Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   20 / 54

57K to 60K   out of 159.5K words

*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, AKOY WA.INDA BASU DA ACCNT, TOH ZAKU IYA TURO DA KATIN KU TA NAIRA DARI BIYU, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




7??


*Free page*



Ire iren abinda ke faruwa da rayuwar Abdul kennan, baya iya kwana biyu ba tare da mace ta zo ta sauke masa nauyin dake kansa ba , idan kuwa ya yi toh zai shiga wani hali ne na takura da rashin lafia, shi kuwa yaki ya yi aure, shi ke gudun matan, dan kuwa matansa biyu bai san inda suke ba, iyayensu kansu sun tabatar masa da suna son saki aman kuma basu fadi dalili da kuma inda suke ba, zamani na daurewa yaya, zamani na soyayar yaya, bai ga laifinsu ba, ya yi masu uzuri ne, rayuwace....

Sai da ya gama abinda zai yi ya mike ya dauki hula ya dorawa kansa ya fito ya nufi motarsa,
Direba ke jansa ya dauki hanya,
Doguwar tafia ce sosai suka yi kafin su karaso inda take,

Suna zuwa ya sauka ya shiga ya samu waje ya zauna yana sauraronta bayan ya gaisheta,
Cikin sanyin murya ya ce" aa, bana so, na yi me da Bodyguard bayan wa.inda ke bibiye da ni a nan gasu nan har mutun biyar dake karkashina dan kare lafiata? Me yasa kike tsoro har haka ne Ummi? Ki daina , ki cire tunanin wani na jikina ke kashe min mata, lokacinsu ne ya yi,

Kanta ta dafe, gardama ce yake mata aman cikib sanyin murya tamkar mai fadin maganar dadi, sai da ya yi shiru ta ce" ban yarda da su ba, mutanen da ka dauka a haka shanshakai? Mutanen da kake biyansu dan kudin da ba zai yiwu su sadaukar da yaruwarsu dan taka ba? Mutanen da ana iya siyansu ta hanyar basu kudin da ya fi yawa su ilata ka? Wai kai baka gannin hankali ya fara juyowa kanka dalilin kudadan dake bankina da sunnanka? Ba niger ba, ba nigeria ba, har saudiya kudinka dake cikin banki sai da ya saka prince Muhamad ya nemeka kuka gaisa?

Bakinsa ya tabe ya ce" Ummih, Kudi, Kudi, Kudi, Ummi ba kowa kuddi ya rufewa ido ba, eh ana kisa dalilin kudi, ana abubuwa dalilin kudi, aman ummi dukanama nawa nake? Ban tafasa bama bale na kone, ba zai yiwu da kananun shekaruna 31 na zauna du inda na saka kafata wani gardi ko wata gardiya na tsaye kaina wai kareni, adu.o.in da nake basu isa su kareni ba? Ummih, ina da sirri, inada rayuwa tawa, ina yawo kasashe, ni ba zan zauna da gardi yana tsarona ba sai kace wani soko, haka kuma ba zan wani zauna sarkacecen kato da ni mace ta yi gadina ba sai kace dan daudu,

Tsura masa ido kawai ta yi, ta san an rina, muryarta ta sanyayar ta ce" aman ka san doguwar tafiar da na yi dan samo wannan solution din? Ka san yanda nake gagara rintsa ido du lokacin da ka fita da sunnan wai kai ka tafi nema? Ka nemo me? Ka samo me? Du wanda ka tara ko jikokin jikokinka ne zasu yi wadaka daidai da zamaninsu, aman sai kace wani kogima na son kari, kuma du abinda dibansa ake kawai ba.a kara masa watarana zai zama babu,
Shiru ta yi kafin ta kara tausasa murya tamkar itace yar (kun san mutanenmu na yanzu da shegen son yaya bale yan gayu) ta ci gaba da fadin" kai daya na malaka gidan duniya, yayarka ta mutu, mahaifinka an kashe min, ya hankalina zai kwonta idan na ga kana rayuwar garari? ABDUL a cikin mota zaku je diner, ka fita amsa waya ka dawo ka tarar da gawar mace tamkar tana barci,
Tafia ta biyu washe garin aurenka ta tashi da ciwon ciki, itama ta tafi,
Ta uku a cikin gidana, na tarar da gawar yarinyar da an daura aurenku muna saka ran zuwanka cikin satin , ni na mata wanka, da idona na ga shaidar jan jan abu wajen wuyanta na kamar an shaketa da wani abu mai kauri ne,
Mata biyu sun gudu ba tare sa kun yi zaman auren ba domin sun tsinci labarin komai!
Abdul, duka matan nan ba wace ka yi ainahin rayuwar aure da ita, kowace hakan baya tabatuwa ake katse lamarin, har yanzu shekara 31 baka san aure ba, ka yi aure har biyar, why ba zan damu ba? Danme ba zan kawo abubuwa a raina ba? Da idonka muka kalli vidon da jirgin da mahaifinka ya watse ciki, yana zaune kamar an lika shi ne a saman kujerar, da ido yake magana sannan yanda ya zaro ido kamar yana kallon wani ne ya tsare shi, kamar an sakawa mahaifinfa glue ne an dafke shi, har vidion ya dauke,
Abdul, ka yarda ka ji? Ka amsani

Fuskarsa ya shagwabe, daga inda yake zaune ya tashi ya karasa kusa da ita ya zauna ya kara yin takwaf takwaf da fuska ya ce" Ummih, ki yi hakuri, ba zan iya yawo da kowa ba, ni rayuwar yanci nake so, bana son rayuwar shiga hanci da kudundune, ki bar magnar nan kin ji?

Da kallo ta bishi a kasan zuciyarta tana fadin" zaka sauko ne, sai ka yarda in sha Allah, zan yi ta lalabaka (toh fa>?? wollah da oo ne, cewa kawai za.a yo kai maza an daukar maka bodyguard, zai amsa da to mama, ba maganar ehyane=? ?)


Gidan horo


Sannu a hankali ta gama fahimtar eh lale wannan aiki da aka kawota aka hadata da mutane aiki ne mai mahinmanci, mai girma, mai hatsari, wanda cikin su su goma sha biyar dan an karo wasu, duka duka mutun hudu ake so, idan har bata ci wannan Jarabawa ba, to fa zata koma rayuwar KuTkale ne , rayuwar da abinda ya fi damunta a cikinta irin yanda ko adinninta yake da rauni, sannan ake harin mutuncinta!
Hakan ya sa ta tatara hankalinta, ta maida baki daya hankalinta kan wannan aiki,
Bata ji , kuma bata gani,
Abu mai mutunci a wajenta a wurin nan shi ne!
Suna yin excercise kala kala kamar : Gudu, gymnastic, karin koyon espanol, larabci, inglish, hausa, wanda shi ke ajiye su class, iya tafia, iya magana cikin sanyi da kyakyawan yannayi, iya saka kaya, kare rayuwar abokin aiki fiye da taka, iya girki, kai du wani abu na rayuwa ana koya masu cikin kwarewa da hikima,

A haka suka dauki wata uku, wanda zuwa lokacin su bakwai kawai suka rage,
Sai ya zama wata irin rayuwa ta ba mutunci, ba tausayawa dan uwa, uwa uba harin rai, somin kuwa a bakwai din nan ba wace ke so a cireta, gogagu ne, fitatu ne, a haka aka fara sama masu mission dan kara tabatar da hazakarsu, mission din da idan sun fita ana biye da dukan wani motsinsu,

A haka wata mata ba za.a kirata datijuwa ba, ba kuma za.a kirata da yarinya ba, ta dauki Hafsat a matsayin wace zata bata kariya na tsayin wata biyar sakamakon wata shari.a da ta dauka, domin lauya ce mai zaman kanta, kuma gagarumar yar kasuwa ce, hakama gidansu an tara, tana aikin lauyanci ne dan ya kasance passion dinta,
Matar bata da aure, aman kuma yayanta biyu wa.inda ta yi adopted,
Tana zaune da su a gida guda inda su kansu sun girma sun zama baban saurayi da budurwa sosai, sannan suna karatu ne a kasar,

A lokacin da aka gama bata labarin irin aikin fa zata yi, aka bata damar yin tambaya, ta jima tana rubuta dalilin aikin nata sannan ta dago da kanta ta ce" wace irin shari.a ce ta zata gabatar? Da wa da wa shari.ar ta hada?

Sai an fada maki sirin shari.ar ko me? Da kike son sannin sirrin shari.at bisa wani dalili?

Hannayenta ta hade waje guda , dogon wando sakake ne jikinta sai riga mai hannaye daidai gwuiwar hannu, sai hula irin ta mazan nan wace ta yar kofar bayanta ta fitar da gashinta dake daure da dan karamin ribom, ba wani abin kwaliya a fuskarta ko dis, aman wani sirririn sirin kyau ne a tatare da ita, ita kanta idan ta mike din zaka yi mamakin wannan yar abar har zara iya kare lafiar wani?
Aman kuma mu je zuwa dai,

Cikin nutsuwa ta fitar da harshenta ta lashi lebenta na kasa, sannan ta fitar da hakoranta na sama ta dantse leben nata,
Sai da ta yi wal wal da idannuwanta sannan ta ce" wannan bai shafeka ba!

Da mamaki yake dubanta, shi ne bai shafa ba? Shi zata rainawa wayo? Karamar yarinya dan tana ganninsa a bagas? Dan tana tunanin zama Bodyguard din fake kila wa kala shine har zata fara maida masa magana haka gatsal? A me ta dauki kanta? Bayan ga mutanen da suka fitar da ita suna jiranta su daga?

Muryarsa ya daga ya ce" ni zaki maidawa magana a haka tamkar wani sa.anki ko wani class dinki? Ko yau kika fara aiki baki isa ki kamo ni a dukiya ba sai kin yi aikin shekara ashirin na rayuwarki! Shi ne zaki kalleni ki ce da ni ina ruwana? Kin manta ni ke hora ki?

Datijon da ya daukota daga kutkale, wanda shi ne mai gidansu baki daya ne hankalinsa ya kawo wajen hayaniyar da SB yake yi, dan haka ya mike ya nufo wajen ba tare da ya yi ma masu jiran nasa magana ba,
Nan matar ta mike itama da dan sauri ta bi bayansa, dan kuwa ba mai hana shiga a kofar,

Cikin nutsuwa daga zaunen da take ta ce" aman ai na ga nan ba filin horo bane bare in bi du abinfa ka ce ko?

Me ke faruwa? Ya jefo tambayar a dake, sannan fuskarsa ba alamar sasauci

Gaba dayansu suka mike suka sara masa,
Nan ya shiga kora masu bayannin abinda ya faru,

Dubanta ya yi ya ce" baki dauki lesson din ladabi da biyaya bane na maida ke baya ko me?

Kanta ta girgiza tana dubansa ta ce" GN, an yi mana lessin din ladabi da biyaya, kuma an yi mana ta mahinmancin lokaci da maida amsa wajen da aka yi tambaya da kuma kiyaye yin tambayoyin da basu da ma.ana!

Ido suka zari su duka, sun gama sarewar shikenan ba za.a dauketa ba, tana zubawa wanda ya horata irin wannan fitsarar wa zai dauketa? Bayan wannan ai sai ta bata image din wajen, dan kuwa an sansu da bin na gaba da su ido rufe,

Bai so haka ba, sam bai so haka ba, irin abubuwan da ya take ya kutsa ya tarba dan gannin ya cirota daga cikin gidan yari, bai so haka lokaci daya ta tarwatsa komai ba, dan kuwa a lokacin da aka yi shari.arta yana wajen, yana zaune a wajen, shi da shi aka kama dan ta.adar, ya san waye shi, sannan a lokacin da aka bata damar ta yi magana a kotu magangannun da ta jefowa lauyan suka kara saka shi shakun abinda ake tuhumarta da shi du kuwa da irin yanda lauyan ya tafi da imanin du wanda ke wajen,
A haka ya ringa bibiyar zamanta a gidan yarin, a hankali ya ringa samun amsoshin wasi wasin da ya ringa yi kanta, sai dai baban tashin hankali maganar dake dakatar da shi wace kaf anguwar su yarinyar ba wanda ke mata shaidar arziki, wani idan ya buda baki ceqa yake wa wai Khadija? Ai sunnayenta da yawa muguwar yar daba ce....
Su sunai haka fasara daban ta irin mugun rashin jin maganarta, da mugunta wajen fadanta,
Iko kuwa zai yiwa maganar fasara daban duba da irin halin da aka kamata aka ce itace da hakan,
Suturar da aka kamata da ita, ba wani dan kwali, ba hijabma sun taimaka wajen bada gudunmuwar rashin samun tudun dafawa,
Hakan ya saka shi jin tausayin irin hidimar da mahaifinta ke yi, da irin hirarsa dadaya da ya tsinta a masalaci da aminansa kan yarinyar, ya saka masa tausayi da son yin ceto,
Shi ya saka shi ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya hana kansa baci sai da ya samu ya yi convaincre (ya ci galaba) din wanda ya yanke mata hukunci aka yarda da zata iya wannan aiki, aka bata dama dan karancin shekarunta da tarin iliminta ana hasashen zata kawowa kasa ci gaba, aka kawota sai gashi du ta shanye wahalhalun da jarabawar da yawa sai yanzu da za.a fita da ita take faman farke komai a gaban wannan lauyar da tana iya ja da kowa bata da dar, wanda hakan na iya ja, a yau a yanzu a mayar da ita gidan kason da bata taka ba, bata karya ba!
Hakan ya saka shi tafka mata tsawa ta hanyar fadin" *LA FERME SOLDAT* (CHUTUP SOLDIER)

Shiru ta yi da maganarta sannan ta kame ta sara masa,

A hankali matar ta karasa shigowa tana dubanta da kyau, sai da ta gama karantarta ta ce" menene dalilinki na son shiga hurumin shari.ar bayan ke kariya kawai aka ce ki bani?

Shiru ta yi kanta a sade, jikinta kam ya mutu dan karara ya fada mata cewar ta maida hankali, wannan aikin shi ne tikitin fitarta daga *KUTKALE*,

Hankalinsa ya maida wajen lauyan ya ce" MADAME BILKISSU, ki yi hakuri, zamu maida ita baya mu bata horo,

Kanta tsaye ta ce " ina son na ji amsar tambayata,

Kallonta ya yi da yannayin takaici ya ce" ki bada amsa!

A hankali ta dago da dubanta ta saka dara daran idannuwanta cikin na matar ta ce" na yi wannan tambayar ne dan ina son na yi bincike a tsanake kan wanda ya dace na fi saka idona a kansa a harkar aikina,
Shin wa.inda kuke shari.a da su ne? Abokin shari.arki da su ne? Ko kuwa a cikin gidan da kike rayuwa ne? Ki yi hakuri aman an koya mana cewa mu kasance komai ba jikinmu ya zama idannuwa, kwakwaluwarmu ta kasance tana aiki kowani lokaci, aman kuma mu tabatar da muna da abinda zamu fi sakawa ido,
Ba nan na nufa ba, ta yiwu wa.inda kuke shari.a da su, kaurin sunansu ya sa aka kalubalance su cewar menace din da kike samu na za.a kashe ki su ne, mai yiwuwa wani ya fake da haka ne dan ya cinma wani burinsa,
Makashi, baya bada damar a gyara ko ya yi kisa, makashi na yin kisa ne sai dai kowace wace, an kwana da sannin cewa ba zaki ja da baya kan ra.ayinki na shari.ar da ta tunkaroki ba, kokonto ne ya darsun mani na cewa, wanda kike shari.a da shi....anya kuwa mai laifi ne kamar yanda ake hasashen yana iya bi ta kasa ya tsorataki dan ki bar shari.ar da kike? Ko dai kaurin sunnansa ne ya jaza masa jafa.i?????
Ta karashe tana mai duban GN wanda ta yi maganar kaurin sunna ya jazawa mutun balaki da biyu.....

Gaba dayansu ita suke kallo,
Lokaci guda Madame Bilkissu ta kara shigowa face to face da Hafsat ta ce.......



>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




3?? 3??





Cikin murmushi, da yannayin raini Abdul ya dora yatsarsa saman lebensa ya ce" shiiiiiiit,
Sai da ya kikifta ido sannan ya ci gaba da fadin" Huraira? Not Furaira, u.r wlcm yar uwa, ku ware mata daki, wannan da kuke ganni an sameta ne ta hanyar kauna, ita din yar kauna ce

Wani dan murmushi ta saki , a hankali ta janye hannunta ta ce" thanx

Kafadunsa ya daga yana tsaye ya ga soja biyu sun nufi dayan bangaren dan ware mata dakin da zara zauna

Juyawa suka yi ita da Bahija dan zuwa wajen, yana kallon su

Sai da ya ga Bahija ta kusa shiga ya kalli gefen da Hafsat ke ciki, cikin yannayin basarwa ya ce" kirawota

Nunatan da ya yi ya saka ta gane wace yake nufi, juyawa ta yi ta nufi wajen su ta kirawotan saannan ta dawo ta tsaya inda take tana mai satar kallonsa

S lokacin da ta zo daf da shi, hannunsa ya mika mata yana kallonta

Hannunta na rawa ta saka cikin nasa, da yannayin nunin soyaya ya janyota a hankali jikinsa yana mai daga kansa ya hangi window din Ni.ima dake tsaye tana kallon du abinda ke faruwa, ya kuma maida dubansa wajen masu tsaron ba tare da wani dar ba

20 / 54