Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   3 / 54

6K to 9K   out of 159.5K words

Abdul din

Sai da ya dan dubeta, sannan ya girgiza mata kai ya rabata ya shige

Hannayenta duka biyu ta dora saman kanta a fili ta furta" shikennan, sun cin maka Abdul,

Hannunta mai ciwo ne ta ji kamar wani abin ya kara sukarta, dan haka ta dan ajiye shi a ranta tana tunanin harbin ne ke hadasa mata haka, aman a hankali sai ta dan juyo hannun dan dubawa

Sai da gabanta ya fadi irin abinda ta gani, rubutu ne, da larabci a bayan hannun nata,
Da sauri ta juya ta fada dakinta ta kunna wutar dakin ta je gaban madubi ta ja ta tsaya tana kallon hannun,

A hankali ta karanta abinda aka rubutan kafin ta fasarce da kalmar hausa cewa *maganin ruwan zamzam da dabino ta hanyar da jinnin ya yawaita*

Ta karanta ta maimaita ya fi a kirga kafin kamar a mafarki abinda mutumen da ya damki hannunta a wajen taron nan ya dawo mata,
Tabas wannan mutun shi ne ya damki hannunta daidai wajen nan wanda ta gani rike da bindiga har ta yi ihun mutun da bindiga,

Da sauri ta ruko idannuwanta domin kuwa ba zata manta ba da ya fadi haka sai da ya kure mata waje kafin ya furta mata sunnan *ABDUL*

Baya baya ta yi dabas ta zauna a kasa,
Tsoro da rudu ne suka shigeta a lokaci daya,
Ta shiga rudanni tsakanin amsoshi biyu ta fanni biyu,

To waye shi? Me zai saka shi ceton Abdul? Idan fa ba cetonsa bane zai yi aa karasa shi ne zai yi ta wannan hanyar? Aman kuma ruwan zamzam waraka ne, tsaftacen ruwa ne, zai cutar da bawa ne?
Eh to ana iya hada shi da wani abin ya cutar din mana,
To aman da dabino ne aka hada shin fa, dabinoma ai warakar ne,
Yannayin mutumen bai bata kalar mai tausayi ba,
Yannayinsa bai yi mata nuni da zai iya ceto ba, idannuwansa sun tsoratar da ita, irin rikon da ya yi mata ya tsoratar da ita,

Tana nan zaune tana sakawa tana warwarewa har ta ji alamar kukan ambulance

Mikewa ta yi cike da mamakin ambulance kuma? Ina kwakwaluwar BS zai bari a kai shi asibiti a ambulance? Idan fa an yi haka ne dan a tarbi motar a karasa shi?? Baya tsoron daga ambulance din wani mugun abin ya same shi??

Da sauri ta nufi hanyar fita ta fice a dakin ta tunkari dakin Abdul din

Tana zuwa yanzun tsaye ta yi gaban Bodyguard din ta bashi bayannin ita ke kula da ci shan Abdul, ya dace ace tana kusa idan za.a saka masa karin ruwa da du wani abu, idan ya hanata shiga Abdul ya tashi zata kai karansa wajensa dan kuwa ya hanna mata yin aikinta yanda ya kamata

Sai da ya yi mata kallon baki da wayo, sannan ya yiw BS magana da abinda Hafsat ta fada,

Jimm BS ya yi na dan lokaci kafin ya ce" barta ta shigo

Hanya ya kauce mata ta shiga ya bi bayanta da kallo yana mamakin to idan ta fadawa Abdul din sai me? Shi ya san kan aikinsu ne? Kuma yayama aka yi take kama sunnansa kai tsaye tace *ABDUL?*

Tana shiga wajen BS ta zarce tana kallon yanda Abdul ke kwonce shame shame an cire masa rigar jikinsa daga shi sai wandon rigar , likita da Muhammad na kusa da kusa da shi
Haka kawai ta ji zuciyarta ta karye, ya salam, mutun, mutun ba komai bane, mutun ba komai bane, yanzu Abdul ne lokaci kankani ya dawo haka? Mutun shi ya dauki kansa wata tsiya!

Sai da ta yi da gaske ta hana idannuwanta zubar da hawaye, a haka ta karasa gaban BS dake tsaye ta dago da idannuwanta ta lunshesu sosai ta bada kalar tausayi da son ya saurareta ta ce" BS, ya zaka yarda a tafi asibiti da shi?

BS ya tabe baki yana kawar da idannuwansa daga yannayin fuskarta fanma kar zuciyarsa ta karye ya ce" kin san dai a haka ba za.a iya tafia da shi asibiti a motarsa ba ko? Dole sai an jona masa abin taimakon da dole sai an saka shi a ambulance domin a ciki ne za.a iya samu!

Hafsat ta kara matsawa kusa da shi sosai , ta rage karfin muryarta ta ce" mutumen da ya rike hannuna, dubi abinda ya rubuta min a bayan hannu, idanfa an saka masa poison ne sai wannan ne makarinsa?

Wani duba ya yi mata kafin ya ce" ta ina aka kai gareshi? Marabinku da shi shigarsu cikin motar dan minister, jikin ku jikinsa fa, a iska aka saka? Idan a iska ne yaya aka yi mu bamu shaka ba?
A abin sha aka bashi? Sannin kanki ne ko abinci bai yarda da shi ba , shi ke girkawa ya ci da kansa ko *abincin ki* bai yarda da shi ba!

Da sauri ta dube shi, wai ko abincinta, dan me za tana wareta da su?
Kanta ta kawar tana dubansa ta ce" wannan likitan, baban likita ne da ake takama da shi a garin nan, tun da na shigo ni banda kame kame da desespoir din dake nuna bai san kan abinda ya hadasawa Sire wannan rashin lafia ba bana gannin komai,
Yana maimaita ko ya shaki wata iska ne? Ko wani abin?
Yace a kai shi asibiti dan su shiga bincike su ga abinda ya same shi ya hadasa masa haka, binciken da kan iya daukan awowi domin inji ke bada amsoshin ba mutun ba,

Shiru ta yi kafin ta kara dubansa da idannuwanta da suka ciciko da kwallah cikin wani irin sanyi da murya mai rawa rawa ta ce" *idan fa ya mutu kafin lokacin?* jinni ne fa ke zuba daga hancinsa *Bashir*

Tsai ya tsayar da idannuwansa cikin nata jin yau na farko kennan da ta taba kiran sunnansa kai tsaye, ashe ta san sunnan? Ashe ta san sunnansa?
A gaskiya maimakun yannayinta ya saka shi cikin shaukinta sai ya saka shi cikin halin damuwa, shi fa ko me za.a ce ba za.a iya saka shi yarda da wai Hafsa na haka dan samun yanci bane! Dan haka shima cikin dakewa ya ce" idan ya mutu, ai lokacinsa ne ya yi, akoy wanda ya isa ya hana shi tafia ne?

Mamaki, tsoro, duka suka daketa tana duban BS yana dubanta ya furta mata haka?
A hankali ta hadiyi yawun dake bakinta dan kadan wanda da shi da babu kusan daya, ta lumshe idannuwanta hakan ya saka hawayenta zubowa bisan kumatunta,

Wannan karron muryarta ta daga ta ce" na rantse da wanda raina ke hannunsa idan akoy wanda zai fita da wannan mutumen yau sai dai idan harbe ni zaka yi kafin a fice da shi! Ban ga wani dan adam din da zai kara nisan kusancina da Malan ba!

Juyawa ta yi da sauri tana kokarin ciro karamar bindigar dake kugunta BS ya yi saurin damko hannunta ya juyo da ida inda du su Muhammad da docter suka juyo wajen da suke dan kuwa da gaske ta tayar da kukuma gata tsurut a gabansa

BS na kallonta da takaici ya ce" kin san ba ke daya ke anfani da bindiga a wajen nan ba ko? Kuma kin san gaba dayanmu manyanki ne ko? Ke ko kunya bakya ji saboda shi zaki yi haka?

Hannunta ta fizge ta ruruko idannuwanta, wato dai masifar ta motsa ta ce" me ya kai kudi daraja a wajenka? Kai saboda kudi kana iya yin komai ko? A tsaka mai wuya muke daga ni har kai! Ka harbe ni kawai ka huta da ni, idan ka harbe ni me za.a yi? Ba abinda za.a yi kana iya cewa kan aikinka kake na tare maka hanya BS!

Hannunta ta kara fuzgewa daidai lokacin Hasana ta shigo domin dai sabon Bodyguard dinma na casan kokowa da Ni.ima wace sai zuwa lokacin da ta ji kukan Ambulance ake fada mata mijinta ne ba lafia dan haka ta fito da rigimar sai ta je inda yake

Hasana na shigowa ta kai dubanta wajen BS tana jiran umarnin yanda za.a yi da Hafsat, sai dai ga mamakinta sai ta ga ya saki hannun na Hafsat din ya barta sai da ta fara tafia wai kamar BS ya sandeta ya buga mata hannunsa dake mike a bayan keyarta hakan ya hadasa mata zuwa duniyar summa

Bata gama jin tsanar Hafsat ta darsun mata ba sai da ta ga BS ya kinkimeta ya dorata saman kujera mai cin gurin mutun hudu ya mikar da ita ya gyara mata kwonciya sannan ya mike yana kallon Muhammad dake jefo masa kausasun tambayoyi kan abinda ke faruwa,

Muryar docter ce ta katse masa hanzarinsa inda ya furta cewa maza a shirya shi a dora shi kan gadon mararsa lafia a fita da shi a saka shi Ambulance


A lokaci guda BS ya mike ya zuba masu ido su duka ya kalli wannan , ya kalli wancen, ya kalli Hafsat dake kwonce filat da ita,

Ya shiga rudu, gashi a tsaka mai wuya........

Sai da ya fara tafia ya ce"""




*shin, za.a yarda a fita da Abdul bayan tabas gaskiyar Hafsat ne komai na iya faruwa, dan kuwa ko doctern kansa ana iya sayensa irin wannan naci na a fita da Abdul? Waye wannan bawan Allah da ya damki hannun Hafsat? Zai bada taimako ko zai cutar ne? Meye dalilinsa na yin daya cikin biyun? Me ya faru a wajen daurin auren da Abdul ya tarwatsa? Hafsat, me ke damunta? Idan wannan magani da ta fada na cutarwa ne fa? Idan aka ki yi masa kuma a je shi din ne magannin da zai bashi taimakon? Ku biyo ni mu je zuwa daga alkalamin yar mutan Niger........*



Dan Allah ki yi hakuri da rashin yawansa, ina jinyar yar muleka=??=??=??=??
>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 8??



*HELLO READERS, DAN ALLAH KAR KU DAMU DA YAWAN PAGES, DU RANAR DA NA GA DA HALI ZAN KAWO MAKU 2, AMAN A HAKANMA KUN GA AI DA YAWA>?#?*



Irin dirar da ya yi ya kare ainahin wajen da ba.a son gannin da tawul dinsa kafin ya dafe goshinsa ya leko gaba dayansa yana daura tawul din ya dubeta irin yanda ta rintse ido, bata ga ainahin abinda ba.a son a gannin ba, aman ta ga cinyoyinsa, kai harma da kusan cibinsa ta gani, ga kirjinsa dake dauke da wani gashi tsakiya har zuwa cikin tawul dinsa, wanda da gangan yake aske sauran ya bar iya nan su wani bada kala,

Kansa ya dafe da hannunsa ya fito daga bayin ya karaso inda take tsaye ya tsaya sosai daf da ita, ba abinda ya dame shi da irin yanda jikinsa ke bugawa sanadiyar wuni cir a wajen da sai shi kawai ya sani, ba wanka ba iska, gashi garjejen kato me zai hana shi bugawa? Ya dubeta da kyau ya ce" yanzu, fisabililahi, banda soyaya da dan ta.ada da kike wai harda neman gannin ogana? To me kike son ganni in ba fitina ba, Hafsat shekarunki duka duka 21 fa, kin shiga ta da biyu yau da wata hudu da kwana ashirin da biyu da awa ashirin da minti goma sha hudu da second tik tak tik tak tik tak......., yaushe kika san dadin namiji haka? A gidan yarin *KUTKALE* , ko a yawon neman fada lungu lungu? Ko dai da saurayin naki ne dan gidan abansa? Ko mijin da aka baiwa ke sadaka ya dana ne can dama a biye ba.a sani ba?

Da sauri ta dube shi, duba irinnan tsoro, da fargaba,
A hankali ta ce" kaka je neman labarina ne? Dama fitar da ka yi tawa ce?


Wata dariyar da ya jima bai yi bace ta kubuce masa, kafin ya dubeta da kyau ya ce" du na rasa aikin yi, na tashi na fita zuwa neman labarin ki? Kin manta wanda ya dauko ki daga gidan yarin gaba dayansa a tafin hannu na yake? Kin manta yanzu duniya ta zama ta yanar gizo?
Ina zaune sai da na gama hutawa, na shiga yanar gizo na bincika wacece ke, nan aka bani labarin da na kasa hadiyewa, dan haka ina zaunen nan ina shan shayi hankalina kwonce na danna kira aka bani cikaken wacece ke, duka a yan mintunan da basu cika sitin ba, wato awa! Yaya zaki yi tunanin darajar ki, ko haye min da kike zai saka har na yi irin fitar nan da na yi dan sannin ke ko wacece?

Ba ke ce yar gidan malan ba? Wace kika ci sunnan mahaifiyarsa, kin taso cike da abubuwan mamaki, kin kare a soyaya da dan ta.ada da dan gidan dad? Abinda ya fi tsaye min a rai shine dan ta.ada, ta yaya? A ina kika gan shi? Na kasa yarda da hakan, ni ba sakarai bane da za.a bani wannan labarin na hadiye, ki sani wani labarin duniyar medias, da bakunnan mutane basu isa su baka ba, kamar yanda kika ji wasu abubuwan a kaina, baki isa a duniyar bincike ki san wasun ba sai dai idan ni na fda maki, haka naki labarin rayuwar ban isa na san wasu abubuwan ba, du irin fitinata da neme neme na, du karfina da dukiyata sai idan mai labarin ta fada da bakinta, meye sirrin rayuwar ki? Me ke damun ki? Me ya kai ki gidan yari da tsauri haka? Wace ratuwa kika yi a gidan yari? Yaya aka yi daga zama budurwar dan ta.ada kika dire a gagarumar bodyguard da kasa da mutan wajen kasa ke rububi? Kin zama karamar hamshakiya daga yar caskale,
Hafsat, wacece ke?

Idannuwanta ta bude daga lumshe sun da ta yi, ta zuba masa su, sun kara wani girma, sun cika da ruwan hawaye, haka kuma bakin na ciki ya kara girma,

Sai da ta hadiyi yawu ya kai sau uku kafin ta dube shi da kyau ta kuma lumshe idannuwan nata ta bude a hankali ta ce" *ina ka je? Ka saka mu a balaki, ka bamu damar kawo maka talafi Abdul, ka taimake ni mu yi mu bar maka gidanka Abdul*
Ta karashe maganar sosai tana mai sauke ajiyar zuciya,

Gabansa ne ke ta faduwa, shi kam ya rasa wannan jarabar da me ta yi kama, du in zai kadaice ya yi koda maganar minti daya da yarinyar sai gabansa ya fadi, baya son faduwar gaba dan kuwa saka shi take jikinsa ya yi sanyi, komaima nasa ya yi sanyi,

Haka ta juya ta fice a dakin ta jingina da kofar ta sada kanta kasa, a rayuwa daga bakin lokacin da ta tsinci kanta a gidan ladaftar da shege wato *Kutkale* ta gane mecece rayuwa da mahinmancin iyayenta, daga wannan ranar idan kana son ka ga ka ruguzata ..to ka yi maganar iyayenta, ka takalo maganar su, a nan har kuka sai ta yi maka, tana son Malan da mama, tana son su sosai, tana son komawa gare su ta yi masu biyaya, tana cikin duhu, shin malan ya daura aurenta? Idan ya daura da auren wani kennan a kanta? Ita din matar aure ce ko me? Idan har matar aure ce, shi ne take irin wannan rayuwar? Ita dake neman sauki wajen Allah kuma take irin wannan sakacin? Yaya take tunanin gannin haske bayan idan har da aure a kanta tana wasa da sunnar ma.aiki?

Idannuwanta ta lumshe, hawayen da take rikewa ya yi nasarar zubo mata a kumatunta, ta bude idannuwanta a kasan zuciyarta ta ayyana Malan idan na dawo, walahi koda mahaukaci, ko wani irin mutun ne ka aura min zan zauna da shi, na yi masa biyaya, malan in sha Allah zan rike mutuncina komai rintsi, malan ka yafe min=?O?
Abdul kuwa yana tsaye yana kallonta har ta fice a dakin,
Shima wani iri ya ji , sosai ya ji ba dadi,
Shi bai yi fitar nan dan ita ba, ya yi fitar nan dan zuwa gannin yar Elhaj da ya kama ya boye a can yankin ghana cikin wata rigar fulaninsu wace ya saka yan tsaro tsareta wanda ita hakan ya yi mata dadi dan kuwa cike take da bakin cikin ubanta ya shiga dakin uwarta ya kuma shiga nata! Gashi kiri kiri ba wata magana dake hadata da uwar tata, uan uwanta maza du an yi nesa da su basa kasar, kai ko suna nan du daga wanda ya mayar da giya ruwan shan sa, sai wanda ya mayar da mata lumfashinsa, ba wanda zata tarba ta yiwa maganar ya fahimta bale har ya ji ciwo,
Tana faman kashe kanta , tana tunanin hakan a tafiarta da ta yi wanda abanta ya sakar mata kudade dan yin yanda take so ta dawo su dora daga inda suka tsaya (wa iyazubillah) , har ta shiga neman abinda zai dauke numfashinta ya shigo rayuwarta ya sace ta, bai san alfarma ya yi mata ba, bai san taimakonta ya yi ba, bai san ya cire mata masifar da ta fi damunta ba, dan kuwa har ta fara bushe bushe, wajen da ya boye ta nan akai mata magani dan ta dawo clean,
Baki dayansu jira suke, jiran ranar kin dilaci suke,

Ya gudu ya je gareta a yau ne dan yana

3 / 54