Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   41 / 54

120K to 123K   out of 159.5K words

ya ringa gyadawa har ta gama sannan ya riko hannunta yana kallonta
Murmushi ya sakar mata a hankali ya ce" ki dauke mu mu duka tamkar yayanki momy, na roke ki...yin hakan zai bani kwarin gwuiwar risinawa koda bana so=?O?


Murmushin ta sakar masa ita din ma sannan suka fito daga dakin

A lokacin da suka fito tana zaune inda suka barta kanta a sade kasa tana dan kada kafarta

Muryar momy ce ta sakata dago da kanta, momy ta ce" yarinya kina zaune ko ruwa ba.a kawo maki ba?

Abdul ya karasa kusa da Hafsat ya zauna saman kujerar , da kafarsa ya dan mintsinota hakan ya saka ta dan matsa kadan tana kallon kasa bata ce komai ba

Daidai nan aka kawo jus, sai dai bata kai ga dauka ba Abdul ya mike ya ce" momy tafia zamu yi

Mikewar ta yi itama ta rako su har wajen mota, bata ce su ci kansu kuma ba sukai salama suka fito a gidan

Sai da ta ga sun fito ta dage nikaf dinta cikin yanayin tashin fitsara ta ce" Abdul wannan wani irin wulakanci ne? Ya zaka dauko ni ka......
Wani wawan birki ne ya taka wanda ya saka taratsun maganar da ta dauka tana zazaro mai ido ta hadiye lokaci guda ta dan yi gaba Allah ya taimaketa da belt a jikinta ya mayar da ita kujerar

Yana tsayawa, bai bari ta dawo a doguwar rikicewar da ta yi ba ya kara daukan hanyar kara rikitata,
Lokaci daya Abdul ya janyo Hafsat jikinsa bayan ya kunce belt din jikinta ya janyota sosai jikinsa ,
Cikin kankanin lokaci ya hade bakinsa da nata....a hankali ya lashi lebenta na kasa,
Idannuwansa dake lumshe ya dan daga gani ya yi ta zazaro ido haka kuma kofofin hancinta kansu sun bubude da mugun mamaki da tsoro

Idannuwan nasa ya lumshe ya fitar da harshensa kadan ya kara lashe lebunanta baki daya, a hanakli ya saka harshen nasa a bakinta yana dan zagayawa hakan ya sa ta kara daga bakin cike da mamakin girman fitsararsa da kallon abinda yake mata wani iri

Abdul ya yi haka ne dan ya kashe bakinta wajen yi masa ihu, ba zai iya daga mata murya ba zai so ta gane haka itama ta daina daga masa murya

A hankali ya karasa damkar harshenta ya shiga kissing passionately, wani irin hucin numfashi ya fara fitarwa lokaci daya hannunsa da ya ririke hannayenta ya sake au ya shiga hayowa da daya har wajen kanta ya talabe bayan keyarta yana kara tsotsor bakinta tamkar ya samu alewar kara

Dayan hannun nasa dake rawa rawa ne ya saka a hankali ya shiga lalubar hanyar da zata bashi damar saka hannun cikin rigarta...lokaci daya kuma yake kokari kara dorata saman cinyarsayana shafa bayanta a hankali yana sama da hannun yana neman zif din rigar tata

Lumfashin da yake saukewa ne ke shiga ilahirin jikinta yana sauka a fuskarta mai wani irin dumi da kanshin maclean na ananas mai sanyi

Ajiyar zuciya yake saukewa a kai a kai, lokaci daya yannayin yanda ya samesu da Muhammad ya fado masa a cikin idannuwansa,
Da sauri ya cika leben nata, q haka kuma ya ririketa a jikinsa da wani irin karfi
Kansa ya cusa cikin dokin wuyanta , muryarsa na rawa ya ce " *HaHafsssssssat, me ya maki a ranar nan?*


Wannan karon damkar da ya yi mata ya fi gigitata fiye da taba mata jikin da ya gama yanzu yanzu, lokaci daya ya birkice mata kamaninsa suka canza mata,
Gaba daya ya hade ya zame mata tamkar kumurci sannan ya yi mata tambaya ya tsareta da wani mugun kallo

Gabanta ne ya shiga dokawa,
Lokaci daya ta shiga tambayar kanta wa? Wa yake tambaya? Me ya yi mata a wace rana????


Hafsat baki fahimci wanda yake nufi ba ko?>??>??>??


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




5?? 4??





Cikin bacin rai ya dago da dubansa yana kallonta ya ce" ki bani amsa ke nake sauraro Hafsat, me ya maki? Me da me ya maki?

Wai wa kake nufi Abdul?
Hafsat ta fada tana dan matsawa daga irin maysewa juna wajen da suka yi

A hankali ya maida bayansa jikin kujerar ya jinginar
Ya jima a haka dan a kadan ya dauki minti goma sha biyar inda Hafsat ta takure jikinta tana kallon kasa tana murza hannayenta a kasan zuciyarta kuwa sai yawo take mata, tsoro ne ke faman halakata, a gaskiya ta tsorata da yannayinsa gashi ya yi mata tambayar da bata fahimta ba

Hannayensa gaba daya ya dora saman kansa, gashin kansa da ya caje ya yi tsaf da shi ne ya saka yatsunsa ya cakule tsarin gashin

Yatsun nasa ya yi ta cusawa cikin kan kafin yake samu ya dan saisaita kansa

A hankali ya kai dubansa jikin rigarsa , wajen wandonsa
Ajiyar zuciya ya sauke ya kali agogon hannunsa sannan ya tayar da motar ya kama hanya

Tuki yake ba tare da ya kuma yi mata magana ba a haka har suka isa kofar gidan malan

Ja ya yi ya tsayar da motar, bai kaleta ba bai kuma yin magana ba sai dan sada idannuwansa da ya yi dan baya son ta san waye shi a fagen bacin rai, zuciyarsa idan ta kai makura suma yake , hakan kuwa shi ya fi zama alkhairi domin da bai suman ba sai dai kuwa shi ya summar dan riko yake yiwa mutun wanda sai dai idan ya fadi mutun ya gudu hakan kuwa komai girmanka raf yake yi da kai sai dai a yi abinda za.a yi, baya gudun ya kama mutun du shekarunsa

Kallonsa ta kara yi, jikinta ne ta ji ya yi mata mugun sanyi, eh lale ta san waye shi, tana iya fadin kadan daga halayarsa da ta sani , ta san rigimame ne shi mai mugun fada aman kuma bata san shi da hadiye bacin ransa a kanta ba hakan ya saka jikinta yin mugu mugun sanyin

A hankali ta saka hannunta ta bude motar

Kafarta daya ta fitar tana kokarin fitar da dayar ya riko hannunta na hagu dake kusa da shi

Murya can ciki ya ce " ban lamunce fitarki ko kofar gida ba

Yana gama fada ya sakar mata hannun, a hankali ta juyo da dubanta ta tsayar a ka fuskarsa

Dan tsai ta yi sannan ta fice gaba dayanta ta bara masa motar


Daga wannan lokacin, Abdul bai kuma kiran layinta ba , ya san ita ba zata kiraye shi ba dan haka bai kankara hakori a hakan ba, bai kuma zuwa gidan malan dan su hadu ba daga karshe tafiama ya yi bayan kuma an saka ranar da za.a kaita gidanta wace bata fi sati daya ba domin malan ba.ai masa kowani sabgar aure da ta fi saukar alkur.ani


Sosai abin nan ya tsaye mata a rai, takan zauna a dakinta idan yan uwanta sun bata sarari ta dan huta ta zurfafa a tunanin me kuma hakan ke nufi? Me abdul ke nufi da ita ne?
Ta sha ta dauki waya dan yi masa message sai kuma ta ajiye ta yatsina fuska a fili ta ambata koma me kake nufi da ni daidai nake da kai malan, nima ba sonka nake ba bare abin ya dame ni

Abinda ya fi madaukakin bata mamaki shi ne message din bank da ta samu da makudan kudi a ciki, sai bakuwar lambar kasar waje da ta yi mata message cewa kudin aikinta da ta yi a matsayin bodyguard ne,
Sai kuma wasu kudadan da suka shigo mata bankin ne dai, accmpte din da bata san lokacin da ta bude ba dan ita dai bata taba budawa ba aka kuma shaida mata da kudi sun shigo wayarta da sabon message da number dai an saka mata
Idan kina da wata bukata ki min message

Kanta ta girgiza ta ajiye wayar, bata ma fadawa kowa ba dan ta fahimci cewa Abdul ne ke wannan aikin, shi mai kudi ko? Ita zai hau ta haka ko? Itama ta shiga layin matan nasa kennan, ya aura ya wulakanta so yake ya ga tana biye da shi tamkar jela, yo ita da ba dan ta san idan ta tsiro da maganar bata sonsa da aure ba mahaifiyarta zata fita hankalinta ba da ta nuna masa ita zata fara neman sakin a wajensa, ba zata taba bari ya wulakantata ba a haka, bata nemi ya rufa mata asiri ya aureta ba bale har ya mata iza!


Abdul kam ya sadar da kansa garin Minna,

Gidan horon da ya kai Muhammad ya yiwa tsinke, nan ya tarar da shi tamkar ba shi abinka ga farin mutun da ya saba rayuwar hutu,

Tsayuwa ya yi gabansa bai furta masa A ba yana kallonsa yana so ya dago su yi ido cikin ido sai dai ina ya kasa dago da kansa bale har ya yi ido hudu da shi dan kuwa wani mugun tsoronsa yake ji, yanzu haka da aka barshi daga shi sai shi gaba daya jikinsa bati yake, da haka azabar wahala take? Da haka duniyar da ba dadi ba sanyin ac ba abinci ba barcin kirki bare wajen kirki yake? Da haka matsatsatsin gidan duniya yake bama na kiyama ba? Shi da yake daukan kansa wani shege har yake tunanin a kan soyayarsa ba abinda ba zai iya ba, ba irin wahalar ba zai jura ba sai gashi wahalar duniya kawai ta saka shi ya fara zarewa dan a yanzu daga ya ga duhun magariba ya fara yowa ya fara ihu tun karfinsa yana neman ceto, wai hakan a duniyar kennan, shi da ya kashe rayuka tamkar kiyashi ashe ko karfin jinnin su ba zai masa adalci ya saka shi zama fitacen masifafe ba? Shi kam ya ga rayuwa, yana cikin ganninta....
Yana so ya buda bakinsa ya duka gaban Abdallah, sai dai ya sani ne mai yiwuwa ya matso da zuwansa kabari!

Sai da Abdul ya gama kallonsa sannan ya juya ya fice a wajen, nan aka ja shi kiiiii aka jefar cikin gagan yan kurkukun dake jiran ko ta kwana!


Ya jima cikin mota, kansa hade da sitiyarin motar ya rintse idannuwansa,
Zuciyarsa yake ji ba dadi, abubuwan da zuciyarsa ke raya masa a kan rayuwa da rayuwar amininsa ya saka shi dagawa zuwa saudiya
Ya kusanta kansa da Allah ko zai samu sasaucin sake saken da ruhinsa ke masa... wannan shi ne mafarin dagawarsa zuwa saudiya


Yan uwa sun je gidan da Abdallah ya fada dan gyarawa Hafsat daki wanda ba yanda bai yi ba kan ba sai an kai komai ba aman malan ya ce ya jima yana shirin kayan dakin mamansa

Sun gigita da gannin wai a wannan gidan ne Hafsat zata yi zaman aure, Hafsat dai maman malan? Ita ce da daukaka haka? (Yanzu mutanen mu idan ka yi aure ba.a wani tunani sai na sharetan gidan da aka kai ka>?#?>?#?>?#?, )
Lale yar malan ta samu waje

Har suka yi suka gama basu ji alamun da wata halita a gidan ba, basu ma san mijin na da wata matar ba, haka suka dawo gida a lokacin an rufe daki anaiwa Hafsat kunshin tukunya ga dumin dakin kadai wani tashin hankalin ne, suka zo suna ta santin gidan da tsare tsaren gidan da irin abincin da aka kawo masu wai daga gidan mamansa sai dai basu ga maman nasa ba

Ita dai mama bata ce komai ba, sai su aunty dake amsawa a haka har aka gama aka watse da niyar gobe wajen yama za.a dawo a raka amarya dan kowa ya sani gidan malan ba.ai masa bidi.a


Tsakiyar dare wajen karfe uku mama ta tasota daga dakinta ta kamo hannunta ta hau da ita dakin malan

A lokacin yana zaune saman salayarsa yana jan carbi, suna shigowa ya daga hannayensa ya shafa fatiya sannan ya mike ya dawo saman kafet din kamar yanda suka zauna suka tankwashe kafafuwansu shi dinma hakan ya yi

Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" Alhamdulilah, yau dai Allah ya nuna min ranar da zan sada mamana da dakin aurenta,
Mama?

Da sauri ta dago da dubanta domin kanta a sade jikinta kuwa sai rawa yake,
Subahannallah shi ne abinda na fada, domin wani irin goshin amare da ake cewa da na hanga a fuskar Hafsat yana wani irin kyali, gaba dayanta ta canza, gyaran amare ya mugun karbanta, ga jan kunshin da akai mata na zamani na amare abin ba.a cewa komai

Idannuwanta kuwa tamkar sun kumbura, da alama kuka maman maman malan ta yi, yannayinta da ya gani ya dan karyar masa da zuciya sai dai ina a yau ita ce ranar karshe, baya so safiya ta waye bai yi magana da ita ba, dan haka ya ci gaba da fadin" shin zaki zauna a dakin mijinki ki yi biyaya ki girmama sunnar ma.aiki? Mamana, zaki je ki rayu da niyar sai dai a fitar da gawarki daga dakin ki? Ummana zaki je zaman bauta, gwagwarmaya da zuciya daya da niyar neman sakamako a wajen Allah?

Gabanta ne ya shiga dokawa, irin yanda mahaifinta ke mata magana a yanzu

A hankali kuma ya sasauta muryarsa ya ce" kowani uba burinsa ya yiwa yayansa aure, Allah ya cikan burina, zan so y'ata ta zauna dakin aure,
Mamana rayuwar aure wata sabuwar rayuwa ce da zaki shiga mai wuyar fasara,
Hakuri, hakuri, umana hakuri,
Ko wa kike aure, komai girman son da yake maki to fa lale sai kin juri wannan kalma ta hakuri sannan zaki ga haske a rayuwar zaman auren ku,
Ki yi masa biyaya, sai ku wanye lafia
Mamana, Abdallah dai mai aure ne, kin san da yana da aure, kema kin tashi gidan da mahaifinki ba daya ya ajiye ba, ke koda mamanki daya nake aure idan kin auri mai mata sai ku zauna lafia!
Na hane ki fitina, na hane ki taurin kai, rashin kunya ko gardama,
Mamana ki kasance........ kukan da ta rushe da shi ne ya saka mahaifinta sada kansa, har cikin ransa yake jin irin yanda take kuka, da ba dan mamanta na kusa ba ya tabata zai yi shiru ne da nasihar ko zara daina kuka,
Allah ya saka masa kaunar yarsa mai girma a ransa, yana rokon Allah ya sa rashin jin maganarta shi ne iya jarabawar da zai yi masa da ita, Allah ya sa mijinta ya zauna lafia da ita, kar ya wulakanta masa mamansa

Duban da mama ta yi masa ya bashi kwarin gwuiwa, dan haka ya rintse ido ya ci gaba da yi mata mata nasiha mai ratsa dukan gabai har ya saka ka yi sanyi tamkar ruwan sama ya dake ka

Tun tana kuka muryarta na fita har ta kwontar da kanta a cinyar mamanta take gurnani gaba daya muryarta ta disashe ta daina fita
Sai da aka fara kiraye kirayen salar farko ya saka shi mikewa bayan ya yi mata wata irin doguwar adu.a, ya yafe mata dukan abinda ta yi masa wanda ya sani da wanda bai sani ba, mahaifiyarta ma haka, sannan ya umarta da a kaita kowani daki ta nemi gafara, ya mike yana mai shaida masu Abdallahnma zai shigo nan da sati domin yana saudiya har yanzu bai gama ba

Kamar a lokacin za.a tafi da ita gidanta, gaba daya mama ta kasa mikar da ita, a hankali muryarta na wata irin magana take furta" Abanna, ni ba zan je ko.ina ba, ni a barni a wajen Abanna, wayo Abanna

Mama kam ta san za.a rina, shi kansa ta san fama ne yake ya gudu ya zubar da hawayen zai rabu da mamansa, murmushi ta yi ta cicibata da kyar ta kamata a jikinta ta fito daga dakin malan din ta nufi dakinta da ita,

Suna shiga ta cire mata hijabin jikinta ta zaunar da ita,
Wata dilkar ta zo ta shiga cude jikinta da ita, ba abinda ya dameta da irin kukan da take ta san za.a rina kuma dole ta yi hakuri ta je domin kowama da haka ya saba

Sai da ta gama filketa ta shiga ta dauro alwallah

Tana gama sallah har sai da rana ta fito ta tashi ta kamata daga saman salayar da take zaune ta kasa tashi ta dauketa ta kaita can kurya

Ba.a jima ba aunty mariama ta zo

Tana zuwa ta tube hijabin ta kawo garwashi ta mikar da Hafsat ta saka turare a cikin bokicin karfe ta sakata zama bisa

Hafsat na zama ta ji yanda hayakin ke ratsa jikinta, a hankali ta lumshe idannuwanta sai wasu hawayen ke zubo mata, karo na biyu kennan, karo na biyu zata bar gidan mahaifinta ta je gidan wani ba da son ranta ba, eh lale ba da son ranta ba domin bata son sa kuma baya son ta


Aunty ce ta kaleta ta ce" Maman malan, menene??

Idannuwanta da ta ci kuka da su har sukai mata hadari hadari bata iya daga su da kyau ta dago ta zuba mata,

A hankali ta ce" Aunty

*Ni BANA SON SA, KU SHIMA YA TSANE NI!*


ido Auntyn ta tsura mata tana kallonta kafin ta mike ta bude humurar da ta zo da ita katuwar kwalba guda ta bude ta debo mai yawa ta zo kusa da ita a hankali ta ja zip din rigarta ta yi kasa da ita sosai ta shiga murza mata shi

41 / 54