Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   12 / 54

33K to 36K   out of 159.5K words

na tsonci kaina a ciki,
KUTKALE ko fita ka yi dan guduwa baka da hanyar bi bale ka kai kanka gida, Kutkale gidan kason masu mumunan laifi, yai gani cikinsa, ban kashe ba, ban birne ba, ban ci kudin wani ba, na tainci kaina ciki sanadiyar rashin jin maganar iyayena,
Sai da ta nisa kafin ta ce *Mijin da suka aura mini*, Ya Allah ka..........
Bata karasa adu.ar ba ta ji an doke hannunta, cikin hargagi ta ce" dan ubanki jiya ki rasa wanda zaki bi sai Usman? Du mazan gidan nan ki rasa wanda zai zaga da ke sai saurayina? Shigiya mai fata kamar ta bunsurun dan akuya! Usman ya fi karfin uwarkima ba ke ba!

Hannunta ta kuma dagawa ta karasa adu.arta da gagawa ta shafa, daidai lokacin ta fincike mata dan rufar kan nata da ta yi salar da shi,

Mikewa ta yi da sauri ta warce abin, domin shi kadai ne da ita da shi take sallah,
Wurgawa tsohuwar nan dake girgiza mata kai ta yi , bata tsaya wata wata ba, bata dubi irin raunin jikinta ba, bata karya ba, daman jiya ta kwonta bata ji ba, ta ja tirjiya kafin ta yi ciki da abokiyar fadan nata suka je kiiiii suka fada cikin tabo da kwatar dake wajen......



*WACECE WANNAN?*
*ME YA KAWOTA PRISON?*

MENENE MAKOMARTA?



KU BIYO NI, DAN JIN ME KUTKALE YA KUMSA?


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 8??





Tana kokarin tayar da mashin din ta hango wani irin mutun,
Mutun ne zabaya namiji kuma wada ,
Kai ba dan ba dan ba sai tace ko ta yi gamo ne? Dan kuwa mutumen tsayawa ya yi yana kallonta kamar ya ga bakuwar halita

Adu.a ta yi sosai ta tofa masa yana kallonta tana kallonsa,
Gannin ya ki motsawa ya kuma kin yi mata magana ya sakata saukowa a hankali ta nufe shi inda gabanta ke luguden kida

Tsayawa ta yi dan nesa da shi ta yi salama,

Ga mamakinta sai ta ga ya matso kusa da ita sosai

Sai da ya daga kansa ya kaleta domin ya matso kusa da ita kafin cikin muryarsa dake nuni da manyantakarsa ya ce" ke kuwa, kin ari musulunci ne ko musulmar ce ke?

Kanta ta sada dan kallonsa da kyau itama kafin ta ce" kama gare su ne musulmai ko salamana ne bai cika ba?

Kansa ya gyada kafin ya juya da niyar tafiyarsa ,
Gane hakan da ta yi ya sakata matsawa da sauri ta ce" dan Allah, ka taimake ni, ina son sannin waye Muhammad bine Abdul Basid Abdallah? Ko zaka iya kai ni inda yake?

Sai da ya kare mata kallo sannan ya ce" ki je dare ya yi, ki dawo zan kai ki wajensa, aman yanzu akoy nisa ga kuma dare

Ta so ta yi magiya ko zai saurareta, sai dai gannin bashi da niyar hakan ya saka ta juyawa ta hau mashin din ta tayar ta dauki hanya wanda a lokacin tuni isha ta kawo kai, a kadan zata iya kaiwa awa uku ko zata isa

Gudu kawai take yi, gashi a lokacin da zata bar gidan Abdul sai da ta ajiye du wani abin aikinta da zai bada damar a san inda ta nufa, ta tabata yanzu an farga da bata nan, fatanta kar ta kai BS bango ya dauki mataki a kanta ya kawar da wani gudun bacin ranta ya saba mata!


Ta jima, ba karamar wahala ta sha a hanyar ba kafin ta karasa anguwar, a haka har ta karasa kofar gidan

Tun daga irin kallon da sojojin ke binta da shi ta dan sha Jinnin jikinta, sai dai bata saka komai a ranta ba ta samu ta shigar da mashin din ta karamar kofar sannan ta sauka ta shiga tura shi ta ci uwar tafia kafin ta karasa farfajiyar gidan

Dare ne, aman ko.ina ya dauka da hasken fitila , hakan ya saka du wani mai motsi ana iya ganninsa da dukan abinda ke tare da shi

Tun da ta shigo gabanta ya yanke ya fadi, dan kuwa du wani bodyguard da ya kwana ya tashi a gidan yana tsaye cirko cirko , BS sai doka waya yake haka kuma sai duba agogo yake, gefe kuwa Abdul ne tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa ya zubawa hanyar da ta fito ido


Turus ta yi da babur din gannin yanda BS ya nufo inda take tsaye gadan gadan ta tsura masa ido sannan ta sadakar cewa idan ya zo yana iya dauketa da mari

BS na karasowa hannunta dake rike da mashin din ya damka yana dubanta ya ce " ina kika je? Ke da wa kuka je? Me kika je yi? Bakya tsoron wata fitina ta same ki?

Idannuwanta ta kikifta tana kallonsa,
A hankali ya sasauta damkar da ya yiwa hannunta ya rage ihun muryarsa ya ce" baki damu da damuwata ba? Ya dace ki damu da aikin ki, dan wanda ya dauke mu ya san takun mu

Yawun bakinta ta hadiye a lokaci guda kuma ta dan leka bayansa,
Ido hudu suka yi da Abdul sannan ya juya ya shige ciki ba tare da ya ce da kowa komai ba

Sai a lokacin ta jinginar da mashin din dake kauri ta ce" BS, ka yi hakuri, na gaji da zaman waje dayan ne, shi yasa na fita na sha iska

Hasana dake tsaye ido ta zaro tare da fadin" me? Ke kina da hankali kuwa? Ke Bodyguard har wani lokacinki gare ki bale muradinki? Ki dubi idannuwan mutane ki ce wai kin tafi shan iska? Ba laifi, tunda kin shawo iska sai ki zo ki zagaye balbalin gidan nan sau hamsin!

A tare suka dubeta, daga BS har Hafsat,

Hafsat kam dukawa ta yi ta kara gyara takalmanta sau ciki sannan ta cira da gudu da daren nan ga tarin gajiya , ga yinwa, ga bukatar yin wanka ta shiga gudun punishment domin kuwa Hasana dai ta isa ta sakata ko ta hanata a bangaren aikinta dan gaba take da ita ya zama wajibi ta yi mata biyaya

Hannun Hasana ya damka ya juya da ita da wani irin karfi ya hankadata gefe inda ba za.a iya hangosu ko a ji maganarsu ba ya ce" ke a wa zaki shiga hurumin da ba.a saka ki ba? Ina ruwanki da amsar da ta bani? Ke idan a halayanki zan bi ki kina tunanin zan bar ki ki numfasa ne?

Bayanta da ya buga da bango ta dafe kafin ta ce" BS , saboda na hora yarinyar dake kokarin rainaka a gabana ne kake wulakanta ni haka? Menene tsakaninka da ita? Wacece ita? Me ya sa na ga du kuna wani rawar kai a gabanta? Idan tana zagayawa da wancen da muke yiwa aiki kaima kwoncin kake da ita ko?

Cikin daga murya ya ce" ki rufe min baki da fadin magangannun da ba tsari a nan,
Kin ga yarinyar can da kika raina? Ni ita nake so, kuma ki daina kokarin zaginta dan ko daya , ba irinki bace, yanda take jana a kas ya saka nake kara mutuwa kanta, ta san ina sonta, har yanzu ta kasa so na, dan haka ki girmamata kar ki yarda ki mayar da ita abokiyar gabanki , dan na rantse maki ta ishe ki tuwo da miya

Sosai magangannun nan sukai mata zafi, tana dafe da bayanta ta ce" aman ka san da ni kake soyaya ko? Kuma ka san aikinka ya haramta maka soyaya da dalibar da ba.a yaye ba ko?

Sai da ya shafa gaban goshinsa da sankon kansa sannan ya ce" to ki tona, ke bari ki ji, abinda zai hana ni samunta daya ne, idan ta ce da ni Bashir ka barni haka, bana son ka!


Yana gama fada ya juya ya fice ya tsaya can gefe yana hangen yanda Hafsat ke gudu tana raba hanya,
Kwarai yana da damar hanawa, ya isa ya hana dan shima yana matsayin gaban Hasana, sai dai ba zai shiga ba ko dan ya kori tsargi sannan ya rike girmansa a wajen yarensa, tausayinta yake ji, kaunarta yake yi, ji yake dama zai karbar mata gudun!


Abdul dake tsaye kusan windows din dakin Muhammad ya rike dan labulen ya tsura mata ido yanda take gudu, Muhammad na yi masa magana shi walahi kwata kwatama bai san me yake cewa ba, a haka ya juyo ya ce" *daga ina take?*

Muhammad dake dana waya yana nuna masa sabuwar motar da kanfanin Helix suka kera wace ke da tsananin tsada ya dago yana dubansa
Sai da ya matso inda yake tsaye ya ce" wa kake tambayar inda ta je?

Sai a lokacin Abdul ya farka, tamkar an dan tsikare shi ya dubi Muhammad da kyau, sai kuma ya shiga takawa ya ce " ina zuwa.......

A wannan dare haka kowa ya yi barci zuciyarsa a cinkushe, tun daga Abdul, Ni.ima, Hafsat, BS , Hasana, da du wani ikon dake gidan wanda sanadiyar rashin gannin Hafsat da tabatar masa cewar ta fita a mashin ya saka tayar masu da hankali da rantsuwar su saurari du irin abinda zai sameta walahi da hannunsa zai masu! Hakan ya saka du suka firgice suna masu jin haushin juna da jin haushin wanda ya ara mata mashin din

Ko da safe ba wanda ya shiga sabgar wani, kowa bakin aikinsa yake tun safe har yama,

Ko da yama ta yi , yauma fitowar ya yi , sai dai yau wani bakin yadi sidik ne ya saka ya fito ya nufi wajen shakatarwarsa

A lokacin da ya zauna ya mike kafarsa ya kali BS dake kai kawo ya ce" ka ce da dayar nan ta fita can baya ku kuwa ku zo kai da wancen ina son gannin ku

A nunin da ya yi, yana nufin a cewa Hasana ta fita, su kuwa ya nuna su zo saman kujerar dake kusa da shi yana son gannin su

Abinda ya bukata BS ya aiwatar, inda suka zauna a kujerar dake gabansa su duka suna kallon yanda ya tsura masu ido ya kalli wannan ya kalli wancen

Sai da Abdul ya gama kallon su sannan ya ce" *wai ku yaushe kuke zance ne? Wace irin soyaya ce kuke haka bakwa bata kulawa? To yau ku yi zance!*

Sai da suka kalli junna sannan suka kale shi a tare tamkar hadin baki,
BS ya dan gyara zamansa yana kallon Abdul,

Abdul ya girgiza kai ya ce" kai yanzu, katoto da kai, kake jin tsoron wannan yar yarinyar? Bashir maza ka rako duniya ko me? Ka fito kace da Hafsat cewa kana son ta aman sai ka ringa hauka har kowa ya gane kana sonta ita ka kasa fada mata kiri kiri?

Sai da BS ya mike tsaye, sai kuma ya koma ya zauna tamkar an dangwarar da shi yana zare ido yana kallon yanda Abdul ke kada kafarsa dake wanke tas tamkar a side,
A haka ya bi shi da kallo har fuskarsa, kai shi ko a lakuru bai ga kwalon dan duniya irin Abdul ba,

Dubansa ya maida wajen Hafsat ya ga ta tabe bakinta ta dafe gaban goshinta, kuma abinda ya bashi mamaki bai ji ta yiwa Abdul ihun kar ya yarda ya kama sunnanta sunnan mahaifiyar malan ce, ohk wato sai su da aka raina ko?

Katse masa tunaninsa ta yi ta hanyar fadin" *ABDUL*

idannuwansa ya dauke daga duban gefen da yake , ya saka cikin idannuwanta har da takabe kumatunsa yana kallon yanda ta kankance idannuwanta wai kennan zata yi jaraba ko?
Dubansa ya kai wajen BS ya ce" Bashir, ko jaraba zata yi kyau take mata, bara ka ga yanzu ta ce" Abdul, menene haka? Ka bar mu mu koma bakin aikin mu....
Sai ta wurgan harara, sai ta mike ta tabe baki kuncinta ya lotsa , sai ta koma bayana ta yi tsaye ta hade rai dan Hafsat bata son raini!


Kallon junna suka kuma yi ,
Nan Hafsat ta lumshe idannuwanta tana son tunanin girman rainin hankalin Abdul,
Sai dai bai bata wannan damar ba ya katse mata tunani da fadin" kina tunanin zan baiwa soja mashin na kasa saka masa abinda zai nunan inda yake shiga?
Hafsat me kika je yi cikin jejin da ba wani mahaluki dake rayuwa a cikinsa a sanina? Kina son na saka maki ido a motsinki ne?

Shiru ya yi, kafin ya ci gaba da fadin" BS nah? Ka tambayi wajen wanda ta je dan ba zan lamunci hakan ba!

Mikewa ya yi ya mayar da bakin gilas dinsa ya juya da niyar tafia,
Sai dai sunnan da Hafsat ta ambata ya kusan tainke masa lumfashi,

Wani irin ja ya yi ya tsaya sannan ya juyo a haukace ya.......


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 6??



A lokacin da suka fito gaba dayansu da yannayin na zakunna, kowane na jefa kafarsa inda ta je, suka tsaya gaba dayansu a tare sakamakon ganninta tsaye ta zuba masu ido su duka,

Sai da gabansa ya yanke ya bada wani irin sautin da kunnayensa suka jiyo masa,
Tsaye take kawai, hannayenta gaba daya a sake, wandon dake jikinta irin mai lafewa a jiki ne aman kuma sakake wajen mazaunanta kawai ya rike , sai riga mai botura da wata a ciki wada dalilin bale boturan da ta yi ya saka ake ganninta, kanta dauke da asalin gashinta ba wancen atach din ba,
Fuskarta babu ko digon kwali bale a yi hangen hoda ko wani abin,
Aman wani fayau da shiga ido da take sai a hankali, dole ta girgizawa namiji lafiyaye zuciya sai dai idan zuciyar taka na hangen wata sai ka kyasa a ranka ka huce wajen,

Hannayensa ya daga ya cusa cikin gashin kansa da ya bar suma ta taru sannan baya gyarawa,

Sai da ya dan waiwaya ya ga tsayuwar me kuma suke a bayansa? Sannan ya daga kafarsa ya tunkareta,
Hannunta na dama ya damka ya jata tamkar rakumi da kala haka ta bi shi ba tare da ta warci hannun nata ba, ba kuma ta yi masa gardama ba,

Da kallo suka bi su, inda BS ya daga kafarsa ya bi bayan su da saurin gaske, sai dai yana karasawa Abdul na banko kofar da wani irin karan sautin dake nuna halin bacin ran da yake ciki,

Wani irin hankadata ya yi cikin dakin dake mamaye da duhu, wanda yake daya daga cikin dakunan gidan, shi kansa bai san ainahin inda zai je ya kuna fitila ba, sannan tun da ya hankadata yama rasa inda ya hankadata,

Garu ya yi nufin kaiwa naushi, wanda sai da ya naushi iska sau uku kafin ya samu hannunsa ya naushi garun da wani irin karfin da da normal ne sai ya ji jiki ainun, aman da yake ransa bace ne sai ihun bacin rai da ya saki murya kausashe ya ce" me kika ji? Me ki ka ji nace?

Inda yake kallo daban, inda muryarta ta fito daban, domin ita a bayansa take, a hankali, cikin mutuwar jiki ta ce" ina bayanka,

Juyowa ya yi ya yi shiru, inda ya dauke numfashinsa, yana so dole ya lalubota ta habyar numfashin da take saukewa,

Fahimtar hakan da ta yi ya sakata tsayar da numfashinta sannan ta canza waje da sauri ta saisaita ajiyar zuciyar da take yi, ta dan labe wajen labulen wajen ta ce" a wajen formation din zama gagarimin sojan dake aiki wa kasashen duniya baki daya, wanda yana da damar yin operation inda ya ga dama, yana da takardun shaidar shi dan kasar da du ya yada zango ne, shi dai wannan mutun ko shugaban kasa na mangarinsa domin ba.a bayar da formation dinsa a kananun kasashe sai irin su chaina, dubai, ko su Saudiya. Japan...da dai sauransu....
Wanda a cikin mutun hamsin bai fi biyar su fita ba, kai ana iya goge kowa a hanawa duka hamsin

12 / 54