Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   51 / 54

150K to 153K   out of 159.5K words

ta shiga bashi taimako domin zuciyarta bata da muradin da ya fi a koma abinda aka dauki lokaci ana yi

Abinka da kwarare a fannin sai kawai Abdul ya karbi tayin maman malan ya kara lulawa duniya mai cike da lada yana hako du wasu arnawa yana kashe au cikin sauki

Shi kansa ya tausaya mata a lokacin da komai ya lafa , cikinta ta damke tana hawayen wai yinwa take ji

Taimaka mata ya yi da niyar ta fara wanka kafin ta ci? Sai dai ruf ta rufe ido kan sai ta ci

Ido kawai ya tsura mata a lokacin da take kai loma bakinta , wato tana yin hannu baka hannu kwarya ba sasautawa
Ba ita ta dan dakata ba sai da ta ji wajen da kamar an mata sata ua cike sannan ta dawo hayacinta harma ta fara jin mugun zogin da jikinta ke mata
Sai a lokacin kuma ta tuna cewar ta rushe tsarin jan ajin da ta yi niyar yi in dai tana gabansa na cin abinci, wato sam ba zata yarda ya gane irin yannayin cin abincinta ba, sai gashi rashin lafiar da take son kai kanta asibiti wace ta sameta a kwana biyun nan na cin abinci ta tona mata asiri a gabansa

Fuskarta ta tsuke,
Ta mugun hafe girar sama da ta kasa ,
Ta hade gabas da yama
Irin ba zata saki fuskar da za
a kawo mata wargin bama

Murmushi ne ya subuce masa yana kallonta
Hannayensa duka biyu ya saka ya talabe habarsa,

A hankali ya ce" ban taba hora kaina irin na jiya da yau ba

Dara daran idannuwanta da suka sha wahala suka wani lumshe da su ta maido kansa,
Bata yi masa tambaya ba, sannan bata daina kallon kyakyawar fuskarsa mai sakata jin yana fuzgarta

Hannayenta ya kamo, du da kuwa ta so kin bashi, sai dai ta kasa hakan sakamakon babu wani karfi a tare da ita, tunanin bata da lafia ya fara damunta

A hankali ya ce" Hafsat?

Idannuwanta da suka fara cika da kwallah ta zuba masa tana kallonsa

A hankali ya kuma cewa" ban iya karya ba, ban iya tsokana ba, ban iya wasa da wannan lamarin ba.....ni dai na samu kaina a ciki tun lokacin da kika kasance mai shiga lamarina, kikai min fada dan ina aikata masha.a
Hafsat, shi ne damuwata, tashin hankalina, Hafsat du yanda na yi dan kar wani ya birge ki, sai da ya tashi ya wani shiga rayuwarki, ina ji ina kuma ganni harma zai aure ki
Shiru ya yi yana dan murza hannayenta,

Muryarsa ce ta kara yin wani irin sanyi ya ce" sai dai wani baya auren matar wani, can can dama Allah bai yi ba shine mijin ki,

Idannuwansa ya dago ya sauke a fuskar tata, a hankali ya ce" zaki taimaka ki rufa min asiri, ki daina maganarsa ko tunaninsa? Walahi idan kika ci gaba lumfashina zai iya barin gangar jikina domin hakan na kai ni tunanin cewa har abada ba zaki tana so na ba dan kina da wanda kike so,

Jikinta ne take ji yana amsawa da dukan kalamansa,
Jikinta ne ya yi sanyi,
A hankali ita din ma ta ce" Abdallah, tambayar da na yi maka a ranar nan ce ta saka ka daukan fushi da ni?

Idannuwa kawai ya tsura mata ya kasa amsata

Hannayen nasa ta dan jimke kafin ta ce" ban san dadin so da har zai kai ni haka ba, ban san muguntarsa da har zai kai ni tunanin wani da kalmar so bayan da aurena
Koda makiyina na aura a duniya ina fatan daga bakin da na amsa kira da sunnansa zan girmama igiyarsa dake kaina
Wacece ni?
Me na aikata na tarin ladan da zan yi tunanin koda na kauce hanya haka zan ci riba wa wajen?
Na yi maka tambayar nan ne da ina cikin damuwa, na yi maka ne dan ina cikin tunani mai zurfi, mamakin dan adam ne ya kashe ni na irin kalaman dan adam da suka zama na yaudara

Abdallah ban san yanda zan kwatanta maka lamarina da Bashir ba, aman ka sani babu *kalmar so* a tare da lamarin

Idannuwansa ya sada yana jin nauyin da kirjinsa ya yi masa ya ragu,
Dadi ne ya ji na irin yanda har ta iya fahimtar da shi abinda ke ranta, ashe zata yi saukin kai da dadin zaman gidan aure haka? Ashe du irin taurin kanta da rigimarta da tsayayarta idan aka zauna magana ta fahimta da ita za.a ga laushinta?

Ajiyar zuciya ya ringa saukewa kafin ya dago ya saka idannuwansa cikin nata, a yau ya kara gane wani lamari cewa Hafsansa baiwa ce da Allah ya bashi domin kuwa a wasan da ya buga da ita a yau ya nuna masa idan ta gama zama kwarariya idan ya shige daka sai safe>?#?

A hankali yana kallon kwayar idannuwanta wa.inda ta ki cire nata dan tana son ya yarda da maganarta , sam ita bata wani saka maganar son Bashir ba , ta yi tambayarta ne dan gane dalilinsa na wulakantata a ranar aurensu
Bata tsamaci kalmar da zai yi mata kennan ba, bata tsamaci zai yi mata wannan tambayar ba hakan ya saka ta shagalta da kallonsa tana jin dadin yannayinsa a ranta, rigarsa mai botira ce kawai ya dora saman gajeran wandonsa baki , bai baka botiran ba hakan ya bashi kalar black American din nan

A hankali ya ce " *Hafsat? Dan Alllah, ni zaki so ni? Watarana zaki so ni? Kina tunanin na saka hakuri da juriya na tsayin lokaci watarana zaki so ni nima? Hafsat Ni Ina son ki*

Ji ta yi tamkar za.a jefota daga kujerar da take zaune
Dakin ne ta ji ya yi masu kadan su su biyu rak,
A hankali ta fara jin lumfashinta na gudu ba kamar da ba,
Ita dai bata da cutar athsma, sai gashi lokaci daya ta shiga huka da tari tamkar mai ciwon Athsma,
Sama da kasa kirjinta yake nan da nan ta mike ta shiga neman wajen da zata je ta tsere ta labe kar ya kashe ta,
Jikinta na rawa tama faman kaucewa rikotan da yake kokarin yi
Kuka????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ne ta ji zai kwace mata, wani irin dadi da kuma tsoro ne suka haifar mata da emotions din da ta sakata tarin mai huka, zubewa ta yi jikinsa tana kallon tashin hankali karara a fuskarsa,

Zata so shi?
Shin watarana zata so shi?
Shi yana son ta?
Ita kanta sai ta tsinci kanta da yiwa kanta tambayar shin menene ke saka ta a irin wannan yannayin a duk lokacin da take tare da shi tun farkom lokacin da ta ganshi tare da mace na neman tubewa dan ta bashi kulawa irin wace bata cancanta ba a matsayinta na baligar da ba muharamarsa ba
A hankali ta ringa tariyo irin yannayin da takan shiga a duk lokacin da ta je kakabe masa shinfidar da ta tabata ya je dakin matar nasa ne dan sqnub nutsuwa da ita duda ba hutuminta bane sannan ita Na.ima din ta kasance matarsa ta sunna sai ta wuni cikin kasala da bacin rai
Tana tune da lokacin da aaka so harbinsa harbin ya sameta ajiyar zuciyar da ta sauke ba na ta samu kare mutun a kan aikinta take bane, aa, ta sauke nanauyan ajiyar zuciyar dake nunin ta ji dadin da ba shi ba aka harba abin ya sauka a kanta?
Murnar aurenta da Bashir da ya taya ta sai ta tsinke waya ta ringa jin haushinsa? Shin na menene?
A hankali ta ringa jin lumfashinta na daidaita a lokacin da ta fahimci idan ba da kyar ba tama rigaye shi fadawa a tarkom da ya fada na soyayarta, ashe itama zuciyar tata lusara ce? Har take jin haushin yan matan dake nuna masa suna son sa ashe itama halin da tata zuciyar take kennan? Har take mugun jin haushin matarsa irin yanda so ya sakata zama tana jurar kayan haushinsa ashe du jirgi daya ya kwaso su? Bambancin su kawai ita bata fito da maitarta ba, bambacinsu ita bata nuna ba,
Ashe ashe tashin balagar tsararan shegantakarsa itama ya haukata tunaninta?

A hankali ta saka hannunta ta bayansa ta rungume shi,
Bakinta ta kai daidai kunnensa ta ce" is ok Abdellah

Shima rungumeta ya yi a jikinsa yana mai jin tashin hankalin kar dai ba zata taba son nasa bane har ya sakata cikin wannan yannayin? Dan haka ya ce" i....i.m sorry,

Hafsat ta lumshe idannuwanta tana mai jin yannayinnan fiye da kowani yannayi, dama haka ake ji? Kamar ya kunna wani abu ne a jikinta dake mace a da, can kasan zuciyarta ta masa shi da I love u too, aman a fili sai ta ce"""""""





Saura kiris....eh saura kirisss in sha Allah

>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




6?? 8??



Aman a fili sai ta ce" kar ka bani hakuri, baka yi min laifin komai ba

Shiru ya yi yana sauke ajiyar zuciya cike da mamakin irin jan ajinta, ya tabata da wata ce da tuni ya samu amsar zata so shi ko aa, aman ita ta bar shi a duhu ya kasa gane gabas din maganarta tamkar tandun kwali.

Basu su tashi a wajen ba sai da kiraye kirauen sallah ya fargar da su,
Nan ya taimaka mata suka mike suka nufi dakinsa

A keana biyun nan sun kasance cikin aminci, shakuwa, kulawa, madaukakiyar soyaya

Hafsat cancara kwaliyarta take kafin ta koma bangarensa idan ya fita,
Eh lale bai ji da bakinta ta furta masa kalmar so ba, aman yannayinta , ayyukanta a gare shi, irin yanda a yanzu take bashi hafin kai a bed, harma ta neme shi dan kanta wanda shi kansa yana mamakin dama harijar mace ce ita? Irin yanda idan yanai mata hira take bashi hankalinta baki daya harma ta dara na darawar, na jimami fuskarta ta nuna, komai na zaman lafia sai dai ya godewa Allah
A haka har lokacin fitarta a aiki ya yi sukai wata irin rabuwa tamkar zata bar gari, tamkar ba zasu kuma haduwa ba dan kawai zasu raba kwana na kwana biyu kacal, hakan ya sakata hawaye da ta koma bangarenta sannan ta tashi da azumi domin a gaskiya ita ta san wannan lamari na bukatar mijinta dake damunta ya fice misali, sarai take cikin damuwar rashin mijinta, sai dai ta kwana da sanin ba na ita kadai bane dan haka sai ta gayato hakuri ta yafawa kanta ta tura masa sakon tana azumi danma kar su yi tsamaninta wajen kari da kuma cin abincin dare

Sarai tausayinta da tausayin kansa ya kama shi, a hankali ya mike bayan ya salami Na.ima daga cin abincin safe ya nufi bangarenta kafin ya fita aiki

Dakatawa ya yi daga bakin kofa tun da ya shigo yana kallonta,
Tana yannayin mutun mai sanyi, tana yannayin damuwa

A hankali ya karasa inda take kwonce
Hannunsa ya dora saman mararta ba da nufin wani abu ba sai dai taurin da ya ji wajen ya yi ne ya saka shi sauke idannuwansa a kan fuskarta da sauri

Itama jin ya tabata da kuma jin zafin dana mararta da ya yi ya sakata saurin zabura tana kallonsa

Da yannayin damuwa yake kallonta, a hankali ya saka hannayensa ya janyota jikinsa, cikin nutsuwa ya ce" bab, me ke damun ki??

Murmushi ta kakalo tana kallonsa a hankali ta ce" ba komai, ina azumi ne

Idannuwansa ya lumshe yana kallonta ya ce" me ya sa mararki take da tauri haka?

Kallonsa take, ita kam bara san mararta na da tauri ba dan bata taba ganewa ba, takan ji dau marar tata ta yi mata nauyi sosai, sai dai sam bata taba jin taurinta ba

Kallonta ta kawar daga fuskarsa a hankali ta ce" ban san tana da tauri ba

Mikewa ya yi ya ce" kwonta na ga?

Irin kwoncin da ya tarar da ita ta yi ta kuma yi tana kallonsa
Tamkar wani likita ya kara yaye rigarta ya shiga dana cikin nata a hankali yana kallon yannayinta

Rike hannun nasa ta yi tana yatsina fuskarta dan walahi ita zafi take ji sosai

Daina danawar ya yi ya shiga shafawa a hankali yana kallonta ya ce" yaushe rabonki da al.ada?

Hafsat ta amsa shi a cikin sanyin murya cewa" wannan watan ma na yi

To me ke damun ki?

Hafsat ta daga kafadarta

Abdul kam ji ya yi hankalinsa ya kasa kwonciya, gashi tana jini da sai ya ce cikin ne bai fita ba, mai ke damunta?

Agogo ya kalla ya ga takwas har ta yi dan haka sai kawai ya mikar da ita ya bata hijab dinta ya ce" saka mu.je asibiti

Kallonsa take bayan ta saka din ta ce" aman ni ai lafiata kalau, bana jin wani ciwo fa

Abdul ya gyada kansa ba tare da ya bata wata amsar ba ya kama hannunta ya jata a hankali suka fice

Suna fita motarsa suka zarce
Kys ya yiwa motar kafin su kama hanya

Ita dai kawai kallon hanya take, bata san na me zai kaita asibiti haka ba ita lafiarta kalau
Gabanta ne ya fadi na tunanin ko dai shima yana tsantsamin bata da lafiya ne sakamakon wannan yanayi
Harhade fuskarta ta yi tana jin kamar ta dadage ta zunduma ihu ko zai mayar da ita gida tun kafin ya kaita a fadi wani abinda zata ji kunya

A haka suka karasa cikin clinik din

Wannan karon kin ya riko mata hannun ta yi ta dai bi bayansa har suka shige wajen gannin likitan matan

Sun taki sa.a mace biyu ce kawai zaune dan haka suka zauna suma yana mai binta da kallo sai ta ga ya sakar mata murmushi aman kuma bai yi mata magana ba

A haka har zuwansu ya zo suka mike suka shiga tare

Tun da ya shiga ya ga wani jikeken namiji mai kalar fatarsa zaune yana aikin duba matan mutane gabansa ya fadi, ransa ya yi masa bakikirin ,
Bai aune ba sai gani ya yi har ta zauna a farar kujerar duba mararsa lafia ta bada hankalinta wajen likitan

Sai da ya gama rububuce rubucensa ya dago ya zuba masu kallo,
Fuska Abdallah ya yatsina yana kallonsa, a zuciyarsa kuwa fadi yake mumuna ne kai, sam baka da kyau

Daga kafa ya yi da sauri ya karasa shima ya samu waje ya zauna sai muzurai yake

Likitan da ya gama kallonsa ya ga bai bashi hannu a matsayin wanda ya tarar suka yi musabaha ba kuma dai a yannayinsa bai ga yannayin mai duhun kai ba sai shima ya ki bashi

Sai da ya buda katon litafinsa sannan ya dube su ya yi masu tambayar waye ba lafiar? Yaya sunnansa? Shekarun haihuwarsa?

Tana shirin yin magana ta ji Abdul ya ce" Hafsat , Madame Abdul Jabar, shekarunta ashirin da uku

Kallonsa ta yi, inda shima likitan ya kaleta yana tunanin to ko kurma ce ita din??

Rubutawa ya yi sannan ya basu hankalinsa kacokam ya ce" menene damuwarta? Wace irin rashin lafia ke damunta?

Abdul ya hadiye abin haushin da ya tsaya masa a makogwaro sannan cikin isa shima ya ce" mararta ke da tauri, tana daukan zafi, bayan as nrmal marar mutun bata haka

Kansa ya gyada ya kara yi masu tambayoyin da ya dace kafin ya mike ya nuna mata bed din da zata kwonta kusa da wani allon haskawa wato wata yar karamar tv

Irin kwonciyar da ta yi kanta sai da cikinsa ya juya, wannan a haka din idan ba shi zai haye ruwan cikinta ba gaskiya wani garjeje ba zai kale masa yannayi mace ba ehe!

Bai gama fahimta ba sai da ya ga ya kai hannu zai yaye hijab din jikinta ya kai wajen mararta, waje mai daraja da daukaka a idannuwansa, waje mai tarin sirrinsa

Hannunsa ya kai da sauri ya tare nasa hannun,
Dago da idannuwansa dake cikin gilas ya yi sukai ido hudu,

Abdul ya lumshe idannuwansa ya kuma budewa yana kallonsa bai ce da shi komai ba

Doctern ya saki murmushi kafin ya janye hannunsa a hankali ya juya ya fice a office din

Hade fuska ya yi tamkar bai san meye daria ko fara.a ba inda Hafsat mamaki tamkar ya kasheta

Kanta ta girgiza tana kokarin mikewa da niyar sai su tafi ai tunda likitan ya bara masu office din baki daya!

Bata kai ga tashi ba sai ga likitan ya dawo tare da wata likitar mata

Zuwa ta yi cikin fara.a suka gaisa ta gabatar da kanta ita din ma doctern mata ce

Waje Abdallah ya matsa ya bata ya tsaya gefe kusa da kan Hafsat dake binsa da kallon ga irinta

Shi dai ko a ransa saima maida hankalinsa a wani ruwa ruwan da likitar ta matso ta shafa a marar Hafsat din

Dora abin ta yi ta shiga yawo da shi a hankali tana kallon allon wannan karamar tv din

A hankali ta ce" haka ne doctern, gayanan dan jaririn foetus

Da sauri Hafsat ta rintse idannuwanta tare da jin gabanta ya fadi, Foetus? Aman ai tana al.ada, kennan cikinta bai fice ba? Cikinta yana nan? Gabanta ne ya fadi cike da tsoron me mijin nata zai yi shi da baya wannan ra.ayi a yanzu?

Sai dai yannayin da ya shiga a lokacin da likitar ta tsayar masa wajen da dan karamin halitar da ba.a gama ba aman ana iya gannin abin tamkar wani kadangare sai ya ji gaba daya jikinsa ya dauka

Tsurawa abin ido ya

51 / 54