Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   26 / 54

75K to 78K   out of 159.5K words

ya fadi, ta dan tsura masa ido aman sai ta kasa ce da shi komai,

Murmushi ta sakar masa sannan ta shige ciki da dan gudu gudu hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya juya ya tafi ya shiga galeliyar motarsa yana tunanin sai dai a waya ya mata maganar aikinta da kuma dukiyarta


Can wajen karfe biyun dare, dare ya tsala Hafsat na zaune tsakiyar gadonta daga ita sai dan gajeran wandonta da yar rigarta na barci ta yi zuru da wayarta a hannunta tana dannawa tana game

Message ne ya shigo mata kamar haka " *KAURIYATA, NA KASA BACI*

kurawa harufan ido ta yi tana kallo, bugun zuciyarta ne ya canza lokaci daya hannunta ya fara rawa,
Du duniya ba wanda ke haye mata irinsa, shi ne, walahi shi ne

Wayar ta ajiye tana kallon rubutun tamkar wanda ya yi da hannunsa idan hasken wayar zai dauke sai ta danna ta kara kallo

A hankali ta rubuta " *ME YA HANA KA BACI?*

mikewa ya yi zaune daga kwoncen da yake yana mai hararar wayar, kafin ya rubuto " *ke, gida kika je kika tara samari haka? Bakya dan jan aji daga yi maki magana har ki bani amsa ko kin sanma da wa kike magana ne?*

A lokacin da ta karanta sai da ta saki murmushi, sannan ta rubuto" *na san ko kasuwa na yi a tsakiyar dare irin na barawo? Dole bazawara ta ringa damka da karfi karfinta mana*

Wani uban tsaki ya ja a lokacin da ya karanta message din,

Zama ya gyara ya shiga dandankara magana son ransa, har ya so saki sai kuma ya koma da baya ya zauna ya jinginar da kansa jikin bed din, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon waje daya sai kuma ya rubuta message kamar haka" *Na yi missing din ki amaryar BS*

Numfashinta ne ta fara ji yanai mata sama sama, lokaci daya kuma ta koma ta mike kafafuwanta saman bed din , sai da ta yi mika nitsatsiya sannan ta rubuta message kamar haka.........



>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




3?? 2??




Sai da ya gama yi masa wani kallo sannan ya ce" kai, banma taba sannin irin girman rainin hankalin da ka yi min ba sai yau da na tabatar da abinda na dauki shekaru ina fada maka baka yarda ba!

Muhammad ya nemi waje ya zauna yana dubansa, da irin duban da yake masa a kulun idan ya yi maganar cewa mahaifinsa na raye, ya tabata yau din ma maganar ne dan haka ya yi masa wani zuru yana kallonsa irin kai nake sauraron nan

Abdul ya gyada kansa yana kallonsa,

Girgiza kai ya yi ya Mike ya gyara rigarsa da ta yakune sanadiyar daukansa da aka yi har sau biyu,

Tsaki ya ja a fili mai mugun karfi ya juya ya fita shima a dakin ya bar Muhamad zaune yana mai binsa da kallo

Sai da ya tabatar da ya fita ya dauko wayarsa ya kara shiga dakin ya danna wata number ya shiga waya cikin rage murya sosai yanda idan ba kai ne yake yiwa maganar ba zaka yi ba, hakan ya saka ban fahimci abinda yake fada ba


Abdul, yanda ya ga dare haka ya ga rana, zuciyarsa ciwo take masa, yana mai jin wani irin tsananin haushin Hafsat da ta tare masa gaba ta tsayar da shi wa aikata abinda ya fi buri a rayuwa, bai taba tunanin wata halita zata shiga gabansa , ta tare masa aiwatar da harbe Abdul basid, muten da ya yi sanadiyar mutuwar mahaifiyarsa, da kanwarsa, sannan yake neman rayuwarsa, sai gashi, yarinyar karama da zai yi kanwa ta biyar da ita, yarinyar da bai hada komai da ita ba ta zo ta shiga gaban mutumen da yake nema ruwa a jalo aman ya ji gabansa ya yanke ya fadi, hannunsa ya kwashi rawa?

Saman bed din daya daga cikin sauran dakunnansa ya kwonta ya mike kafafuwansa ya lumshe idannuwansa,

Tamkar an dake shi ya zabura ya zauna, dan kuwa hasko masa ita ne aka yi a lokacin da ta yi tsaye da bindigarta ta yi rantsuwar sai dai ya kasheta kafin ya kashe mutumen nan,
Hannunsa ya saka ya mari gefen fuskarsa ya ce" ABDUL me ya hana ka harbeta kafin ta yi shiru a maganarta? Abdul me ke damunka har haka? Abdul kana ji kana gani ya kubuce maka bayan ka gansa a raye? Ba zaman jeji ba ko zaman cikin rami ko rijiya zaka koma sai na kara samo inda kake , kuma ba wai wannan yarinyar ba, ko wa ya shiga tsakanin bindigata da kwakwaluwarka sai na harbe shi kafin na harbe ka!

Idannuwansa ya kuma lunshewa yana sakar zuci, shi dai a tambaya daya ya tsaya wace ya rasa amsarta gamsashiyar da zata saka shi kawar da kai ya manta komai hakan ya saka shi kwana zaune, yanda ya ga dare haka ya ga rana


Washe gari wajen karfe tara na safe, hayaniyar da ya ringa jiyowa kasa kasa ce ta saka shi mikewa daga saman salayar da ya keana kaiwa Allah subahanahu wata.ala kukansa

Labulen dakin ya dan ja ya leka kansa,

Ikon Allah, shi ne kalmar da ta fara fitowa da bakinsa zubewa lebensa

Ido ya kurawa yan mata biyun da yake hange daga dakinsa,

Wannan matarsa ce Bahija, wace ta gudu ita da Mariam, kwarai wannan bahija ce, dayar da ta bayar da kanta gefe ce bai fahimta ba,
Aa, yaya aka yi bakin fuska suka samu damar shigowa har tsakar gidansa? Yaya aka yi haka?

Tsayuwa ya yi ya harde hannayensa yana kallo da kyau

BS ne ya yi tsaye a gabansu ya ce" dan kina tsohuwar matarsa bai bamu damar dan kina haka ki zo kai tsaye ki shiga har inda yake ba, ki juya wanda ya baki damar shigowar da ya sanki ya shigo ya hau wajen Sire ya tambayo shi ya kuma sako ki ciki, aman daga inda nake tsayen nan ba zaki shiga ba

Kallonta ta sauke saman kansa a yatsine, ta mayar da dubanta wajrn daidaikun sojojin dake yawo a tsakar gidan, haka kuma ta mayar da dubanta kan BS da kuna abokin aikinsa dake tsaye wanda BS ne kawai ya bata amsa kan ba zata shiga wajen Abdul ba, hakan ya saka take ta hayaniya tana karawa kan sai an barta ta shiga, domin gidan mijinta ne, tana da ikon zuwa a lokacin da ta ga dama, harma ta gayaci wanda ta ga dama

Dubansa ya maida wajen abokin aikinsa, yana tunanin sakawa a fitar masa da wadinnan yan matan yan rainin hankali

Abdul ne ya bude kofar dakinsa ya fito cikin takunsa na kakarfan namiji

Jikinsa sanye da doguwar riga ta sallah baka mai dan adon goldin

Fuskarsa ba fara.a ko ta naira biyar, ya hade fuska tamkar zai kai duka

Wata irin firgita Hafsat ta yi a lokacin da ta ga fitowarsa domin bata shirta hakan ba, sam bata yi tsamaninsa a irin wannan lokacin ba

Sai da ya ja ya tsaya kamar yanda ya saba, ya kai dubansa wajen Hasana dake tsaye ta shiga taitayinta jira kawai suke ya yi gaba su bi bayansa,
Haka kuma ya kai duban nasa wajen Hafsat,
Irin kallon dake bata wahalan nan dai ya yi mata, wani kallo mai kama da tsana tsana mai shige da harare hararenta,
Tsai itama idannuwanta ke cikin nasa kafin a hankali saman lebent ta furta" *ABDELLAH* ta karasa ta lumshe dara daran idannuwanta ta kuma budewa hakan ya saka ta tara masu ruwan kwallah a cikinsu

Gabansa ne ya ji ya rikida ya fadin masa, hakan ya saka shi kawar da dubansa yana mai jin wani ruwa ruwa kadan a goshinsa

Hannunsa ya kai wajen goshin ya dan shafo, ya kalla da idannuwansa, *ZUFA* ZUfa ce yake yi dan ya yi ido hudu da yarinyar nan?

Juyawa ya yi da sauki ya nufi kofa hakan ya saka su mara masa baya da sauri


Yana fitowa BS na gama rufe bakinsa cewar a fitar da su

Yarinyar da ta baiwa wajen su BS baya kan ba zata iya yin cacar baki da su bane ta juyo da sauri jin an ce wai a fitar da ita

Sai da ta yi masu kallon sama da kasa kafin ta ce" *GIDAN UBAN NAWA ZAKU CE A FITAR DA NI?*

Abdul da ya sanyo kai ya fito da sauri ya kai dubansa saman kanta,
Itama idannuwan nata ta zuba masa cikin wani kallo na rainin wayo irin na ka.ide tabas shi ne,

Gyaram murya ya yi, hakan ya saka su Abdul ja gefe sannan suka sara masa

Kallon su ya yi a fakaice sai kuma ya kai dubansa wajen matar da ta gudu da igiyar aurensa kan wai yana cikin hatsari da kuma yar farar yarinyar da suke tare

Bai yi magana ba sai idannuwansa da ya jefa masu tambaya da su ta hanyar buda masu su baki daya ya dadage masu giraransa sannan ya dan gumtse bakinsa

Bahija ce ta shiga dan kara jan abayar dake jikinta tana kara rufe jikinta sannan du rawar kan nan da take yi nan da nan ta nutsu, ta sada kanta ta kasa kuma dago da kanta ma bale har ta dubi idannuwansa dake firgitata

Wace suke tare ce ta kalli yannayinta, murmushi ta yi a ranta tana ayyana lale na yarda matansa na tsoronsa tamkar rai, kamar ba Bahija ba ta wani nutsu nan da nan daga gannin mutun tsaye a gabanta,

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta mika hannunta irin su yi musabahan nan ta ce" *hi kanina, sunana Furaira ana kirana da Fulawa, wato fleur, ni yayarka ce wace aka fara haifa kafin a haifi mamanka*

Hannun nata ya bi da kallo, nan ya ga baki bakin hannayen nata irin na kana shafe shafen nan sosai ya kasance jikinka ne farin banda hannun naka, sosai ya kone mata hannun du irin kinshin da akai mata dan boye shi kuwa tsaf ana ganninsa

A haka ya kuma binta da kallo ita din kanta,
Wata irin farar hoda ce akai mata mak up da ita ta yi mata bau da ita, sai gashin idon nan manyan wato na karshen tsayin nan an sakawa idannuwanta da suka fara dan jemewa irin man shafe shafe ya ci fatar idon du ya yamutseta,

Wani irin kwali ne aka saka mata mai mugun baki sannan aka ja shi saman idonta sosai kafin a dora mata far bau mai ruwan ja ya yi mata wani irin bau a fuskar, sai jan baki da aka saka mata a leben wanda ya saka bakin yin wani irin dambarere da shi , kai kana gannin fuskarta ka ga rikakiyar yar bariki

Abdul kam kallon tsaf yake mata tun daga kanta har kafarta, hakan ya saka hannun da ta miko da gatsali da iya yi ya fara gajiya har ta fara jin wani iri hakan ya saka ta bude bakinta da niyar yin magana tana dan satar kallon yan matan dake bayansa wa.inda ta tabata bodygurads dinsa ne ta yannayin shigarsu wato su Hafsat, da Bahija da su BS sai shi kansa wanda ta zo dominsa ta ji muryarsa a tsakiyar kanta inda ta yi gagawar kallonsa da yannayin mamaki Abdul ya ce"




*Dan girman Allah, ku yi hakuri yan uwana, walahi doguwar tafia ce na yi tun karfe biyar na suba sai karfe biyu na dare muka karaso, zaman mota hakan ya saka ina tare da gajiya sosai gabaina na ciwo=? ?, ku yi hakuri da kadan dinsa, kun san hannuna zaku ji da yawa daga na ji garai*


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 6??



A lokacin da suka fito gaba dayansu da yannayin na zakunna, kowane na jefa kafarsa inda ta je, suka tsaya gaba dayansu a tare sakamakon ganninta tsaye ta zuba masu ido su duka,

Sai da gabansa ya yanke ya bada wani irin sautin da kunnayensa suka jiyo masa,
Tsaye take kawai, hannayenta gaba daya a sake, wandon dake jikinta irin mai lafewa a jiki ne aman kuma sakake wajen mazaunanta kawai ya rike , sai riga mai botura da wata a ciki wada dalilin bale boturan da ta yi ya saka ake ganninta, kanta dauke da asalin gashinta ba wancen atach din ba,
Fuskarta babu ko digon kwali bale a yi hangen hoda ko wani abin,
Aman wani fayau da shiga ido da take sai a hankali, dole ta girgizawa namiji lafiyaye zuciya sai dai idan zuciyar taka na hangen wata sai ka kyasa a ranka ka huce wajen,

Hannayensa ya daga ya cusa cikin gashin kansa da ya bar suma ta taru sannan baya gyarawa,

Sai da ya dan waiwaya ya ga tsayuwar me kuma suke a bayansa? Sannan ya daga kafarsa ya tunkareta,
Hannunta na dama ya damka ya jata tamkar rakumi da kala haka ta bi shi ba tare da ta warci hannun nata ba, ba kuma ta yi masa gardama ba,

Da kallo suka bi su, inda BS ya daga kafarsa ya bi bayan su da saurin gaske, sai dai yana karasawa Abdul na banko kofar da wani irin karan sautin dake nuna halin bacin ran da yake ciki,

Wani irin hankadata ya yi cikin dakin dake mamaye da duhu, wanda yake daya daga cikin dakunan gidan, shi kansa bai san ainahin inda zai je ya kuna fitila ba, sannan tun da ya hankadata yama rasa inda ya hankadata,

Garu ya yi nufin kaiwa naushi, wanda sai da ya naushi iska sau uku kafin ya samu hannunsa ya naushi garun da wani irin karfin da da normal ne sai ya ji jiki ainun, aman da yake ransa bace ne sai ihun bacin rai da ya saki murya kausashe ya ce" me kika ji? Me ki ka ji nace?

Inda yake kallo daban, inda muryarta ta fito daban, domin ita a bayansa take, a hankali, cikin mutuwar jiki ta ce" ina bayanka,

Juyowa ya yi ya yi shiru, inda ya dauke numfashinsa, yana so dole ya lalubota ta habyar numfashin da take saukewa,

Fahimtar hakan da ta yi ya sakata tsayar da numfashinta sannan ta canza waje da sauri ta saisaita ajiyar zuciyar da take yi, ta dan labe wajen labulen wajen ta ce" a wajen formation din zama gagarimin sojan dake aiki wa kasashen duniya baki daya, wanda yana da damar yin operation inda ya ga dama, yana da takardun shaidar shi dan kasar da du ya yada zango ne, shi dai wannan mutun ko shugaban kasa na mangarinsa domin ba.a bayar da formation dinsa a kananun kasashe sai irin su chaina, dubai, ko su Saudiya. Japan...da dai sauransu....
Wanda a cikin mutun hamsin bai fi biyar su fita ba, kai ana iya goge kowa a hanawa duka hamsin din!
Sai kuma bodyguard , ana koya masa irin wannan abin a sama sama ba a zufafe ba saboda halin rayuwa......

Labulen da ya damka ne ya sakata saurin matsawa ta canza waje ,

Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta ce" a ciki.... *WANENE KAI ABDUL JABAR ABDUL BASID?*

Gabansa ne ya wani irin bugawa sakamakon irin yanda ta ja sunnansa lokaci daya take neman sannin waye shi, a iya yau, a iya hafuwar yau, awowin da ba zasu fi goma sha biyu ba , wanda da yawa da suke tare shekara da shekaru.basu san hakan ba?

Jikinsa ne ya yi la.asar, sanyi ya yi sosai da sosai, dan haka sai ya daina neman lalubo infa take ya saki abin sauraron da ta laka masa nan ya juya ya lalubi kowa ya bude ya fice a dakin,

Bai yiwa kowa magana ba, sai dakinsa da ya je ya shige ya rufe ,

Bakin bed dinsa ya zauna ya dora kafarsa daya kan daya ya daga kansa sama,

Wasu zafafan hawaye ne suka shiga bin gefen kumatunsa a lokacin da ya tuna mahaifiyarsa da irin rayuwar da ta yi cikin duhu, haka kuma irin mutuwar da kanwarsa ta yi, da irin rayuwar da mahaifinsa

26 / 54