Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   42 / 54

123K to 126K   out of 159.5K words

a hankali a wuyanta sannan ta daga hannayenta ta ce" du saurin ki, ki kasance cikin kanshi Maman malan,
Ki ringa shafa turare a gurbi gurbi na jikin ki, kin ga daga kasan wuyan ki, bayan kunnen ki, hamatar ki, kasan maman ki, tsakakanin cinyoyin ki, cibiyar ki, du inda ya dace wannan humura ta zamo ita ce ta sirrin jikin ki kafin turaran wuta,
Idan kina haka zaki kasance daban, bata da daci bale hakan ya damu abokin zaman ki, bata da karfi bale ta dame ki ko ta dame shi,

Hannunta Hafsat ta rike ta shagwabe fuska sai ga hawaye ta ce" yanzu aunty kai ni zaku yi? Aunty yaya ina magana bama zaki kula ni ba??????



Comment zafafa ke saka ni rubutu bilahi>?-?


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




5?? 5??






Tsayar da abinda aunty take ta yi, sannan ta duka gaban Hafsat domin so take su yi ido cikin ido da ita

Ai kuwa suka hada idon, hakan ya saka Hafsat dan kawar da dubanta a hankali

Aunty ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" kar ki damu maman malan, zaki so shin ne

Hafsat ta zumburi bakinta gaba, ita kai ji take da ta je gidan Abdul a yau gwarama ta yi ta zama a gwauruwarta a yi ta yi mata gorin in dai zatana gannin mamanta da malan sai me?

Daina kulata suka yi, kowa yake hidindimunsa na shirye shiryen kaurar da ita gidanta, domin yan uwanta mata baki daya kulewa suka yi a dakin mama suna ta kimtsa dukan abin kimtsawa

Sai da magariba ta yi sannan aka samu fitowa da Amarya
Abin mamaki ga kowa mama da kanta ke janye da Hafsat, wace ke cikin lulubi cikin farin abin rufa ba.a gannin komai nata, yan uwanta sun zagayeta kamshi kam sai rabawa take

A hankali aka shiga dakin Hajia mama da ita,

Suka da ita mama ta yi, cikin nutsuwa ta kalli hajia mama ta ce" mamanta, ta zo yin salama da neman gafara, a yafe mata zaman yau da kulun

Hajia mama dake zaune da sauran matan a dakinta ana ta cicira maganar irin motocin da suka zo daukar Hafsat motar ba wasu masu yawa ba aman hameur biyar ce cif dukansu bakake wulik sai haska wajen suke, suna tsaka da tautaunawar aka shigo da hafsat din hakan ya saka suka bi su mama da kallo da mamaki


Hajia mama ce ta tabe baki ta ce" a yafe

Murmushi mama ta yi ta kama Hafsat ta mikar da ita daga tsugunnin da akai mata

Kama hannunta ta yi suka juya har sun kusa fita amarya kasa kasa ta ce" ba girin girin din ba, ta yi mai, ai shi matsalar irin haka ba ridi ba daraja sai dai a je a dawo

Aunty nana mariam ce ta ja ta tsaya, sai dai kallon da mama ta yi mata ya sakata juyawa suka fice a dakin
Sai da suka zo kusan kofar gidan mama ta ja ta tsaya ta damka hannun Hafsat a cikin hannun Aunty ,

Da sauri ta juya domin raf Hafsat ta rike hannun taki saki sai da mama ta janye da karfi ta yi ciki tana jiyo irin yanda Hafsat ke kuka , ita kanta sai da ta labe ta yi hawaye kafin ta saku ta shiga sha.aninta tanaiwa yarta fatan alkhairi


Su Aunty kansu sun yi adu.a da fatan alkhairi a irin gidan da Hafsat ta samu, sun yi fatan Allah ya sa mai hakuri da datako ne mijin , hakan zai sa su jima zaman nasu ya yi karko

Tamkar zata suma a lokacin da zasu tafi su barta
Sai dai aure ne, daga shi sai mutuwa su ke rabaka da iyayenka, da danginka , su canza maka muhali, yannayin rayuwa,
Haka suka rabu da yar uwarsu bayan dogon jawabi da rarashi,
Sun yi mamakin gannin ba wanda ya leko su ko ya aiko masu da sakon su ci kansu, sun kuwa lura da gidan akoy mutun domin fitila a kunne take kuma da dan hayaniya

Suna tafiya ta nemi waje ta zauna kasa saman kafet dinta ta saka hannayenta bibiyu ta yi tagumi tana bin dakin da kallo
Jin abin da gannin abin take a wai, wai ita ce matar Abdul? Mutumen da ta hadu da shi dan kawai ta zama bodyguard dinsa sai gata yau ta zo gidansa a matsayin katarsa?
Rabonsa da ya yi mata wata maganar arziki tun da suka fita zuwa gidan dinki,
Gaba dayansa ya canza mata tamkar ba shi ba, ba wata magana bale kulawa, wai yau ake kawota gidan miji ba danginsa ba wani nasa shi kansa baya nan bare har ta ji kanta tamkar amarya ko ta rufe fuskarta anai mata oyoyo ana zolayarta ana jan rufarta,
Gata dai zaune a dakin da mahaifinta ya wani irin kashe kudi ya zuba mata kaya, kayan alatu, kayayaki masu kyau da gayu, an tafi an barta daga ita sai halinta!

Rufar da ta aka lulubo mata ta yaye baki daya,
Mikewa ta yi tana jin kanta har yanzu da zafi irin kitson nan da aka yaryara mata kananu har haka, kitson tamkar da alura aka yi su, sun yi cas sun cika sun yi tsayo sun kuma zanu

Hannayenta ta bi da kallo,
Ita kanta kunshin jan lalen hannunta na birgeta sosai

Cire rufar ta yi baki daya ta nufi wajen kular abincin da aka kawota da shi
Budawa ta yi hankali kwonce ta zauna ta ci abincinta,
Kanta ta baiwa hakuri cewar zamanta da abdul ba wani zama bane dan ba zai iya da halayanta ba itama ba zata iya da wulakancinsa ba, dan haka kar ta wani saka damuwa a ranta ta tsamure ta lalace a wofi, zata koma kusa da iyayenta soon


Sosai Hafsat ta saki jikinta ta saki ranta a tankamemen bangarenta , bata rasa ci, sha , sutura, kayan kwalam da makulashe, bata rasa abin kallo ba, ga Ac da take sha kowani lokaci,
Sangartarta take zubawa da barna kala kala,
Takan hada fruits ta markade ta juye peak da kananfari da dabino ta zauna ta yi ta sha abinta
Karshema da yawa ta yi ta saka a frij ya zama ruwanta, koda yaushe zata didika ta je ta mike abinta

Karshen neman magana Hafsat na farkawa daga baci ta yi ra.ayin buda facebook, tana budawa ta dora hotonta a dp dinta ba tare da dar ba, sannan ta saka sunnanta tsaf Hafsat maman malan, ta koma Whatsupp ta buda
Sai da ta budar ne ta shiga neman numbobin yan uwanta du ta saka ai kuwa ta shiga takura su sun ki lekota sun kawota har sun kare da ita kennan?

Su kam suna bata amsa suna rarashinta su a tunaninsu ta kwontar da hankalinta har mijinta ya bata damar hawa whatsup da facebook


Saukowarsa kennan daga masalaci
Ya nemi waje ya zauna, balarabiyar dake masa girki ta kawo masa tea da dan abinci kadan wanda salak nema kawai aka gyara da kayan lambu da mayonaise ta juya

Cikin nutsuwa ya sha tea din, yana gamawa ya mike ya dauki wayarsa ya shige can kuryar dakinsa ya dauki wayarsa katuwa kirar iphone 11 pro ya zauna bakin kujera baba ya danna kiran number Na.ima

Na.ima dake kwonce saman bed doguwar kujerar falonta ta daga kiran

Tana dagawa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta shiga shasheka tamkar wace zata fashe da kuka

Idannuwansa ya lumshe, a hankali ya ce" menene?

Sai da ta sauke ajiyar zuciya jin muryar muradin ranta sannan ta ce" ka dawo gida

Abdul da idannuwansa ke lumshe ya ce" kin daina fushin?

Na.ima ta yi shiru, sai kuma ta saki wani dan marayan kuka irin na shagwababun yara, tana yi tana jan majina sosai hawaye na bin kumatunta

A hankali ya ce" zan kashe fa

Da sauri ta ce" ka yi hakuri, Abdul dan me mani kishiya? Me na gaza Abdul? Abdul haka zaka ci gaba da aure aure ko fada min ba zakana yi ba bale har na yi tunanin zan samu rarashi?

Idannuwansa ya bude sosai , a hankali ya kuma fadin" Na.ima, tun yaushe kike so na? Wani irin so kike min?


Na.ima ta gyara kwonciyarta ta ce " ina son ka da dukan karfin jikina, ina jin kaunarka har bargona

Abdul ya lumshe ido yana mai jin tausayinta har cikin ransa, a hankali ya kuma cewa" dan me zaki yi fushi dan na sako mace cikin gidana dan na kara raya sunnar ma.aiki da ita? Na.ima, a tunanina ko kura na kawo maki zaki kulata ki ciyar da ita

Zaune na.ima ta mike, a hankali ta ce" Abdul, ko zaki ka kawo min, zan bashi nama, aman idan macen da zata rabarmin ni.imatacen kuma tsadadan jikinka ne, ina kishinta, Abdul.kishiya ka min ba yar uwa ba, ban iya boye abu ba bale na yi munafurcin zan so ta, ban taba ganninta ba, bana so na hadu da ita, Abdul bana son ta!

Abdul dake sauraronta da mamaki ya kali wayar, murmushi kawai ya sakar mata a wayar ya datse kiran


Mikewa ya yi ya bale agogo hannunsa ya ajiye, kansa ya daga ya kali agogon dakin, karfe biyar ne na yama, ya yi daidai da karfe goma sha daya a Niger,

Doguwar fara kar din jalabiyar jikinsa ya cire ya kwonta saman bed,

A hankali ya lumshe idannuwansa,
Murmushi ya saki, a fili ya ce" kina ina? Kina me? Ke da wa? Shin kin saki ranki a bakon waje? Har yanzu kin tsane ni? Na san ba zaki taba so na ba, Hafsat kin raina ni sanadiyar sannin na kayar da zina abin yi a da, da wahala ki ga girmana bayan na sha yin izgili kala kala a gabanki, kin dauke ni mai wulakanta mata dan kin ga rayuwar taka tsantsan da na yi da matata kin dauki hakan a matsayin ni mai kudi ne, mai halayar wasu masu kudin

Murmushi ya yi yana dauko wayarsa ya kunna ya shiga whatsupp dan kiran kampaninsa, a fili ya ce" ba dole ba ki raina ni, ke da kike zuwa ki kakabe min kurar dakin mata kafin na raya sunna? Ke da kike gannin ke ke bani tsaro?

Yana shiga ya yi kiran su, aka hasko masa kayan da ya yi oder,

Yana kashewa haka kawai ya shiga bin sunnayen wayar yana ware wa.inda zai goge daga wayar

Sunnan Kauriyata ya kurawa ido,
Hotonta ne daga ita sai hulaa a kanta ba ko dan karamin hijab bale baba a saman dp

Da sauri ya shiga cikin sunnan yana kallon yaushe rabonta da hawa ko tsohon whatsup ne bai taba sannin tana da shi ba??

Ga mamakinsa a lokacin ma tana online

Lokaci daya ya ji gabansa ya yanke ya fadi, a hankali ya fara share zufa yana kallon wayar,

Ya rubuta message ya fi a kirga yana gogewa,
Ina bata isa na mata message ba, bata isa ba!


Shi ne abinda ya fada

Mikewa ya yi ya dauki wayar tafi da gidanka ya yi kira fada

Ana dagawa ya yi maganar yana bukatar su hadu da wuri yana son juyawa gida


A wannan ranar sai da ya fasa wayarsa sannan ya daina kokarin yi mata magana ta whatsup din

Mamaki kawai yake, whatup?

A washe gari yana fitowa daga meeting din da suka yi, ya zauna a wata yar cafetaria

Ya fara shan cafe din kennan ya dauki sabuwar wayar da ya saka layinsa kirar samsung ya yi gagawar shiga facebook

Tunani ya fada, sunnayenta sun fi million a duniyar nan, idanfa ta shiga da wani sunna daban?

Wata zuciyar ta ce da shi" kai yanzu gani kake rashin jin maganarta har zai sakata ta shiga Facebook? Ba zata aikata haka ba mana Abdul

Wata kuma ta ce da shi" kai rubuta maman malan!


Ai kuwa har hannunsa rawa yake ya shiga dora maman malan

Maman da suka hayo ba kadan bane, a hankali ya shiga bi yana jin zuciyarsa na dokawa

Sai da idannuwansa sukai masa arba da Hafsat maman malan, ya duba da kyau yar ina ce da komai ya tabatar masa Kauriya ce ya ajiye wayar hannunsa

Bakinsa ya hade waje daya ya cije lebensa, lale kauriya ta gama raina masa wayo a gidan duniya, yanzu shi shi shi? Shi zata wulakanta? Talar kanta take ko me? Ko wani rikeken dan iskan take so ya ankara da tsarin kayatuwar halitarta na fulawer da Allah ya kagota irin Mamuda take so? Ni ko? Ya fada a fili wanda hakan ya saka daidaikun laravawan dake wajen dan kallonsa

Mikewa ya yi ya saka bakin gilashinsa ya fice a wajen

Yana zuwa gida ya dauki passport dinsa dake ajiye gaban sif din dakinsa na baci ya shiga dubawa, yana gamawa ya danna kira dan tambayar shin zai samu jirgi ne????????

A ranar bai samu tafia ba ba jirgi, sai an saka shi a tafiar gaba

Bayan kwana uku ta kama lahadi da safe


Hafsat na zaune da aunty Mariam da ta zo kawo mata sauran turarukanta wace bata so zama ba aman Hafsat fir ta boye waren takalminta sai zaunawa ta yi du a takure tana kallon Hafsat da mamaki gannin ta sha wando da riga abinta tana shagalinta ga tamfatsetsiyar tvn gidan na hasko indiyawa suna rawa

Jus din da ta mayar ruwanta shi ta kawowa aunty ta bata

Aunty na sha ta kaleta , jus din ya hadu kauri kitib da shi haka kuma ua sha kananfari, a ranta ta ayanna wa ya koyawa maman malan wannan hadi? Ta san anfaninsa ne?

Gidan ta bi da kallo, ba dati ko daya gidan tsaf tsaf tsaf da shi, ga kanshin turare dake tashi

Da kyar auntu ta samu ta gudu bayan ta kara yi mata nasiha

Ita dai murmushi kawai take har ta tafi ta barta

Dawowa ta yi ta sake wani wanka ta saka doguwar riga marar nauyi fara kal wace sosai ta hade da jikinta dan rigar bata da wani girma bakinta gwuiwarta ta kwonta saman kafet tana kallon fim har baci ya yi gaba da ita


Da kansa ya tuko kansa har cikin gidan nasa

Daga cikin motar ya gyara zama yana hangen bangarorin biyu
Masu yi kasu aiki na ta shawagi, mata ne mazan kwaya hudu ne wa.inda ke tsaron kofa kawai, aman daidai da masu baiwa fulawowi ruwa mata ne, kowace kuma a ma.aikatarta ya daukota, gidan du yan gayu ne ma.aikatan, girki kansa mata uku ke yi, idan wannan ta yi break fast, wancen ta yi na rana, wancen ta yi na dare , sai dai du yin nan da ake basu taba shiga bangarenta ba, hasalima bakinsu bautar bangaren Na.ima domin ko shara basu taba shiga sukai mata ba, yo mai gidan baya nan bai bada umarnin hakan ba, matarsa kuwa bata saka su ba.


Sai da ya jima sannan ya bude ya fito a motar, daga katon kwadon dake kofar Na.ima ya gane bata nan, a hankali ya shiga takawa yana gannin sai a lokacin suka gane shi ne a motar dan sai zubar da abubuwan aikin suke suna risinawa sunai masa sannu da zuwa

Amsa su kawai yake da hannu har ya fice ciki ya karasa dakinsa

Wanka ya yi na kirki da ruwan dumi, sannan ya canza kaya zuwa kananun kaya

Saukowa ya yi ya nufi bangarenta yana ayana irin abinda zai mata na hukuncin buda Facebood da whatsupp ba da izininsa ba ya tura kofar ya shiga ta coridor din dake sada ka da dakinsa domin kowani dagi da hanyar da zata kai shi dakin matan ba sai ya fito ta fili an ga ya shiga dakin matansa ba


Hafsat dake dukunkune saman cafet tana baci bata san da an buda kofarta ba bale har ta yi wani abu,

A hankali ya ringa takawa ya shiga, kamshin turaran wutar dakin ne ke ratsa kofofin hancinsa

Tsayuwa ya yi ya kama tsatsonsa ya buda baki ya ce" *Kauriya* da karfi karfinsa

Wata irin zabura ta yi daga kwoncen da take ta mike tsaye cirrr tana kallon inda ta ji amon murya gaba dayanta a zabure hakan ya saka hannun rigarta ya fado kasa bayin Allahn da ba.a saka masu bra ba suka dan bayana sosai daga sama sannan gaba daya gashin kanta ribom din ya fadi kasa haka kuma rigarta a sama daga kasan har pant din ya dan leko daga baya domin mikewar dama rigar ba mai tsayi bace ta dage mata sosai sai kawai ta yi sama ta haye mazaunanta masu tudu da su

Galala ya yi da bakin da hancin yana kallonta, ba ko kifyawa bale kawai da kai

Hafsat kuwa da ta tsorata kallonsa kawai itama take gana tunanin shi din ne ko kuwa aljani ne? Kun san abin baci da zabura tsoratar cikin baci

A hankali ya ringa takawa yana nufar inda take tsaye....

Sai da ya karaso dan kusa da ita kadan, kamshin humurarta ya yi masa salama sanyaya mai nutsuwa,

Hannayensa ya miko ya....


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR

42 / 54