Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   22 / 54

63K to 66K   out of 159.5K words

mu yi masa mu ga ko za.a samu galaba

BS ya shiga matsowa gabansa na faduwa da irin abinda zai fadawa Abdul din, yana tsoron hakan ya jaza masa matsala, eh matsala mana , Abdul dai an fada masa uban gidansa ne, wannan kuma magana ce ake ta rayuwar Abdul dake cikin hadari=??

Yana zuwa ya zauna sosai kusa da Abdul, hannunsa ya kama ya rike inda Abdul ke binsa da kallo

BS ya sada kansa, sannan ya kuma daga kansa yana jin wani iri, wani tausayin Abdul ne ya ji na lokaci daya bayan aikinsa da yake yi, hakan ya saka ya juye harshe zuwa yaren Hausa , tsagwaronta hausa ta yan garin Damagaran,
Hausa ya yi masa ya bashi maganar du abubuwan da Hafsat ta ce,
Yanzu tambayarsa shi ne, yana gannin wannan magana mai mahinmanci ce ? Sannan ta ina za.a saka masa? Yayanene za.a yi? Shi da ya so ya je a samo rubutu da ake yi, somin ana rubutun hakan, aman kuma ga abinda Hafsat din ta ce

BS ya kirayi Hafsat da sunnan da ta zo da shi na aiki ne, dan bai san cewa Abdul ya san sunnanta harma yake kiran sunnan gatsal ba,
Shi dai da ido yake bin Abdul a lokacin da ya nuna masa ruwan zamzam dake cikin gora gangariyarsa da kuma dabino dake cikin gidansa direct daga saudiya

Baya iya magana, ba zai iya rubutawa ba, dan haka da hannunsa ya yi nuni aka karbo kwanon aikin dake hannun Nurse din dake tsaye da likitan sunna kallon abinda zasu yi, ba damar su dakatar da su, ko au hana su, du kuwa irin yanda aka san likitoci da hana magannin hausa, sai dai takarda BS ta saka ba zasu shiga hurumin nan ba, ba zasu hana ba, dan sunna iya hanawar idan wani abu ya faru sunnansu ya shiga ciki dole dole.

Da hannunsa, ya iya da kyar motsawa ya yiwa Abdul kwatancen cewa ya zuba ruwan sannan ya saka dabino a ciki,

Haka ya yi , sai da ya dan jima kadan Abdul ya yi nuni da a zuba masa a hancin

Jim BS ya yi yana duban Abdul, kowa ya sani, irin yanda ruwa a hanci ke gigida mutun, gashi wannan harda wani abu a ciki kuma da dan yawansa
Gannin Abdul na kara galabaita ya saka BS zuwa ya talafi kansa, bai taba jin wani irin tsoron Allah da son ambatonsa irin na wannan lokacin ba, sai kace bai taba gannin mutuwa ko gawa ba, yannayin da Abdul ke kokowa da numfashinsa ya tsoratar da shi, gadhi dai Abdul ya riki sallah, dan baya wasa da sallah, yana nafila, wace sun sha gani da idannuwansu dan idan suka ji motsi dole su leka, du irin danyen kansa ya kiyaye wadinnan, ga bautar Allah daga boye, baya sadaka ya shaidawa duniya zai yi, bai taba bayar da kyauta ya yarda wani ya san shi ne, yana iya yinsa dan gannin ya kare abubuwa da yawa, yana irin wannan jijiga tamkar mai fitan rai, to ina da shi idan ya fadi rashin lafia? Allah fa zai ce ya kiraya shi marar kunya, Allah zai nema shi mai mantap alkhairi, sai daga baya zai nemi Allah ko me? (Ka tashi bawa, ka tuba, domin kuwa baka san zaka kai goben ba? )

Hannunsa na bari, zufa ta wanke masa fuska haka ya samu ya dildilawa Abdul ruwan zamzam din bayan ya yi bismillah

A hannunsa Abdul ya dage idannuwansa, bakin ya bace sai farin ya sake zuwa duniyar summa ko mutuwace? Wace ta tsoratar da shi har ya ajiye kan Abdul ya diro ya dora hannyensa saman kai ya shiga kai kawo cikin tashin hankali.............





..........comment comment commemt



>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 9??




A haukace Abdul ya dawo gaban Hafsat, gaba daya ya kai gwuiwiyinsa kasa ya zubasu
Bai san lokacin da ya saka hannayensa ya damki hannayenta ba kafin ya ce" kin ganshi? Hafsat ke kin yarda cewar yana raye? Hafsat, kin yarda da maganana kennan? Ke bakya ja da hakan ne?

Hafsat dake kallonsa wani tausayinsa ne ta ji a ranta,
A hankali ta zame hannayenta ta ce" Abdul, me kake nufi? Wa ke raye? Abdul, hatsarin jirgin sama fa, kuma dubai sun shaida ya shiga, Abdul dan me ba zaka daina maganar cewa yana raye ba?

Hannunta na dama ya yarfe yana kallon yanda idannuwanta suka cicika da hawaye ya ce" a lokacin da muke magana irin ta fahimta da shi ya taba ce min" Abdallah, du ranar da halin rayuwa zai sakani canza sunna, ba sunna na zan canza ba , sai dai na jirga sunana,


Juyowa ya yi ya dubeta ya ce" *MUHAMMAD BINE ABDUL BASID ABDALLAH*
Hafsat, sunnan kakana ne Muhammad,
Abdallah sunana ne,
Hafsat,

Mikewa Hafsat ta yi da sauri ta juya ta bar wajen,
Abdulma bin bayanta ya yi yana kugin kiran sunnanta aman har ta shige ciki, hakan ya saka shi shigewa cikin dakin nata kai tsaye

Tsugune ya ganta ta hada kanta da gwuiwarta tana rizgar kuka,

Wajenta ya karasa ya tsuguna infa take tsugunen ya rike damatsunnan hannayenta ya ce" kuka kuma? Kukan me kike? Me ya taba zuciyarki? Hafsat, maimakun ki tsaya ki bani haske a kan gannin macuci kuma azalumin mutumen da yake neman rayuwana shine sai ki gudu ki shiga kuka ? Ni ya dace na zubar da hawaye Hafsat, da zan samu kuka, walahi da na rusa, da zan samu kuka, ni kam da na rera, ki dube ni, waye ni? Banza ne dan fasiki Hafsat!

Abdelah,
Hafsat ta fada da wata irin murya mai fitar da numfashi hadi da kuka,
Hannunsa ta saka hannunta ta riko ta ce" Abdellah,
*zato zunubi ne,....koda ya kasance gaskiya ne*

*Abdul, jinni, mahaifinka Ya haifeka, ya maka sunna, ya tarbiyantar da kai, ya baka ci sha sutura muhali, ya baka sunnansa kake anfani da shi, ya daure maka, ya tare maka, ya tsare maka, Wani irin rudin duniya , ko zigar shaidan ne zai saka shi neman rayuwarka?*

Abdul ya kankance idannuwansa yana dubanta ya ce" ashe baki da hankali? Ashe duban mai nazari ne nake maki ke baki kai can ba? Baki san a duniya babu halitar dake tafe da hadari mai tare da guba irin dan adam ba? Wai dan Adam din zaki yiwa shaida? Shi kuwa keda abubuwan da zai kashe ni, kin manta wace irin rayuwa ya yi gaban iyayensa? Rana tsaka ya mayar da dukiyarsa a sunana komai da komai, *KUDI HAFSAT?* ai masifa ne, kudi dauda ne, kan su yana iya halaka ni,
Baya cutar da gudan jinninsa ya ringa kwonciya da yar da ya haifa?

Da sauri Hafsat ta saka hannunta wajen bakinsa ta rufe tana girgiza masa,
Hannunsa ya saka ya cire nata ya watsa mata idannuwansa da sukai jajajir ya ce" ko a lahira kar Allah ya tsaida ni gabansa, dan ba zan maki rantsuwa ba, aman idan ana iya cakumar mutun sai na shaki kwalarsa!


Abdul Mahaifinka ne fa!

Sai me Hafsat? Na ce sai me? Ubana ne, kuma na tsane shi, idan bai mutu ba, ya shiga uku, dan yanda yake bibiyata sai na bibiye shi!, ko a cikin kaya sai na shiga na mamana masa ita a jikinsa, Hafsat sai na hana shi zaman lafia har mu hadiye zuciya mu mutu mu duka!

Hafsat kam gaba daya abin ya girmami tunaninta, tsana, muguwar tsana Abdul ke yiwa mahaifinsa, wanda take tunanin har ta kwadaitawa kanta idan har za.a samu sasauci ko itama iyayenta zasu dubeta?

A hankali bata saki hannun nasa ba ta ce" Abdul, zuciya mugun nama ce mai saka dan adam ya yi ta tafia har sai ta kai shi ga halaka,
Gagawar yanke hukunci baya haifar da komai sai dana sani,
Tafia cikin zargi, halaka me Abdul,
*Ya Abdul Jabar* baka son kaima ka haihu yayanka su yi maka biyaya?
Shi Abdellah, idan har ka samu yaron da ya yi maka irin haka yaya zaka ji? Komai girman laifin mahaifinka baka isa ka hukuntashi ba Abdul, kai zaka ji dadin zaman duniya idan kana hamaya da d'an cikin ka?

Abdul ya lumshe idannuwansa yana kallon yanda yarinyar da bai hada komai da ita ke son kwontar masa da hankali ta hanyar nasiha,
Mahaifiyarsa ce ta fado masa a ransa,
Ummih bata taba daga muryarta dan yi masa nasiha ba, takan bi shi ta laluma da dabara, ko dan shi kadai ta malaka?

A hankali ya zauna, ya mike kafarsa daya ta je har kusa da gwuiwar Hafsat, ya dage dayar ya lankwasheta ya dora hannunsa na dama a samanta,
Sai da ya ja numfashi, sannan ya sasauta murya ya ce" wace irin rayuwa ce kike hasaso min mai cike da ni.ima haka bayan na mayar da ita mafarki?

Da yatsitsansa ya nuna ya ce" Hafsat, mace , mace mace, sai da na auri biyar a kananun shekaruna aure irin na gata na fadawa duniya, aure irin na garari aman ba wace na yi kwonciyar aure da ita, sai da na birne uku da hannuna biyun suka gudu suka shige duniya,
Ya lumshe idannuwansa ya bude ya ce" Hafsat, mahaifiyata na kokarin hana alburushi taba fatar jikina ya ratsa gaban goshinta ya kaita lahira, firgicin hakan ya saka har aka yi mata sutura ba da ni ba, aka ajiyeta a makwoncinta ba da ni ba, aka rufa mata kasa ba da ni ba,

Hafsat, na bi matan banza, yarinya , baba, harda tsohuwa, in dai zata iya kama jikina ta sakani samun saukin tashin hankalin dake damuna wanda idan ya motsa yanda kika san mahaukaci bana ji bana gani har sai na aikata iskanci nake samun nutsuwa Hafsat,

Shiru ya yi yana kallon yanda take kallonsa kafin ya lumshe idannuwansa ,
Wani hawaye ne ya fito ta gurbin idonsa dan gajere dan kuwa bai idasa sauka daga fuskarsa ba ya tsaya yana dubanta da manyan idannuwansa ya ce" na zama dodo mai shanye jinnin matansa a cikin gari, na zama fasiki mai bin matan banza a idannun kowa, nine atajirin da ya daukowa kansa harka da yan shan jinni har aka kashe min uwa a cikin gari,
Hafsat, a yaya kike son na haihun? Ke idan na yarda na yiwa mace ciki ta haihun mun na yiwa yaro ko yarinyar da zata sama min adalci kennan? A ina nake son su rayu bayan abinda ke faruwa a kasata du inda na saka kafa ya yadu dan ni din cele ne?
So kike na rayu cikin kuncin da yayan cikina su girma duniya ta wulakansu, idan sun gaji kudin ubansu a so su dominsa, idan kuwa basu gada ba su zama yan ta.ada? Hafsat, a haka kike so na haifi y'a mace na haifawa karti? Hafsat na bi yayan wasu, mai yiwuwa harda matan aure, duniya ta lalace inda matan aure ke neman mazaje dan abin duniya, ban taba kwonciya da mace ba aman du daya ne Hafsat,
Ya zan kali idon matar da na aura a lokacin da muka zama daya ta hanyar hayayafa yayan suka ringa tona abinda na birne?

Ban zo duniya dan na ji dadinta ba Hafsat, a hakan kike min hangen rayuwa mai dadi bayan na yi imanin ko yarinyar da aka aura min da tantirin dan iska ne marar sisi daga ita har iyayenta ba zasu dube ni ba bale har su aminta da ta zauna da ni? A halayana , babu macen da zata so ni bani da sisi,

Hafsat ta lumshe idannuwanta ta mike tsaye a hankali ta juyo inda yake sosai ta rage tsayinta ta ce" kar bawa ya fida rai da rahamar ubangijinsa,
*Idan kana numfashi, kana da sauran dama*

Abdul, ka yawaita istghfari, ka kara kadaice kanka da Allah,
Ka sani ko hana haihuwar da kake yiwa kanka idan Allah ya yi sai ka haihun wani sabon ne,
Ka ringa kalamai irin na musulmai Abdel,

Idannuwansa ya zaro sosai ya ce" ke, kina nufin ni arne ne? Oh kalamainama na arnawa ne? Ni ni Hafsat ko?

Hafsat ta hade bakinta ta yatsine ta dan ja baya dan a yada ya ruruko mata idon kamar ya dauketa da su,

Goshinta ta dafe ta ce" malan ya muna magana a nitse zaka rikita? Wai me damunka haka ne? Ba zaka canza maganar ba fa, magana nake maka kan ka nutsu sai ka wani ce kaine ma?

Abdul ya koma ya jingina yana girgiza kai irin ta yi halin , sannan ya ce" ba zan nutsun ba,

Kai walahi sai ka nutsu!
Hafsat ta fada tana galawa bayansa harara ta shiga kokarin bara masa dakin

Muryarsa ya dan daga kadan ya ce" an ki a nutsun Hafsat, nace an ki a nutsun, zan tata yin abubuwan arnawan ki yanka ni! Kuma ki dawo dakin ki ne ni na bara maki, kai na shiga uku yarinyar nan idan na tashi aurar da ke ban san ya zan ba

Da mamaki ta tsaya ta juyo tana dubansa, ya kuwa yi mata tsuru yana kallonta, kamar ba shi ba , yanzu ya yi kalar serius , yanzu ya shiga abubuwa,

Dawowa ta yi tana kallonsa ya mike, cike take da mamakin wai idan ya tashi aurar da ita,
Kasa rikewa ta yi sai da ta ce" bayan ga malan, ga yayuna, ga komai kamar wata wace aka kora sai na zo ka yi min aure, Kai da ba dan uwanmu bama!
Ta karashe tana kebe bakinta gefe tamkar sangartatun yaren nan

Cike da nishadi yake kallon yanda take jajen zai mata aure, dama ya fadi haka ne dan ta bar maganar abinda yake gannin ba mai yiwuwa bane, shi baima san me yasa yake iya zama ya fayacewa yarinyar nan karama abinda yake ji a ransa na game da damuwarsa kai harma da wasu sirikansa, yanzu dai ba wanda ya taba fadawa cewar yana anfani da maganin da zai hanawa mace daukan ciki idan ya yi mu.amala da uta, sai gashi ya saki baki ya zayane mata komai bayan ita batama taba yin auren ba,
Wani sashi na zuciyarsa ne ya ce da shi, ai dan bata fiya hayaniya ba, bata da maganar da zata yada maka sirinka, dan ko na farko ka fada mata dan ka gwadata ne, aman baka tsinci alamun wani ya sani ba, Abdul, ko dai ka rasa abokin yiwa jaje ne?

Murmushi ya yi ya juya da sigar tsokana ya ce" koda yake da Bashari ne zan maki auren ai, shi kuwa zan fada masa idan kikai fushi ya rarasar min ke, dan kuwa Hafsana , ni kawai keda ikon muzguna maki!

Ficewa ya yi a dakin yana mai neman layin yaron da zai tuka shi a tsakiyar daren nan zai je jejin nan, ya tabata Hafsat ta ga wani abin da ya sakata yin gim da bakinta ta shiga yi masa wa.azi, xai tafka masu tsiyar ne a yanzu da ya san su BS sun shiga sallah ita kuwa ya barota a dakinta kafin ta ankara ta biyo bayansa ya daga, dan baya jin hasana, ta gabanta ya yi shigar basaja ya fice bata gane shi ba dan kawai ya saka kayan daya daga cikin sojojin muhammad, zai je wajen nan, ya tarar da mai anfani da sunnan nan, koda fatalwa ne ya kara kashe shi kowama ya huta!

Nan ya bar Hafsat tsaye baki bude, magangannunsa na wahalar da ita, abubuwan da suka tatauna na mata yawo a kwonya, sannan zolayarsa ta yau ta tsaye mata a rai shi koda yaushe yana tafe da sabon salo ne? Ya kuwa iya zolaya,

Murmushi ta saki, wanda bata shirya ba ta ce" Abdel zan so ka gyara idan har mahaifinka na raye ka gane ba kai ya dace ka hukunta shi ba, laifinsa da ya yiwa ubangijinsa ba ruwanka, fatana , baban fatana shi ne ace ba hannunsa a kisan kanwarka da kuma mahaifiyarka=?O?
Hafsat hafsat farka fa=?"?





Sisters, comment comment, comment plz=?
?=?O?

>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




22 / 54