?

Idannuwanta da suka cika da kwallah ta dago ta kali mahaifinta,
Sai da ta ja hanci sannan ta ce" Abana, idan na fita a haka, zan kara jaza maku zagi ne da kai da mamana

Murmushi ya saki wanda daga zuciyarsa ya fito, a cikin ransa ya furta alhamdulilah, ko ba komai duniya ta ladaftar masa da yarinyarsa, yo da da ne ko shigar da ta fi haka muni zata saka kafa ta fice abinta ba abinda ya dame ta da wai kar a zageta ko ta ji kunyar wani ba, a haka kuma idan mai tsautsayi ya yarda ya yi mata wani kallo su cashi junna

Hannayenta malan ya riko yana kallon yanda du ta takure kanta, cikin nutsuwa ya ce" ki ji tsoron Allah Uwata ba wani ba, kin ji? Mu tafi

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon yanda Almajirai suka tataru suna masu nuna murnar gannin malan ne ya dawo harda yan rakiya a yau tsal , da yake yama ta yi sosai mutane du sun dadawo daga nema

Malan ya fara fitowa , nan ya shiga mikawa jama.ar hannu suna gaisawa cikin harda baban dansa

A hankali ta sako kafarta mai sanye da takalmi sau ciki mai dan tudu baki kirin na aiki

Gaba daya hankalin mutanen ne ya fara yowa wajen, a haka har ta fito gaba dayanta

Ai kuwa magangannu ne kasa kasa suka fara tashi, ba dan ba.a saba ganninta da shigar wando da riga ba, ba dan ba.a saba ganninta da takalmi , kai kanta ko fan kwali bata sakawa a da aman a yanzu da dan kwalinta a rufe a kan hakan bai hana mutane mamakin ganninta harda fadin ta dawo daga yawon kennan
Wasu kuwa kasa kasa su ce ita kuwa ba zata shiryu ba jiya i yau? Duniya ta horata kennan?
Kiri kiri wajen ya nemi hautsinewa da dan hayaniya dan kuwa har matan anguwar sun fara lekowa ganewa idannuwansu wai da gaske UWAR malan ce ta dawo?

A hankali ta zagaya mazan nan da suka tare hanya ta shiga cikin gidansu

Tana shiga ta tarar da wata bakuwa bakin baban fanfon tsakar gidan ta tara abin wanke shinkafa tana tarar ruwa da alama girki take yi

Tsayuwa ta yi tana bin gidan da kallo, dan kwata kwata ta shagala da shaukin ganninta a gidan ko salamar ma ta kasa yi

Matar ce ta tsura mata ido tana kallonta dan bata santa ba, batama taba ganninta ba kanwa take a wajen daya daga cikin matan malan ta zo hutun makaranta ne

A dan kiririce ta ce" ke, ke kuwa wacece malama zaki shigo gidan mutane da irin wannan shigar tamkar arniya ko an fada maki gidan nan yana daukan arnawa ne??

Da sauri ta kai dubanta kan matar, dai dai nan matan gifan suka fara fitowa jin hayaniyar nan, haka kuma daidai lokacin malan ya shigo cikin gidan

Gannin Hafsat tsaye ya ce" aa, Uwata me kike tsaye nan sai kace baki san waje ba?

A daidai lokacin da ta juyo dan kallon malan kunnayenta suka jiyo murya a hankali cikin zazakar muryar nan irin nata an ce" *ANMIH*

Da sauri ta juyo haka kuma lokaci daya ta damko hannun mahaifinta

Shima tsayuwa ya yi suna kallon mahaifiyarta dake sanye da wani zumbulelen hijab mai ruwan milk wanda ya rufe mata ilahirin jikinta sai hannunta da fuskarta dake waje,
Tsaf tsaf da ita sai yar ramar da ta yi aman fatar jikinta lufluf daga fuskar da kuma hannayen

Sai da ta lumshe idannuwanta, hawayen dake ciki suka fito sannan ta dago mata hannayenta irin ta zo din nan

Hannayen malan ta saki ta daga kafarta da mugun gudu ta je ta fada jikin mahaifiyarta lokaci daya kuma ta fashe da kuka.....
Tana kukan ta ce" baki yi fushi da ni ba? Ashe ba zaki juya min baya ba? Du laifin nan da na yi maki Ummana?

Bayanta take taping a hankali, sai a lokacin ta tuna a tsakar gida suke kuma ta tabata abokanan zamanta na wajen,

A hankali ta zame jikinta a nata dan a duniya irin mugun kawaicinta da kunyarta? Tana zamewa ta sada kanta bata kuma kallon kowa ba ta shige ciki tana share hawayen kukan farin cikin da ta yi,

Tana shiga Malan ya saki murmushi, yana matsayin girmama lamarin matar nan tasa a nan gidan duniya, sam bai bata labarin inda mamansa take ba, rana tsaka ta shigo gidan da shiga irin ta wada ba.a so, aman bata mike ta shiga jaye jayen jafa.i da mugayen magangannu ba sai nuna tsantsar farin cikinta da ta yi har ta kasa boyewa, bata yi mumunar magana kamar cewa daga yawon duniyarta take ko makamancin hakan ba, sai riketa da ta yi ta nuna mata ta yi missing dinta haka kuma halayanta ba zasu saka ta gujeta ba,

Yana kallo Hafsat ta gaisar da sauran matayen nasa da suka yi cirko cirko wasu na tsoron jarababiya ta dawo, wasu na mamakin wani abin sai a gidan malan yarinya ta je ta yi yawon duniya ta dawo gida anai mata oyoyo

Basu iya amsata ba, sai saurin kauce mata suka bata waje ta shige wajen mahaifiyarta

Juyawa ya yi ya fice a gidan bai ko amsa gaisuwar da suke yi masa na sannu da zuwa ba, dan ba zai iya rufe ido a irin lamarinsu ba

Babar dake cikin matansu ce ta kama habarta ta ce " to fa, uwar masu gidan ta dawo mun shiga uku da ranmu kowace ta yi ta kanta domin a kanta malan sai ya saki mace ko ya tsinewa d'a

Nan fa suka shiga cicira maganar wanda hakan ke iske har inda su Hafsat suke , tana zaune mahaifiyarya sai kwararo adu.o.i take tana godewa Allah

A wannan rana mahaifiyarta ta kai mata ruwan wanka masu dumin gaske, ta tsaya ta yi wanka sun dawo daki, ta bata man zafi ta shafe jikinta haka kuma ta saka abin gasa jiki ta ringa gasa mata gefen fuskarta, ta bata madara hade da maltina ta shanye sannan ta yi mata shinfida saman gadonta dakinta ta kwonta saman lalausan bargonta kafin ta rufa mata lalausan bargonta ta kuna mata panka

Ajiyar zuciya ta ringa saukewa tana hangen mahaifiyarta ta tsura mata ido, bata tambayeta daga ina take ba har yanzu, du dai wani takunta tana biye da shi , sai dai abu daya da maman nata ta yi mata shi ne a lokacin da ta fito a wanka ta dawo daki ta umarceta da ta kwonta zata dubata,
Bata wani damu da hakan ba, hasalima bata san me hakan ke nufi ba dan kuwa ta jima tana mata irin haka ko can baya, irin idan ta cika daren nan da safe sai ta duba ta,

A lokacin da ta gama dubanta kuwa sai ta ga murmushi kan leben mahaifiyar nata, tabas mama ta yi farin cikin abinda ta gani hakan ya sakata kwonciya itama a lokacin da ta fahimci Hafsat ta yi baci itama ta kwontar da hakarkarinta

A washe gari ba ita ta farka ba sai wajen karfe tara dan kuwa tsakiyar dare al.adarta ne ya tasheta ta kimtsa kanta ta koma

Wanka ta fito ta yi cikin nutsuwa sanann ta koma dakin mahaifiyarta

Har kasa ta duka tana gaishe da mamanta hakan ya sakata tsayawa tsai cike da mamaki tana kallonta,

Kasa rike tambayarta ta yi, dan haka ta ce" *ANMIH, INA KIKA JE? ME YA SAME KI? ME AKAI MAKI?*


HAFSAT ta dago da dubanta, ko a yanzun doguwar rigarta ce cikin kayanta na da ta saka, rigar bata matseta ba dan bata kara jiki ba saima daidaituwar halitarta da ta yi sai dai rigar bayanta gaba daya a bude yake, ahigar sam batai mata dadi a ranta ba,

Jiki a sanyaye, muryarma a sanyaye ta buda baki zata yi magana ta kasa, ta kara budawa zata yi sai kawai ta shiga inda indar da bata saba ba, haka kuma jikinta ya dauki rawa, muryarta ne take rawa sosai a lokaci daya ta ce" *MAMA*

muryar mahaifinta da ya kasa hakurin jiran har su je gaishe shi ne ta katseta a lokacin da ya ce" *UWATA?*

A tare suka juya , shi kuwa ya tako ya shiga cikin dakin a nitse, sai da ya kali Hafsat din sannan ya kalli mahaifiyarta ,

Da hannunsa ya yi mata nuni da ta zauna,

Cikin nutsuwa ta zauna jikinta a sanyaye dan ta tsorata da abinda ya tsoratar da yarinyar nata har haka harma ta kasa magana,

Sai da malan ya kara dakin sannan ya zauna cikin nutsuwa ya ce"""

>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER

29 / 54