Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   1 / 54

1 to 3K   out of 159.5K words

??????>??  ?????????????? ?
?
? ?
?
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????


 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?WordDocument????7\0Table????????tData
????????????????????? P? KSKS?7\? ???????VV??????k|
? ???NNNNNNNNP$??e*V??NN????N????N?N??NN?? ?b`????bNormal $a$1$0CJKHmH sH nHtH_HOJPJQJ^JaJTA`????TDefault Paragraph FontOJPJQJ^Jni`????n Table Normal(:V 4?4?l4?4?l OJPJQJ^J? `-???Udl?|\????P??@?????"
H)<<JP?{"?????v????NR8bN(Z?z???t?????p??>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 1??

Cikin tashin hankali a yannayinsa da yannayin muryarsa ya ce " ku kunce ni, ni ba mahaukaci bane! Ku kunce ni!

Likitan da ya shigo da sauri da abin auna bugun zuciya rataye a wuyansa da takarda a hannunsa, bayansa nurse tana tura dan abin dake dauke da magungunna ta auka karaso wajen gadon da Abdul ke faman kuma tayar da wata tarzomar ya yi gagawar zuwa kusan gadon yana daidaita alurar barcin da ya tsira cikin seringe da niyar zubata cikin karin ruwan dake tafia,

Muryarsa cikin yannayi na jigata ya ce" haba docter, kar ka kara min alurar barci mana, sai yaushe zaka barni na je na gana da mahaifiyata? Ka barni haka docter ka ji?

Tsai ya yi yana subansa,
A hankali kanwar mamansa ta matso kusa da shi , hannunta ta dora dake rawa saman hannunsa tana dubansa ta ce" Abdul, idan kana irin haka, ba za.a iya barinka ba, kar ka jiwa kanka ciwo ta hanyar fada a haka ko ka tayar da hawan jinninka, Abdul shin kowani mai rai ba mamaci bane? Dan Allah ka rufa mana asiri ka dawo da tunaninka, ka kwontar daa hankalinka haka Abdul, musulmi ne fa kai, da ciwo Abdul, da firgita, da gigita, sai dai imanin dake tare da kai na kasancewarka musulmi zai hanaka wasu abubuwan, ka nutsu Abdul, ta rasu, ta rasu, ba zata dawo ba, ka farka Abdul, kai da ya dace ace kana tsaye kan kafafuwanka , ka ciri jarumta ka arawa kanka, ka daina haka Abdul, bani da kowa yanzu, daga kai sai Ni.ima, bani da kowa Abdul........
Ita dake bashi baki, sai ta fashe da kuka tana dukewa kasa,
Idannuwansa ya lumshe, bai ci gaba da kokowar da yake yi ba, bai ci gaba da wani hayaniya ba, sai dai fuskarta da irin rayuwar da ya yi a kusa da ita kafin ta amsa kiran Allah, shi, ya yi dandaja da maganarta na daukan mai tsaro ne dan a tunaninsa shi kadai ake iya neman rayuwarsa, ahi kuwa ya san me ya taka, ashe ashe abin zai haura har haka? Ashe za.a cin masa a daidai lokacin da bai yi tunani ba, bai kawowa ransa ba? Shikenan yanzu babu Ummih? Ta tafi, shin ka yi mata adu.a dayama kuwa Abdul?

Da sauri ya bude idannuwansa ya sauke kan fuskar Muhammad,
Da hannunsa ya nuna masa carbin hannunsa, hakan ya saka Muhammad karasowa kusansa yana mika masa carbin,

Karba ya yi yana dubansa ya ce" Muhammad, a kunce ni ka ji?

Muhammad ya gyada kansa ya shiga kwonce belt din da aka daure shi inda docter ya so hannawa aman ya nuna masa ba komai,

Ana kwonce shi ya roki da a kama shi,
Bayi ya shiga ya yi abinda zai yi ya dauro alwallah ya fito,
Zama ya yo saman salaya ya shiga ramuwar salolin dake kansa, ba zai iya yi a tsaye ba domin kuwa juwa yake yi sosai, dan haka ya yi a zaune wanda ya daukan masa lokacin sosai,
Yana gamawa ya dukufa yana ta jan kulhuwa lahu wa mahaifiyarsa, harma da sauran iyayensa, da kuluhin musulmai,
Yi yake ba ji ba gani, har ya dago ya tsurawa waje daya ido yana mai tuna yanda ake sakawa mutun likafani, a hada yatsutsansa a daure , a toshe hancinsa da kunnayensa da kada, a nade shi da likafani yayan an daure kafafuwansa,
(Dan adam kennan a macema daure shi ake), a haka ya yi tunanin irin matsewar rami, a doraka saman hannunka na dama,
a jera itatuwa a rufa kasa kanka,
Shikennan an baroka, kana ji zaka ringa jin takun yan uwanka da iyayenka har su baro makabarta,
Yanzu haka aka kai mahaifiyarsa ba tare da rakiyarsa ba? Haka aka sakata ba tare da sannin shin ana bi a laluma ana ta adu.a ko sakatan kawai aka yi? Shi yaya amsar cikin kabari ta zo mata? A yanzu da take kwana goma da rasuwa, shin tana cikin rahamar ubangiji a cikin wannan daki dan kurkuku wanda yana iya zame mata yalwatace ko akasin haka? Ya Allah ka jikan iyayen mu, Ya Allah ka jikan magabatan mu, Alla ka jikan kuluhin musulmai, ya Allah ka bamu guzurin tarda su na alkhairi.....
Haka ya yi ta zubar da hawayen da yake kukan zuci sosai,
.
......................

Washe gari da ta tashi, sai wajen karfe goma ta shirya dan zuwa makaranta,
Ita dai kallonta kawai take, dan ta yi mata magana ta saka wani damamen wando da yar riga ta dora hula a kanta,
Sai dai ga mamakinta, ko ta nuna mata kar ta saka, saima jakarta da ta miko mata wace ta hada mata kayan bukatarta na makaranta suka fito suka shiga mota,

Dirwba na jan su , Hafsat na kallon titi, ita kuwa ta tsurawa Hafsat ido,

Murmushi ta yi ta ce" hala kin yi fushi?

Hafsat da ta san da ita take sai ta yi kamar bata san da ita take ba,

Hannunta ta miko zata taba cinyar Hafsat da niyar yi mata magana, sai dai hafsat ta janye kafarta ta zabga mata harara ta ce" kar ki yarda ki taba min kafa,

Murmushi ta yi tana janye hannunta irin ta yi hakuri ba tabata zata yi da wata niya ba,
Tana kallonta ta ce" kin san da na girme ki?

Hafsat ta juyo da manyan idannuwanta ta sauke saman fuskarta,
Tsai ta yi da dubanta tana kallonata, tabas ta girme ta,
Kanta ta juyar bata bata amsa ba dai,

Bata gaji ba ta ce" idan har na bata maki rai ne ki yi hakuri kin ji? Kin ga na saka kayan nan ko ki hana ni?

Hafsat ta juya tana kallonta again, ko na hanata? Ita mahaukaciya ce? Ko me?

Kanta ta girgiza kafin a hankali ta ce" ki rike damarki, tun kina da damar hakan, kar wauta, baci, sangarta ya saka ki aikata aikin dana sani, ke naki mai sauki ne, ki fita harkar samarin zamani, idan wani ya hadiye ya kawar da kai, wani zai bilo maki ta inda baki taba zato ko tsamani ba,

Ina iyayenki suke suka barki kike aikinnan? Bauta ce a gayance fa? Bakya baci sai kin tabatar da ina cikin kariya tamkar mahaifiyata? Iyayena kansu suna gefensu suna hutawa ke kuwa kina tsaye kan kafafuwanki? Ke baki da gata ne? Fatar jikinki bata nuna ke din wahala ta kai ki zama mai tsaron lafiar wani ba, baki da dad da mom ne? Ina nufin sun wula ne????
Ta fada da yannayin shakiyanci du dan ta kulata,

Murmushi ta yi na zuci, ta kawar da kanta,
Motar da ta gani tunda suka hau bakin baba layi ce dai bata daina binsu ba, kuma gashi suna faman su shiga ta wani lungu,

Juyowa ta yi wajen direban zata yi masa magana aman ga mamakinta, hular da ta baiwa direban dake tuka su ba itace a kanta ba,
Gabanta ne ya fadi, tabas ta shagala yau, tunanin iyayenta da ta kwana yi da kuncin zuciya ya sakata a duniyar shagalta, wannan du inda ya fito ba direban da yake tukasu bane,

Abayar dake saman wando da rigarta ta anniya kwabewa cikin hikima, kafin ta samu da dabara ta haska madubin dake cikin pos din wayar dake hannunta,
Tabatarwa da ta yi cewar ba shi bane ya sakata saka rigar nan tata ta shako wuyansa,

Ihu yarinyar ta saka inda shima abin ya diro masa a bazata dan haka ya shiga kokarin kwatar kansa da kuma gannin morar bata fadi ta kashe su ba,

Ihu take tana fadin" zaki kashe mu, ke zaki kashe mu,

Kafarta ta saka ta hambara mata kutufo a wajen da ta san koda bata suma ba, tofa zata tafi duniyar jigatar da zai hanata magana,

Suma ya yi, inda ya dora kansa saman sitiyarin motar, da sauri ta tsalaka ta mayar da shi gefe sannan ta warci motar dake tangal tangal tana fama maka su da garu,

Atach din dake saman kanta ta cire da hannunta na hagu ta yar saman direban da ya tafi duniyar summa,

Sai da ta gama tare jinnin hancinta ta dago du a firgice tana ta zarar ido gannin sun canza hanya su da zasu dauki hanyar da zata kaisu university sun canza sun durfafi police station din da ta fi kusa

Ta gama sarewa, inda Hafsat ke wani irin tuki cike da kwarewa da kuma garari har ta samu ta karaso , nan ta ga suna faman juyawa, da gudu ta tsayar da motar kusa da wani police da ya mike ya nuno motarta da bindiga kan ta tsaya ko ya harbeta kar ta shigo masu police station a irin tukin nan,

Tana tsayar da motar ta fito da gudu ,
Takardar dake aljihunta ko mace kati ta nuna masa shaidar ita din ko wacece sannan ta warci babur dinsa ta yi masa nuni da ya tsare mutanen dake cikin motar,

Wani irin tuki take yiwa babur din, inda take magana da BS kan hanyar da ta ga motar dake binsu ta bi, sannan tana biye da motar saman babur

Cikin azama da wani irin gudu suka dauki hanya , nan Allah ya basu sa.ar cafko mutanen cikin kwarewa da aikinsu suka kama su, sannan suka koma police station,

Kallonta kawai yarinyar ke yi da muguwar sha.awar aikinta a yanzun kam,
Ta birge ta, irin yanda ta tuka motar dake faman juyewa da su, irin yanda yarinya karama da ita ta warci babur ta yi masa irin tukinnan, kai da zata samu wannan aikin, ta zama irin wannan baiwar Allah da ta so, ta gama tafia da ita,

A lokacin da ta mayar da Abayarta ta fito cikin nutsuwa tana goge jinnin dake zuba a hannunta wanda ta ji a lokacin da ta daki gilas din motar, ta dubi yarinyar da ta gama baiwa tsaro,
Murmushi ta sakar mata, ta mika mata hannu kan su yi salama

Itama cikin murmushin ta bata hannun suka yi musabaha,
Murya kasa kasa Hafsat ta ce" bawa na tsintar kansa a rayuwa kala kala, idan yana da dabara zai dauketa yanda ta zo,
Babar dabarar da bawa zai yiwa rayuwarsa shi ne, ya iya rike opportunity.....bata fiya zuwa sau biyu ba, *FREIND*

Da haka ta saki hannunta ta juya cikin tafia ta yanga irin ta yar budurwar da ta cika ta batse take takama da sura mai kyau, Hafsat ta gama hardace abubuwan d aka koya mata hakan ya sa ba zaka taba tunanin tana iya juyewa ta daki fada na mamaki

Tunda ta taho ya shagalta da kallonta, yannayin yanda take shawagi, ga sansanyar iskar safiya na kadata,

Murmushin da bai shirya ba ya saki yana kara kallonta, kafin ya waiga inda aka saka mutanen da aka kama da direban cikin motarsu,

Tana zuwa ta zagaya ta shiga motar ta zauna mazaunin direba,
Idannuwanta ta lumshe tana mai jin yanda mitar ta dauki shiru,
A hankali ta mika hannunta wajen kuna redion motar ta kuna, sai waka ta shiga tashi ta hayaniya irin wannan,

Hannunsa ya kai ya kashe, da hannu ya yi mata nuni da GN na sauraronsu fa,

Dan karamin lebenta ta tabe sannan ta shiga bin garin da kallo, tana mai tunanin abinda zai kara fitar da ita, wata mission din?

Ko da suka karasa computernta ta dauka ta shiga yanar gizo tana bincijen abinda ya shafi aikinta hankali kwonce, idan ta motsa daga inda take dan ta gabatar da ibadarta ne,

A cikin wannan daren suka tashi da tashin hankali, daya dake cikinsu da ta tafi kasar Span dan baiwa wani atajirin saurayi tsaro, an cin mata, an zo harbe shi rana kusa aka hada da ita, inda shi bai mutu ba, aman ita a lokacin ta amsa kiran Allah,
Wannan lamari ya girgiza su, domin yarinyar bata da damuwa, bata da dagin kai, duda yar wani ce bata da wata damuwa da hakan,
Haka suna ji suna gani aka shirya gawarta cikin sanduki hayan an yi mata likafani aka kuma nadeta da drapo din niger ana sakata a sanduki aka tafi da ita inda za.a yi mata sutura tare da iyayenta wa.inda sai dai su ga sandukin, ba zasu ga gawarta ba,

A wannan ranar wajen mutun uku suka ce sun fasa aikin, inda wajen ya rikice da rigima da koke kokensu, sun tsorata, harbi a kai? Ta tafi shikenan? Sun matukar girgiza, kowace so take ta samu mahaifinta , bata so, ta fasa wannan aikin mai cike da gadari.....su sun dauki hakan a matsayin gayu da nunawa duniya su din jarumai ne, aman haka kawai sai a kawo gawar daya? Aa......

......................................................

Bayan kwana arba.in

Du wani na nesa da na kusa, qminan arziki dama yan uwan yan uwa du sun tatara sun koma daga gaisuwar rasuwar mahaifiyarsa,

Kanwar mahaifiyarsa da Muhammad kawai suka rage, shima Muhammad ya yi zuwa uku kasarsa ya dawo ne,

Abdul Jabar ya zana wani silent man
Askin nan da yake yi kwalkwal ya aske kai, rabonsa da shi tun kafin rasuwar mahaifiyarsa hakan ya saka suma ta fito sosai kansa, suma mai yawa mai kuma tauri tauri hakan ya saka kan ya cika da gashi irin yanda samari ke tarawa ,
Sajensa da a da yake askewa baya barin ko kadan, yanzu ya fito sosai ko.ina ya zagaye fuskarsa,
Gemunsa ya kara cika, lebensa suna da dan girma, dan ba zaka taba kiransa da mai kananun lebe ba, aman kuma ba dambatsa dambatsa bane,
Idannuwansa sun fi komai girma a fuskar tasa idan ka cire karan hancinsa mai tsini, idannuwansa jajajir suke, rabonsu da su yi haske tun a lokacin da yake tataunawa da mahaifiyarsa yana mata murmushi itama haka,

Zaune suke su su uku,
Su biyun suna dan taba hira, ba ta komai ba sai ta zaman duniya da jimamin yau da gobe wanda bai bar talaka ko mai kudi ba,

Tunda suke magangannun shi dai kansa a kasa yana sauraron su, bai ce da su komai ba, haka kuma bai hana su maganarsu ba,

A hankali ya bude bakinsa, muryarsa da ta zama wata iri mai amon irin muryar nan ta kakarfan maza ko wa.inda giya ta kashe masu zakin murya ya ce" aure nake so.

Muhammad dake magana da aunty Firdausi ya juyo da sauri yana kallon Abduk Jabar,
Itama auntyn hankalinta ta maido kansa,

Dago da idannuwansa da a yanzu in dai ba dole ba , mutun ba zai so su kurewa juna kallo ba, ya sauke saman kansu,
Lebensa na kasa ya kamo da harshensa ya shiga dan tsotsa yana kallonsu bai ce da su komai ba,

Kai aunty ta kawar daga dubansa ta ce" Aure?

A hankali ya saki bakin nasa ya ce" eh, aunty na san kin san na yi rayuwar rashin jin magana,
To bana so na sake , dan ba zan so a tayar da mahaifiyata a nuna mata abinda nake daga kabarinta ba, kuma gashi ina son mace a kusa da ni, dan haka zan yi aure.....


Muhammad ya shiga jinjina kai yana mamakin jaraba irinta abokinsa,
Aman kuma ba laifi tunda yanzu ya nemi ya kara wani auren.....aman kuma wani abu ya tsaye masa a rai, ba irin maganar da ba.a fada masa kan ya daina harkar mata ko dan mahaifinsa idan baya tsoron sauran abubuwan, ya ji kunyar Allah, ya kuma kaucewa mahaifinsa shiga halaka ta dalilin sabon Allahn da yake,
Yakan ci gaba da shagalinsa , aman yanzu ya nuna zai fasa dan mahaifiyarsa? Me abansa ya yi masa haka? Ko dai da wata a kasa? Irin rayuwar rashin sannin ciwon kan da ya ringa tafkawa?

Dubanta ta kawo saman kansa bayan ta yi dogon nazarin maganarsa, a hankali, a nitse, da yannayi na rarashi, da neman cin galaba kan maganarta ta ce" aure ba laifi, za.a nema maka auren ko yar gidan wa kake so,
Sai dai da sharadi Abdul,....
Maganar *BODYGUARD* da mahaifiyarka har ta rasu tana fama yana nan daram bai canza ba,
Za.a je a dauko kwararun bodyguard biyar,
Daya zata baiwa matar da zaka aura tsaro.....
Hudu zasu kasance da kai idan maza kake so ko mata, a dukan motsinka,

Abdul kar ka yi min gardamar haka, dan na rantse maka da Allah



Ku yi hakuri, i.m sick ne,=?
?, na gode da adu.o.inku, Allah ya saka da mafificin alkhairi

>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo

1 / 54