Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   17 / 54

48K to 51K   out of 159.5K words

ya dauke kafarsa ya yi kwontan bauna , jira yake sa.a ta kama shi ya damketa

Kara tsoratar da ita ya yi cikin hikima , kafin ta hakura ta fita da shigar abaya kamar yanda Hafsat din ta saka itama suka fita tare suka nufi university wajen daukan karatun yar budurwar .....wannan itace mission din Hafsat ta biyu da ta samu, inda take baiwa budurwa tsaro mai shekaru ashirin da biyu a duniya, wace ke bata wahala sosai don kuwa sam bata bata damar da zata yi aikinta yanda ya kamata, tana nuna halin yarinta da sangarta, tana matukar wahalar da aikin, hakan na konawa Hafsat rai, domin irin tsayayar da yarinyar ke nunawa na tuna mata muguwar rayuwar da ta yi har ta taka san barawo, gashi kuma mahaifinta da mahaifiyarta sun daure mata , basa gannin matsalar dake tare da su,

Bayan sun dawo, dare ya tsala,
Daren alhamis ne, wato wayewar juma.a, daren da yawancin bayi masu nema wajen Allah suke raya shi,
Tun karfe goma mutuniyar tata ta yi baci, hakan ya sakata gyara du abinda zata gyara, ta cire abin kunnen nata ta ajiye shi ta fito cikin shiga ta abaya tare da yane kanta da mayafi baki,

Tafiar kafa ne ta ci ta mamaki, wace ta sha mamakin yanda aka yi ta gane hanyar kanta,

A hankali, ta rabe kofa tana kallon yanda ake dan raragewa, sai muryar malan dake tashi yana ta wa.azi,

Sai da ta jima nan tsaye kafin ta yi wuf ta shiga, ta baya ta yi sando ta shake mutumen dake tsaye nan ya tafi duniyar suma, dama daga shi sai malan, ya fito sake alwallah ta yi wuf da shi,..

A hankali ta shiga masalacin,
Bayansa take hange, ta rakube tana dubansa,
Wasu zafafan hawaye ne suka shiga siraro mata, tana kallonsa ta saka kafarta bayan ta cire takalminta da safarta ta dan fara takawa da niyar karasawa wajensa sai dai ji ta yi an rufe mata idonta da bakinta an dauketa cimak an fita da ita inda take wutsil wutsil da kafafuwanta........

Malan dake zaune tsai ya yi da wa.azin da yake ya dan waiwayo bayansa,
Wani abu ya ji kamar uwata ta ziyarci wajen,
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke, idannuwansa ya lunshe ubda ya shafi gemun fuskarsa,
Hawaye ne ya ji sun cika masa ido, walahi ya san da ta mutu da Allah ya saka masa dangana a kanta, tana raye, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,
Haka kawai sai ya cire wa.azin ya shiga wata irin kira.a ta hanyar daukan suratul Yusufa ya lumshe ido yana yi yana mai tuna irin tarihin yusufa zuciyarsa na kara tsumuwa tana kara kusanta shi da ubangijinsa........


Basu direta ko.ina ba sai cikin bakar motarsu, suka ja da mugun gudu suka nufi anguwar da take aikin,
Nesa da gidan kadan suka yi parking kafin a saketa,

A yanda ta hayayako da sun yi sanya wajen kare kansu tabas da ta jiwa wani,

Ido cikin ido suke kallon juna ita da BS, tsaye su dukansu cikin motar inda ya saka mutun ukun da suka kamota fita aka batsu daga shi sai ita,

Tamkar wasu zakaru irin yanda kowa ke kallon kowa da tarin haushin dan uwansa,

San me kike saka kanki a uku, danme kike son saka mini zuciya cikin tunani da hargitsi? Me yasa ke du motsinki na wanda zaki tarwatsa min tunani ne? Ke dake bakin aiki ashe kina faman tarwatsa komai? Idan har kika je ya ganki a yanzu koda zaki saka masa glue kin isa ki hana shi yada cigiyar nemanki, a tv, a redio? Ku ku goma sha shida na hora, ban taba zuwa gado dan yin baci baki fado mini a idannuna ba! Zan so ki kiyaye dokokin gidan nan ki yi doguwar rayuwar da zan iya rayuwa da ke !

Idannuwanta da ta ruruko dan masifar dake cinta na son ta ga mahaifanta, gata ga mahaifinta ya saka aka kamota ta matso sosai kusa da shi cikin murya kakausa ta ce" mahaifana? A raye? A cikin kasa daya da ni? Zaka hana ni ganin su?

Shima muryar tasa ya kausasa ya ce" du lokacin da kika yi kokarin guduwa harbe ki shi ne abinda aka ce na yi!

To ka harbe ni mana! Ka harbe ni na huta da wannan rayuwar! Ka harbe ni su tabatar da na mutu da rayuwar da suke a matsayin wada na gudu dan gudun auren dole ko me?

Ki fice!
Ya daka mata tsawa yana kara kusancinsa da ita,
Idonsa ya saka cikin nata har jijiyar goshinsa na kara tsayawa dan neman balaki ya ce" ki fice a nan!

Idannuwanta ta lumshe dan kokarin mayar da hawayen dake son kubce mata sannan ta karbi abin kunnenta ta mayar ta juya ta fita a motar ta shiga gidan dake zagaye da masu tsaro ta katanga ba tare da sun san da shigarta ba,

Tana zuwa waje ta samu ta tsaya ta sada kanta kasa,
Wasu irin hawaye masu zafi ne suka shiga bin kumatunta, ta sani ne, in dai wannan maganar ta fita zuwa manyansu to fa za.a iya mayar da ita *KUTKALE*.

Gaba dayansu ya tara su su ukun ya tsare su cikin yannayin da ba zasu taba gigin tunanin da wasa a lamarinsa ba ya ce" koda wasa, na tsinci maganar cewa mun kamo BD 01 ta je gannin mahaifinta sai na bibiyi daga inda maganar ta fito na hana mutun zaman lafia! Da hanuna zan shakewa mutun wuyansa har ya daina numfashi!

Haka ya gama da su ya koma motar ya zauna ya kai hannayensa saman kansa yana shafa kan cike da yannayin rashin karfin jiki,
A cikin zuciyarsa ya ayyana *Sonki nake, kuma ni ne mai rabin samun ki* (ko?)


Bai wani jima sosai ba maganin bacin ya sake shi, nan ya ga an dadaure jikinsa jikin bed din da yake kwonce magani na shiga cikin jikinsa,

A hankali ya ringa gani da kyau har ya sauke idannuwansa kan sojojin kasar saudiya tsaye kusa da prince Muhammad,
Gefe daya kuma kanwar mahaifiyarsa da ta yi saura a family dinsu ce zaune da dogon hijab dinta blue mai ruwan byro, dakin shiru kowane cikinsu na jan carbin dake hannunsa, yannayinsa zai nuna maka halin da zuciyarsa ke ciki,

A hankali ya maida idannuwansa ya lumshe dan basu san da ya farka ba,
Wani zazafan hawaye, mai mugun zafi da radadi a kwarmin ido ne ya samu damar tsinke masa,

Abinda ya hango a lokacin da ya shiga gidan mahaifinyarsa, mamansa ce yashe saman tiles din tsakar gidanta, hasken motar da ya dala ya nuna masa harbin bulet din da aka dana mata a gaban goshinta,
Zai iya tuna cikin al.adarta ne idab ta kore shi, tana biyowa tace da mai gadi idan ya dawo yace da shi ta yi tafia, dan ya dauki maganar da suke da mahinmanci,
A dalilina, aka kashe uwata? Ni na kashe ki Ummih.....

Bugun zuciyarsa ne ya tsananta hakan ya sa injin dake jikinsa mai shaida yannayin hawan jinninsa ko saukarsa ya shiga shaida jinninsa ya fara hawa,

Da sauri Muhammad ya nufo wajen gadon yana kiran sunnansa a hankali,
Kanwar mahaifiyarsa kuwa ta fita da gudu dan kiran docters,

A hankali ya buda idanjuwansa da sukai masa nauyi ya kai dubansa kan Prince Muhammad,
A hankali ya buda bakinsa da muryarsa da ta canza amo ya ce" Muhammad, ya haka aka kule ni tamkar mahaukaci?

Muhammada na son fada masa dalilin daure shin da aka yi ya ji ya daga murya da karfin amo ya ce".......



Alhamdulilah, an gama freee
Du mai son ci gaban labarin naira dari biyu ne ga yan Nigeria,
Yan niger kuwa dala dari ne sahelcom ta numberna kamar haka 91466605
*Taku ce, yar mutan niger*


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 6??

*wannan nvl na kudi ne, idan kin biya kin shiga na roki alfarmar dan girman Allah ba dan ni ba kar ki fitar min da shi ki yi hakurin har na gama shi sai ki fitar da abinki ki yi yanda kike so da shi bani da matsala da hakan, dan Allah idan kin san dan fitina, ko dan ki wulakanta min kika shigo ki min magana pc daga ni sai ke na biya ki kudinki wato naira 200 ta hanyar accnt din ki ko kati, dan alfarmar soyayarku da annabi muhammad kar ku fitar min da novel, ku bari na gama shi, in sha Allah ba mai tsayin da zai saka ku gajiya da jira bane=?O?



Likita ne ke ta kokarin danna kirjinsa,
Kin dawowar da ya yi ne ya saka fa sauri aka kawo abin dannar kirji

Aka mikawa likita aka matso likid din nan aka goga a sama sannan aka shiga kokarin kara tayar da shi ta hanyar murza abubuwan nan biyu aka dora saman kirjinsa,

Sai da ya dago baki dayansa sannan ya koma yarab tamkar matace

Wani ihu BS ya saka a fili ya furta" shikenan, ya mutu, mun karasa masu aikin su, mun kashe shi!

Kallon da docter ya yi masa ne ya saka daya daga cikin nurse kokarin fitar da shi yanzu kam, sai dai tirjewar da ya yi ya sakata sakinsa ya kara dawowa yana kallo za.a dora masa a karo na biyu

Sai da aka kara jonawa aka dora masa,

Wannan karron kam alhamdulilah, yana yin saman da kirjinsa sai ko injin ya shiga bada wani kukan dake nuni da ya dawo duniyar masu rai,
Da sauri Doctern ya shiga gyagyara du abinda zai gyara nurse na daimaka masa tana bashi du abinda ya ambaci sunnansa,

A haka suka gama komai sannan du suka tsaya sunna kallonsa,

Nurse di Docter ya umarta da su je, bayan ya cire safar hannun ya rage daga doctet sai BS tsaye kuri sunna duban Abdull

Ya jima, ya jima sosai, domin a kadan ya dauki minti talatin a wannan yannayin ,
Sai can ya shiga kokarin bude idsanuwansa, sannan bakinsa ya shiga motsawa yana mai adu.ar tashi a barci

Kamar kuma wani hadin baki sai wani bakin jinni bulbul ya bulbulo daga hancin wanda ya sanya Docter zabura ya nufe shi ya saka abu yana dauke jinnin, inda Abdul ya ringa jin wani sanyi sanyi wani sakayau, a hankali abinda ya rike gansa da wani irin nauyi da duhu ya ringa barinsa har ya sake shi baki daya,
A hankali ya bude idannuwansa da suka kara girma sukai jajajir ya sauke a kan BS da docter, sai da ya gama yi masu kallo, sannan ya juya ya shiga bin dakin da yake kwonce da kallo

Shi dai bai ce komai ba, har aka jima sosai domin Docter ya fice da jinnin dan aunawa gannin abinda ya hadasa masa haka, ya rage daga shi sai BS sun yi shiru su duka ba wanda ya ce wani abu, ba wai dan muryar Abdul bata dawo ba, aa kawai bin BS da kallo yake yana tunna wasu abubuwan da ya gani da wanda yake tine, saima suturar dake jikinsa wato daga shi sai gajeran wando

Docter ya jima da fita kafin ya dawo, sai da ya dawo yake tambayar ya shi ko sha wani abu?

BS ya ce" ai bai fara magana ba har yanzu bare na ji abinda yake son ci

Docter ya juya wajen Abdul dake dubansu ya ce " to ka kwatanta masa mana, idan baya magana na san abin wahalar da ya sha ne kafin muryarsa ta saki,

Matsowa suka yi su duka biyun sunna duban Abdul, nan fa suka shiga kokarin yi masa yaren kurumci sunna kwatanta masa abin ci ko na sha wane yake so, kuma wani kalla?

Sai da ya kare kalle su baki dayansu sannan ya yi murmushi yana kokarin mikewa zaune

Kama shi suka yi suka zaunar da shi, nan ya dube su kuma, sannan ya ce" bana jin yinwa

A tare suka dubi junnansu, kai dama yana magana ka ce bai fara magana ba? Docter ya tambayi BS

B???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?S kam mamaki ya hana shi magana bale ya baiwa docter amsa, sai kawai ya shiga murmushin shima yana duban Abdul na kokarin cire allurar dake bashi karin ruwa da kansa,

Docter ne ya ce " aa kar ka cire, wannan na karin ruwaa ne ko zaka ji dadin jikinka

Abdul ya dubi docter da kyau ya ce " likita, ina jin jikina da wani irin karfi walahi, ban jigata ba, hancina ne ya dan zubar da jinni, ba.a dake ni ba,

Docter kam zuwa wannan lokacin baima san abinda zai cewa bayin Allahn biyu ba,

Abdul ne ya dago yana kallon yanda Docter ke kwonce masa yan abubuwan allurar da ya saka ya sasaka masa a jiki ya yi kamar ya daure shi ya ce" likita, bana son ana daure ni, du sai na ji na rikice , in dai ba mutuwa na yi ba, kar a daure ni

Docter kansa kawai ya gyada ya karasa kunce Abdul yana son fada masa sai gobe za.a salame su, domin yama ta yi an fara kiraye kirayen la.asar sai gannin Abdul ya mike ya yi yana kallon dakin bai ga ko irin rigar mararsa lafia ba bale ya dauka ya saia

Dubansa ya kai kan BS dake tsaye ya ce" ina rigar asibiti ne??

Docter ya dube shi da kyau kafin ya yi murmushi ya ce" ai oga bamu da shi a nan mu, wannan dakinma mun tanadeshi dan irinku, ba kowa ake sakawa a ciki ba,

Da mamaki ya dube shi, ya ce" ku su wa? Wace asibiti ce?

BS ya dan zaro ido , kafin ya tari numfashin Doctern ya ce" am, am sire mu je kawai, ga rigata da wandona bara na je cire sai na je na tsayar da taxi,

Abdul kara zaro ido ya yi, taxi? Taxi fa yace? Me ya hada shi da taxi? Shi ko a saudiya bai shiga taxi ba, yana kallo BS ke kokarin cire kayansa, bai hana shi ba, dan walahi ba zai yarda ya ratsa gari ba kaya ba, idan fa ya hadu da wanda ya sani? (Abdul, a taxin? A dazu da ka ratso ko dan kana duniyar summa ne?

Bawan Allah BS haka ya cire kayansa, Allah ya taimake shi, shi wandon na ciki ya kai har gwuwarsa sannan sakake ne, dan haka da mamaki ya bi Abdul da kallo har ya saka kayansa inda sukai masa wani kabe kabe rigar ta wani irin tamke shi dan sun masa kadan, wandon kansa ya tsalake masa sosai tamkar dan izala aman kuma da damamiyar riga,

Ido ido sukai da doctern sannan ya fice ya nemi taxi ya tsayar

Nan fa Abdul ya shiga taxin gidan baya ya hakimce inda BS ya shiga gaba ya fadawa mai taxi cewar sun yi shata har inda za.a kai su

Shi dai Abdul yana kallon gari, da irin yanda motar ke sama da kasa da shi, da irin yanda suke kutsawa sunna wani rin gudu, a haka suka zo suka wuce danjar da ta bayar da jar wuta a guje inda Abdul sai da ya dora hannunsa samman kansa ya leka da kyau ya dubi mai taxi din ya ga ba yaro bane datijo ne sosai aman yake wannan tukin
Sai,da suka zo danja wace polisai ke tsaye ya ja ya tsaya kafin ya lailayo wata ashar ya dura ya ce" mutanen banza ido yay masu kuri, ka fice ka janyowa kanka balaki, to ba dai aljihuna ba!

Abdul kam komawa ya yi ya zauna yana mamakin ashe bai ga komai ba? Shi bai taba shiga taxi ba, yana hawan tsofafin mashin ya shiga wurare masu hatsarin gaske, aman yau gashi a taxi zata kashe shi!

Tafiar da idan a motocinsa nene bai fi su yi minti ashirin ba, sai gasu a minti kusan arba.in

Ko tsayuwar da direban motar zai yi sai da ya wani irin ja ya yi wani kuuuu motar ta fitar fa hayaki sannan ya tsaya ya fitar da kansa ya ce" ikon Allah, jama.a ku ga ginnin gida tamkar ba za.a mutu ba? Yanzu mai gidan nan haka zai mutu yana ji yana ganni a nutsa shi a kabari? Han gaskiyar mabaraci da yace a baku a nan mu a can mu samu

BS tamkar ya mangare mutumen haka yake ji, gashi tsaf sai da Abdul ya gama sauraronsa ya bude ya fita daga motar yana duban yanda BS ke hararn mutumen, aman cikin ikon Allah sai mutumen ya ce" kai yanzu bawan Allah shaye shaye ka yi ka tunkaro gidan nan mai zagaye da arnawan sojoji ko rigar kirki baka da ita , ka dauko wannan shi kuwa da wata riga a dame a jiki tamkar bazawarin kwarto da wani wando ko sauka kasa bai yi ba yana lumshe ido uwa ya hadiyi jinjirar tinkiya?

Tsayuwa ya yi ya dafe tsatsonsa sai da mutumen ya gama ya shiga kokarin tayar da mota yana mika hannu BS ya bashi kudinsa motar sai tayar da hayaki take abinta Abdul ya dubi BS da du ya daburce ya kankance ido ya ce" ni, ni

17 / 54