Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   28 / 54

81K to 84K   out of 159.5K words

jikinsa ya danna kira,

Ana dagawa ya canza harshe ya shiga magana cikin yannayin zafi zafi , yana yaran larabawa wanda Hafsat da Malan suna fahimtar duka kaf abinda yake fada

Cikin yannayin tsoronsa ta kafe shi da dara daran idannuwanta, dan kuwa ya fito sak a baban mutun ma.aikaci mai zaman kansa mai iko da kansa wanda ya san hakokinsa da wa.inda ba.a isa a take masa ba

Maganar da ya karasa da uta shi ne" *in dai ba za.a sake shi a saki amininsa a fili a basu damar kashe kansu ba, to fa ba.a isa a tura shi saudiya ba, a barshi a Minna su yanke masa hukunci....a kai shi Niger a saka shi a cikin gidan kason KUTKALE*

Yana gama fada ya ajiye wayar ya daga manyan damatsunansa ya cusa hannayen nasa a cikin gashin kansa

Ya jima a haka ba wanda ya ce komai a cikinsu har ya yi niya da kansa kuma ya juyo a hankali

Yana juyowa ya kurawa Hafsat dake kusa da BS ido,
A hankali ya kai dubansa wajen BS din, da kuma Hasana....
Haka kawai ya tsinci zuciyarsa na cewa" ba abinda basu gani ba

Rigar asibitin ya shiga cirewa hakan ya saka Hafsat saurin sada kanta daga dubansa da take, ba ita daya ba du wanda ke wajenma sai ya kawar da dubansa a kansa , wasu na mamakin shi bashi da kunyar cire kaya ne? Wa.inda suka san ko shi waye kuwa basu wani yi mamaki ba

Wando da riga ya saka bakake lut, sannan ya saka gilas a fuskar tasa ya juyo wajen Malan dake tsaye,

Zuwa ya yi sosai kusa da shi sannan ya duka har kasa, a hankali ya ce" na gode da mutuntani, da adu.o.i da nasihohi, in sha Allah zaka juya da Hafsat a yau yau.....zan zo nima domin zaman kasar nan ya fice min a rai

Malan kam kansa kawai yake gyadawa yana kallonsa, haka ya mike ya fice inda suka mara masa baya gaba dayansu

Suna fita daga asibitin ya mikawa BS waya,

BS na gama sauraron maganar ya kalli Hafsat da sauri, sannan ya kali Abdul,

Ganni ya yi Abdul din ba wani alamar fara.a a tare da shi, dan haka ya mika masa wayar ya je kusa da Hafsat ya yi mata bayanin abinda aka ce

Ji ta yi kamar tsokanarta yake, dan haka da wani irin gudu ta karasa inda Abdul yake tsaye,

Haki ne ya hanata magana sai nuni da take masa,

Abdul ya lumshe idannuwansa yana mai jin nauyinta har cikin ransa ya ce" ki je

Hawayen idannuwanta ne suka bale, cikin yannayin kuka ta ce" kana nufin..shikenan? Kana nufin na zama mai cikeken yanci? A yanzu ta waya ka saka aka sake ni daga kason da na shiga? Kana nufin zan ga mahaifiyata

Dariyar da take ua saka shi tsurawa fuskarta ido,

Hannunsa ya dago a hankali, hakan ya saka hannun nasa dake bari bari ya dora yar yatsarsa a gurbin kumcinta da ya lotsa sosai , sannan ya kama dan mayafin nata da ya fadi a kafadunta ya dora saman gashin kanta sosai ya rufe,
Idannuwansa ne ya sauke saman kirjinta, lokaci daya gabansa ya buga da mugun karfi, lokaci daya kuma ya rintse idannuwansa a hankali ya ce" *zan waiwaye ki*

Suna tsaye suna kallo ya shige wata mahaukaciyar bakar mota ya tayar ya harba bakin titi inda su hasana suka mara masa baya

Gaba daya jikinta ne ya mace mata, bata son tafia ta barshi du irin zumudin gannin wannan ranar,
Gata dai ga mahaifinta, sannan an tabatar mata da ta bi mahaifinta ta je gida ta huta ba tare da an tsara mata tsarin rayuwarta ba,
Sai dai kash, yau ta tabata sabo tirken wawa ne, ita kuwa ta yaya zata iya sabawa da rashinsa bayan ya saba mata da shi a ko wani motsi nata?

Dubanta ta kai wajen BD dake tsaye yana yi mata murmushi, sai a lokacin ta waiwaya sai ta ga mahaifinta baya nan,

Da sauri ta ce" ina Abih?

BS ya saki murmushi yana kallonta ya ce" sun tafi da Abdul, daga can za.a kai shi aeroport n??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????e, akoy abinda zasu yi, mu je a can zamu hadu

Ajiyar zuciya ta sauke ta daga kafarta ta shiga motar da ya nuna mata ya tayar suka kama hanya

Ko a hanya hira ne BS ya cikata da shi, wanda dadaya take tsinta sai dai ta yi masa murmushi

Cikin nutsuwa ya ce" kin taka sa.a, babar sa.ar rayuwa, wace ba kowa ke samun irinta ba,
A yau na ga abubuwa da yawa, na ga ribar zuciya daya da girman adu.a, tabas a baya na yi sake da na ringa wasa da Sallah, ashe dai wanda ya rike Allah ba zai ji kunya ko ya wualakanta ba?

Hafsat ta sakar masa murmushi tana mai kallon gari, itafa walahi har wata iska mai sanyi ce take ji tana ratsa gabanta.....

Muryar BS ce ta tsinke tunaninta a lokacin da ya ce" *me zai hana ki cika min nawa burin nima? 1ki karbi tayin soyayata ki so ni tamkar yanda nake son ki Uman Malan?*

Tsurawa fuskarsa ido ta yi tana kallonsa,
Menene aibunsa? Dama sallah ce, a yanzu yana yin sallah tun karfinsa,
Idan ta kai warhaka da karfinta a sha.anin kutakale tabas harda taimakon BS

Yana biye da ita ne dan yana matsanancin son ta,
Ita kuwa isan bata so shi wa zata so? Mutun ne shi mai daraja da daukaka, ya kasance mai kaunarta tun bata zama Bodyguard ba, ya kasance mai kawar da kai a irin halayanta na yau da kulun, ya jure iskancinta kala kala, baya hukunta ta, baya sakata kwana cikin maza.......yana kishinta, to ita kuwa wa zata samu ya yi mata irin wannan son?

Kanta ta sada cikin yannayin kunya, abinda bata taba nuna masa ba a hankali ta budi bakinta ta ce"........


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 1??

Mamaki ne ya cika zuciyar BS, haskiya ne, shifa ya ga abubuwan da suke da girman da isa da iza ba zata saka a koya ba , sai dai idan an ginaka da abin,

Wayar ya kashe ya koma ya dauki jibrin da aka gama yiwa dinki suka nufi gidan Abdul dan ba zai yiwu ya bar shi ya yi jinya a asibiti ba,

A lokacin da suka karaso, ya jima tsakanin dakin da aka baiwa Hafsat da nasu, yana ta kai kawo kafin da kyar ya iya bugawa yana saurare da bugawar zuciyar Allah ya sa ta bashi damar shiga, dan wani irin kwarjini take masa kamar ba yarinya karama ba.

Amsawa hafsar dake zaune kasa bayanta jingine da gadon dakin , laptop gabanta ta yi shiru tana duban screen din cike da rashin kwarin gwuiwa domin kuwa lale Abdul ya bata labarinsa aman ba wai ya bata sunaye bane, komai a dunkule a baibai ya bata, ta tabata ya yi haka ne dan karta ce zata shiga lamarin da ba nata ba, ya yi haka ne dan kar wani ya kutsa kai cikin abinda bai shafe shi ba,
Gashi dai tun da ta shigo sallah kawai ta iya yi ta samu waje ta zauna tana ta binciken abubuwan da ba amsa, sai canke canke take ko zata dace har BS ya shigo dakin nata,

Waje ya samu ya zauna a kasa kamar yanda ta zauna yana kallonta,

A hankali ya ce" yaya jikin ki?

Hafsat ta dube shi da kyau tana mai rufe laptop din,
Hannun ta kalla, sannan kuma ta dubi BS , kafadarta ta daga kadan kafin a hankali ta ce" Alhamdulilah,

BS ya kureta da kallo, a nitse ya dan muzkuta yana dubanta sannan ya ce" wa ya cire maki bullet din?

Itama wannan karron tsura masa idon ta yi, sannan ta ce" Abdul ne,

Abdul? Ya maimaita yana mai nuni da wata manufa, sannan ya kawar da kansa gefe yana dan murmushin yake ya kuma dubanta ya ce" da sunnansa kike kiransa haka?

Dan sasaucin dake saman fuskarta ta yi kokarin kwashewa, inda ta dora yannayin rashin walwala sannan ta kawar da dubanta daga kansa,

BS ya juyo da nasa duban jin ta yi shiru, ya dago hannunsa yana dubanta ya ce" kar ki yaudari kan ki, kar ki sakawa kanki wani tunanin abinda ba zai taba yiwuwa ba, kin san shi kuwa? Kin san ko shi waye? Kina kokarin yin wasa da wuta, kina son saka kanki a halaka ne? Ki sauko daga inda kika hau, aiki ya kawo ki, ki yi shi kawai, ki duba ki ga yanzu da harbin nan a wani wajen da zaki mutu aka yi shi da shikenan kin mace wajen kokarin gannin kin birge shi ko me?

Da sauri ta juyo da dubanta wajensa,
Ta jima tanai masa wani kallo kafin ta sada idannuwanta , ranta ne take jin yana wani irin tafarfasar da ba zata so yin wani furuci a gabansa a wannan yannayin ba,
Me yake tunani da ita, au shi ba zai cire wannan shirmen dake dawainiya da shi a kanta ba? Dan ita bata ga dalilin da zai saka shi duban kwayar idannuwanta ya jefeta da magangannun dake nuni a sakarai ya dauketa ba, an fada masa tana neman kai ko ta zo dan haka ne?

Sasauta yannayin muryarsa daga bacin rai zuwa rarashi ya yi ya ce" ba ina miki haka dan na tsaneki bane, ina so ne ki farga tun kafin ya zame maki matsala

Hafsat ta dube shi da idannuwanta ta ce" kar wani yannayi naka da ka kasa daidaitawa ko tsayarwa ya kai ka aikata baban kuskure a rayuwarka BS! Kar ka mayar da abokiyar hamayarka....
Shiru ta yi na dan seconni kafin ta dago da idannuwanta da yannayin she's vry serious da abinda take fada kafin ta taune lebenta da hakorinta ta ce" *dan walahi sai na bika har gawarka sai na yi kokowa da ita!*

Idannuwansa ya zaro yana dubanta, inda gabansa ke tsannanta faduwa kan irin lamarinta,
A dan hargitse ya ce" saboda shi din ne zaki mayar da ni abokin gabanki ko me kike nufi?

Hafsat ta kankance idannuwanta dan jaraba hannunta na ciwo aman bakinta ya ki mutuwa ta ce" dan me saboda shi? Me kake tunani tsakanina da shi? Ina jin da ni fasika ce, da na jima da bayar da kaina kafin na shiga *kutkale!*

Aman ai dan na yi maganar nan ne kika bata rai haka ko?
Ya fada yana dubanta da kyau yana dan matsawa kusa da ita kafin ya dakata yana dubanta , sasauta murya ya yi ya ce" bana daukan ki a fasika, bana miki kallon wawuya, hasalima idan har ya kai ki wajen da zaki sha wahala zamu sha ta tare ne,

Shiru ya yi gannin ta kura masa ido, daya daga cikin sunnayenta ya zaba dan kiranta domin ta hana shi kama na asalin, a hankali ya ce" Ummi, ina son ki, kin jima da sannin haka aman kike wasa da zuciyata? Bayan kin san da daya daga cikin sauran na so, da da gudu zata amince min harma ta bini inda zan je ko? Ki bari haka, ki daina haka, ya karashe yana mai dubanta kamar yanda take dubansa,
Sai da ta lumshe idannuwanta ta ce" BS, ka yi hakuri ka ji? A yanzu, babar damuwata shine na fita a aikin nan lafia na samu incina na yawo inda nake so a lokacin da nake so, na sadu da iyayena mu sansanta tsakanin mu, walahi na fada maka gaskiya rabona da na ji wai ina iya soyaya tun wace ta kai ni *KUTKALE* me ta anfana min ne soyaya? Ita ta saka na kara zama fitsarariya, dalilin soyaya na tarbi gaban malan gaban yayansa masu jin kunyarsa na yi tsalen albarka na ce" *Malan, ba aure zaka min ba? To sai na yanka mijin!*

Haka ya bini da kallo da adu.a, na sha na tashi tsakiyar dare na ga mamana na tofa min adu.a, cikin ikon Allah sai na je na yi wanka wai na wanke adu.ar dan ta dankwafar da ni ne take min tofi salon a min auren ko yana wulakanta ni na zauna ko? To kar ta kuma min tofi!
Dalilin soyayar nake duban du wani yayana da ya yi garajen tsawata min na lalaya masa maganar da zai ji ya tsane ni har karshen rayuwarsa,
Dalilin soyayar na ringa kirta rashin mutunci da nake jin daidai ne, kaina daidai yake da na kowa idan dai za.a taba min abin so na! Wata alfarma ta yi min soyayar dake saka ni fita tsakiyar dare tare da kato mu je gidan rawa ni ba karuwa ba, ni ba arniya ba, ina kallo ana abubuwan da ba daidai ba aman a gobema na koma dan bacin ransa na nufin tashin hankalina?
Ita soyayar nace dan ubanta me ta tsinana min bayan *bakin jini, hau, tabewa, shiga uku, rayuwar da ko a mafarki ban taba tunanin ganina ciki ba, wato rayuwa irin ta dakarun sojoji?*

Tsagaitawa ta yi da maganar da take yi jin kanta na sarawa ta dube shi ta ce" ban ce bana son ka ba, ban kuma ce ina son ka ba, hasalima na mance kalar soyaya ne...ko nace na rasa sunnan da zan bata, *fara, ko bak'a* aa, *zaki ko madaci ce?* , *rayuwa ko mutuwa ce?*, a yanzu burina shi ne *ABDUL* ya rayu, ya fita a damuwarsa ko zai salame mu mu koma gaban GN ya bani inci cikake na arta a guje sai gaban Malan

Shi kam du kallonta ne yake, wai bata soyaya? Wai ta daina so take son fadi? Shi kam ya kasa yarda, yana tsoron irin yanda kusancinsu yake da girma tsakaninta da uban gidansu ya girmami tunaninsa ya zarce mizanin dan bashi tsaro ne kawai

Kansa ya kawar gefe, har tsakar ransa yana jin haushin irin yanda yake wareta ita kadai yana bata kulawa, du sun lura ba shi kadai ba irin yanda yake sakar mata murmushi ko idan ita ta yi masa tambaya zai tsaya ne ya bata amsa yanda take so , yana bata lokacinsa , har tsayuwa yake ya cire mata hular gashin dokin da take dorawa, yakan dora kujera idan sun biyo bayansa in ya zile masu ya zauna dangagal a matsayin da gare shi a dukiyarsa ya ringa binta da kallo tana faman kuftayar a saketa ta yi masa kashedin kar ya kuma yi masu haka, da an harbe shi fa? Me yasa hannayin damuwar da take nunawa ke birge shi? Ko meye hakan ke nufi? Ita kanta takan nuna bacin ranta da dukan karfinta tamkar an taba rayuwar wani na jikinta wanda take matukar so? Eh lale haka ake koya masu, ana koya masu cewar rayuwar wanda zasu je baiwa kariya ta fi tasu mahinmanci, su baiwa rayuwar girma su kareta da dukan karfin su, aman ita ta zurma da yawa, ta shiga da yawa, haka ake yi?

Har ya mike, ya dawo ya tsugunna yana dubanta kafin ya ce" ki kwana lafia, ki kwontar da hankalin ki, in dai gidan nan ne za.a turo wa.inda zasu canje ku, domin kun ji ciwo ba zai yiwu ku ci gaba da aiki ba, a gobe gobe GN zai turo masu canzarku ke da Jibrin, a mayar da ke camps, hankalina zai fi kwonciya, ki je can ki yi jinyar hannun ki, idan kika warke sai a sama maki wata mission din mai sauki ki yi ki gama a baki damar fita inda kike so, a lokacin da kike so!

Yana gama fada ya juya ya bar mata dakin cike da yannayin damuwa, da tsoron rasata, dan shi sonta yake , koma mecece ita sonta yake

Da kallo ta bi shi,
Ya Allah, hakane fa, za.a iya mayar da ita fa, shikennan yanzu ta sha bulley din banza kennan? Eh mana tunda dai wata mission din za.a kuma fitar da ita, bayan ta shiga wannan? Bayan ta sha wahalar nan maimakun idan an mayar da itanma a ajiyeta a matsayin ta gama fita mission da sunnan camps din sai dai a turata wata?

Idannuwanta ta rintse tare da shiga tashin hankali, ita fa so take daga nan ta je camp a matsayin wace ta ci nasara ta samu incinta!

A hankali ta buda idannuwanta ta shiga kokarin mikewa bayan ta kashe laptop din

Fitowa ta yi ta nufi dakinsa kanta tsaye,
Tana zuwa ta shiga bugawa, jin shiry ya sakata kara kunnenta, sai dai abinda ta dan fara jiyowa ne ya sakata saurin matsawa gefe tana mai jin gabanta na faduwa,
Sai a lokacin ta dafe kanta da hannun da bashi da ciwo ta ayyanawa kanta cewa....kema baki da kai, a wannan lokacin kike tsamanin samunsa a hayacinsa?

Zama ta yi a wajen, inda BS ya yi kai kawo ya fi a kirga yana aikinsa bai ce da ita komai ba, ya ajiyeta a zata yi ta gama ne,

A kadan sun kwashe awa uku a wajem, daga masu baiwa Ni.ima tsaro, da BS da ita kanta,
Suna kallon juna lokaci zuwa lokaci, suna jiran fitowar Ni.ima , kowa na kallon kowa da ido , basu da abin cewa, sunna zaune ne, kowa kuma

28 / 54