Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   53 / 54

156K to 159K   out of 159.5K words

lako lako ba

A lokacin Hafsat na tsaye gaban gadonta zintir haihuwar mamanta tana shafe jikinta da man zafi ko zata ji damar ciwon da yake mata domin ita cikinta bai zo mata da wani ciwace ciwace ba sai dai taunar jiki da abubuwan da ba za.a rasa ba

Turus ya yi yana kallon bayanta da ta baiwa kofa,
Dukawar da ta yi dan lakato Victago din ta kuma bin jikinta da shi ne ya kusan dauke numfashinsa
Da sauri ya rintse idannuwansa sai dai yana rintsewar ya ji idannuwan sun kuma budewa suna kara waruwa kan abincin su

Shi da ya shigo da niyar yi mata wankin banban bargo sai kawai ya ji ta shiga bulale shi da taimingiyar dukan rakumi!

A hankali ya taka ya karasa bayanta
Rungumeta ya yi a jikinsa tare da lumshe idannuwansa
Ta so tsorata dan bata ji shigowarsa ba ta raja.a a abinda ke gabanta sai dai jin kamshin jikinsa ya sakata sauke ajiyar zuciya ta lumshe nata idannuwan itama tana jin yanda yake bin jikinta da shafa cikin nutsuwa yana jan numfashi

A hankali ya dora hannunsa a kugunta pamkameme da shi kafin ya shafa kasan mararta
Murya can kasa tamkar ba muryar da ya gama kirta fada da ita ba ya ce" cikin ki a shafe yake sosai, a haka akoy ajiyata na wata hudu? Ki ringa cin abinci Kauriyata kar ki haifa min yaro da tamowa

Hafsat ta saki murmushi tana jin wai yaro da tamowa, ita kanta mamakin cikinta take a haka wai da mutun a ciki?

A hankali ya kuma shafota ya ce" na kai ki bangaren Na.ima a farko.ne dan tana matata ta farko kafin ke, ita ce uwar gidana ke kuwa amaryata, ina so ki girmamata itama ta girmama ki, ban fi son wata fiye da wata a cikin ku ba, dukanku zabina ne Hafsat ba na kowa ba, dan Allah, ku taimake ni ku hada kanku ku yi zumunci tsakaninku hakan zai haifar min da kwonciyar hankali harma na samu karfin gwuiwar fita nema cikin nutsuwa

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juyo jikinta na dan rawa rawa ta kama lebensa na kasa ta shiga tsotsa idannuwanta a lumshe

Ya fita haukacewa , jin zai zarme ya sakata dakatar da shi a hankali ta rada masa a kunnensa cewa yau ranar auntyna ne,

Sakinta ya yi shima yana janyo numfashinsa ya sauke mata manyan idannuwansa da suka canza kalla yana kallonta

Murmushi ta yi ta mana masa kiss a kuncinsa a hankali ta furta" i love u

Hannunsa ya kara mikowa dan ya damkota ta saki karamar dariya ta zile da sauri sauri gudu gudu da gaya ta afka bayin dakinta tana juya jikinta wanda hakan ya saka shi yin sakalau da baki ya bita fa kallo

Sai da ta bacewa ganninsa sannan ya saki murmushi ya ce" Yar malan, bakya jin magana walahi.

Juyawa ya yi ya fice a dakin tun kafin ta karasa shi dan ya lura hanyarta ta hukunta shi kennan

Sai da ya fita ya tsaya ya dafe bishiyar wajen cike da mamakin abinda ya faru, aa, ya zo ne da niyar itama ya sauke mata abinda ya saukewa yar uwarta, aman yaya aka yi ya bige da yar murya? Yaya aka yi bai balbaleta da balaki ba?
Wato da ake cewa akoy matan da suke da kwarjini shi ne wannan? Matar Abdallah maman malan ta fi karfin ya kirta mara rashin mutunci?

Murmushi ya yi ya girgiza kansa ya daga kafarsa ya nufi bangarensa yana ayanna bara ya koma itama ya rarasheta ko dan kwatanta adalci a tsakaninsu, bale a yau yana bukatar taimakonta ko dan kunosa da maman malan da ta yi



>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




7?? 1??

Nd
Nd
Nd
Nd
Nd
Nd
Nd
*Alhamdilah*


Ba karamar jajircewa Abdul ya yi dan gannin iyalansa sun hada kansu, yakan hada su ya sake a cikinsu ya yi ta jan su da hira da wasa da dariya
Idan sun kadaice daga su sai shi yakan yi nasiha da nuna irin yanda yake son su hade kan nan nasu

Sam baya nuna wata ta fi wata tsakanin su,
Yana bakin kokarinsa dan kamanta adalci tsakanin su, baya baiwa wata fuskar kawo maganar wata idan ba alkhairi zata fada ba, shi baya daukan sirrin wata ya fadawa wata, baya yaba wata gaban yar uwarta dan ya bata mata rai

Ba laifi ya samu abinda yake so , domin a cikin watani hudu da suka karu ya yi tafia sau uku kan harkar shagunan da zai bude a maradi, kowace tafia yakan saka ido sosai dan gannin shin daya zata nemi daya? Abin farin ciki shine ba.a wuni dare ya yi daya bata leka yar uwarta sun gaisa ba, duda ba wani hira can can ba ko wani sakin jiki irin wannan , aman haduwa a yi zumunci suna yi, idan kuma daya ba lafia dayar na tsayawa kamar yana nan ba wani abinda zai ragu
Sukan dan zagaya a tsakar gidan tun da docter ya bada umarnin zagayawar

Sosai Hafsar ke samun kulawa bangaren mijinta, iyayenta, mahaifin mijinta da abokiyar zamanta

A haka har watan haihuwarta ya tsaya inda Abdul ya murje ido kan ba inda zai motsa, sam ba zai je ko.ina ba yana tare da ita , harma ya baiwa saudiya amsar zai je bincike aman da sharadin idan matarsa ta haihu zasu je tare

Wani yamacin juma.a, Hafsat na gidan malan ta je gaishe su du kuwa da irin nauyin da ta yi, Abdul ne ya kaita da kansa ya ce bayan salar magariba zai zo ya dauketa dan ta shiga yan uwanta ko zata warware dan kuwa kwanakin nan haka kurum ta cika fushi, abin fushi da ba na fushin ba tanzu zata fashe da kuka ta samu da kyar ta mike ta barawa mutun waje, an ce da shi idan cikin mace ya tsufa takan fitar da sirfa kala kala

Zaune take zugum tun da ya ajiyeta wajen karfe goma na safe
Ciwo take ji na fitar hankali bayanta cinyoyinta kai harta da idannuwanta bata so ta daga su da karfi dan ji take har su ciwon suke

Mahaifiyarta na lure da rashin walwalarta, sai ta ringa kokarin gannin ta sakata walwalar domin cen dama maman Hafsat ba mai basu damar yawon kawo korafin gidansu bane????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
bale har ta saurare su ta basu kofar shirme

Ita dai Hafsat daga zaune ta kasa yiwa abin dariyar mamanta dariya, a haka har aka kawo abincin rana

A lokacin da ta muzguta dan wanke hannunta ne ta ji wani irin bulbul ruwa mai yawan gaske ya zubo daga pant dinta daga zaunen da take
Di kira ta yi ta sanar da ubangiji kafin ta kai dubanta wajen kafafuwanta inda ruwan gayannan har ya fara gudu

Gabanta ne ya fadi, irin gargadin mamansu na tsafta ne ya fado mata inda take fadin ba ruwanta da iskancin matan zamani wai dan kina da ciki shikennan ke an tara kazamta a tare da ke, ki zubar da wannan ki ci ki bari ba ruwanki da wanki wanka ko wanke waje, ke ga mai ciki kina wari kina karni fuska ba kwali a yi magana a ce ciki to ba a kanki aka fara ba bare a gama a kanki, yau ta shiga uku fitsari ne ta yi zaune a dakin mama? Mama da tsantseni ba mai hanata cewa a gidanta ma haka take,gashi duka duka yanzu karfe uku ta yi bale ta sa ran Bawan Allah zai zo ya dauketa su yi tafiarsu, yau ta san mai rabata da mama sai Allah dan haka a hankali ta dago suka hada ido da mama da ta yi sokoko tana kallonta da yannayin mamaki da tsoro a fuskarta

Da Sauri Hafsat ta daga dan yatsarta manuniya sama ta ce" mama, na rantse da girman Allah ban taba yin fitsari a jikina ba , komin dare sai na sauka na saka takalmina zan je bayi na yi na dawo, kuma ki tambaye shi, itama auntyn ki tambayeta, sannan shi wannan fitsarin ban ji ina jinsa ba ban san zai fito ba sai fitowarsa da na gani mama, wly shi kadai ke zuba

Da sauri mama ta koma ta rufe dakinta ta karasa kusan Hafsat ta duka ta ce" maman malan kina jin ciwo wani waje ne? Tun yaushe kika fara jin ciwon? A asibiti sati nawa suka baki?

Hafsat na kallonta ta ce" mama tun da watan nan ya kama nake fama da ciwon baya da cinyoyi sai na ji marata ta kara nauyi sannan ta sauki dumi, ban fadi ba dan kin hana ni yawan korafi

Mama ta gyada kanta kafin ta kamata ta ce" mu je saman bed, cire zanin nan ya jike

Hafsat ta cire tana mamakin mama batai mata fada ba, sai dai tana kokarin mikewa gaba dayanta ta ji wani irin ras ras ras wanda bashi da misali

Da sauri ta so durkushewa mama ta riketa gam ta taimaka mata ta dorata saman bed dinta

Nan da nan mama ta saka safar likitoci ta hannu ta gyara Hafsat da kamar jira ake ta motsa a gagabo mata ciwo ta dubata

Tabas Hafsat nakuda take har nakudar ta kankama domin a 3 take hakan ya saka mama saurin kallon agogo ta dauki wayarta ta shiga neman layin Malan

Malan dake tare da jama.a yau juma.a sam bai ji wayarsa na kuwa ba, a wajen kuwa Harda Abdul suna ta hira da jama.a wanda shi kuwa ya baro tashi wayar a cikin mota

Gannin ta yi ta doka wayoyinsu ba.a dagawa sai ta nemi ta babar yarta wato Aunty ta doka kira

Aunty dake kicin tana gyara abincin mijinta da bakinsa sam bata ji kira ba hakan ya saka natama har ya yi ya tsinke shiru a lokacin kuma har karfe gudu ta zarce sosai

Da sauri mama ta ahiga safa da marwa tana kallon Hafsat wace idan ciwon ya lafa sai ta dafe goshinta saman hannunta tana sauke ajiyar zuciya

Bata taba fita ba da izinin mijinta ba koda halin rashin lafia ne, bata san yaya zata yi ita dai likitar mata ce mai karbar haihiwa aman ba zata so Hafsat ta haihu a gida ba hakan ya sa ta dauki hijab dinta ta fita tsakar gidan tana bin dakunan samarin gidan ko zata samu wanda zai taimaka ya kira mata malan

Da kyar ta samu ta aiki salihu bayan ta fada masa a gagauce ne

Tsaye ta tana yarde zufa, ta kasa komawa dan tsoro, haka kuma ta kasa fita ta tarbo malan din da kanta

Ya kai minti arba.in tana safa da marwa sai ga malan da Abdul sun shigo a tare domin gannin irin misscal din da mama ta yi sai hankalinsu ya tashi

Da sauri ta tarbe shi, bayan ta yi masa sannu a gagauce ta ce" UMMA ce ke kan gwuiwa

Da sauri malan ya ce" Me? Kuma kuke gida baku je asibiti ba ?

Abdallah da ya kwararo ido ai bai san lokacin da ya shige kai tsaye ya nufi dakin mama ba

Yana zuwa ya tura kansa ya shiga
Muryarta ya jiyo a hankali tana fadin" ALLAHUMA LA SAHLA, ILAMA JA.ALTAHU SAHLA, WA ANTA TAJ.ANUL HAZNA IZA SHI.ITA SAHLA

Da sauri ya karasa ya tsuguna inda take kwonce kanta na kallon sama
Hannayenta ya kama cikin nasa hakan ya sakata rintse ido ta damki hannun nasa da wani irin karfi kafin ta saki wani mugun nishin da ya saka mama afkowa da gudun tsiya ta karasa shiga cikin dakin

Gaba daya jikinsa da nata rawa suke, wani irin hawaye ke taruwa a idannuwansa yana gogewa yana kallon yanda take jijiga sannan adu.a a bakinta ta kasa dainawa

A haka maman malan ta haifo danta, dan jaririnta wanda yana saukowa a hannun kakarsa ya calara kukan da ya saka malan kaiwa kasa a nan kofar dakin yana tazbihi ga ubangiji

Abdallah kuwa muryarsa sama sama yake fadin" Alhamdulilah

Mama na gyara yaron ta dora mata shi kan cikinta bayan ta janye farar rigar dake jikinta mai girman gaske sannan ta zagine ta cire kunya ta shiga kiciniyar gyarata haihuwa mai gayar dati gashi yau an mata ita a kan gadonta>?#?

Gannin ya ki fita ya saka mama ce masa" yawa ka je daga waje na kimtsata

Kallon mama ya yi, kai da ba dan ita bace gaskiya da ba inda zashi, haka ya dauki yaron yana ta kallo ya nade a zannin mama mai kyau sabo fill abinsa ya fice waje

Yana fitowa malan ya mike a zabure yana kallon yaron, sai kawai ya ji hawaye ya zubo masa, a fili ya ce" ya Allah, ka baiwa mamana ladan nakuda da haihuwa, ya Allah ka baiwa mamana lafiar shayarwa da ladan shayarwa, Allah kar ba baiwa wannan yaro damar saka mamana hawaye, ka shiryar mata zuriyarta , ya Allah kar ka jarabi mamana da yaya masu rashin ji, domin ni na yafe mata duniya da kiyama hakama mamanta, Allah ka ja da kwanakin mamana su zauna lafia da mijinta da kuma abokiyar zamanta ka basu zuri.a dayiba

Abdul amsawa yake, dan ya tabata wannan adu.ar malan ce ta zuci ya kasa rikewa, kai yana jinjina soyayar da da uba ba kamar ta malan da mamansa

Alhamdulilah maman malan ta sauka lafia a gidansu, Na.ima sai dai gannin mutane ta yi sun dawo mata da yaro da kuma mai taya wankan jego, hakan ya sakata wata irin murna da nan nan da yaron, ta rike shi a hannunta sai kallo take, jinsa take har cikin ranta, sonsa take tamkar ita ta haife shi
Sanadiyar haihuwar yaron nan ta kara kusanci tsakaninsu domin idan ta fito tun safe sai kwonciya ke mayar da ita bangaren oga, wanda take mugun jin ya matsa mata da cinada dan kuwa da Hafsat da sauki sauki sai a kwana biyu bai hau ba yanzu kuwa ita daya ce keken tuki kawai yake!
An yi sunna mai sunna sunna, yaro ya ci sunnan *FAHAD* , an sha shagalin sunna kamar ba gobe, an dagargaje an more an yi gatsa

Maman yaro wato Na.ima ta yi kaya akwati uku manya shake da kayan jariri ba abinda ta manta
Mahaifinsa ya yi masa kaya shi da mamansa daki guda
Kakaninsa sun yi masa kaya wanda Hafsat ta gyada kai a fili ta ce" Fahad haihuwarka na karyar kafar baya=? ?

Jinni bai wani dauki lokaci ba ya dauke mata, nan fa suka shiga wasan buya da mai gidan dan kar ya gane ta samu kanta, domin a hakanma da yaya ta kare kulun yana nanuke da ita ya tsotsewa Fahad milk dinsa ya barshi da darwAyar kwano ina da ya ji lamari ya koma yanda yake

Mama kuwa daga bangarenta ta zage tana ta aiko mata da kayan gyara masu inganci, ita ce kaza mai nonon rakumi, an mayar da icen gongoli ruwanta, du abinda zai karkaro mata mutunci ta yi tsaye jina tana gyara maman malan inda aljihun malan ya yi kuka domin da ta fada masa abinda za.a yi sai kawai ya cire zif sin jaka ya bar mata a bude take diba tana taka rawa da liki

Harda hadin shananak, da sa buzu ihu akai mata ta shanye kora guda hakan ya saka ita kanta sai ta ji tamkar tana fitsari tsabar yoyo

A haka har ta yi arba.in da kwana biyar cif, kafin ta shirya dan kanta ta kai Fahad wajen mamansa da nononta a fida uku aka saka a firij da pampos dinsa da komai ta yi masu salama ta kada abinda ba wani shaku ko dar dan ta yarda da soyayar Na.ima dama halayenta domin sai da ta karanceta ta gane ita mutun ce marar munafurci mai fitar da abinda ke ranta komai dacinsa idan tana sonka zara fada maka ne idan kuwa bata sonka ko waye kai zata fada maka dan haka itama ta lamunce mata suke zaune lafia

A hankali ta karasa bangarensa, tana zuwa ta tarar da shi zaune gaban laptop yana dane dane,
Abayar jikinta ta cire ta yar daga inda take kafin ta karasa ta haye bed hakan ya saka shi amsa wannan gayata....a wannan dare ba.a ji motsinsu ba har wajen karfe taran dare, inda suka raya daren suna ibada, lada lodi lodi wanda Abdul ya kasa gane yaya aka yi ya ji wajen tsammmmmmm, matarsa duniyarsa


FAHAD na da shekara daya da wata biyu maganar tafiarsu ta tashi gadan gadan wanda akai masu alkawarin albashi mai mugun tsoka

Sun shirya a matsayin almajirai masu neman wankau zasu je gidan

53 / 54