Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   49 / 54

144K to 147K   out of 159.5K words

ya goge gefen hannunsa da ya yi masa mugun yago wanda ya saka jini fitowa
Tsaki ya ja yana kallon yanda ya yaga masa rigar jikinsa ya tabe baki a fili ya ce" mai fada irin na mata

Tada motar ya yi ya nufi cikin gari dan bashi da jiyar komawa gidan nasa a irin wannan lokacin

Hafsar kam ta wuni cikin zulumi da tunani, daga baya ta baiwa kanta hakuri ta nemi bed ta mike dan wani irin baci ke damun idannuwanta

A kwana biyun nan da Na.ima ta yi kwata kwata bata samu fuskar Abdul ba,
Idan ba lokacin cin abinci ne ya yi bama sam bata ganninsa, ko wajen cin abincin sai ta yi dagowa goma sam bata tsintar idannuwansa a kanta kamar yanda ya saba binta da kallon nan mai sakata jin wani irin shauki

Ba wani cin abincin take ba, dan gata gabanta hasalima ita bata sha.awar cinsa har a gama, sam baya ce mata ta ci ko ya dameta da murmushi, baya taba jikinta ko ya rakota ya rungumeta a jikinsa, ita kam ta rasa gane kanta, ba zata boye ba tana missing din hakan
Tana jinsa da matarsa suna magana a hankali, harma ta ji tana dariya

Ba wani abu tsakaninta da kishiyarta, basa fada sam, basa yade yaden magana, aman kuma basa shiga harkar juna,
Idan sun zauna cin abinci zasu gaishe da juna a gaisuwa mai gajarta,
Ba wani dake shiga harkar wani, idan daya na magana da miji ba mai tankawa, ba ruwansu da junansu, basuma shiga sabgar juna ba bale idan wata ba lafia su yiwa juna ya jiki, ko idan abin dadi ya samu a yi maka murna ko na jaje a yi maka jaje.....wani kishi suke na shiru wanda kowace a zuciyarta kadai ta san irin abinda take ji kan yar uwarta

Suna ciki da cin abinci a yau da ta kama aikin Hafsat, Hafsat da ta fi kusa da Abdul, tun da ta shigo yau din ma da wani zumbulelen hijab har kasa a jikinta, ra samu waje ta zauna

Bayan gaisuwar nan ba abinta ya hada ta da su duka mai tsayi ko mai zurfi,
A lokacin ta lura da ciwon dake hannunsa wanda ya yi kama da an yayage shi sosai din nan dan kuwa sosai wajen yana da girma

A ranta ta afka duniyar tunanin me ya same shi? Me ke damunsa? A ina ya ji ciwo haka?

Sai da ya gama cin abincin ya kale su baki daya,
A hankali ya ce" Hafsat?

Dago da kanta ta yi da sauri ta sauke idannuwanta a cikin nasa, wanda ta ga ya yi saurin kawar da duban tsakiyar idon da ya yi mata na yan sakwani
A hankali ya ce" tafiar, yau ne da yama...zan yi kwana biyu ne, Na.ima tafia ta taso min dazu da safe

HAfsat ta tsura masa ido sosai, sam ba gaskiya a kan lebensa hakama furucinsa
Lokaci daya ta ji ta muzanta, du irin sanyin ac din dakin sai ta ji ta fara hada gumi, gaba daya lamarin yana sukar nutsuwarta

A hankali ta yi murmushi tana kallonsa, murmushi irib mai fitar da sauti sannan ta ce" eh, ai ka ce daga mun gama cin abinci zaku tafi jiya da ka yi kirana da dadare, shi ya sa nake son mu yi salama na koma kaina ke dan min ciwo me amor

Daga shi, Har Na.ima kallo suka bita da shi, shi yana kallon mamakin gila masa karyar wai ya yi kiranta jiya da irin yanda ta nuna halin ko.in kular da ta nuna na zai yi tafia a irin wannan lokacin da yake ranar aikinta, kennan ita ko a kwalar rigarta ko? Yana so ta gane kurenta na kiea masa sunnan wani kato ua horata sai dai yana gannin kamar ya yi hakan da wuri dan sam ba soyayarsa a zuciyarta bale har hakan ya hanata sukuni

Ita kuwa tana dubanta da mamakin yaya aka yi tun jiya ya sanar da ita yana da tafia bayan ba aikinta bane, wani faduwar gaba ne ta ji ta ziyarceta da tsoro, tashin hankali wanda ba.a saka masa rana ......kar dai a je wannan ita ce wace ta sacewa mijinta zuciya?????





*Na san ni mai laifi ce, dan Allah ku min uzuri...idan fa wa.inda suka saba min novel dina sun san bana wasa da typing ko jan ra????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  i, idan haka ta kasance a yanzu ina mai fatan a yi min uzuri......lafia uwar jiki=?
? na gode*


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




6?? 4??


A hankali ta katasa maganarta tana dubansa kasa kasa irin duban nan na kasan ido, kafin ta mike cikin nutsuwa ta zagaya kusa da shi
Rankwafawa ta yi a hankali inda kamshin turarenta ya shiga hancinsa, kanshi mai saka nutsuwar zuciya
Ita kanta nata idannuwan ta lumshe jin nasa kamshin ya jara cika mata zuciya

A hankali ra mana masa kiss a kuncinsa, ta rage murya sosai da sosai ta ce" Allah ya tsare

Tana gamawa ta mike ta tafi , har ta fice a falon nasa da kallo suke binta su duka kafin a hankali ya mayar da dubansa wajen Na.ima
Gaba daya fuskarta ta canza yannayi, yannayi na bacin rai da tashin hankali da wani kallo irin na ka ci amanata!

Mikewa ya yi da tissu a hannunsa ya fice a wajen ba tare da ya furta kalma daya ba

Yana shiga dakinsa ya je ya shiga canza kayan jikinsa,
Ya zo daidai bala mabalin ya rintse idannuwansa da sauri dan kuwa zafin kiss dinta da karansa ne ya daki kunnayensa lokaci daya kuma ya buda idannuwan nasa ,
Sun kade tamkar ba nasa ba, yana jin lamarinta da dukan karfin jikinsa da tunaninsa, yana jin du wani abinda ya shafeta a gangar jikinsa,
Bai san yaya aka yi ya yi sake har haka ta same shi ba, yana kallon ina? Dan me ya yarda har irin wannan abin ke kokarin cin karfinsa? Ya sani ita ce ra farkon da ta yi masa musu, ta farko da ta yi masa tsayaya, ta farko da ta yi masa fada, ta farko da ta fashe da kuka dan abinda ya shafe shi shi ba wani ba, ta farko da ta tsaya kai da fata take nuna masa hanya, mahaifinta ne na farko da ya dube shi ba tare da ya san shi ba, na farko dake dubansa da tarin dukiyar tasa da takamarsa ba ruwansa ya saka shi a hanya mai bilewa ha wani dar ko tsoron kar ya kubuce masa tunma kafin ya zama sirikinsa,
Tabas ta taka mahinmiyar a rayuwarsa, ta girgiza tunaninsa, aman kuma shi kansa ya yi mugun saken da ta cin masa a lokacin da vai shirya ba,
Wai shi maman malan zata nuna bai isa ba? Ba zata nuna ta damu da shi ba? Kennan ba zai taba samun matsayi a zuciyarta ba du kuwa da irin yanda yake kokarin yi mata biyaya a bukatunta?
Shi ke binta ba ita ke binsa ba, ashe haka ne idan kai ke son mutun dole kai zaka ringa binsa du abinda ya yi niya? Ba laifi ta je din!

Ya karashe yana mai daukan wayarsa da makulin motarsa

Fitowa ya yi ya fice a dakin ba tare da ya rufe ba ya yi gaba abinsa

A motarsa ya shiga ya kama hanyar tuki, bai dauko komai ba sai katinsa ta banki sai takardunsa na zuba mai a stations
A irin lokacin nan ya shiga tukinsa ya dauki hanya mai tsayi dan niyarsa zai yada zango a garin maradi, garin da yake son buda reshe na kampaninsa mai tatar mai

Ya wuni cir yana tuki da kansa dan kwata kwata baya jin dadin yannayin da yake ciki, yakan yi murmushi ya girgiza kansa, dan bai taba tunanin zai kamu irin wannan kamuwar haka ba, sai dai ya tabata ba wani abinda zai bashi wahalar da ta fi wada ya sha na tsayin rayuwarsa , ya ga rayuwar da baya tunanin da mace ta ki shi zai mutu, tunda har yanzu zuciyarsa ke harbawa yanda ya kamata baya tunanin soyayar mace zai tsayar da ita sai dai idan lokacinsa ne ya yi

Yana zuwa hotel ya sauka,
Wanka ya yi ya dauro alwallah ya gabatar da sallar shafa.i da wuturi sannan ya zauna bakin bed din dakin

Hannayensa ya saka saman kansa yana dan yin gaba da baya da hannun nasa

Mikewa ya kuma yi ya dauki jakar goyon fa ya zo da ita ya zuge zip din jiki

Takardu ya shiga fitarwa sannan ya ciro laptop wani dan karami ya bude ya kunna shi

Da wifi din hotel din ya shiga internet,
Sai da ya gama aikin da zai yi sannan ya shiga tarin messages din da ake turo masa wa.inda ba kowa bane sai mahaifinsa

Du messages din magangannu ne na rayuwar yau da kulun, baki daya nasiha ne na zamantakewar rayuwa,

Ajiyar zuciya ya sauke bai kashe laptop din ba ya samu waje ya kwonta ya lumshe idannuwansa

Wani irin yarr ya ji tun daga cikin kwakwaluwarsa har zuwa dan yatsansa sakamakon tuno irin zazafan kisss din da ta mana masa a lokacin da ta mike dan ficewa a dakin
Da sauri ya kama fillon dake gefensa ya rungume shi sosai a jikinsa , a hankali ya fara tunanin yanzu da yana gida, da tabas a irin wannan lokacin tana cikin dakinsa,
Koda kuwa bai yi yinkurin zuwa duniya mai nisa da ita ba da ya tabata harshenta na cikin bakinsa yana baiwa lokacin mahinmanci ta hanyar side du waji loga na jikinta

Idannuwansa ya buda da suke kara yi masa nauyi, lokaci daya ya mike ya zauna yana kallon wayarsa dake ajiye gefe

Hannunsa ya mika ya dauko yana kallon messafe din da ya samu du daga Na.ima ne, message ne da suka kunshi kalaman yabo, adu.a, fatan alkhairi sai zafafan kalaman soyaya a ciki

Idannuwansa ya lumshe ya jinginar da jikinsa jikin bed din
Sai a wannan lokacin ya fara dan bambance tsakanin rayuwar da ya gani da irin karfin rugurguzar soyaya
Baya so ta so shi dan tana tausaya masa ko dan dole,
Baya so ta yi masa son jeka na yika
Da ace zata iya gane menene farin cikinsa ta bashi? Da kau ya huta

A hankali ya buda idannuwan nasa ya shiga wajen message

Bai taba bata rspons a kan irin kalamanta ba
Tabas ya yarda da yau ta cancanci amsa

Cikin nutsuwa ya rubuta amsa kamar haka" *ki huta lafia matar Abdul, i miss u*

Tura message din ya yi sannan ya kuma lumshe idannuwansa

Ji yake zuciyarsa na yi masa wani irin mugun nauyi
Why? Why? Hafsat me na rasa? Me na rasa na namiji?

Wata zuciyar ta ce da shi....ko bata gane yarenka na abinda ke damun zuciyarka da ita ba?

Idannuwansa ya lumshe ya kuma budewa....eh lale ban furta mata ba
Ya baiwa kansa amsa a fili
Sai kuma ya kuma cewa....aman ban taba furtawa kowa ba hasalima yannayina ya cancanci nuna mata me nake ciki

Wara idannuwansa ya yi sosai yana jin ba zai iya rintsawa ba, me take ciki? Yaya jikinta? Ko ta daina jin tsamkin dake damunta?

Wasa wasa sai da ya mike dan daukan laptop dinsa sai ya ga har kusan karfe biyun dare

Daukowa ya yi ya zauna yana jin kirjinsa na yi masa zafi,

Buda wajen message din da ya yi masa ya yi ya kuma karantawa a tsanake

Kansa ya girgiza kafin ya rubuta message kamar haka" *na yi nesa da ita ko zan samu sauki halin da nake ciki a kanta, sai dai na kasa samun hakan sai ma cushewar tunani da nata da ya same ni, shin akoy ayar da zata ciren abinda nake ji ne na lazumta??*

Turawa ya yi kafin ya rufe laptop din baki daya ya koma ya kwonta ya ci gaba da yabon nata


Bangaren Hafsatma wuni ta yi tana al.amuranta kamar yanda ta saba, kama daga girkinta, gyaran bangarenta dan zagaya tsakar falonta dan jikinta ya sake domin sam bata wani jin dadin jikinta sosai

Sai da ta gama cin kayan kwadayinta son ranta ta je ta yi wanka hankali kwonce ta fito ta kwonta domin a hali na rashin sallah take

A lokacin da ta rufe idannuwanta kamar an hasko mata hotonsa sai kuwa ta yi saurin budewa
Lokaci daya abinda ke damunta ya shiga bijiro mata,
Abinka da mace sai kawai Hafsat ta janyo hijabinta da kyau ta rufe kanta ta fashe da kuka

Kuka take hankali kwonce tana rerawa,
Gani take zuciyarta batai mata adalci ba, shin auren cushe ya taba yin daraja ne? Lale da da ake ce mata so bai san ciwon kansa ba, mugun dan shishigi ne da saka bawa a uku bata yarda sai yanzu da ya mike ya shiri shiri ya lulukata a kasa sannan ya bita a guje ya dane kanta

Dan me yake wulakanta ni? Dan me yake da son kansa da yawa?
Take tambayar kanta da kanta,
Tafia? Bai tashi tafiar ba sai da ranar girkina ta zagayo bayan ya kwana biyu cirrr yana min fushin da ban san laifin da na aikata ba? Abdul, ni ko? Ni?
Tamkar wata sabon kamu ta girgiza kanta ta ce" a kanka malan ya taba daga hannunsa a kaina, kai kake min laifin dan ka tsane ni kuma ka fi ni zuciya? Da wace kake so din ce ai da baka yi mata laifi ba!

Kukanta ta ci na arziki kafin ta shiga shashaka a hankali tana rage karfin kukan

Sai kuma ta kankame jikinta a hankali ta ce" me ya ji maka ciwo Abdellah? Hannunka da ciwo wa ya taba min kai?????




>?z?>?z?>?z?>?z?>?z?=??=??=?? i.m back=??>?#?>?#?>?#?>?#?>?#?


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




6?? 5??



Wasa wasa haka ta yi ta juyi, sai barci barawo ne ya yi awon gaba da ita a irin wannan halin,

A washe gari Abdul na daukan wayarsa ya duba call din da ya yi missing

Bai bi ta kai ba dan da wuya su samu abinda suke so, domin aiki ne ake nemansa ya gabatar a kasar maroco, binciken sirri na wani ahli da daga an haifi jariri a gidan sai a wayi gari a nemesa sama ko kasa, gasu da samari sai aute suke suna hayayafa mace daga wata ta barsuma wata zama take ko dan dukiyarsu,
Shi ne baban dan gidan ya nemi da a bashi kwararen malamin sirri, dan sam bai yarda da cikin gidansu ba, hakan ya saka kasar da ta hore shi nemansa dan ta tura shi gidan a matsayin dan aikin giran har ya gabatar da bincikensa

Laptop dinsa ya kuma kunnawa,
Message din amail dake nuno masa ya danna

Ba wani hayaniya akai masa ba sai amsa da aka bashi kamar haka *da zata dawo min, ko cikin ramin ginnin rijiya take sai na je na zauna da ita*

Ajiyar zuciya kawai ya sauke dan ya fahimci wada mahaifinsa ke nufi, wato matarsa mahaifiyarsa

Rufe komai ya yi ya fice ya tafi cikin gari dan karasa abubuwan da suka kawo shi garin

Sosai ya wuni yana zirga zirga da kansa, sai da ya tabata ya ga wajen da ya dace da shi sannan ya karbi number mai wajen ya fice hotel din
A lokacin tuni wani daren ya kara zagayowa dan haka sai kawai ya nemi waje ya yi ibadarsa sannan ya nemi kwonciya

Ko yau hakan take a bangarensa, domin ya kasance mai tunani a kanta, daren ya yi masa tsayi ga gajiya, ya matukar wahala wanda tun karfe shida bayan ya gama sallar asuba da adu.o.insa ya dauki hanyar garin shugaban kasa , a cen take, ya yarda koda yanai mata fushi to fa yiwa kansa adalci shine zama a inda take, idan har ya yarda ya yi nesa da ita to fa ya tabata wannan shafa ruwa ne a alwallar dake gabansa dan haka ya baiwa kansa baki ya shiga murza sitiyarin motarsa ya dauku tafiar mai tsayi


Zaune take da yarinyar da auntynta ta turo mata dan ta yi mata kunshin

49 / 54